Nazarin Zaman Gandu A Garin Zazzau (3)

     Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

    NA

    SHEHU MUHAMMAD TAFIDA

    BABI BIYU: Ma’anar Tubulan Bincike da Gabatr da Tushen Bicike

    2.0 SHIMFI’DA


    A wannan babin an yi k’ok’arin kawo yadda masana suka bayyana ma’anar kalmomin gandu da zama don fito da aikin fili, ta yadda za a fahimce shi da kyau. Aikin ya nuna yadda zamantakewar Bahaushe take tare da iyalansa. Sannan an kawo bayanin yadda zaman Bahaushe yake a gargajiyance da kuma irin yadda zamansa a zamanance yake. An yi hakan ne domin fito da tsari da yanayin zamantakewar Bahaushe a k’asar Hausa, musamman ma a garin Zazzau. A k’arshen babin an nad’e shi ne da tak’aita bayanin abin da aka tattauna a cikinsa.

    2.1 MA’ANAR ZAMA


    Masana sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar kalmar Zama, misali :

    Bargery (1937), ya bayyana ma’anar zama da cewa: “kishiya ce ta tsayuwa wadda ta samo asali daga aikatau. Wato a zaune a k’asa ko a wani abu”.

    Skinner (1959), ya ce: “zama na nufin sharad’i ko gwamnati ko yankin k’asa ko kuma girma duk hali ne na zama”.

    K’amusun Bayero (2006), an bayyana ma’anar zama da cewa: “kasancewa magana ta gaskiya, ko kasancewa a zaune kishiyar tsayuwa, ko kuma zama mai wayo”.

    Idan aka yi la’akari da ra’ayoyin masana da suka bayar dangane da ma’anar zama, za a iya cewa zama na nufin hawa kan wani abu don hutawa, ko yarjejeniya ta kusantuwa tare, don taimakon juna ta fuskar rayuwa. Ana amfani da kalmar zama a muhalli daban-daban. Misali:

    Zama da mad’aukin kanwa

    Zama da kishiya sai dole

    Zama wuri d’aya tsautsayi inji kifi

    Zama lafiya ya fi zama d’an-sarki

    Duk wad’annan jimlolin na adon harshe ne, da ake amfani da kalmar zama. Amma wannan aikin zai yi amfani da kalmar zama ne ta fuskar tsarin rayuwar iyali. Wato zaman gandu kafin a warware zancen sai an kawo ma’anar mahad’in Kalmar ta zama a wannan binciken wato gandu, domin fito da bayaninsu fili.

    2.2 MA’ANAR GANDU


    Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da kalmar gandu misali:
    Bargery. (1937), ya bayyana ma’anar gandu da cewa: “Iyalai ne  da ke k’ark’ashin jagorancin maigida da ke ciyar da wad’annan iyalan”.

    Skinner (1959), ya bayyana tasa ma’anar da cewa: “k’asa ko kud’i da ke k’ark’ashin kulawar gwamnati, ko gonar da iyalai ke noma abin da za su rayu a kansa”.

    K’amusan Bayero (2006), an bayyana kalmar gandu da cewa: “babbar gona ta sarki, ko ta wani babban gida”.

    Bunza (2012), cikin laccar darasin aji hud’u na digirin farko mai taken; ALH 402 ya ce: “Gandu ta samo asali ne daga bayi masu yi ma sarki bauta, k’ark’ashin kulawar sarki. Sarkin ne ke samun tafkekiyar gona wad’annan bayin na yi masa noma a cikinta”.

    Mawak’an baka na Hausa su ma sun tofa albarkacin bakinsu, dangane da kalmar gandu. Misali inda Haruna Uji ke cewa:

    Ni Haruna Uji mai wak’a,

    A Kano sitet aka yi ni,

    A Had’eja a gandun Sarki….

    A nan Haruna Uji ya tabbatar da cewa babbar gonar sarki ana kiranta da gandu.  Masana sun yi namijin k’ok’ari wajen bayyana ma’anar gandu. Domin kowa ya ba da ma’anarsa daidai da da fahimtarsa da ya yi wa kalmar ta gandu. Daga ma’anar tasu duk da cewa a dunk’ule take, ana iya warwareta kamar haka:

    Gandu na nufin duk wata dukiya ko kadara ko jama’a (iyali na Zuriya), da suke k’ark’ashin kulawar mutum d’aya a matsayin jagoransu. Musamman mazauna k’asa d’aya ko gari ko unguwa ko gida. Wad’anda tsarin rayuwarsu ta yarda da a tafi tare bisa biyayya da d’a’a da ladabi ga jagoransu.

    A nan idan aka dubi kalmomin zama da gandu ana iya cewa: zaman gandu shi ne zaman tare na zuriya ko al’umma da suke k’ark’ashin jagorancin mutum d’aya, a matsayin shugabansu da ke kula da lafiyarsu gaba d’aya.

    2.3 ZAMANTAKEWAR BAHAUSHE DA IYALANSA


    Al’ummar Hausawa, al’umma ce da ta kafu bisa tsararriyar al’ada ta kula da zuriyarta. Kama tun daga zamantakewar ta iyali da mak’wabtaka da sana’a da abokantaka da sauran al’amurran rayuwar yau da kullun, duk a tsare suke bisa wasu k’a’idoji da al’umma ta tanada.

    Bahaushiyar al’ada ta tanadi yadda ya kamata a gudanar da zamantakewar aure da na shugabanci a rayuwar al’ummar Hausawa. A zamantakewar aure wadda aka fi sani da zamantakewar iyali, Bahaushe ya tanadi wani tsari mai ban sha’awa, wanda maigida yake jagorantar zuriyarsa.

    Amma abin da ya kamata a kula da shi a zamantakewar iyalan Bahaushe shi ne, jagoranci wanda a mafi yawancin lokuta ana saman jagoranci ne daga gida, zuwa gari baki-d’aya. A wani lokaci zuriyar da  ta fi kyakkyawar d’abi’a, wato wadda ta fi kula da tarbiyar zuriyarta ita ta fi kowace zuriya d’aukaka ga al’ummar Hausawa.

    Lokacin da addinin musulunci ya sami al’ummar Hausawa, ya same su ne cikin kyakkyawar al’ada, wadda ta taimaka wajen inganta halin Bahaushe na addinin musulumci.

    Zamantakewar iyali ga Bahaushe tana da tsari kamar haka:

    Maigida  (kaka)

    ‘Ya‘ya (Iyaye)

    Jikoki (‘Ya‘ya)

    Tatta’ba kunne (Jikoki)

    Maigida shi ne tushen zuriya kuma shi yake kula da tarbiyar gida tare da yanke hukunci kan duk wanda ya sa’ba dokokin da zuriyar ta ginu a kansu. Wasu lokuta sai ‘ya’ya (Iyaye) sun taimaka masa idan zuriyar ta yawaita. Domin ba zai iya gane wasu bak’in abubuwa da suka shigo cikin gida ko zariyarsa ba, sai da taimakawar sauran ‘ya’yansa da suka kai matsayin magidanta. Akwai yanayin rayuwar zamantakewar Bahaushe iri biyu kamar yadda za’a gani a kaso na gaba.

     

    2.4 ZAMANTAKEWAR GARGAJIYA


    Zamantakewar Hausawa na gargajiya, ingantacciyar rayuwa ce mai d’auke da ban sha’awa. Bahaushen da ya rik’i wad’ansu abubuwa muhimmai wad’anda su ne gishirin rayuwa, wad’annan abubuwa kuwa su ke sa a sami iyali na gari. Wannan ne ya sa Bahaushe yin takatsantsan wajen aure, da tattali don gudun kada ya  shiga tsaka mai wuya. Wannan ne ya sa shi kula wa da harkar iyalinsa da kuma addininsa da sauran al’amuran zamantakewa.

    A zamantakewar Bahaushe da ya gabata an san Bahaushe da jaruntaka da d’a’a da gaskiya da rik’on amana da zumunci da hak’uri a duk wani halin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki. Bisa ga wad’annan dalilan, Sauran al’ummun da Bahaushe ke gudanar da mu’amalarsa da su, suke ganinsa da kima da mutunci. A da al,ummar Hausawa na gudanar da Zamantakewar su ne a manya-manyan gidaje da ke karkara mai d’auke da tsarin  unguwanni, Tsarin mulki irin na sarakuna da masu unguwani, wannan tsari na da muhimmanci, domin idan wani abu ya faru mai unguwa kan sa a sanar da jama’a ta hanyar yin shela. Al’ummar Hausawa an san su da gudanar da ayyuka    n da za su kawo ci gabansu da garuruwansu.  Bahaushe yana da wani tsari na aikin gayya, wannan aikin gayya  yana da matakan da ake gudanar da shi tun  daga gida. Ana gudanar da shi ne bisa matakai kamar haka; aikin gayya na gida (zuriya),

    A wannan matakin   ana had’uwa domin a gudanar da aikin gayya kan aikin gona, inda ake yi wa ‘yan’uwan da shekarunsu suka yi nisa ko surukai. Haka kuma abokai kan hud’u su yi wa wani abokinsu da ya sami wata matsala ta rayuwa aikin gayya.

    Aikin gayya na gajri a yayin aikin gayya na gari, magidanta da matasa, kan had’u su gudanar da aikin gayya irin na gyaran hanya a lokacin da ruwa ya ja baya, da bud’e magudanun ruwa don gudun toshewa, su haifar da rugujewar gidajen jama’a.

    2.5 ZAMANTAKEWAR ZAMANI


    Domin samin yanayin zamantakewar Hausawa na zamani ya kamata a d’an yi tsokaci a kan zamantakewar gargajiya. Al’ummar Hausawa ba a zaune suke kara zube ba. A gaskiya ko da addinin musulunci ya iso k’asar Hausa ya tarar da Hausawa a zaune cikin tsari da ingantattun al’adunsu na auratayya da zumunta da sauran nau’o’in zaman tare. Da yawa daga cikin wad’annan al’adu, sun yi shimfid’a ta fuskar zaman tare. Misali: Da ma can Bahaushe bai aminta da ya auri mace d’aya tal ba, kana iya samun mutum d’aya yana da mata hud’u zuwa tara, dai-dai yadda mutum yake da hali. Da addinin musulunci ya zo sai fad’uwa ta yi dai-dai da zama da Saboda irin dammar da ya samu ta Bahaushe damar auren mata hud’u idan yana da hali.

    Hausawa sun sami addinin musulinci ne sakamakon shigowar bak’in Larabawa ‘yan kasuwa, wannan ne ya sa Hausawa rabauta da ilimin karatu da rubutu bisa harufan larabci Da zamani ya zo da shi. Sai da aka sami zamani mai tsawo sai aka sami masu jihadi, Bayan bak’in Larabawa sai bak’in Turawa ‘yan mulkin mallaka da suka kawo ilimin karatu da rubutu irin nasu da ake kira ’’ Boko’’.

    Ana iya cewa tun daga had’uwar Hausawa da bak’in Larabawa yanayin zamantakewar Hausawa ta fara sauyawa sakamakon kar’bar addinin musulunci da Hausawa suka yi. To amma irin ci gaban da Turawa suka zo da shi ya sha bamban da na Larabawa domin ya bar baya da k’ura, in ana biye za a ji ko wace irin k’ura ce.

    Tun kafin zuwan bak’in Turawa ‘yan mulkin mallaka Hausawa na gudanar da wasu lalurorin rayuwa. Irin su:

    Mulki

    Shari’a

    Tattalin Arziki

    2.5.1 MULKI


    Mulki ne kad’ai zai tabbatar da zaman lafiya yadda kowa zai sami damar yin harkokinsa na rayuwa domin neman abinci da arzikin duniya. Wato dai, idan babu mulki a al’umma to rud’ani da cutar juna za su tabbata. Kafin zuwan Turawa k’asar Hausa, Hausawa ne ke mulkin k’asarsu. Wannan ne ya tabbatar da bin umarni da zaman lafiya da kwanciyar hankali da al’ummar Hausawa suke ciki. Duk da cewa sun yi fama da yke-yake da juna tsakanin wannandaula ‘yar’uwarta.masu jihadi su suka kawar da wannan zamantakewa. Inda ska shimfid’a mulki irin na musulunci. Bayan shekaru sai Turawa suka shigo. Zuwan Turawa sai suka k’wace mulkin a fakaice, ake mulkin amma cikin tsarin da suka bar mana.

    2.5.2 SHARI’A


    Tun kafin zuwan Turawa k’asar Hausa, Hausawa na amfani da Shari’ar musulunci. Wannan tsarin shari’ar cikin larabci yake wanda ba kowa ya iya ba balle ya fahimta. Sai dai an samar da hukunce-hukunce a cikin tsarin rubutun ajami na Hausa.  Ko da Bature ya zo shi ma dai bata sake zani ba domin shima ya maisheta ne cikin harshensa wato Turanci, bisa tsarinsa.

    2.5.3 TATTALIN ARZIKI


    Duk da cewa Hausawa sun nak’alci iya ciniki, to amma zuwan Turawa ya kawo wani sabon salo dangane da tattalin arziki. Da yake babu k’asar da za ta dogara da kanta kawai, dole sai ta yi huld’a da mu’amala da wata k’asarta hanyar gudanar da mu’amalar cinikayya stakaninsu. ta bud’e, musamman da wad’anda suka ci gaba. Yin hakan sai ya jawo neman hanyar da za a gudanar da ma’amala. Wato wane harshe ya kamata a gudanar da cinikayyar.

    Rashin sanin sirrin tattalin arziki irin na zamani yana da illa, amma dole a rungume shi. Domin kafin ‘yan-k’asa su farga sai da Turawa suka yi abin da suka ga dama da ma’adanen k’asar Hausa. sannan suka ce sun ba  da  ‘yanci bisa ga tsarin mulkin da suka tsara, irin na zamani. Bayan ‘bangaren mulki da shari’a da tattalin arziki, da zamani ya yi wa sauyi akwai wasu muhimmman ‘bangarori kamar:

    Harshe

    Al’ada

    2.5.4 HARSHE


    Harshe dai wata muhimmiyar kafa ce ta sadarwa da d’an’Adam ke tink’aho da ita. Hasali ma ita ta raba mutum da dabba. Domin da harshe ake neman illimi, da harshe ake mulki, da harshe ake shari’a, da harshe ake kasuwanci. Sannan da harshe ake aiwatar da addini da sauran mu’amalar rayuwa.

    Harshe na d’aya daga cikin abinda ke sa a  bambance al’ummomi da daman a duniya. Amma sakamakon zamantakewar zamani yasa harshen Hausa na fuskantar barazana daga harshen Ingilishi. Duk inda ka je sai ka ji ana amfani da harshen Ingilishi mai makon harshen gida wato Hausa. Irin wannan ba zai haifar mana da d’a mai ido ba, sai mun koma yin amfani da harshen gida wato Hausa a gidaje da makarantu da wuraren sana’o’inmu da sauran al’amura, maimakon harshen da zamani ya zo da shi wato Ingilishi.

    2.5.5 AL’ADA


    Al’ada na nufin k’ololuwar tunani da fasaha ta sarrafa abubuwan da aka gada ka ka da kakanni ko aka aro daga wad’anda suka gada aka gadance ta ko wanda aka k’irk’iro ta yi daidai da rayuwar masu amfani da ita.

    Hausawa sun Sami abubuwan ci gaba na rayuwa da zamani ya kawo, kamar tufafi da abinci, da sana’o’i da yanayin mu’amala na jama’a, da ma wad’anda zamani ya maye gurbinsu da wasu. Misali:

             Gargajiya                     Zamani                          Ingilishi


    Akushi                          Kwano                             Pan

    K’oshiya                       Cokali                              Spoon

    Taguwa                       Shet                                    Shirt

    Taga                            Window                            Window

    Fad’e                              Silifas                                      Sleppers

    Adiko                           ‘Dankwali                         Headtirel

    Zamani ya yi hani da wasu al’adu da ya tarar ana aiwatar da su kamar

    Bori

    Shan giya

    Bautar wani abu da ba Allah ba

    Tsafin kan-gida

    Auren mata fiye da hud’u

    Hani da cin wasu nau’o’in abinci

    Hani da aikata zalunci

    Duk irin wad’annan addinin musulunci ya yi hani da su da ma sauran wasu abubuwa da ba a kawo su ciki ba. Sai had’uwar Hausawa da Turawa. Haduwar Hausawa da Turawa ne Hausawa suka sami ilimin karatu da rubutu irin na Boko, domin ko da Turawa suka zo k’asar Hausa basu sami Hausawa cikin jahilci da duhun kai ba. Sun same su da ilimin karatu da rubutu wanda ake yi da haruffa irin na larabci wato ’‘ Ajami’’.

    Sai dai bayan ilimin karatu da rubutu irin na Boko da Hausawa suka samu a sanadiyar bak’in Turawa ‘yan mulkin mallaka akwai fannin fasahar k’ere-k’ere kamar su:

    Keke

    Babur

    Mota

    Jirgin k’asa

    Jirgin ruwa

    Jirgin sama

    Rediyo

    Telebijin

    Ba a nan abin ya tsaya ba, zamani ya ta’ba har wasanni da aka sani na Hausawa kamar su, Tatsuniya aka maye su littafan soyayya, wasannin dandali aka maye su da finafinai, wak’e-wak’en gargajiya aka maye su da na zamani, magungunan gargajiya aka maye su da k’wayoyi na zamani. A gaskiya ana iya cewa Bahaushe ya samu ci gaba wanda zamani ya zo da shi.

    2.5.6 MUHALLI


    Hausawa kamar sauran al’ummomi duniya suke. Kowa ce al’umma tana farawa ne daga karkara. Irin wannan zamantakewar ana fara ta ne da d’aid’aikun mutane, idan aka yi aure aka hayayyafa daga nan sai a sami rukunin jama’a da ake aiwatar da wannan zamantakewar tare da su. Za ka iske muhallin da ake gudanar da wannan zamantakewar cike da ‘ya’ya da jikoki da suaran dangi na jini da ma wanda ba na jini ba k’ark’ashin kulawar maigida guda. Irin wannan ya ta’allak’a ne da yanayin yawan zuri’ar gida ko al’ummar.

    Amma komai rashin k’arfin mutum ba za a rasa shi da dangi da suke zaune a muhallin nasa ba.domimin taimakon juna ta fuskar rayuwa ba. Sannu a hankali yanayin mahillin Hausawa ya sauya sakamakon huld’a da bak’i musamman Turawa, da suka fito mana da tsari irin na su ta ‘bangaren zamantakewa. Akwai nau’o’in unguwanni da Turawa suka k’irk’kira don yanayin zamantakewar muhalli da aka fi sani da (G.R.A), wato rukunin gidajen Turawa da kuma (LOKOST), rukunin gidaje masu sauk’in biya da kuma (KWATAS), rukunin gidajen ma’aikata. Sai kuma rukunin gidajen haya, wanda duk su suka zo mana da su.

    Idan ba a mance  ba  a baya an ce zamantakewar zamani ya bar baya da k’ura. Wannan k’ura kuwa ita ce ta shiga cikin al’adu da ‘babi’un Hausawa na zamantakewa ya yi kaca-kaca da ita, musamman ma zamantakewar gandu. Tunda Hausawa suka koma yin zamantakewa irin na bak’in Turawa wato daga kai sai ‘ya’yanka. Wato dai kowa tashi ta fissheshi. Wanda yasa martabar da aka san Bahaushe da ita da kima ta dushe, sakamakon ararriyar al’adar da ya d’auka.

     

    2.6 NA’DEWA


    Cikin tak’aitattun bayanan da suka zo a sama an bayyana ma’anar zama kamar yadda masana suka kalli ita kalmar inda suka ce zama na  nufin hawa kan wani abu don hutawa, ko yarjejeniya ta kusantuwa tare don taimakon juna ta fuskar rayuwa. Kalmar gandu kuwa na nufin dukiya ko k’adara ko jama’a (Iyali na zuriya) da ke k’ark’ashin kulawar mutun d’aya a matsayin jagora.

    An kawo yanayin zamantakewar Bahaushe na gargajiya inda aka nuna yana da jaruntaka, da d’a’a, da gaskiya, da rik’on amana, da zumunci, da hak’uri a duk wani halin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki. Daga k’arshe aka kawo yanayin zamantakewar zamani, inda aka nuna ya fara ne sanadiyar shigowar bak’in Larabawa da Turawa da suka yi mana sauye-sauye a yanayin zamantakewa da sauran mu’amalolin rayuwa. Da k’arshe aka nad’e babin da tak’aita bayanin abin da aka tattauna a kansa.

     

     

     

    https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

     

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.