Gargadi ga Kyautata Zamantakewa: Fadakarwa Daga Alkalamin Isan Kware Dan Shehu

    Citation: Usman, B.B. & Sani, A-U. (2019). Gargaɗi ga Kyautata Zamantakewa: Faɗakarwa Daga Alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu. In East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, Volume-2, Issue-10, Pp 621 - 632. ISSN 2617-443X (Print) | ISSN 2617-7250 (Online). Available at: https://www.easpublisher.com/get-articles/950.

    Abstract

    The paper is an analysis of a poem titled “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” (The Rights of a Believer Upon a Believer and the Upbringing of Children) written by Isan Kware Ɗan Shehu. Attempt was made to bring out the major and minor themes of the poem as they relate to the social life of the Hausas. The various stylistic devices that he used in the poem were identified to be symbolism, metaphors and alliteration among others. Ɗangambo’s 2007 model of analyzing poetry was used. It was found that, he used a simple language and showed expertise in his choice of words to pinpoint socio-religious issues directed at the Hausafolk. The paper finally suggested that experts need to analyze more of such works as an effort of inculcating good moral values to the general society.
    Keywords: Rights; Social Interaction; Child Orientation; Isan Kware


    Gargaɗi ga Kyautata Zamantakewa: Faɗakarwa Daga Alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu


    Dr. Bello Bala Usman1 and Abu-Ubaida Sani2
    1. Department of Nigerial Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
    2. Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria

    Tsakure
    Wannan takarda nazari ce na “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware Ɗan Shehu. A cikin takardar, an yi ƙoƙarin fito da babban jigon waƙar da kuma ƙananan jigogi tare da warware su domin gane haƙiƙanin saƙon da waƙar ke ƙoƙarin isarwa. Bayan nan an yi ƙoƙarin fito da ire-iren salailan da mawaƙin ya yi amfani da su a matsayin dabarar isar da saƙo. Sun haɗa da salon alamci da siffantawa da sauransu. An ɗora wannan nazari ne a kan hanyar nazarin waƙa na zamani wanda ya ke ƙarƙashin mazhabar Ɗangambo, (2007: 10). Daga ƙarshe kuwa an kawo sakamakon nazarin haɗe da shawarwari. Takardar ta fahimci cewa, sha’irin ya yi amfani da harshe mai sauƙi da kuma zaɓaɓɓun kalmomi domin isar da saƙonninsa. An ba da shawarar cewa, manazarta su ƙara ƙaimi wurin nazartar ire-iren waɗannan waƙoƙi domin fito da saƙonninsu fili, tare kuma da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin karantar da waƙoƙin a makaranti, wanda hakan na iya tasiri matuƙa a ɓangaren gyaran tarbiyya.
    Muhimman Kalmomi: Alhaki; Zamantakewa; Tarbiyyar Yara; Isan Kware

    Taƙaitattun Kalmomi
    WAMBMTY: Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara
    Bt.:                  Baiti
    Ɗg:                  Ɗango
    Ƙ:                    Ƙarni


    1.1 Gabatarwa
    Wannan aiki ya shafi nazarin waƙa ne. Waƙar kuwa rubutacciya ce wadda ta kasance cikin jerin waƙoƙin ƙarni na goma sha tara. Masana da dama sun bayyana ma’anar waƙa a rubuce-rubucen da suka gudanar a matakan ilimi daban-daban.[1] Daga cikinsu akwai Ɗangambo, (2007: 5) da Sarɓi, (2007: 1) da Yahya, (2016: 26) da sauransu. Rubutacciyar waƙa dai tsararren zance ne da ke tattare da hikima da fasaha da zalaƙa wanda ake rubutawa cikin salo da zubi da tsari na musamman. Wannan ya ƙunshi abubuwan da suka haɗa da jeranta tunani da amfani da amsa-amo da kari da salailai daban-daban.
    Waƙa aba ce mai matuƙar amfani a tarihin ɗan’adam musamman saboda tasirinta ga zukata da kuma saurin isar da saƙo. Tarihi ba zai taɓa mantawa da rawar da rubutattun waƙoƙi suka taka ba a ƙarni na goma sha tara (Ƙ19) musamman lokacin jahadi ƙarƙashin jagorancin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Hassan, (2019: 1) ya bayyana cewa, masana da dama sun tabbatar da ingancin waƙa wajen isar da saƙo. Waɗannan masana sun haɗa da: Abdulƙadir, (1974: 7) da Abdulƙadir, (1979: 10) da Dumfawa, (1990: 26) da Omar, 2013: ix) da Yahya, (2016: 2) da Idris, (2016: 1) da Bunza, (2016: 29).
    An raba wannan takarda zuwa manyan rukunoni guda biyar (5). Na farko shi ne gabatarwa inda aka yi tsokaci kan mawaƙin (Isan Kware) da kuma waƙar da ake magana a kanta “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara.” Ɓangare na biyu kuwa ya mayar da hankali ne kan jigo, inda aka kawo babba da ƙananan jigogi sannan aka warware su. A rukuni na uku kuwa, an yi duba ne zuwa ga zubi da tsarin waƙar. Ɓangare na huɗu ya mayar da hankali ne kan salo, inda aka fito da misalan salailan da waƙar ta ƙunsa. Ɓangaren aikin na ƙarshe (5) yana ɗauke da sakamakon nazari da sharhin da kuma kammalawa.

    1.2 Manufar Nazari
    Manufar wannan takarda shi ne nazarta da kuma yin sharhi kan “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware. Takardar za ta mayar da hankali kan:
    i.                    Nazartar babba da ƙananan jigogin waƙar domin fito da manufar marubucin fili.
    ii.                  Nazartar ire-iren salailai da mawaƙin ya yi amfani da su domin isar da saƙonsa.
    iii.                Nazartar irin harshen da mawaƙin ya yi amfani da shi na dangane da zaɓen kalmomi da tasirin al’ada ko addini cikin zaren tunaninsa.

    1.2 Isan Kware
    Ali (Mrs), (2019) ta yi ƙoƙarin kawo Tarihin Malam Isan Kware (Autan Shehu) cikin jaridar Leradership. An haife shi a garin Gwandu a shekara ta 1816. Sunan mahafiyarsa Mariya. Ya kasance ɗan Auta a wurin mahaifinsa wato Shehu Usmanu Danfodiyo. Nana Asma’u ‘Yar Shehu ita ce ta rene shi, sannan a wurinta ne ya hardace Alƙur’ani tun yana ɗan shekara goma a duniya. Daga nan ne kuma ya ci gaba da karance-karancen littattafai da waƙoƙi.
    Dangane da zuwansa Kware kuwa, ya je ne lokacin da yayansa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya naɗa shi Sarkin Yamma. Wannan ya faru bayan da an ƙwace garin daga hannun Abdussalami a shekarar 1836. Ya gudanar da mulki har na kimanin shekaru talatin da biyar (35). Duk da cewa akwai ruwayoyi mabambanta game da haƙiƙanin lokacin da ya rasu, Wazirin Sakkwato Alhaji Junaidu ya yi hasashen Malam Isa ya rasu ne a wajajen shekara ta 1872. Waƙoƙin da Isan Kware ya rubuta kafin rasuwarsa sun haɗa da:
    a.       Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara
    b.      Waƙar Tuna Mutuwa
    c.       Waƙar Halin Duniya

    1.3 Game da “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara”
    Wanda ya rubuta wannan waƙa shi ne Isan Kware (Autan Shehu) duk da bai rubuta sunansa cikin waƙar ba.[2]  Waƙar ‘yar tagwai ce, sannan tana da adadin baitoci 54. Ya rubuta wannan waƙa a shekarar hijira ta 1288 wadda ta yi daidai da shekarar 1858 a shekarar Girigori. Ya bayyana hakan a baiti na 52 cikin waƙar inda yake cewa:
    52.  Ramzi na hijira tai Fiyayye kun jiya,
    SHURAFA’UHU haƙƙan ina bege nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 52)

    Ga yadda lissafin ya kasance:
    SH – 1,000
    R – 200
    F – 80
    H – 8
    1,000 + 200 + 80 + 8 = 1288

    2.1 Jigo
    Sarɓi, (2007: 70) ya ba da ma’anar jigo da cewa: “Jigo a fagen adabi na nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa, jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke son sadarwa ga jama’a.” Babban jigon “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware shi ne gargaɗi da faɗakarwaAkwai ƙananan jigogi da dama waɗanda suka taru suka ba da wannan babban jigo. Dukkannin ƙananan jigogin na da nasaba da wannan babban jigo. Sun haɗa da:
    i.                    Haƙƙoƙin mumini bisa mumini
    ii.                  Haƙƙoƙin iyaye kan ‘ya’yansu
    iii.                Haƙƙoƙin ‘ya’ya kan iyayensu
    iv.                Haƙƙoƙin mata kan mazajensu
    v.                  Haƙƙoƙin bawa bisa ubangidansa

    2.2 Jigo a Taƙaice
    Sha’irin ya yi amfani da salo mai armashi wurin jeranta saƙonnin da ke ƙunshe cikin waƙar ba tare da an samu kwan-gaba-gwan-baya ba. Ya rattabo su cikin waƙar bi-da-bi kamar haka:
    a.       Baituka na 1 da 2 sun kasance mabuɗi ga waƙar.
    b.      Daga baiti na 3 zuwa baiti na 9 an bayyana haƙƙoƙin mumini bisa mumini da suka fito cikin hadisan Manzon Allah (SAW).
    c.       Daga baiti na 10 zuwa na 14 an bayyana haƙƙoƙin maƙwabci kan maƙwabcinsa.
    d.      Daga baiti na 15 zuwa na 23 an bayyana haƙƙoƙin aboki kan abokinsa.
    e.       A baiti na 21 da na 23, an yi magana ne kan haƙƙin iyaye.[3]
    f.        Daga baiti na 24 zuwa na 40, an bayyana haƙƙoƙin ‘ya’ya kan iyayensu.
    g.      Daga baiti na 41 zuwa na 44 kuwa, an yi magana ne game da haƙƙoƙin mata kan mazajensu.
    h.      A baituka na 45 da 46 kuwa kawo haƙƙoƙin maza kan matayensu.
    i.        Baituka na 47 zuwa na 50 na ɗauke da bayani kan haƙƙoƙin bawa bisa ubangidansa.
    j.        Baituka na 51 zuwa na 54 kuwa na ɗauke da rufewa.

    2.3 Warwarar Jigo
    Kamar yadda aka bayyana a sama, babban manufar wannan waƙa shi ne gargaɗi da faɗakarwaWannan ya ƙunshi jan hankali da faɗakarwa tare da tunasarwa dangane da yadda hulɗa tsakanin jama’a ta dace ta kasance. Hakan kuwa ya haɗa da ba wa kowa haƙƙinsa yadda ya kamata, musamman kamar yadda addini ya tanadar. A ƙoƙarin marubucin na cim ma muradinsa (bayyana haƙƙoƙin mumini bisa mumini), ya samar da ƙananan jigogi kamar dai yadda aka ambace su a sama. Tun daga baiti na uku Isan Kware ya bayyana manufarsa ta rubuta wannan waƙa inda yake cewa:
    3. Daɗa za ni bayyana alhakin kau mumini,
    Bisa mumini, gai sai wurin gamuwa tasa.
    Yayin da aka yi la’akari da baitin da ke sama, za a tarar da cewa mawaƙin ya bayyana manufar waƙar tasa kai tsaye wato “bayyana alhakin … mumini bisa mumini” (Isan Kware, WAMBMTY: Bt.: 3, Ɗg.: 1). A haƙiƙanin gaskiya, wannan ya ƙunshi dukkanin jigogin waƙar tun daga babba har ƙananan jigogin. Dalili kuwa shi ne, duk wani abin da ya shafi alhakin wani ko wasu rukunin jama’a bisa wasu mutane na daban, to ya shafi zamantakewa ne. A ɗangon waƙar na biyu ya fara lissafo ire-iren waɗannan haƙƙoƙi. Na farko da ya kawo shi ne gaishe da mutum yayin da aka haɗu da shi.
    Daga wannan gaɓa (Bt. 3) har zuwa baiti na 8, mawaƙin ya bayyana haƙƙoƙin mumini bisa mumini yayin zamantakewa waɗanda suka fito a cikin hadisai daban-daban. Shi da kansa ya faɗa a baiti na 9 cewa, haƙƙoƙin da ya zayyano a waɗannan baituka (na 3 zuwa na 8), Annabi ne ya faɗe su, wato kenan sun fito cikin hadisai. Ya faɗi hakan inda yake cewa:
    9. Daɗai ka ji an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
    Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 9)
    Su kuwa baitukan da ya bayyana waɗannan haƙƙoƙi da asalinsu ya samo daga hadisai, sun kasance kamar haka:
    4. Ka riƙai riƙon girma ka yo fara’a da shi,
    In yak kirai ka ka zo ka karɓi kira nasa.

    5. In yai atisshewa ka zam yin godiya,
    Ka yi addu’ar rahama garai ka mayas masa.

    6. Lotton da yai ciyyo ka gai sai anka ce,
    Lotton da yam mutu duk ka zo ka biso nasa.

    7. Koyaushe yai zance ka karɓam mai walau,
    Ko ba shi nan ka tsare tutut mus’ha tasa.

    8. So mai ga zucci abin da kas so, ƙi masa,
    Ga abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 4-8)
    A baiti na 4 kamar yadda yake a sama, ya fito da biyu daga cikin haƙƙoƙin. Na farko shi ne fara’a, na biyu kuwa amsa kira (wato dai amsa gayyata yayin da aka yi gayyatar).[4] A baiti na 5 kuwa, ya bayyana wani haƙƙin na daban wato amsa wa wanda ya yi hacitawa tare da yi masa addu’a.[5] A baiti na 6 ya kawo cewa, haƙƙin mumini ne kan mumini ya gaishe shi yayin da ba shi da lafiya.[6] Bayan haka, haƙƙinsa ne ya je bisonsa (jana’iza) yayin da ya rasu.[7] A baiti na 8 kuwa, ya bayyana wani haƙƙin na mumini bisa mumini wato ya so wa ɗan’uwansa abin da yake so wa kansa, sannan ya ƙi ma ɗan’uwansa abin da yake ƙi ma kansa.[8]
    Bayan waɗannan, Isan Kware ya ci gaba da lissafo haƙƙoƙi daban-daban na mumini bisa mumini yayin zamantakewarsu. Misali a baiti na 10 ya bayyana cewa, haƙƙi ne na maƙwabci ya taimaka wa maƙwabcinsa ko da kuwa bai tambaya ba. Ya ce:
    10. Hakana maƙwabci an yi foro taimaka,
    Ko bai biɗa ba ka ba shi kyakkyauta masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 10)
    A cikin baiti na 11 kuwa, ya kawo cewa lallai haƙƙi ne a gai da marar lafiya. Wannan ciwo na iya kasancewa na jiki ko na zuciya.[9] Haka kuma a taya shi murna yayin da wani abin farin ciki ya same shi. Ga abin da yake cewa:
    Ga farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 11)
     A cikin baituka na 12 da 13 ya yi magana ne game da cimaka wato abinci. Ga abin da yake cewa:
    In ba ka ba shi rabo ka ɓoye ido nasa.

    13. Ka hana ma yara fita da shi shi gani zama,
    Ba ka ba shi, ɓoye mai da shi da ɗiya nasa.

    (Isan Kware, WAMBMTY: 12, 13)
    Kamar yadda yake a misalan baitukan da ke sama, haƙƙi ne kada mutum ya nuna wa maƙwabcinsa wani abinci idan dai har ba zai ba shi ba. A baiti na 13 har yake cewa a hana yara ma fita da shi duk dai domin kada maƙwabcin ko kuma ‘ya’yansa su gani.
    A ƙoƙarin Isan Kware na bayyana haƙƙin mumini bisa mumini cikin zamantakewa, ya kawo maganar aboki. Ya bayyana cewa, tun a matakin farko ya kamata wanda ya tashi neman aboki ya nemi abokin ƙwarai “mai mutumci.” Sannan kuma ya tsare abotar tasu da gaskiya da riƙon amana, wanda ya haɗa da taya shi lamuran da suka sha kansa. Ya bayyana hakan a baituka na 15 da 16 kamar haka:
    15. Ga wajen abutta yaf fi ƙarfi an faɗai,
    Biɗi mai mutumci yo tsaron sahuba tasa.

    16. Ka riƙai da amfani walau bai tambaya,
    Ka tsare laluratai ka zam tanyo nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 15, 16)

    Marubucin ya ƙara bayyana wasu haƙƙoƙin da suka haɗa da taya shi ayyukansa da na iyalansa domin rufa masa asiri (Bt. 17), da kuma yabon sa bisa duk wani abin ƙwarai da ya aikata (Bt. 18), sannan a riƙa yi masa uzuri a kuma ba shi haƙƙoƙinsa gaba ɗaya (Bt. 20).
    A ci gaba da magana dangane da hulɗa da jama’a, Isan Kware ya kawo haƙƙoƙin ‘ya’ya kan iyayensu. Ya nuna cewa, matakin farko shi ne tabbatarwa da an zaɓa musu uwaye da masu reno na ƙwarai domin yaran su taso da tarbiyya mai nagarta. Sannan a tabbatar da an ba su ilimi mai inganci. Ya kuma ƙara da cewa, har suna ma a zaɓa masa irin na addini. Ya bayyana hakan cikin baituka na 24 da 25 da kuma 26 inda yake cewa:
    24. Haƙƙi na ɗa ga wajan uwaye kun jiya,
    Zaɓam ma ɗa asuli ga adddini nasa.

    25. A yi mai karatu nai a ba shi shi sha kuma,
    Mai ba shi mamma daɗa da mai yaye nasa.

    26. Duka masu addini a zaɓam mai daɗa,
    Sunansa ras suna a yanka mai bisa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 24, 25, 16)

    Isan Kware ya ci gaba da bayyana haƙƙoƙin ‘ya’ya a kan iyayensu dangane da abin da ya shafi tarbiyyantar da su. Wannan ya haɗa da yin bisimilla kafin fara cin abinci da kuma cin abincin da hannun dama (Bt. 27). Wani abu kuma shi ne hana yara hulɗa da abokai da ba su da nagartar tarbiyya (Bt. 28). Sauran ɓangarorin tarbiyya da mawaƙin ya taɓo sun haɗa da cin abin daɗi koyaushe (sagarta yaro) da sanya tufa na ƙawa da nusar da shi game da ibada da biyayya ga na gaba da sanin ya-kamata. Ya kuma yi nuni da a tausaya wa ‘ya’ya tare da yin amfani da dabaru wurin yi musu hani ga aikata ba daidai ba.
    Daga baiti na ishirin 41 zuwa na 44 na ɗauke da bayani kan haƙƙoƙin mace kan mijinta. Sun haɗa da ciyarwa da shayarwa da samar da muhalli. A cikin haƙƙoƙin ya kawo har da sadaki da kuma ilimantarwa da daidaita kwana.[10] A ɓangare guda kuwa, mawaƙin ya lissafo wasu haƙƙoƙin maza a kan matansu da suka haɗa da yi masa biyayya da riƙe amanarsa da kuma yi masa ado (Bt. 45 da 46).
    Daga baiti na 47, Isan Kwari ya tsunduma cikin zayyano wasu haƙƙoƙin bayi kan iyayen gidansu. Sun haɗa da ciyar da su da tufatar da su da musu rangwame (kada a musu tsanani) da kuma guje wa dukansu. Dangane da haka ne ma ya nuna a baiti na 50 cewa, dukansu saɓo ne a wurin Ubangiji, inda yake cewa:
    50. Kada kai fushi ka bugai ka saɓi Ubangiji,
    Shi ad da shi nan anka ba ka riƙo nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 50)

    Yayin da aka yi la’akari da saƙonnin da ke ƙunshe cikin baitukan wannan waƙa, lallai za a tarar da cewa tana magana ne game da hulɗa da jama’a. Wannan kuwa ya shafi musamman haƙƙoƙin da suka wajaba mutum ya lura da su yayin zamantakewa. Kamar dai yadda aka gani cikin baitukan waƙar, haƙƙoƙin sun haɗa da na tsakanin abokai da maƙwabta da ‘ya’ya da iyayensu da mata da miji da kuma bawa da uban gidansa.

    3.0 Zubi da Tsari
    Zubi da tsari a rubutacciyar waƙa na nufin hanyoyin da mawaƙi ke bi domin tsara rubutun waƙarsa. Yayin da take magana dangane da zubi da tsari a waƙoƙin Mu’azu Haɗeja, Omar, (Mrs) (2013: 39) cewa ta yi: “… hanyoyin da yake bi wajen tsara da zuba tunaninsa.” Wanan ɓangare na aikin zai duba yadda zubi da tsarin waƙar ta Isan Kware ta kasance.

    3.1 Tsarin Baituka
    “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware na da adadin baituka 54. Baya ga haka ta kasance mai zubin ƙwar biyu (wato ‘yar tagwai). Tun daga baitin waƙar na farko har na ƙarshe (54), ba a samu taƙadarin baiti ba ta ɓangaren sauya adadin ɗangwaye. Ma’ana kenan, duka baitukan na ɗauke da ɗangwaye biyu-biyu ne.

    3.2 Mabuɗi da Marufi
    Mabuɗi da marufin waƙa sun shafi irin kalamai ko bayanan da aka yi amfani da su a farko da kuma ƙarshen waƙa. A ra’ayin Usman, (2008: 164): “Abin da ake nufi da mabuɗi a sharhin waƙa shi ne irin yadda marubuci ya buɗe waƙarsa wato abin da ya fara da shi wanda ke nuna cewa farkon waƙar ke nan.” A shafi na 173 kuwa, ya bayyana ma’anar marufi (salon rufewa) da cewa: “A fagen rubutacciyar waƙa marufi yana nufin yada ake rufe waƙar ko kuma abin da ke nuna alamun ƙarshen waƙa.” A wannan gaɓa, aikin zai nazarci “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” domin duba yadda abin ya kasance.

    3.2.1 Mabuɗi
    Mabuɗin waƙa na iya kasancewa addu’a ko yabon Manzo ko neman ƙarin ilimi da sa’a ko bayyana jigon waƙa ko dai wani abu mai kama da wannan. Akan samu kuma waƙoƙin da suka zo da haɗakan biyu ko sama da haka na daga cikin abubuwan da aka lissafa. A wasu lokutan kuwa, ana iya samun waƙar da aka fara ta kai tsaye ba tare da ɗaya daga cikin waɗannan ba. A waƙar “Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware, an fara da yabon Ubangiji da kuma salati ga Manzo (SAW) tare da alayensa da kuma sahabbansa a matsayin mabuɗin waƙar. Ga yadda abin ya kasance:
    1.      A mu gode Sarki Wahidun Rahama tasa,
    Ita ta ishe mu zumai mu zam gode masa.

    2.      A mu zam salati ga Annabinmu da sallama,
    Allai Sahabbai nai da masu biya tasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 1; 2)

    Idan aka yi la’akari da baitukan da ke sama, baiti na farko yana ɗauke ne da godiya ga Ubangiji dangane da rahamarsa. Mawaƙin ya ma ƙara da kira ga al’umma da su gode masa a ɗango na biyu (zumui mu zan gode masa, Bt. 1, Ɗg. 2). Baiti na biyu kuwa na ɗauke da salati ne ga Manzo da alaye da kuma sahabbansa. Haƙiƙa ba abin mamaki ba ne da aka samu waƙar ɗauke da wannan nau’in salon buɗewa kasancewarta waƙa ce da aka rubuta ta a ƙarni na goma sha tara. Da ma dai dukkanin waƙoƙin ƙarni na goma sha tara ba su da wani jigo wanda ba shi da dangantaka da addinin Musulunci.

    3.2.2 Marufi
    Mawaƙi na iya rufe waƙa ta hanyar godiya ga Ubangiji, ko salati ga Manzo, ko bayyana adadin baitukan waƙar, ko bayyana shekarar da aka wallafa ta, ko kuma ya yi amfani da biyu ko sama da haka daga cikin abubuwan da aka ambata (har ma da makamantansu da ba a ambata ba). Isan Kware ya rufe waƙar a cikin baituka huɗu (na 51 da 52 da 53 da kuma 54) kamar haka:
    51.  Daɗa na cika Allah shi ba mu farin ciki,
    Don Annabinmu zumui mu zam gode masa.

    52.  Ramzi na hijira tai Fiyayye kun jiya,
    SHURAFA’UHU haƙƙan ina bege nasa.

    53.  Allah shi dawwama assalatu da sallama,
    Bisa Sayyadinmu da Sahabu har Allai nasa.

    54.  Na gode Allah wanda yat tanye ni don,
    Ƙari shikai haƙƙan ga masu yabo nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 51, 52, 53, 54)

    Yayin da aka lura da waɗannan baitukan kammalawa, za a tarar da cewa suna ƙunshe da abubuwan da suka haɗa da:
    i.                    Roƙon Allah ya faranta musu zukata (Bt. 51)
    ii.                  Bayyana ramzi ko shekarar da aka wallafa waƙar (Bt. 52)
    iii.                Salati ga Manzo da alaye da sahabbai (Bt. 53)
    iv.                Godiya ga Ubangiji da ya taimake shi ya samu ikon yin waƙar da fatar samun falalar yin godiya wato ƙarin wasu alherai (Bt. 54)

    3.3 Amsa-Amo
    “A cikin rubutacciyar waƙa, amsa-amo sauti ne da layuka ko baitukan waƙa ke ƙarewa da shi” (Sarɓi, 2007: 90). A cikin “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara,” Isan Kware ya yi amfani da gaɓar kalma “sa” a matsayin babban amsa-amo. Ya fi yin amfani da kalmar “nasa” a matsayin kalmar ƙarshe na ɗangon ƙarshe da ke kowane baiti. Duk da haka, babban amsa-amon bai kasance kalma ba domin kuwa akwai baituka da suka ƙare da wasu kalmomin na daban, misali kalmar “masa” a baituka na 1 da 5 da 10 da 14 da 18 da sauransu. Haka ma an yi amfani da kalmar “tasa” kamar a baituka na 2 da 3 da sauransu. A taƙaice kenan, babban amsa amon da aka yi amfani da shi cikin waƙar shi ne gaɓar kalma na “sa” duk kuwa da cewa kalmar “nasa” ta fi yawa a ƙarshen baitukan. Wato a ɗaukacin waƙar ya yi amfani da doguwar ‘yar mallaka (nasa, tasa da masa) a matsayin uwar goyon amsa-amo babba. Dangane da ƙaramin amsa-amon waƙar kuwa, kasancewar waƙar a zubin ‘yar tagwai ya sa ba a samu daidaiton harafi a ƙarshen layukan farko na baitocin waƙar ba.

    3.4 Gangara da Saɓi-Zarce
    Wannan wani al’amari ne da ke faruwa cikin waƙoƙi wanda yakan kasance a cikin baiti (tsakanin ɗango da ɗango) ko kuma tsakanin baiti da baiti.  Usman, (2008: 208-209) ya yi bayanin ganganra da cewa: “A gangara ana fara zance ne ko wata manufa amma sai a ja ta zuwa ga ɗangon da ke biye kafin a ƙarasa.” Yayin da yake bayani game da saɓi-zarce kuwa, sai ya ce: “Saɓi-zarce kuwa gangara ce mai zurfi wadda ake fara zance a baiti amma sai a baiti na gaba ne za a ƙarasa maganar” (shafi: 210).

    3.4.1 Gangara
    A cikin “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara,” akwai wurare daban-daban da marubucin ya yi amfani da gangara. Ga misalansu kamar haka:
    1.      A mu gode Sarki Wahidun Rahama tasa,
    Ita ta ishe mu zumai mu zam gode masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 1)

    A wannan baiti na farko, za a ga yadda mawaƙin ya fara da godiyar Ubangiji (Sarki Wahidun), inda har ya ba da ɗaya daga cikin dalilan da za a gode masa, wato rahamarsa da ta ishe ‘yan’adam (kamar yadda mawaƙin ya ambata “… rahamar tasa ita ta ishe mu…” Bt. 1, Ɗg. 2). Ya faro maganar rahamar ne a ɗangon farko na waƙar, amma bai cika zancen ba sai a ɗango na biyu inda yake nuna rahamar ce ta ishe mutane, wanda ya kamata a masa godiya bisa wannan. Isan Kware ya sake amfani da gangara a baiti ba 3 inda yake cewa:
    3. Daɗa za ni bayyana alhakin kau mumini,
    Bisa mumini, gai sai wurin gamuwa tasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 3)
    A wannan baiti da ke sama, mawaƙin ya fara zance a ɗangon farko inda yake ƙoƙarin bayyana manufar waƙar. Ya nuna cewa ƙudurinsa shi ne “… bayyana alhakin kau mumini… Bt. 3, Ɗg. 1.” Bai ƙarasa wannan zance ba. A ɗango na biyu ne ya kammala shi inda yake cewa “… bisa mumini… Bt. 3, Ɗg. 2.” Yayin da aka karanta baitocin biyu ne za a fahimci manufar mawaƙin wato “bayyana alhakin … mumini bisa mumini.” A baiti na 8 ma an samu irin wannan inda mawaƙin ke cewa:
    8. So mai ga zucci abin da kas so, ƙi masa,
    Ga abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 8)
    Abin da Isan Kware ke son bayyanawa shi ne, mutum ya so wa ɗan’uwansa abin da yake so wa kansa, sannan ya ƙi masa abin da yake ƙi ma kansa. Ya fara wannan batu a ɗango na farko, amma zancen bai kammala ba sai a na biyu. Sauran misalan baitukan da mawaƙin ya yi amfani da gangara sun haɗa da na 2 da 7 da 12 da 13 da 19 da 21 da 24 da 34 da 35 da 36 da 40 da 46 da 48.
    A baiti na 14 a lura da yadda ya raba kalmar gidanai (gidansa) zuwa gida biyu; wato ya saka farkon kalmar a ɗango na farko, amma sai ya ɗauko ƙarshen kalmar zuwa ɗango na biyu, inda yake cewa:
    14. Foron da anka yi kar ka dubi cikin gida,
    Nai ka ji kar ka matsai ka yalwanta masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 14)
    Yana bayanin cewa, an yi horon duk mumini kada ya yi leƙon gidan maƙwabcinsa, domin kada ya haifar da yanayin da zai kawo matsatsi tsakaninsu har ya ji an sauya ido a harkokinsa.

    3.4.2 Zaɓi-Zarce
    A misalin zaɓi-zarce a lura da yadda ya ja ma’anar zance da yake yi daga layin ƙarshe na baiti na 23, inda yake cewa:
    23.  A hana shi kwanan ana kwantawa tutut,
    Bisa shimfiɗa hakana ayukkan kai nasa.

    24.  Sannan a sa shi daɗa ga addini shi bi,
    Foron uwaye nai da mallammai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 23-24)
    A nufinsa yana nuni da cewa sai ‘yayan da suka bai wa iyaye haƙƙin da Allah ya ɗora a kansu ne za su shiga aljanna. Wato duk wanda ya saɓa wa iyaye kuma bai yi musu biyayya ba ko bai darajanta su ba, to sakamakonsa wauta ne. Sannan iyaye ko sun ƙi ‘ya’ya idan sun yi musu biyayya to wannan ba zai shafi ‘ya’yan da komai ba, balle ma ya ka kamata iyayen su gafarta ma ‘ya’yan da suka ba da haƙƙin Allah.
    3.5 Kari
    Kari na nufin bahari ko daujiyar muryar da mawallafi ya gina sautin waƙarsa a kai. A wannan fuskar, waƙar tana bisa zubin karin Kamil ne inda ƙafa ta takwas ta maimaita kanta sau uku (8 + 8 + 8) tare da zihafin Ilmari wanda ke mayar da ita ta shida a wasu wurare. Ga misalin yadda abin yake:

    v      v      –  v   – / –    –   v  –  /   v   v   –    v   –
    A   mu   gode   Sarki   Wahidun   Rahama   tasa
                             v     v    – v     –  /  v   v       –     v        –/–  – v –
    Ita   ta   ishe   mu   zumui   mu   zan   gode masa

    4.0 Salo
    Salo hikima ce ko dabara ta isar da saƙo cikin siga mai jan hankali da ƙayatarwa. Yahya, (2016: 29) ya ba da ma’anar salo da cewa:
    Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa.
    Akwai salailai daban-daban da mawaƙa ke amfani da su cikin waƙoƙinsu. Wannan ɓangare na aikin zai nazarci “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta Isan Kware domin fito da ire-iren salailai da ke ciki.

    4.1  Siffantawa
    Sarɓi, (2007: 172) ya bayyana ma’anar siffantawa da cewa: “Kwatantawa ce da ta shafi daidaita tsakanin abubuwa biyu kai tsaye. Dabara ce ta jawo hankali ta hanyar ɗaukar wani abu a ce shi ne wani abu daban.” A yayin siffantawa, ba a amfani da kalmomi irin su “kamar” ko “sama da” ko “irin” da makamantarsu (wato saɓanin yadda lamarin yake a kamantawa). Mawaƙin ya yi amfani da salon siffantawa a baiti na 11. A cikin baitin ya siffanta ‘taya maƙwabci murna yayin da abin farinci ya same shi’ da “rabo” (rabo nasa):
    11. Gai sai da ciyyo dud da ciyyon zucciya,
    Ga farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 11)

    4.2  Alamtarwa
    “Alamtarwa wata hanya ce wadda ake bayyana wani abu ta ba shi wata alama da ta yi kama da shi ta fuskar siffa ko yanayi ko ɗabi’a ko hali ko asali ko jarumtaka ko ƙasaita da sauransu” (Gusau, 2011: 37). Lura da wannan ma’ana, alamtarwa na nufin dabara ko hikimar yin amfani da kama ko siffar da wani abu ke da shi domin a bayyana wani abu na daban a kaikaice. Isan Kware ya yi amfani da alamtarwa a baiti na 8. Ya yi hakan ne yayin da yake nuna cewa, haƙƙi ne mumini ya so wa mumini dan’uwansa abin da ya so wa kansa. Haka ma ya ƙi masa abin da ya ƙi ma kansa. A cikin baitin sai mawaƙin ya yi amfani da “rai” a matsayin mutumin sukutum. Kenan dai, “rai” a cikin baitin na wakiltar mutumin da ake batu kansa (mumini da ke da haƙƙi). Ga abin da yake cewa:
    8. So mai ga zucci abin da kas so, ƙi masa,
    Ga abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 8)

    Mawaƙin ya sake amfani da salon Alamtarwa a baiti na 12. Ya nuna cewa, yayin da maƙwabci ba zai ba da cimaka (abinci) ga maƙwabcinsa ba, to ya ɓoye masa (wato kada maƙwabcin nasa ya gani). A maimakon Isan Kware ya ce a ɓoye masa kai tsaye, sai ya ce: “… ka ɓoye ido nasa” (Bt. 12, Ɗg. 2). A nan ya yi amfani da “ido” domin su wakilci shi mutumin da ake magana a kansa, wato maƙwabci.
    12. In ka raba in cimaka ta ka jiya,
    In ba ka ba shi rabo ka ɓoye ido nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 12)
    4.3 Jaddadar Ƙarfafawa
    Ɗangambo, (2007: 48) ya ba da ma’anar wannan salo da cewa: “Dabara ce ta jawo hankali da ƙarfafa manufa. Akan maimaita wasu kalmomi ko rukunin kalmomi, da sauransu, a yi musu wani irin jeri mai ban sha’awa cike da hikima.” A baiti na 9, mawaƙin ya yi amfani da jaddadar ƙarfafawa. Ya yi hakan ne yayin da yake ƙoƙarin nuna matsayin haƙƙoƙin mumini bisa mumini da ya zayyano cikin baitocin waƙar (daga baiti na 3 zuwa na 8). Ga abin da yake cewa:
    9. Daɗai ka ji an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
    Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai nasa.

    A ɗango na farko ya jaddada inda yake cewa: “… an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa” (Bt. 9, Ɗg. 1). A nan, ya jaddada kan dukkanin haƙƙoƙin da ya lissafo domin dai ya ƙarfafa zancen. A ɗangon ƙarshe na baitin sai ya ƙara jaddadawa inda yake faɗin: “Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai nasa” (Bt, 9. Ɗg. 2). Bayan wannan, ya sake yin amfani da wannan salo a baiti na 18. Ya ce:
    18. Ka yabai tutut ga abin da kas san ka sani,
    Hakana mutane nai ka zam ka faɗa masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 15 da 16)

    4.4  Jerin Sarƙen Daidaito/Bambanto
    Wannan salo yana kama da salon Jaddadawar Ƙarfafawa domin kuwa dukansu biyu sun shafi jeranto kalmomi domin jaddada wani batu. Yayin nuna bambancinsu, Ɗangambo, (2007: 49) ya ce: “Shi jerin sarƙe, bayan jaddada, akan sami sarƙaƙƙiyar daidaito ko ta banbanto, wato akan sami makusanciyar dangantaka tsakanin kalmomi iri daban-daban a baiti, wannan dangantakar tana iya zama ta daidaito ko ta bambanto. Mawaƙin ya yi amfani da jerin sarƙen daidaito a baiti na 33. A cikin wannan baiti ya kawo kalmomi biyu da ke da dangantaka da juna ta fuskar daidaiton ma’ana wato “kwana” (bacci) da kuma “kwantawa.” An dai sani cewa, a bisa al’ada akan yi bacci ne yayin da aka kwanta. Ga abin da mawaƙin ke cewa:
    33. A hana shi kwanan ana kwantawa tutut,
    Bisa shimfiɗa hakana ayukkan kai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 33)


    4.5  Ƙarangiya
    Gusau, (2011: 39) ya bayyana ma’anar ƙarangiya da cewa: “Dabara ce ta luguden haruffa ko kalmomi ko wasa da harshe cikin baƙaƙe da kalmomi a lokacin da ake ƙoƙarin isar da wani saƙo.” Mawaƙin ya yi amfani da ƙarangiya a baiti na 29 inda ya kawo jerin kalmomi masu ɗauke da harafin /ƙ/. Haƙiƙa furta kalmomin a jere kamar yadda suka fito a baitin na samar da wani salo na gagara-bami. Ga abin da yake cewa:
    29. Kada ko shi saba cin abin daɗi kaɗai,
    Da tufan ƙawa shi ƙawai ƙawa a gaya masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 29)

    4.6 Gamin Bauta
    Gamin bauta a nazarin waƙa na nufin yin amfani da kalmomi guda biyu wuri guda waɗanda ke ɗauke da ma’anoni da suka yi hannun riga da juna. Mawaƙin ya yi amfani da salon gamin bauta a baiti na 48. A cikin baitin ya kawo kalmar “rage” da ke ɗaukar ma’anar sassautawa ko ɗebewa ko ragewa da ya shafi adadi ko mizanin wani abu. Ya haɗa wannan kalma da kalmar “tsanantawa” wadda ke ɗaukar ma’ana da kai tsaye ta yi hannun riga da kalmar ta farko. Ga yadda abin ya kasance:
    48. Mu rage tsanantawa ga bauta kowane,
    Yak karɓi bautawa mu zam kyauta masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 48)
    4.7 Tasirin Al’adu
    Ala’ada na nufin abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya. Ta kuma shafi rayuwar al’umma da harkokin da suke yi don zaman duniya (Ibrahim, 1982: ɗiii). Yayin da aka nazarci waƙar “Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara,” za a tarar da akwai tasirin addinin Musulunci kan mawaƙin. Baituka da dama suna ɗauke da wannan tasiri na addini. Mafi yawa na abin da mawaƙin ke faɗa cikin waƙar sun samu asali ne daga addini. Tun wurin buɗe waƙar ya fara da yabon Ubangiji da kuma salati ga manzo da iyalan gidansa da kuma sahabbansa. A baiti na farko ya kawo kalmomin “Sarki” da “Wahidun” da “Rahama” waɗanda ke nuni ga tauhidinsa. Irin waɗannan kalmomin fannu da suka shafi addini sun mamaye waƙar baki ɗaya.
    A ɓangare guda kuwa, an samu tasirin karin magana[11] a cikin waƙar ta Isan Kware a baiti na 31. Akwai karin maganar Hausawa da ke cewa: “Hannun da ke bayarwa shi ke a sama.” Mawaƙin kuwa sai ya ce:
    31. Liddinsu anka halatta sawa tai ku san,
    Mai ba da kyauta ya fi mai karɓa masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 31)

    4.8  Salon Samarwa da Korewa
    Wannan salo ne da ya shafi kawo bayanai da ke nuna yarda ko rashin yarda a cikin ɗangogin baitukan waƙa. Ɗangambo, (2007: 53) ya yi ƙarin bayani dangane da wannan salo da cewa: “Wannan ita ma dabara ce ta jan hankali wada mawallafa kan yi amfani da ita don samun yarda daga makaranci ko mai sauraro. Cikin wanan dabara, sukan kawo “yarda” ko “rashin yarda” wato “samarwa” da “korewa.” A wannan gaɓa za a nazarci waƙar domin ganin ko marubucin ya yi amfani da irin wannan salo?
    4.8.1 Samarwa da Korewa
    Samarwa da korewa na nufin wurin da aka samu mawaƙi ya kawo jimla ko furucin samarwa, sannan jimla ko furuci na korewa ya biyo baya. Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo cikin waƙarsa. Misali a baiti na 14 yana cewa:
    14. Foron da anka yi + kar ka dubi cikin gida,
    Nai ka ji kar ka matsai ka yalwanta masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 14)

    4.8.2        Samarwa da Samarwa
    A misalin baitin da ke ƙasa, mawaƙin ya yi amfani da haɗin samarwa da samarwa. Ga yadda abin ya kasance:
    11. Gai sai da ciyyo + dud da ciyyon zucciya,
    Ga farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 11)
    4.8.3        Korewa da Samarwa
    A wannan wuri kuwa, mawaƙin ya kawo ɗango da ke ɗauke da korewa da samarwa. Ga yadda abin ya kasance:
    13. Ka hana ma yara fita da shi shi gani zama,
    Ba ka ba shi, + ɓoye mai da shi da ɗiya nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 13)
    4.8.4        Samarwa
    A baiti na 23 kuwa, za mu iya tsintar misalin ɗangon da ke ɗauke da samarwa kawai. Ga yadda abin yake:
    23. Ka shiga gidan Aljanna ko sun tonyatai,
    Shi kam haƙiƙan sai su gafarta masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 23)

    4.8.5        Korewa
    Ɗangon waƙa na iya zuwa da furuci ko jumla mai ɗauke da korewa kawai. An samu irin haka a baiti na 48 inda mawaƙin ke cewa:
    48. Mu rage tsanantawa ga bauta kowane,
    Yak karɓi bautawa mu zam kyauta masa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 48)

    4.9 Zaɓen Kalmomi
    Mawaƙin ya yi amfani da karin harshen Sakkwatanci a baituka da yawa na cikin waƙar. Kalmomin rukuni da ya yi amfani da su cikin waƙar sun haɗa da:


    a.       Zumai (Bt.1) = ‘yan uwa
    b.      Daɗa (Bt. 3) = kuma
    c.       Lotto (Bt. 6) = lokaci
    d.      Tutut (Bt. 7 da 33) = kullum
    e.       Biɗa (Bt. 10) = nema
    f.        Cimaka (Bt. 12) abinci
    g.      Tonyatai (Bt. 23)
    h.      Abutta (Bt. 15) = abokantaka
    i.        Miyau (Bt. 35) = yawu
    j.        Wargi (Bt. 35) = wasa
    k.      Amre (Bt. 41) = aure
    l.        Bananci (Bt. 43) = zamananci
    m.    Gyarta (Bt. 45 da 46) = gyara
    n.      Tanye (Bt. 54) = taimake


    Baya ga wannan kuma, akwai kalmomin aro da Isan Kware ya yi amfani da su a cikin waƙar, musamman daga harshen Larabci. Wasu daga cikinsu an yi musu kwaskwarima bayan an are su. Wasu kuwa an yi amfani da su yadda suke a harshen na Larabci. Ga misalan kalmomin aron da aka yi amfani da su:


    a.       Wahidun da Rahama (Bt. 1)
    b.      Salati da Alai da Sahabbai (Bt. 2)
    c.       Mumini (Bt. 3)
    d.      Rahama (Bt. 5)
    e.       Mutu (maiti na 6)
    f.        Musha (Bt. 7)
    g.      Biɗa (Bt. 15)
    h.      Salihi (Bt. 32)


    4.10 Zubin Jimloli
    Akwai baitukan daga cikin waƙar da ke ɗauke da ɗangwaye masu giɓin jimla. Za mu tarar da wannan misali yayin da muka nazarci baiti na 47, inda yake cewa:
    47. Bayi mu ba su abin da muka ci dud su ci,
    Da tufanmu alher(i) na mu zam ko yi nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 48)

    A wannan misali da ke sama, mawaƙin ya yi amfani da kalmar alheri a ɗango na biyu inda a maimakon sanya kalmar ta “alheri” sai ya yi amfani da “alher.” A taƙaice dai ya bar giɓi a cikin jimlar.

    5.1 Sakamakon Nazari
    Wannan nazari ya fahimci abubuwa kamar haka:
    1.      Wannan waƙa ta Isan Kware mai suna “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” tana ɗauke da muhimman jigogi masu magana kan “zamantakewa”. Mawaƙin ya yi matuƙar ƙoƙari wurin bayyana haƙƙoƙin mutane a tsakanin junanansu ga matakan zamantakewa daban-daban. Sun haɗa da haƙƙoƙin maƙwabtaka da haƙƙoƙin abota da haƙƙoƙin da ke tsakanin iyaye da ‘ya’yansu da kuma maaurata sannan da bawa da uban gidansa. Wasu daga cikin waɗannan haƙƙoƙi ya ɗauko su ne daga hadisan manzon Allah (SAW) kamar yadda ya faɗa a baiti na 9 inda ya ce:
    9. Daɗai ka ji an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
                Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai nasa.
    (Isan Kware, WAMBMTY: 9)
    2.      Isan Kware ya yi amfani da salailai domin jawo hankali da kuma samun damar isar da saƙon waƙarsa. Waɗannan salailai sun haɗa da salon Alamtarwa da siffantawa da gamin bauta da jaddadawar ƙarfafawa da makamantansu.
    3.      Mawaƙin ya yi amfani da harshe mai sauƙi wurin isar da saƙonsa duk da cewa waƙar ta ƙunshi Sakkwatanci a wasu ɓangarorinta. Baya ga haka kuma, waƙar cike take da tsattsafin tasirin addinin Musulunci da mawaƙin ke da shi.

    5.2  Kammalawa
    Haƙiƙa “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara” ta amsa sunanta, domin kuwa ta zayyano ire-iren haƙƙoƙin da suka rataya kan rukunnen mutane da ka iya tsintar kansu cikin hulɗa da zamantakewa ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Lura da yadda waƙa ke tasiri ga zukata da kuma sauri da sauƙin isar da saƙo, wannan aiki ya tanadi shawarwari ta la’akari da sakamakon nazarin kamar haka: Manazarta su ƙara ƙaimi wurin nazartar ire-iren waɗannan waƙoƙi domin fito da saƙonninsu fili, tare kuma da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin karantar da waƙoƙin a makarantu wanda hakan na iya tasiri matuƙa a ɓangaren gyaran tarbiyya. Wata hanyar da ka iya taimakawa ita ce amfani da kafafen sadarwa da suka haɗa da gidajen rediyo da talebijin da jaridu da kuma kafar intanet.

    Paper Citation: Usman, B.B. & Sani, A-U. (2019). Gargaɗi ga Gyautata Zamantakewa: Faɗakarwa Daga Alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu. In East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, Volume-2, Issue-10, Pp 621 - 632.  ISSN  2617-443X (Print) | ISSN  2617-7250 (Online). 

    Rataye (Appendix)
    Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini da Tarbiyyar Yara ta Isan Kware Ɗan Shehu
    (The Rights of a Believer Upon a Believer and the Upbringing of Children)


             Ita ta ishe mu zumai mu zam gode masa.

    2.      A mu zam salati ga Annabinmu da sallama,
              Allai Sahabbai nai da masu biya tasa.

    3.      Daɗa za ni bayyana alhakin kau mumini,
             Bisa mumini, gai sai wurin gamuwa tasa.

             In yak kirai ka ka zo ka karɓi kira nasa.

    5.      In yai atisshewa ka zam yin godiya,
            Ka yi addu’ar rahama garai ka mayas masa.

    6.      Lotton da yai ciyyo ka gai sai anka ce,
           Lotton da yam mutu duk ka zo ka biso nasa.

    7.      Koyaushe yai zance ka karɓam mai walau,
             Ko ba shi nan ka tsare tutut mus’ha tasa.

    8.      So mai ga zucci abin da kas so, ƙi masa,
          Ga abin da kaƙ ƙi ga zucciyakka ga rai nasa.

    9.      Daɗai ka ji an yi ƙidansu su duka ɗan’uwa,
            Ka tsare su Annabi yaf faɗe su da kai nasa.

    10.  Hakana maƙwabci an yi foro taimaka,
             Ko bai biɗa ba ka ba shi kyakkyauta masa.

    11.  Gai sai da ciyyo dud da ciyyon zucciya,
             Ga farin ciki ka yi mai ka ba shi rabo nasa.

    12.  In ka raba in cimaka ta ka jiya,
             In ba ka ba shi rabo ka ɓoye ido nasa.

    13.  Ka hana ma yara fita da shi shi gani zama,
    Ba ka ba shi, ɓoye mai da shi da ɗiya nasa.

    14.  Foron da anka yi kar ka dubi cikin gida,
    Nai ka ji kar ka matsai ka yalwanta masa.

    15.  Ga wajen abutta yaf fi ƙarfi an faɗai,
    Biɗi mai mutumci yo tsaron sahuba tasa.

    16.  Ka riƙai da amfani walau bai tambaya,
    Ka tsare lalura tai ka zam tanyo nasa.

    17.  Ka yi mai ayukka nai sa’annan naka kau,
    Hakana iyali nai rufe aibi nasa.

    Hakana mutane nai ka zam ka faɗa masa.

    19.  In an yabe shi ka bar gwada mai al’amar,
    Duka mai wuya, laifi ka gafarta masa.

    Balle zumu ka tsaya ma alhukka nasa.

    21.  In ka raba fara da shi sanna uwa,
    Sanna uba shi ko ka ba shi rabo nasa.

    22.  Sanna abukkan haifuwa kuma ka jiya,
    Sai mai tsaron hakkin mahifayye nasa.

    23.  Ka shiga gidan Aljanna ko sun tonyatai,
    Shi kam haƙiƙan sai su gafarta masa.

    24.  Haƙƙi na ɗa ga wajan uwaye kun jiya,
    Zaɓam ma ɗa asuli ga adddini nasa.

    25.  A yi mai karatu nai a ba shi shi sha kuma,
    Mai ba shi mamma daɗa da mai yaye nasa.

    26.  Duka masu addini a zaɓam mai daɗa,
    Sunansa ras suna a yanka mai bisa.

    27.  In za shi ci sunnammu Bismillahi ai,
    Shi ci ko da hannun dama nan wajje nasa.

    28.  A tsare shi kar shi shigam ma yara mawargata,
    Balle fa masu ƙawa a zam ka hana masa.

    29.  Kada ko shi saba cin abin daɗi kaɗai,
    Da tufan ƙawa shi ƙawai ƙawa a gaya masa.

    30.  Da tufa na zinari azurfa alharin,
    Mata ka sa su cikin gida a tuna masa.

    31.  Liddinsu anka halatta sawa tai ku san,
    Mai ba da kyauta ya fi mai karɓa masa.

    32.  Ga wajen karatu nai kai shi ga salihi,
    Salla shi yo ta shi yo ibadadi nasa.

    Bisa shimfiɗa hakana ayukkan kai nasa.

    34.  Sannan a sa shi daɗa ga addini shi bi,
    Foron uwaye nai da mallammai nasa.

    35.  A hana shi wargi kau gaban manya da kau,
    Tofin miyau sai nesa duk a gwada masa.

    36.  In an bugai lotton karatu nai a ce,
    Wayyo na bayi na a kwankwamta masa.

    37.  In ya ƙiya sau ɗai a bar shi a hanƙure,
    Lotton da yaƙ ƙara a yo ruɗi nasa.

    38.  Ɗau anniya kai kun jiya foron uwa,
    Tsoro daɗa taka ba shi nan da uba nasa.

    39.  Raba yara in sun kai ga shekarru bakwai,
    Kowa rufa shi daban tufa ga wuri nasa.

    40.  A buge su nan lotton faɗin salla akul,
    Sun kai ga goma da ukku nan ga faɗi nasa.

    41.  Koway yi amren macce haƙƙan ci da shi,
    Da wurin shiga duka an aza su ga kai nasa.

    42.  Bisa ya cika mata alhakinta da shar’u duk,
    Shi as sadaki wanda anka azama masa.

    43.  An kai ta nan aka son walima tai shi yo,
    Mata nan bananci dud da ko murna tasa.

    44.  Shi sanad da mata nai sanin addin shi kau,
    Daidaita kwanakki shi gyarta gida nasa.

    45.  Daidaita kwana mustahabbi na, ta zam,
    Jin ko batu nai duk ta zam gyarta masa.

    46.  Ta tsare daɗa ajiyad da yay yi ta sa ƙawa,
    Ga jikinta dud da tufanta don girma nasa.

    Da tufanmu alher na mu zam ko yi nasa.

    Yak karɓi bautawa mu zam kyauta masa.

    49.  Daɗa wanda yaƙ ƙi mu bar bugu nai kun jiya,
    Rabuwa da shi das sannu ya fi bugu nasa.

    50.  Kada kai fushi ka bugai ka saɓi Ubangiji,
    Shi ad da shi nan anka ba ka riƙo nasa.

    Don Annabinmu zumui mu zam gode masa.

    52.  Ramzi na hijira tai Fiyayye kun jiya,
    SHURAFA’UHU haƙƙan ina bege nasa.

    53.  Allah shi dawwama assalatu da sallama,
    Bisa Sayyadinmu da Sahabu har Allai nasa.

    54.  Na gode Allah wanda yat tanye ni don,
    Ƙari shikai haƙƙan ga masu yabo nasa.







    [1] Ana ba da ma’anar waƙa ne ta fuskoki guda uku wato: (i) Ma’ana ta gaba ɗaya ko (ii) Ma’anar rubutacciyar waƙa ko kuma (iii) Ma’anar waƙar baka (Idris, 2019).
    [2] Ɗandatti, (1979: 52) ya tabbatar da cewa Isan Kware ne ya yi wannan waƙa.
    [3] Idan aka lura za a fahimci cewa, baituka na 21 da 22 da kuma 23 na ɗauke da batun haƙƙin iyayen kan ‘ya’yansu da kuma haƙƙin aboki kan aboki.
    [4] Manzon Allah (SAW) ya ambaci haka cikin hadisin Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) mai lamba 2162 a cikin Sahihul Muslim.
    [5] Abin da addini ya koyar shi ne, wanda ya yi hacitawa zai ce: “Alhamdulilla” (Godiya ta tabbata ga Allah). Amsa masa haƙƙi ne inda za a ce: “Yarhamakalla” (Allah ya maka rahama). Wannan batu ya zo a cikin hadisin Abu Huraira (Allah ya yarda da shi). Hadisi ne mai lamba 5870 a cikin Sahihul Bukari.
    [6] Wannan batu na cikin Hadisin Abu Huraira (Allah ya yarda da shi). Hadisi ne mai lamba 12 a cikin Sahihul Muslim.
    [7] Abu Huraira (Allah ya yarda da shi), shi ne ya rawaito wannan hadisi. Ya zo a cikin Sahihul Buhari mujalladi na ɗaya, lamba na 81).
    [8] Wannan hadisi ne sananne wanda aka karɓo daga Baban Hamzata (Allah ya yarda da shi). Hadisin na zo cikin Sahihul Buhari. Yana da lamba 13.
    [9] Masana Hausa musamman al’ada sun kasa cuta ta hanyar la’akari da abubuwa daban-daban. Daga cikin rabe-raben akwai abin da ya shafi cutukan jiki (waɗanda suka kasance bayyanannu) da kuma cutukan zuciya (waɗanda suka kasance ɓoyayyu) (Gobir, 2012: 165).
    [10] Ana samun maganar daidaita kwana ne yayin da namiji ya kasance ba mata guda yake aure ba. A irin wannan lokaci, daidaita yawan kwanaki da yake yi a ɗakin kowacce, abu ne da addini ya nuna a kula da shi. Wannan ne kuma mawaƙin yake magana a kai.
    [11] Gulbi, (2014: 8) ya bayyana ma’anar karin magana da cewa: “Wani zance ne da akan shirya cikin hikima da naƙaltar harshe wanda kan zo da sigar taƙaita zance.”

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.