Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Jam’iyyar PDP 2 Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.
 

Jagora: Ya Allah na kwan rok’on ka,

Allah ya gwada muna ran za’be,

An k’irga PDP ta ci,

Yara:   Amin, amin Haji ‘Danba’u,

Wannan magana babu kuskure.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: In Allah ya so ya yarda,

Mu za mu yi winin Nijeriya,

Lokal gammon da siteg gammon,

Yara:   Mu ke winin had da federal.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: Manufar fatinmu na PDP,

Mutunci fawa da walwala,

Ka yi yanda kake so Nijeriya,

Yara:    Ban san wani mai takura ka ba.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

 

Jagora: Kai ji wane yai tahiyar kura,

Yana gaba ya koma baya,

Inda ya nuhwa ba a kar’bai ba,

Ya dawo bai ishe kowa ba,

Yay yi shiw ya rik’e baki,

Nac ce duk mai koraj jama’a,

Yara:   Sai ya bid’i mai ba shi shawa.

https://www.amsoshi.com/2018/01/15/wakar-yusuf-musa-illela-ta-alhaji-musa-danbau-gidan-buwai/

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

Jagora: Ku ji kyanwa mai saurin tahiya,

K’ark’arin takai ta ci kihi,

Dur rad da k’aya tal lak’e miki,

Yau kowa bai tagaza miki,

Sai dai ki mace ‘yar damtcen uwa,

Yara:    Don mu kula ‘barnarki tai yawa.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: Mai k’ark’arin hawan iccen kwakwa,

Idan ka hwad’o kak’ k’alle,

Kai ciki dubu nika tona ka,

Yara:   Bak’ar magana wad da kai muna.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: Haji Modi na Yabo a gaishe ka,

Zaki mai k’arhin mutum dubu,

Ka gama da ‘yan kwakwa baya,

Yanzu kwakwa ba ta da tasiri,

Yara:   Sai dai su yi bammi su sha giya.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: kowa ke zagin Shagari,

Da Iro Gusau d’an Muhammadu,

Wannan k’arshe nai jin kunya,

Yara:   Don sai an gyara mishi zama,

Ya tabbata ba zarumi ba ne.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: in dai Allah ya yi abinai,

Kowa ya tsaya sai dai kallo,

Zubairu S. Magori a gaisheka,

 

Jagora/Yara:  Ga allura mai shiga jiki,

Gaishe ka ni kai d’an Attahiru.

 

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: Rak’umin Gwadabawa ya wahala,

Don ya d’au kaya mai nauyi,

Yara:   Ya hwara zuhwa har ga kunnuwa.

Jagora: General Ibrahim Babangida,

Lokacin da ka rik’a Nijeriya,

Wanda bai da mota yai mota,

Wanda bai da kud’i yai kud’d’i,

Talakawa duk sun gode,

Yara:   Wannan magana zahiri take.

https://www.amsoshi.com/2018/01/12/na-tinkari-tsautsayi-da-shirin-yaki-tawakkali-ta-tsai-da-ni/

Amshi: PDP hasken Nijeriya,

Fati mai k’arhi da martaba.

 

Jagora: Wada waziri mai komi dozin,

Wada waziri birnin D’anbatta,

Wada waziri baban soja,

Ka yi zarumi ko birni wa,

Har na ji mutane suna hwadin

Yara:   Ka zam hitila maganin dugu.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Post a Comment

0 Comments