https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Sauraro Da Rubutawa


Hirabri Shehu Sakkwato


08143533314


https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: In mutum zai shiga fati,

Ya zauna ya yi lassafi×2

Ya duba shi da kyau,

Yara:    Ya gane wa nad’ d’auko shi.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ga d’an asali,

Da shi da D’anmasanin Sakkwato,

Ga Azzika Tambuwal da Tambari na Tafida,

Ga Modi na Yabo Maigida babban jigo,

Wanda yac ce bai son ku babu shakka wawa ne,

Yara:    Ko a Sakkwato birni wad’anga su ne am manya.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

 

 

Jagora: Na yi mamakin wane,

Don siyasa ta hurce,

Shi muddin yag ga nan,

Ya canza man huska,

Ga siyasa ta dawo,

Ga mu mu ku mun dawo,

An ce a had’e,

Ba mu buk’ata ‘Danba’u,

kowa ya tsaya wutinsa

A buga a gani,

Yara:    A gane wa zai rinjaye.

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: ‘Yan siyasa ku yi hank’uri da Musa ‘Danba’u,

Kun san ku nawa ne,

Sannan ni naku ne,

Ko da kun k’i ni mai kamata kuka so,

In kuka k’i ni da d’a,

Yara:     Kun ganan da jika na goya.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Dubara batutuki dubara banza ce,

Yara:    Ya kiraye ruwa kuma mun ga alamar sun ci shi.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ko cikin mata,

Wance ‘yar jidalin mata ce,

Kullun habshi takai,

Kamar karya zango,

Yara:   An yi an k’are ke bakin jidali ya hwarma,

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ku ‘yan mata,

Akwai jawabi wajanku,

Dud da macce ka kwakwa,

Ba za ta samun aure ba,

Yara:   Sai a gan ta ga titi tana ta yawon iskanci.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Wanda duk ke kwakwa,

Ba mutumen kirki ne ba,

Yara:    Daga d’an k’waya sai d’an dara sai ko d’an daga.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Wanda duk ke APP,

Ba mutumen kirki ne ba,

Yara:    Daga d’an k’waya sai d’an dara sai ko d’an daga.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

https://www.amsoshi.com/2018/01/15/wakar-jamiyar-dpn-ta-alhaji-musa-danbau-gidan-buwai/

Jagora: Babu mai cin bashi,

Cikin siyasar PDP,

In kana son ka shigo,

Cikin siyasar PDP,

Ka biya bashin banki,

Ka je mu je tare da kai,

Kar tafiya ta yi nisa,

Yara:    Ka je ka goga man la’bo.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ga d’an’asali,

Uban su Nasiru Dattijo,

Harsashe kai ka maganin,

Mai taurin kai,

Yara:   Baba alk’awali na,

Da ni da kai kyautar mota.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Alhaji Hadi ciyaman,

Hadi D’anmalan,

Yara:   Na sarkin bak’i,

Ka kashe kwakwa wajenmu.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ashe wane barazanarka,

Aikin banza ce,

Ba ya da kowa,

Garinsu ko ran shi d’ai ne,

Yara:   Mun ji labarin ko gidansu,

An ce ya sai da.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Rak’umi na tafiya,

D’auke da kayanai,

Ya isko kunama yat taka,

Naj ji ya buga rura,

K’asa akwai shaggu,

‘Yar abig ga ‘yar tcito,

Ga shi yanzu ta halban,

Yara:    Har na gaza d’aukar kayan nan.

 

Amshi: Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP.

 

Jagora: Ga wani d’an takara da doro,

Abu dai zuk’wi-zuk’wi,

Ke kuma bushiya ki ‘boye doronki,

Yara:    Ba ki bakin komai,

Wurin hwarauta banza ce.

 

Jagora: Na ga baki bakin komai,

Yara:   Wurin gwarauta banza ce.

 

Jagora: Maigida Modi na Yabo,

Maikid’a ya gode ma,

Yara:   Ban rena mai ba,

Tun da hairan yab ba mu.

 

Jagora: Bana Duna bak’in kare Dubara ta k’are,

Kai dare d’auke k’afarka,

Na ga gungun ‘yan yara,

Yara/Jagora:   Kar su ‘bata ma tsari.

 

Jagora: Mutane na tcegumi,

Suna mamakin shigar da ni yi a PDP,

Yanzu ba mamaki tunda akwai babba huja,

Yara:    Wanda bai ra’ayi na ba ni buk’atar kayansa.