Ticker

6/recent/ticker-posts

Nahawun Magana: Jereƙen Biyar Diddigin Ma’anar Magana da Rabe-Rabenta a Bahaushen Tunani



Magana ita ce mutum, da ita ake rarrabe shi da sauran halittun dabbobi, ƙwari da tsuntsaye. Kowace iri martaba da ɗaukaka ɗan Adam yake da ita idan ya rasa magana ba su da wani tasiri a rayuwarsa. Magana ita ce cigaban ɗan Adam ta farko gabanin ya iya sarrafata a rubuce wani ya karanta ta a fahince shi. Tunanina na gabatar da wannan muƙala shi ne, a fayyace nahawun magana gwargwadon yadda ɗalibin harshe zai gano cewa, lallai nazarin harshe ba ƙaramin ɗaukaka gare shi ba ga rayuwar ɗan…
NAHAWUN MAGANA
(Jereƙen Biyar Diddigin Ma’anar Magana da Rabe-Rabenta a Bahaushen Tunani)

Aliyu Muhammadu Bunza
Faculty of Humanities and Education
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau.

Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu Augi College of Education Argungu, Kebbi State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga Maris, 2017 da ƙarfe 10:00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa



Gabatarwa:
Magana ita ce mutum, da ita ake rarrabe shi da sauran halittun dabbobi, ƙwari da tsuntsaye. Kowace iri martaba da ɗaukaka ɗan Adam yake da ita idan ya rasa magana ba su da wani tasiri a rayuwarsa. Magana ita ce cigaban ɗan Adam ta farko gabanin ya iya sarrafata a rubuce wani ya karanta ta a fahince shi. Tunanina na gabatar da wannan muƙala shi ne, a fayyace nahawun magana gwargwadon yadda ɗalibin harshe zai gano cewa, lallai nazarin harshe ba ƙaramin ɗaukaka gare shi ba ga rayuwar ɗan Adam. A fahintarmu, mu ɗaliban Hausa, sirrin sanin magana da iya ta yana cikin sanin nahawunta. Matuƙar ba a san nahawunta ba, ba a gane bakin zarenta. To, mene ne nahawun magana?

Nahawun Magana:
A iya ɗan bincikena, Farfesa Isa Mukhtar ne manazarci na farko da ya yi zuzzurfan bincike kan “nahawun Waƙa” a digirin MA Jami’ar Bayero, Kano. A taƙaice, nahawu kalmar Larabci ce. A Larabci tana nufin “ma’ana” ko a ce “kamar” ko “misali” ko “daidai”. An ce, Sayyidina Aliyu (RA) ya fara fito da ita ga ajamawan da ba su iya Larabci ba, in sun karanta ko faɗa a kan kuskure, ya ce “nahwi haazaa” ko “nahwu kazaa”. A fagen karatu, “nahawu” ya fara cin gashin kansa da sunan daidaita magana da biyar ƙa’ida ga ma’abotanta bisa ga tsarin yadda suke faɗarta, furtata, jeranta kalmominta su gina jimlar da za ta fito da ma’anar da za a gane abin muradi ba da mamare ba. Ashe ke nan, nahawu shi ne fasalta abu dalla-dalla yadda za a kakkaɓe masa kowace irin ƙurar da za ta hana a fahimce shi. Burina a wannan ɗan bincike shi ne, fayyace ma’anar abin da ake cewa “magana” wadda ɗaliban nazarin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa za su yi madogara babba a kai. Haka kuma, ma’anar ta fito da sigogin da kowane Bahaushe ɗan asali zai kama ma’anar abubuwan da aka ƙwalailaice kai tsaye.


Sunayen Magana:
A nawa tunani, ina ganin zai fi dacewa mu fara bijiro da ire-iren sunayen da Bahaushe ke yi wa “magana” domin da an ji su, an san magana yake nufi. Bahaushe na yi wa magana suna da: magana, batu, zance, shirme, shiɓa, batutuwa, ɗumi, maganganu, sabbatu da sauransu. Bari mu ƙwalailaice su mu gani:
Magana: wadda ake furtawa a baki ko a yi nuni da wani abu da za a fahinci abin kai tsaye. Ga wata waƙa ta Tashe da yara suka fassara magana:
Jagora:        Ke magana ke!
          Wata magana ta wuce baki
Yara  :         Da ɗuwawu aka yin ta.

Batu  :         Yana ɗaukar wata magana ta musamman kamar zancen sharholiya in ji Narambaɗa.
 Gindi:        Gwarzon shamaki na malam toron giwa
          :         Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

Zance:        Magana ce musamman a fagen yin hira da wani ko wasu a faɗar Aƙilu Aliyu
Hana mata leƙa wajen matanka
Don kar tai musu zancen banza.
                             (Waƙar ‘Yar gagara).

Shirme: Maganar da ba ta da gaɓar kamawa. Ma’anarta ta ƙi fita
          sarari.
Ban gane abin da yake faɗa ba. Shirme kawai yake yi, ba ya da hankali.

Shiɓa: Maganar da ba ta kama hankalin kowa. A fassarar Kaftin
          Umaru Ɗa Suru ita ce.
Bakunansu sai warin taba
Me suke faɗa in ban da shiɓa.


Batutuwa: Jam’in “batu” ke nan, amma ana amfani da ita ga
maganar fitar hankali irin kirari kamar yadda Sambo Wali Giɗaɗawa ke cewa a waƙar Janborodo:

Da sunanka Alla za ni fara batutuwa
Tunawa da manya masu yaƙi  da garkuwa,
Fito-na-fito ka yi ta ba ta ƙidayuwa,
Yabon bajini ad dole don ba ya gasuwa,
Zaman ba a giwa da raskwana ba ya faruwa.

Jagora:        Ya watse batutuwa na Jekada ya taho gida
Yara  :         Kunya ga ta nan gare ku mutanen banza
Gindi :         Gwarzon shamaki na Malam toron giwa
          :         Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

Jagora:        Batutuwan da nikai don mahassada su ji haushi
Yara:           Waɗanga yanga da kara, wa ka rufa ma baki?
Gindi: Koma shirin daga gwarzon bahago ɗan Iro.

Dumi: A Sakkwatance idan an ce ɗumi ko ɗumumuwa ana danganta su da magana maras tushe ko ta banza.
Magangannu: Magana tilo ce jam’inta maganganu. Maganganu su ne zantukan fitan hankali na ruɗewa da raki da jin tsoro.
Sabbatu: Magana ce da ake yi cikin ɓatar hankali. Ga yadda Sambo Wali ya ruwaito ta:

Idan an ka ce ga Bube duk sai su raurawa,
Maza sai su zan mata suna ‘yan batutuwa
          Na saiɓi da sabbatu ƙafafunsu na rawa.
                   (Waƙar Janborodo).


Nauyin Magana:
A tunanin Bahaushe, cikin fashin baƙin nahawun magana akwai nauyin magana. A awon nauyinta, a wajen Bahaushe, akwai babba, akwai ƙaramar magana. Babbar magana ita ce ke buƙatar kulawar gaggawa da fuskanta gadan-gadan. Gaskiyar Bahaushe da yake da karin maganar: babbar magana ɗan sanda da ya ga gawar soja. Ita kuwa ƙaramar magana, ma’anarta na kai tsaye shi ne tsegumi ko tsince ko an-yi-an-ce. Ita ƙaramar magana tana da harshen damo. Takan kasance doguwar magana wadda sai an yi tonon silili da taliyo. Tana kuma zama gajeruwar magana kamar a ce, wanda ake bi bashi ya tabbatar da ana bin sa, kuma yana da abin biya, sai biya kawai, maganar ta zama gajera.

Sifofin Magana:
Duk da yake magana ba a ganin ta, jin ta ake yi, a wajen Bahaushe tana da sifa ko sifofi. A tunain Bahaushe akwai, Baƙar magana da maganar arziki. Duk wata magana da ba ta arziki ba, baƙar magana ce don haka idan aka yi masa ita yakan ce: “Barka da ta fito bakin mai ita ba ta kashe shi ba”. Bakar magana maganar jin haushi ce da takaici da jiyewa mai mugun zafi ga rayuwar wanda aka yi wa ita. Malamin kiɗi Narambaɗa na cewa:

Jagora:        Baƙar magana ba ɓaci ce ba
Yara  :         Amma ta ɗara, ɓaci zahi
Gindi :         Gogarman Tudu jikan Sanda
          :         Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.

Maganar arziki sananniya ce, irinta ce wadda Garugaru ya yi wa Kassu Zurmi yana cewa:
Jagora:        Maganar garugaru tai mani daɗi,
          :         Tamkar na dama zuma na sha.

A ganin Bahaushe, kowace magana mai daɗi maganar arziki ce, wadda duk ba ta da daɗi bakar magana ce.

Hukuncin Magana:
A al’adance, ana hukunta magana ta fuskar nahawun ma’anarta. Kai tsaye za a ce: Wannan maganar daidai ce, kure ce, gaskiya ce, ƙarya ce, ba’a ce, raki ce, saiɓi ce, ga su nan dai. A nahawun waɗannan zantukan za mu yi musu turke da waɗannan sassan adabi:


Daidai: Ɗan’anace na cewa:

Jagora:        Mai son miya ya auri tsohuwa
          :         Mai son shimfiɗa ya auri budurwa
          :         Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
                             (Waƙar Shago)

                   Wa zai ji wannan ya ce ba daidai ba ne.

Kure:          “Muna cikin tuwo muna cin zaure ko da an ka yi kura ga
walƙiya tsugunne”. Babu gaɓar da babu kure a wannan maganar.

Gaskiya:    Narambaɗa ya kawo bayaninta da yake cewa:

Jagora:        Na hore ki gaskiya bari tsoron ƙarya
Yara  :         Mai ƙarya munafuki Allah su yaƙ ƙi
          :         Har yau ba mu ga in da an ka yi mai ƙarya ba.
Jagora/Yara :         Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi
Gindi :         Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa,
          :         Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

Ba’a: Magana da za a yi don raha da nishaɗi, kowa ya ji ta ya san ba’a ce, ba da gaske ake ba. Tsawon hancin Bazaurar da Sani Ɗanbolɗo ya so ya aura ya ce:
Jagora: Ya kai mil goma misalin dogon hanci.
                             (Waƙar Zaura: Sani Ɗanbolɗo).

Idan hancin ya yi mil goma, yaya misalin tsawon ƙafa da hannu da faɗin kai da tsawon wuya? Wa zai gan ta ya tsaya zancen aure? Tun da cikin waƙa maganar ta fito Bahaushe zai ce: “Kai wannan mutum da ba’a yake”.
Raki: Magana ce da ake yi cikin tsananin sumalin zafin rauni ko wani bone da aka faɗa a ciki. Dubi yadda Bakwai ya yi da kunama ta harbe shi in ji Garba Maitandu Shinkafi:
Jagora:        Yay yi kwance yac ce: “Yo, na mace”
          :         Ku ba ni ruwa in mace ga sanyi ga maƙoshi
          :         Danginai sun ka ce: “Mun ɗaukai mu aza shi
          :         Nan ga jakinmu mu kai gida”
          :         Yac ce: “In kun aza ni, to ita wannan ƙafar
          :         Ina mai ɗauka muku”?
:         Ni kun san ba ni son tana reto
:         Ba ni son ta sha hantsi
:         Na hi son ku ruga ku biɗo gado
:         To kuma in na mace
:         Ku kaɗa ni cikin haki
:         Da kaina da ƙafafu da baina ciwo sukai
:         Kunama ta sa ni dumdumi Ala ebe mata,
:         Ni ko nac ce: Bakwai ka bar zagi
:         Tun da in kana zagi ba ta faɗuwa sai ciwo take
:         Bakwai yac ce: “Nai shiru rufa kat ta jiya
:         Tana cikin ɗaki ban kashe ba
:         Ka san in taj jiya kare in kai ma kiɗi.
Gindi :         Kunama zan wa kiɗi
          :         Zaman ciwo ag gare ta
          :         Ta halban na jiya

Waɗannan kalamai masu kama da na fitar hankali da aka yi saboda raɗaɗi da zagin ciwo su ake cewa “raki”. Duk wata magana irinta sunanta raki.
Saiɓi/Santi: Magana ce wadda ke fita a bakin wanda matsananciyar
yunwa ta kama, yana cikin juyayi aka gabato masa da abinci mai kyau mai daɗi irin wanda ransa ke so. An ce, wani Bafulatani ya sha furar shinkafa mai zuma a garin Maradun, yana cikin sha sai ya tuno da wani ɗan waƙa cikin waƙoƙin Shata ya ɗora hannu a kunne ya rera.

Ɗanfulani    : Kaka ta yi uban zimma
                   : Gyara ta fara zar fata!
Zamfarawa  : Haji Garban Bici yai damu.


Azancin Magana:
Fagen ƙididdige azancin magana nan sirrin nahawunta yake. Cikin azancinta za a ci karo da: Kairn Magana, Salon Magana, Kirari, Daɗin Baki, Waƙa, Zantukan hikima, da sauransu. A nan ce zuciyar nahawun magana yake, domin nan ne za a fito da nahawun azancinta duka.


Karin Magana:              
Zantukan hikima ne da aka gada kaka da kakanni. Jimla ce gajeruwa mai ɗauke da ma’ana mai faɗi:
Magana zarar bunu
Maganar duniya iyawa ce,
Magana ba taka ba bi ta da ihm!
Wata magana sarakuwa baki ce
Baki abin magana
Magana daga bakin wawa.


Salon Magana:
Maganganu ne na nuna ƙwarewa ga harshe da iya sarrafa shi.  Ga ɗan misali:
Da Kalla da abokin Kalla sun tafi kallon kalangu, sai aka kalle Kalla mari wajen kallon kalangu, sai aka ce wa abokin Kalla maza kalla gida da gudu ka gaya wa matar Kalla ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu. Ya kalla da gudu, ya kalla wa matar Kalla kira cewa, ga Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu. Ta kallo kara, da gudu domin ta kalla wa wanda ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu. Da ganin ta da kallallen kara ya kalla da gudu don kat ta kalla masa shi da ya kalla wa Kalla mari wajen kallon kalangu.
Kirari: Magana ce da aka tsara cikin tsayayyun kalmomi masu shiga zuci da kururuta wanda ake yi wa shi ko babu kiɗa ya tsimu. Ga yadda makaɗa Ɗan’anace ya koɗa Shago:

:         Kutuɓi abin aza wa ruhewa
:         Samji irin hakin da ka ramno
:         Burundumi abin zuba shara
:         Yaro hattaraka ga sababi nan
:         Ka da aradu ta farma
:         Halan dai ba ka san halin ƙanen ajali ba?
:         Laapirwaa! Akai miki gawwa!
:         Sanu da ɗibas sheɗa
:         Mutuwa ke daɗe kina kashe bayi
:         To, to, to!------

Duk Bahaushe ya ji saukan amon waɗannan kalmomi zai ce, an zuga Shago ko ya ce: “Wannan kirari ya yi”. Hawa da saukan kalmomin kirari ba irin na yabo ne ba ko roƙo ko waƙa. A ko’ina aka ji zugugutawa da cicciɓawa ta yi yawa za a ce kirari ne aka yi.
Zantuka Hikimomi/Waƙa/Daɗin Baki: Waɗannan duk nau’o’i ne na magana kuma duk sai sun bayyana a cikin waƙa za a ce, ta waƙu, ko ta yi daɗi. Azanci da hikima da daɗin baki su ne waƙa. wani mawaƙin tashe na cewa:

Jagora:        Sai dai a fi mu kalangu da kurkutu
Yara  :         Amma ba a fin mu daɗin baki,
Gindi :         Yau da borin goje,
          :         Kana da borin tashe.
                             (Ayya Mai Waƙar Tashe Taƙaji).

Maganar Zuci da Nahawunta:
Maganar zuci ita ce maganar da ke cikin ƙirjin mai ita, amma ta kasa ta bayyana saboda wani hali da aka shiga ciki ko wani yanayi da aka samu kai a ciki. Garba Ɗanwasa Gummi ya hikayo maganar zuci wurin da yake nuna bala’i ya kai ga sarki ya fito ba naɗi, a bar gari ba shiri, ba a san ina aka dosa ba. A cikin wannan hali ya ce:

Jagora:        Maigida bai kula mata ba
          :         Rannan ko da ana ɗumi sai maganar zuci.
Gindi :         Ya san ‘yan maza gudu ba da laɓewa ba…

Idan ana cikin wannan hali wasulan da ke sa a daidaita nahawun maganar zuci su ne: tsaki, nishi, kuwwa, ajiyar zuciya, kuka, dariya….

Sakamakon Nazari:
A tunanin Bahaushe ma’anar magana ya fi zare tsawo. Duk abin da baki ke furtawa a fahimce shi, ya zama magana. Hanyoyin da ake bi na nuna duk suna cikin nahawun magana amma maganar da ake furci da baki ita ce maganar da nahawunta ba ɓoye yake ba ga manazarta. A fagen nazari, matuƙar ana son a fayayce magana, kalmomin da ke cikinta, da yanayin da aka furta ta, da mai furucinta, ba su ne nahawunta ba. Nahawunta na nan cikin sunanta daga cikin ire-iren sunayenta da za ta ɗauka, da nauyinta a sikelin nahawun al’adar magana, da sifarta ga yadda ma’anar ta zai ɗauka, tilas a fayayce hukunce-hukuncen da za ta hau in ana son a yanke mata hukunci. Magana tana ƙunshe da azanci mai yawa, a nan za a yanke mata hukunci kasancewarta waƙa ko wata taska daga cikin taskokin adabin baka. Duk waɗannan abubuwa suna rataye ga maganar da aka furta, maganar da ba a furta ba, ita ce maganar zuci ‘yan rakiyata su ne tsaki, ƙyaci, nishi, kuka da sauransu. Yana da kyau kowace magana aka tunkara a bincike a san ina gurbinta.

Naɗewa:
Da gangan na yi wa takardata taken: “Nahawun Magana” domin na san kowace magana da muhallinta shi ne nahawunta kuma da shi za a yi mata hukunci. Ba a ɗauko zancen waƙa a salon kambamar zulaƙe a ce, ƙarya ce aka shara domin muhallin waƙa muhallin ba’a ne da raha. Da jin maganar Santi ba irin ta raki ba ce. Idan ɗalibin bincike zai ci karo da kowane irin magana a fagen nazari ya tabbata ya aza ta a kan gurbinta wanda shi ne nahawunta gabanin ya feɗe ta biri har wutsiya. Sanin nahawun magana shi zai sa mai magana ya lura da maganar da ake so da wadda ba a so. Kasawar sanin nahawun magana alamun taɓuwar hankali ce, in ji Malamin waƙa Narambaɗa, domin ya ce:
Jagora:        Kai magana an ce maka tsaya
          :         Ka sake an ce maka bari
Yara:           Kai magana ka san ba a son ta
J/Y    :         Ka ƙi bari waz zan mahaukaci?
Gindi: Ya ci maza ya kwan yana shire
          :         Gamda’anan sarkin Tudu Alu.






MANAZARTA

Bunza, Aliyu Muhammad, 2002. Yaƙi da Rashin Tarbiya, Lalacignnb nb ,
Cin Hanci da Karɓar Rashawa cikin Waƙoƙin Sambo Wali Basakkwace, Lagos: Ibrash Publishers.

Bunza, Aliyu Muhammad, 2002. Narambaɗa, Lagos: Ibrash Islamic
          Publicaiton Centre.

Bunza, Aliyu Muhammad, 2017. “Raaki a Tunanin Bahaushe”,
Takardar da aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Gusau: Jami’ar Tarayya.

Furniss, Graham, 1996. Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa,
London: Edinburgh University Press, for International Africna Institute.

Gusau, Sa’idu Muhammad. 2009. Diwanin Waƙoƙin Baka:
Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Kano: century Research and Publishing Limited.

Mukhtar, Isa. 1984. “Nahawun Waƙa”, Kundin MA, Kano, Jami;ar
          Bayero.

Shinkafi Rabi’u Hassan. 2001. “Garba Maitandu da Waƙoƙinsa”.
          Kundin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yahaya, Ibrahim Yaro. 1988. Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-
          Rubuce Cikin Harshen Hausa, Zariya: NNPC.

Post a Comment

0 Comments