Kundin Neman Digirin Farko (B.A. Hausa) Da Aka Gabatar A Sashen Harsunan Nijeriya Tsangayar Fasaha Da Ilimin Addinin Musuluncin Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
NA
IBRAHIM HAMISU YUSUF
BABI NA BIYU
AZUZUWAN KALMOMI A TASKAR MASANA NAHAWU
2.0 Shimfiɗa
Aƙalla akwai fannoni guda biyar manya da a ke nazari game da nahawun
harshe (grammar). Waɗanda suka ƙunshi; Nazarin gundarin sauti (Phonetics)
da nazari akan fannin tsarin ilimin furuci (Phonology) da nazarin ginin
kalma (Morphology) da nazarin ginin jumla (Syntax), sai kuma nazarin fannin
ilimin ma’ana (Semantics). A fahinta ta zamani (Radford, 1981), nazarin a kan
nahawun kowane harshe ba ya kammaluwa sai ya ƙunshi nazarin tsararre a kan waɗannan
fannoni.
An daɗe a na gudanar da bincike da nazarce-nazarce kan nahawun Hausa, amma duk
da haka a kullum ba a rasa samun waɗansu matsaloli na fahinta waɗanda kan
tilasta yin sabon nazarin mai ƙyau bisa tsari na zamani. A wannan bincike zai
nazarci hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, wanda ya ƙunshi, sanin azuzuwan
kalmomi, da fasalinsu. Sannan a nuna yadda suke kasancewa a cikin jumla, da
guraben da ya kamata kowanne ajin kalma ya zauna a cikin jumla. Za a
bayyana yadda doƙoƙin ginin jumla suke tare da gabatar da fasalin nazarin
jumla, sannan a kawo yadda tsarin bishiyar li’irabin nahawu take a harshen
Hausa.
Ilimin ginin jumla fannin ne da a ke bin doƙokin nahawun harshe domin amfani da
azuzuwan kalmomi (word clases ) a matsayin tubalan da za a yi amfani da su a
jeranta su domin a gina zance bisa ƙa’idar nahawu. A wannan fannin ne ake
bayanin yadda ake sarrafa kalmomi a haɗa su da juna don su samar da jumla
gamsasshiyar.
2.1 WAIWAYEN AZUZUWAN KALMOMIN NA HARSHEN HAUSA
Azuzuwan kalmomi su ne mahimman tubalan da a ke harhaɗawa ɗon gudanar da
nazarin jumloli. Kusan kowanne ajin kalma ya na da nasa muhalli a fagen tsarin
nazarin jumla. Wato abin nufi a nan shi ne, kowanne ajin kalma ya na cin gashin
kansa ne a fannin nazarin ginin jumla.
Bisa la’aƙari da lokaci mai yawa da a ke yin nazarin kashi-kashi, a na kuma ba
kowa ni gida nasa rabon na suna. Akwai ajin sunaye (Nouns) da ajin aikatau
(verbs) da ajin sifa (adjectives) da ajin bayyanau (adverbs). Da makamantansu.
Masana da dama sun ba da tasu gudunmawa wajen fito da yadda azuzuwan
kalmomin suke gida-gida abin lura a nan shi ne masana suna da tsari na musamman
da suke bi na ba da sunaye ga azuzuwan kalmomi. An yi wani zamani a farko inda
aka rika tilastawa harsuna su bi tsarin rabe-raben kalomomi na wani harshe
wanda a ka yi lokacin da harshen latin, (greek), ya gawurta hartakai shi ne
ma’aunin ga sauran harsunan turai wajen raba kalmominsu. Abin nufi shi ne duk
ajin kalma da latin ke da shi, to tilas ne a ce harshen Ingilishi da Faransanci
da Jamusanci suna da wannan aji. Ko ba shi, sai an ƙirƙiro shi!
Rabe-raben kalmomin wannan wani tsari ne da masana ilimin kimiyyar harshe na
zamani (Moden Linguistics) wannan fannin ya ba da dama ƙwarai, ya kuma karfafa
gudanar da bincike mai cin gashin kai na kowane harshe. Masana sun lura cewa ta
hanyar bincikar kowane harshe shi kaɗai, za a gano arzikin harshen dangane da
ire-iren kalmominsa da kuma kebabben tsarinsa nahawun. Masana irin su Chomsky,
sun bayar da guɗunmawa sosai wajen sake fahimtar yanayin tsarin harshe da kuma
kawo hanya mafi dacewa ta aiwatar da nazarin nahawun harshe. Alal misali;
Chomsky ya na nuna cewa akwai wani na bai ɗaya da yake boye a halin yanzu na
tsarin nahawun harshen ɗuniya baki ɗayansu (Universal Grammar). Ya nuna cewa
wata rana za a cimmma wannan tsari na bai ɗaya. Ya ce, to hanya mafi dacewa ta
kaiwa ga wannan gali, ita ce ta yin nazarin zuzzurfa a kebance na tsarin
nahawun kowane harshe, sannan daga baya a tace abubuwan masu kama da juna, ya
ce su ne gagama-gari (Universal), waɗanda suka kasa shiga cikin wannan rukkuni
na ‘yan gama-gari, to sai a jiye su a mala, har sai ilimi ya ƙaru, wanda zai
bada dama a sasu a wannan ajin na ‘yan gama-gari.
Bisa la’aƙari da ajin kalmomi (Lexical Categories). Chomsky (1986:p2) ya
bayyana cewa ana iya raba dukkan kalmomin harshe gida hudu bisa wata daraja mai
baki biyu, wato kasancewa (+) ko rashin kasancewa (-). Ga yadda yayi rabon.
1.
suna (S) = D+S, -Ax
2.
Aikatau (A) = D+A, - Sx
iii. sifa (SF) = D+S, + Ax
1.
Harafi (H) = D.S, - Ax
abin nufi a nan shi ne suna, suna ne (+S) ba shi da alaƙa da aikatau
(-A). Aikatau, aikatau ne (+A) kuma ba da alaƙa da suna (-S), sifa ta
shafi suna (+S) ta kuma shafi aikatau (+A), harafi bai shafi suna ba (-S), haka
kuma bai shafi aikatau ba (-A).
Bayan haka Amfani, 1996. A cikin maƙarlar daya gabata sashen harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato ya bayyana rabe-raben kalmomin Hausa, bayan
haka ya bayyana rukunin mutanen farko da suka yi aikin raba
kalmomin. Abney (1987:P62) ya ƙalubalanci rabo na Chomsky, ya
ce lalle akwai wasu kalmomin harshe waɗanda ba su samu shiga ba, waɗanda kuma
tilas ne a sa su cikin rabon. Shawarar abney it a ce abu mafi ƙyau shi ne a ce
kalmomin harshe sun kasu kasha biyu: masu yin aikin irin na nahawu a cikin
jumla da waɗanda kalmomi ne kawai waɗanda an san gurabun da suke cikewa a cikin
jumla. Don haka kalmomi irin su ƙwayar ma’ana mai nuna mallaƙa (possessive) ko
nasaba (genetive) ko lokaci (tense) ko taƙi (aspect) da makammantansu, kalmomi
ne masu yin aiki na nahawu (functional categories) a cikin jumla. Kalmomin irin
su suna (noun) da aikatau (verb) da sifa (adjective) kalmomi masu gurabe na ɗindingi
(non functional categories) a cikin jumla.
Bayan haka ya raba kalmomin Hausa kaman haka rukunin mutane na farko da suka yi
aikin raba kalmomin Hausa gida-gida Turawa ne, kuma lalle sun yi ƙokarin a za
harshen Hausa bisa tsarin Ingilishi. Yin hakan ya sa har yanzu akwai
matsala game da wasu rabon da aka yi a kalmomin harshen Hausa waɗanda
basu cancanta ba. Alal aƙalla, akwai matsaloli iri uku ɗangane da matsayin
rabon kalmomin a yadda yake a yanzu.
1.
Wasu kalmomin an basu
sunan kasha wanda bai cancance su ba.
2.
Wasu kalmomi ba a sa su
cikin kowane kashi basam.
3.
Wasu kalmomin har yanzu
ba a yi matsaya ba a kansu.
Za mu bi su ɗaiɗai mu ga yanayin kowace matsala kalmomin da suna bai cancance
su ba wakilin suna na gabanin aikatau, (pre-verbial-pronoun).
Galadanci, 1976. Ya na kiran wannan ƙwayar ma’ana da ɗayantau (referential). Ya
nuna cewa abin nan (= kalma) da ke zuwa bayan fa’ili amma kafin aikatau a cikin
jumla. Wakilin suna ne. alal misali Kalmar ta a cikin jumla Bintata
’na’ a ƙaranta jaridaa.
Babu shaƙƙa binciken irin na zamani, (Tuller 1986). Yusuf, (1991), Amfani,
(1996), sun nuna cewa wanannan sai dai a kira ta da ɗiyantau koma baya
(Previous Reference marker).
Lura da ƙwayar ma’ana da ke liƙe da waɗanannan sunaye kuma a kan kira
1.
Riga (r)
2.
Wando (n)
3.
Gidaje (n)
Galadanci (1976) ya na kiran wananna ƙwayar ma’ana ɗanyatau (referential).
Tuller (1986) da Waɗansu masana da dama sun ba da shawara bisa ƙwaƙƙwarar hujja
cewa kiran wanann kwayar ma’ana referential kurum bai wadatar ba. Sun sake mata
suna wanda ya fi dacewa. Sunan shi ne “previous Reference marker” (wato ɗayantau
koma baya).
Mahaɗi (link element)
Ga wasu misalai kan yi nazarinsu.
- Farar mootaa
- Baƙin ta’akalmii
- Doogaayen gidaajee
Kowane misali sashe ne na jumla (phrase), kuma ya ƙunshi sifa (adjective) da
suna (noun). Wani tsari na hausa shi ne a duk inda sifa da suna suka zo tare (ƙunshein
ana kiransa ‘yankin suna’ koda yak e zai fi dacewa a kira shi ‘yankin sifa’),
to lalle sai an tsarma -r ko -n tsakanin su. Galadanci (1976) ya na lura da –r
da –n a matsayin ƙwar ma’ana bisa la’aƙari da aiki, yace, wannan ƙwayar
ma’ana, mahsɗI (link element) ce. Yusuf (1991) ya nuna cewa wannan ‘mahaɗi’ baya
ɗaya daga cikin ajin kalmomi na sauran harsunan duniya (universal category).
Amfani, (1996), ya yarda da maganar Yusuf (1991) ya kuma ɗora a kanta. Ya ce, a
haƙiƙanin gaskiya, wannan ƙwayar ma’ana ba ‘mahaɗi’ ba ce manunin bigire
(location marker) ce. Amfani (1996) ya ci gaba da bayani cewa wani tsari na
Hausa shi ne a duk lokacin da sifa ta yi bayanin suna, to Hausa na da tsarin
mai nuna cewa sifa ta zo kafin suna ko ta biyo shi. Akwai ƙwayar ma’ana ta
musammam mai yin wannan aiki. Wannan ƙwayar ita ce Amfani ya kira su da manunin
bagire (location marker). Idan sifa ta biyo bayan suna wasalin ƙarshen zai zama
dogo kamar haka;
- Mootaa far
- Ta’akalmii baƙ
- Gidaajee doogaay
Manunin lokaci (tense) da taƙi (aspect) masana ilimi kimiyyar harshen sun raba
lokaci gida uku: shuɗadɗ’en lokaci (past) lokaci maici (present) lokaci mai
zuwa (future). Akwai taƙI (aspect) wanda yake nuna cika aiki cif-cif watau
(completive/perfective), ko kuma a na cikin yin shi ba a kare ba
(uncompledted/continuative/imperfective). Masana nahawun Hausa sun zo da
ra’ayuka mabambamta dangane da abin da Hausa ke da shi. Shin lokaci (tense) ne,
kwai ko taƙI (aspect) ko harda hali (model) ko kuma ya ya abin yake?
Galadanci, (1976) ya nuna cewa lokaci (tense) kaɗai Hausa take da shi ya kuma ambaci
lukuta guda takwas.
Skimmer, (1977) ya haƙiƙancecewa taki (aspect) kwai Hausa ta ke da shi. Da
alama Galadanci da Skimmer ba su tsaya tsaf suka yi nazarin jumlar Hausa ba, su
ga cewa lalle ɗukkana abubuwan wato lokaci da taƙi tare suke zuwa.
Yusuf (1991) da Amfani (1996) sun tabbatar da haka. Don haka suka yi matsaya
cewa talle abinda ake dada shi a Hausa shi ne lokataƙ, (tense-aspect), ba
tsurar lokaci (tense) ko taƙIi (aspect) kawai ba. Baya ga wananan matsayin,
akwai irinsu Newman da Schuharma da Fuller waɗanda a wurare da dama sun nuna
cewa abin da Hausa ta keda shi, shi ne haɗakar lokaci da taƙi da hali
(tense-aspect-mood (tam)).
Suna da Rabe - rabensa
Suna kalma ce ta nahawu wadda ke bayanin lafazin da ake amfani da shi
wajen ambatawa kowane abu na rayuwa, mai rai ne, ko maras rai, yana motsi ko ba
ya motsi, mutum ne ko dabba ko wani abu wanda ke kasantuwa a tsarin rayuwar yau
da kullum. Duk a na ambata masa wannan kalma ta suna. Kusan ba wani abu da ɗan’Adam
ya bar shi ba tare da ya ambata masa kalmar suna ba. Misali:
Mutane
Wurare Dabbobi
Ƙwari
Sauran abubuwa
Shehu
Makaranta
Doki
Gwano
Itace
Musa
Zariya
Akuya Gara
Kogi
Citumu
Katsina Raƙumi
Cinnaka
Ciyawa
ɗanladi
Masallaci
Giwa
Tururuwa
Ƙarya
Rabi
Kasuwa
Zomo Kiyashi
Yashi
RABE – RABEN SUNA
Suna ya kasu zuwa rukunoni daban – daban na nazari, gwargwado yadda tsarin da
suna ya ƙunsa.
1.
Sunan yanka.
2.
Suna gama - gari.
3.
Suna gagara - ƙirga.
4.
Suna tattarau.
5.
Suna harɗadɗ’e.
6.
Suna ɗan’aikatau.
Waɗannan su ne rabe - raben ajin suna, bisa la’akari da rukunin da kowanne suna
ya fito. Yanzu za a ɗauke su ɗaya bayan ɗaya a yi bayanin su domin samun haske
a game da su.
Sunan Yanka
Sunan yanka suna ne da al’umma suka amince da shi don su riƙa ambaton sunayen
abubuwa da shi ciki har da sunayen mutane da sauran halittu. Ana amfani da sunan
yanka ne wajen bambance ɗaiɗaikun halittu da abubuwa da shi ta fuskar jinsi da
adadi. Sunan yanka yana iya kasancewa sunan mutane ko dabbobi ko tsuntsaye ko
tsirrai ko duwatsu ko muhalli da makamantan su. Misali:
Musa
Tururuwa
Zaki
Akuya
Makaranta
Nijeriya d.s.
Suna Gama - Gari
Wannan nau’in na suna ana amfani da shi, wajen ambaton abubuwa na
tarayya. Wato ana kiran wasu sunaye da suka cancanci a haɗe su wuri guda don su
samar da sunayen rukuni na tarayya wajen ambato, ba tare da an bambanta sunayen
abubuwan ba zuwa ɗaiɗaikun suna. A taƙaice suna ne da al’umma suka zaɗa wajen
ambata wa wasu rukunonin halittu da suka cancanci ambato a cikin adadi na tilo.
Misali:
Mutum
Dabba
Tsuntsu
Ƙwaro
Littafi d.s.
A nan ba sai an ware wani daga cikin rukunin ba, an ambaci wani laƙabi da ya
shafe shi, shi kaɗai ba. Wato dai ana iya kiran sa da cewa suna ne na bai-ɗaya.
Suna Gagara – Ƙirga
Wannan nau’in na suna, suna ne na abin da ba a iya ƙirga shi da ɗai- ɗai da ɗai-ɗai.
Ire-iren waɗannan abubuwan sun haɗa da:
Madara
Nono
Yashi
Ƙasa
Gishiri
Gari. d.s.
Abin lura a nan shi ne, kowane ɗaya daga cikin misalan da aka bayar, ba wanda
zai iya ɗaukar kowane kaso ya ce zai iya ƙirga shi ɗaya bayan ɗaya don gane
yawan adadinsa. Don haka ake kiran kason da suna gagara - ƙirga.
Suna Tattarau
Shi kuma wannan kashin na sunatattarau, yana ƙunshe da sunayen abubuwa ne waɗanda
galibi ana samun su ne a cikin rukuni ɗaya. Kuma sunan kan zo a adadi mai alaƙa
da jam’i. Abin nufi sunan yakan tattaro sunayen abubuwa da dama waɗanda suka haɗa
da jinsin tamata da na namiji a matsayin suna guda. Kuma ya haɗa da sunayen
abubuwa da na halittu, kamar irin su:
Garke
Ayari
Runduna
Bataliya
Gungu d.s
Waɗannan sunayen ana iya samun kowane jinsi a cikin kowane suna na tattarau.
Harɗaɗɗen Suna
Shi kuma wannan nau’in na harɗadɗ’en suna ana haɗa kalmomi biyu ko fiye ne,
masu zaman kansu ta hanyar liƙa su da karan-ɗori ko ƙwayoyin ma’ana ta –n ko –r
don su ba da sunan wuri ko wani abun amfanin yau da kullum.Misali:
Bayangida
Gidanwaya
Gidanrediyo
Bakinkogi
Tuma-ƙasa
Malam-buɗe-littafi
Cika-ciki
Da makamantrsu.
Haka kuma akwai harɗadɗ’en sunan da yake bayyana sunan wani abu ta hanyar gwama
sunaye biyu da kalmar harafi ta ɗa’ a tsakiyarsu tare da karan-ɗori.
Misali:
Ƙato-da-lage
Ciki-da-alako
Rub-da-ciki
Kau-da-bara
Da makamantarsu
Suna ɗan’aikatau
Shi kuma wannan nau’in na suna ɗan’aikatau ya sha bamban da sauran nau’o’in
sunayen da aka ambata a baya. Domin suna ɗan’aikatau ya fito ne daga kalmomin
aikatau. Wato suna ne mai ɗauke da kalmar aikatau wadda aka yi wa ɗafi ta
koma suna. Misali:
Kalmar Aikatau Cikakka ɗafi da
Kalmar Aikatau Kalmar Suna ɗan’aikatau
Tafiya
ma- + tafiya
Matafiya
Noma
ma- +
noma
Manoma
Su ma-
+ su + -nta
Masunta
Wannan shi ne yanayin ajin suna da rabe-rabensa a nahawun harshen Hausa.
Wakilin Suna
Wakilin Suna yana ɗaya daga cikin ginshiƙan rukunnan nahawun Hausa. Wakilin suna
wata kalma ce da ake amfani da ita wajen tsarin ginin jumla a nahawun harshe
don ta wakilci kalmar suna a muhallin da kalmar suna ta kamata ta fito, amma
saboda wani sharaɗin nahawu ya zama kalmar sunan ba ta fito a wannan muhallin
ba. Ma’ana, amfani ake yi da ajin kalmomin wakilin suna a madadin kalmar suna a
fagen nazarin jumla. Misali:
shi maimakon Audu
Ita maimakon Binta
Su maimakon ɗalibai
Misalin wakilin suna a cikin jumla shi ne;
Musa ya a mare ta
Shi ne ya kama akuya.
Wakilin suna shi ma ya rarrabu zuwa rukunonin nazari kamar haka:
1.
Wakilin suna katsattse.
2.
Wakilin suna
3.
Wakilin suna tambayau.
4.
Wakilin suna madubi.
Wakilin Suna Katsattse
Wannan nau’in na wakilin suna katsattse, ya na iya cin gashin kansa a ƙa’idar
rubutun nahawun harshen Hausa. Abin nufi a nan shi ne ya na iya zama shi kaɗai
a matsayin kalma mai cikakken aiki, ba tare da ya haɗu da wata kalma ta
nahawu ba wajen wakiltar suna a cikin jumla. Kuma ana amfani da shi wajen
fayyace sunan mutum na ɗaya da na biyu da na uku. Haka kuma ana iya nuna adadin
sunan da yake wakilta, wato a san sunan tilo ne ko jam’i. A na iya sanin jinsin
da sunan ya fito, wato sunan namiji ne ko tamata. Misali:
Mutum na ɗaya (Mai Magana)
Tilo
Jam’i
Namiji:
Ni
Tamata:
Ni
---------------
-----
Mu
Mutum na biyu (Abokin Magana)
Tilo
Jam’i
Namiji
Kai
Tamata
Ke
------
--------
Ku
Mutum na uku (wanda ake magana a kansa/Sha Magana)
Tilo
Jam’i
Namiji Shi Su
Tamata
Ita Su
Wakilin Suna Nunau
Shi wannan nau’in na wakilin suna, yana wakiltar suna ne ta hanyar nuni zuwa ga
sunan da yake wakilta. Ana amfani da shi ne wajen nuna wani abu da shi, abin na
kusa ne ko na nesa. Kalmomin wakilin suna nunau iri biyu ne; akwai dogo sannan
akwai gajere.
Wakilin Suna Nunau Dogo
Wakilin suna nunau dogo ya na iya zama da kansa wajen wakilci. Sannan kuma yana
zuwa a cikin jumla don ya wakilci suna. Kuma yana fayyace jinsi da adadi na
sunan da ya wakilta. Sannan yana nuni kan wani abu da yake a kusa ko na nesa.
Misali:
Kusa
Nesa
Jinsi
wannan
wancan
Namiji
wancan
waccan
Tamacce
waɗannan
waɗancan
Jam’i
Wakilin Suna Nunau Gajere
Wannan nau’in na gajeren wakilin suna nunau, gajeren zubi gare shi in aka
kwatanta shi da dogon wakilin suna nunau. Haka kuma ba ya iya zaman kansa har sai
an jingina shi da wata kalma. Dole sai ya sami abin da zai jingina da shi kafin
wakilcin nasa ya inganta. Ana amfani da ƙwayoyin ma’ana na –n da –r tare da
kalmomin wakilin suna nunau. Misali:
Kusa
Nesa
-n nan (gidan nan)
-n can (gidan can)
-r nan (rigar nan
-r can (rigar can)
-n nan (yaran nan) -n can (yaran can)
Wakilin Suna Tambayau
Wannan nau’in kuma kamar yadda sunan ke nuni, ya jiɗanci yanayin tambaya ce.
Duk lokacin da aka yi amfani da shi, to tabbata tambaya ce ake yi. Haka kuma
shi wannan wakilin suna tambayau iri biyu ne: Akwai na gaba ɗaya (wanda ya haɗa
da mutum da abubuwa) da kuma na fayyatacce abu (wanda yake rarrabe mace da
namiji). Misali:
Gaba ɗaya
Wa? Mutum
Su wa?
Me? Abu
Su me da me?
Fayyatacce
TILO
JAM’I
Wanene?
Su wanene?
WAKILIN SUNA MADUBI
Wakilin suna ‘madubi’, shi kuma inuwa ce ta ‘suna’ ko wakilin suna katsattse.
Shi ba ya zaman kansa. Duk inda aka faxe shi, to tabbata an riga an ambaci
sunan nan ko wakilin suna katsattse da ya zo a farkon jumla. Misali:
Mai Magana Tilo
Jam’i
Namiji
kaina kanmu
Tamata
kaina kanmu
-------
------
Abokin Magana Tilo
Jam’i
Namiji
kanka kanku
Tamata
kanki kanku
---------
--------
Sha Magana Tilo
Jam’i
Namiji
kansa kansu
Tamata
kanta kansu
---------
---------
Kowane misali aka xauka a nan, ba zai iya zaman kansa ba. Misali:
Ni kaina
Audu kansa
Shi kansa
Binta kanta
Ita kanta
Sifa
Sifa kalma ce ta nahawu wadda takan zo gabanin suna ko bayansa, don ta fayyace
suna ta fuskar launi ko tsarin jiki da ya shafi girma ko ƙanƙanta da makamantan
su. Tana bayyana jinsi da adadin suna. Misali:
- Binta ta sayi farar
- Jaka faraa Binta taa sayaa.
- Farin gida
ya ƙone.
- Gida farii ya ƙone.
A wannan misalin na (a) da yake a sama an nuna cewa, sifa takan zauna kafin kalmar
suna (Sn.), tare da harafin –n ko –r a
liƙe da ita don ta nuna cewa ta zo kafin suna. Haka abin yake a misalin na (c).
A gurbin misali na biyu (b) da yake a sama kuwa, sifar tana bayan suna ne, kuma
babu harafi a tare da ita, watau a ƙarshenta. Maimakon haka sai wasalinta na ƙarshe
ya zama dogo don ya nuna cewa ajin sifar ya biyo bayan ajin suna ne. Haka kuma
abin yake a misali na (d). ƙwayoyin ma’ana na –n da –r suke
nuna jinsin da ajin sifar ya kasanta. Dole ne idan ƙwayar ma’ana ta –n ta zo
tare da sifa ya kasance sunan namiji ne sifar ke fayyace wa, idan kuwa ƙwayar
ma’ana ta –r ta zo tare da sifa to dole ne kalmar sunan da sifar ke fayyace wa
ta zamana tamata. Misali:
1.
a) ƙaramin gidaa
gidaa ƙaramii
ƙaramar goonaa
goonaa ƙarama
1.
b) kooren ganyee
ganyee kooree
kooriyar ciyawaa
ciyaawaa kooriyaa
1.
c) doogon riimii
riimii doogoo
dooguwar giginyaa
giginyaa dooguwaa
Sifa ma iri-iri ce kamar haka:
1.
Sifa Sassauƙa
2.
Sifa Nanatau
3.
Sifa ‘Yar aikatau
Sifa Sassauƙa
Wannan nau’i na sifa an san shi da tsari ne a sauƙaƙe. Sifar ta ƙunshi saiwar
kalma da ɗafa-ƙeya. Misali:
baƙi
baƙa baƙaƙe
shuɗi
shuɗiya shuɗaye
dogo
doguwa dogaye d.s
Idan an lura za a fahimci saiwar kowace kalma da ɗafa-ƙeyarta. A kalmar baƙi ,
tushen kalmar shi ne ɗaƙ’ da ɗafin wasalin ‘i’ ko na ‘a’ sunan namiji ko
‘a’, a sunan tamata ko ‘aƙe’ a jam’i. kalmar shuɗi, tushen
kalmar shi ne ‘shuɗ’ da ɗafin wasalin ‘-i’, ko ‘a’ sunan namiji ko wasalin
‘-iya’, a sunan tamace ko wasalin ‘–aye’ a suna jam’i. Kalmar dogo mai
tushen kalma ɗog’ da ɗafin wasalin ‘-o’, a sunan namiji ko ɗafin wasalin
‘-uwa’, a sunan tamace ko ɗafin wasalin ‘–aye’, a suna jam’i.
Sifa Nanatau
Nau’in wannan sifa shi ne wanda ke da tsari irin na maimaicin kalmomi. Waɗanda
ba su la’akari da jinsi, ko adadi balle jam’i. Misali:
ƙungiya-ƙungiya
tsibi-tsibi
kashi-kashi
buhu – buhu
launi-launi
ganga- ganga d.s
Sifa ‘Yar Aikatau
Ita kuma wannan sifar kalmar aikatau ke samar da ita. Wato kowace sifa ‘yar
aikatau ta samo asali ne daga kalmar aikatau. Misali:
Kalmar Aikatau Ajin sifa (namiji)
Ajin sifa (tamacce) Ajin sifa (Jam’i)
Wanke wankakke
wankakkiya wankakku
Gina ginanne ginanniya
ginannu
Rubuta rubatacce rubutacciya
rubutattu d.s
Aikatau
Aikatau shi ma ya na ɗaya daga cikin rukunan nahuwun harshen Hausa. Aikatau
kalma ce da ke ƙunshe da aikin da ke aukuwa a cikin jumla. Misali:
Wanke, dafa, ji, ci, d.s
Aikatan harshen Hausa ya kasu kashi biyu kamar haka:-
1.
Aikatau so-karɗau
2.
Aikatau ƙi-karɗau
Aikatau So-Karɗau
Aikatau so-karɗau shi ne kalmar aikatau da suna karɗau ke biyo bayanta a cikin
jumla. Aikatau so-karɗau kalmar aikatau ce da take buƙatar wani abu ya biyo
bayanta a cikin jumla. Abin da take son ya biyo bayan nata shi ne kalmar suna
ko kalmar wakilin suna da kan zo a ƙarshen jumla don karɗar aikin da suna aikau
ya aikata a cikin jumla. Misalan kalmomin aikatau so-karɗau su ne: kaama,
maari, yanka, ɗeeboo, da duk wata kalmar aikatau da suna ko wakilin suna zai
iya biyo bayanta. Misalin su a cikin jumla:
Bala yaa kaamakaaza.
Kande taa maari Audu.
Rabi taa yanka naama.
Yara sun ɗeeboo ruwa
Aikatau Ƙi-Karɗau
Shi kuma wannan nau’in akasin aikatau so-karɗau ne. Aikatau ƙi-karɗau, shi ba
ya buƙatar zuwan suna karɗau a bayansa. Misalan kalmomin aikatau ƙi-karɗau
su ne kamar haka: gudu, dahu, bugu da makamantan kalmomin aikatau waɗanda in
aka faɗe su a cikin jumla basa buƙatar wata kalma ta biyo bayansu. Ga Misalin
kalmomin a cikin jumla.
Audu yaa gudu.
Abincin yaa dahu.
Shinkafa taa bugu.
Bayanau
Bayanau kalma ce da ake amfani da ita cikin jumla don ta ƙara bayani kan kalmar
aikatau. Saboda a san lokaci ko wuri ko yanayin da suna aikau ya aikata aikin a
cikin jumla. Misali:
1.
Baƙii sun iso ɗaazu.
2.
Matasaa sunaa
zaune a kan dakali.
3.
Malam ya a shigo aji d
gaggawaa.
4.
Akuu yana magana a
5.
Hakimii ya a ziyarci ɗalibai
da safe.
Dangane da haka kuma a iya raba bayanau zuwa gida uku ta ɗangaren nazarinsa.
1.
Bayanau na yanayi
2.
Bayanau na wuri
3.
Bayanau na lokaci
Bayanau Lokaci:-
Shi wannan kashi yana da nasa rassa guda uku (3) kamar haka:-
1.
Haɗadɗ’en Bayanau
2.
Nanatau/ruɗayyen Bayanau
iii. ƙosasshen/tsanantau Bayanau
Haɗaɗɗen Bayanau:-
Shi ne mai nuna lokaci na ranakun da aka gudanar da aiki a cikin jumla. Misalan
kalmomin wannan nau’in na bayanau su ne: Shekaranjiya, Bana, Jibi,
Bara, Yau, Ban da gobe, Baɗi, Gobe: da dai makamantan waɗannan kalmomi masu
nuna lokacin ranaku da yake ƙarin bayani kan kalmomin aikatau. Misalin su a
cikin jumla:
(a) Musa yaa kaama kifi jiya.
(b) Rabi taa dafa naama shekaranjiya.
Nanatau/ruɗanyayyen bayanau
Irin wannan nau’in na riɗanyayye ko bayanau na nanatau yana ɗauke ne da wasu
kalmomi na bayanau da ake iya maimaita su don a samar da shi. Ire-iren waɗannan
kalmomin su ne; Jiya-jiya, Yanzu-yanzu, ɗazu-ɗazu, Gobe-gobe, ƙasa-ƙasa.
Misalin su a cikin jumla:
- Lawal yaa tafi kasuwa ɗazu-ɗazu.
- Shehu yaa maari Hauwa yanzu-yanzu.
Tsanantau/ƙosasshen bayanau
Shi kuma wannan kashi yana tabbatar da aukuwar aikin da aka aikata a cikin
jumla. Misalin kalmominsa su ne: ainun, sarai, ƙwarai, sosai,
garau da sauran kalmomi masu aikin ƙarin bayani kan kalmar aikatau
masu nuna tabbatuwar aiki a cikin jumla.
Misalin su a cikin jumla.
- Hafsa taa sari ƙafarta sosai.
- Abdulmalik yaa sami kuɗi ƙwarai.
- Ibrahim yaa warke
Bayanau Na Yanayi.
Bayanau na yanayi ana amfani da kalmominsa ne a cikin jumla don nuna yanayin da
aiki ya gudana a cikin jumla. Ire-iren kalmomin da ake amfani da su waɗanda
suke ƙarin bayani kan kalmomin aikatau don nuna yanayin da aiki ya gudana a
cikin jumla sun haɗa da: da Sauri, a firgice, a fusace, da gaugawa.
Misalin su a cikin jumla:
- Musa yaa shigo aji da sauri.
- Ayuba yaa tafi makaranta a firgice.
- Jafar yaa zo a fusace.
Bayanau Na Wuri
Bayanau na wuri yana nuni ne da wurin da aikin cikin jumla ya faru. Ire-iren
kalmomin da ake amfani da su, a irin wannan bayanau ɗin su ne; waje,
ko’ina ƙasa, sama, a kan, ciki, kusa da sauran kalmomin da suke nuni
da muhallin aukuwar aiki. Misalin su a cikin jumla:
- Audu yaa faɗi ƙasa.
- Adamu ya shiga cikin aji
2.2 NAHAWUN TACIYA
Nazarin ilimin harsuna abu ne Wanda tun farkon bayyanarsa yake tafe da
ra’ayoyin malamai da masana, Wanda kuma a cikin ra’ayoyin nan, kowane na ganin
ga yadda ya kamata a bi a yi nazarin harshe. Da farko tun wajen ƙarni na biyar
kafin bayyanar Annabi Isa (A.S), Wato 5th C.B.C. |ayan nan an sami ra’ayoyin da
dama daga malamai manazarta harsuna. Daga cikin su akwai ra’ayoyi daga malamai
masu nazarin harsunan Girkanci da Latinanci da sauran makamantarsu. Malamai na
wannan lokaci duk sun nazarci harshe ne a ta farkin nahawun gargajiya
Wanda shi nahawun gargajiya ya ta’alaka ne kan wasu dokoki ko ƙa’idoji inda
suke da (mabiya ra’ayin nahawun gargajiya) kuma suna umurta jama’a a kan yadda
za su furta furuci ko kalma, kuma kada ka fadi wani abu (prescriptive grammer).
A bisa wannan hujjar mabiya wannan hanya kuma sun bai wa harshen rubutu
(written language) duk wani mahimmanci maimakon harshen baka (spokkrn
language).
Ganin wannan hanya ta nazarin harshe sai a ka sake bin sawun wasu manazarta
wadanda suka fito suna sha’awa ga nazarin wasu harsuna waɗanda ba nasu ba.
Hanyar da suka bi don wannan nazarin ita ce hanyar da ake kira ilimin
nazarin kwatanci da bin salsalar harsuna (comparative and historical
linguistics). Wannan hanya ta kara fito da wani nazarí harsuna fili don samun
daukaka. A cikin wannan hanya an sami malamai da dama irinsu, Sir Willian Jone,
da Rusmus Rask, da Franz Bopp, da Jacob Grimm, da makammantarsu. Waɗannan
malaman sun taimaka sosai ga wannan fanni. Nazarin harshe ta kan wannan hanya
ya faro tun wajen shekarar 1787 zuwa 1833. A wannan tsakanin, malamai sun
wallafa littattafai da makaloli da dama ɗangane da wasu harsuna.
Ganin yadda mabiya ra’ayoyin nahawun gargajiya suka yi nazarin harshe, ta kai
ma an sake samun bayyanuwar wata hanya ko wani ra’ayi Wanda a ke kira Nahawun ƙwanƙwancewa,
(structural grammer). Wannan ra’ayi, ‘structuralistic’ wato
‘yan ƙwanƙwancewa, a ganinsu ya kamata a yi nazarci harshe kansa ɗungurugum, a
maimakon nazarin wasu ‘yan tsirarun harsuna (Jibril, 1985:p62). Ya kara da cewa
sun karfafa tunaninsu ne a cikin ƙasidu da littattafai masu yawa da suka
wallafa. Bayan haka sun danganta nazarin harshe da kimiyya, ma’ana
nazarin harshe ya shafi daidai da irin ci gaban da a ka samu a halin yanzu.
Abubuwan nan suka taimaka wa wannan fanni akwai malamai irinsu;
De-saussue, da Leonard Bloomfield, da Franz Boaa, da Edwan Sapir da Fries. O.G,
da Zelling S. Harris, da dai makammantarsu bayan haka (Jibril, 1985:p62). Ya
bayyana cewa ƙwazo da bincike da waɗannan mutane ya kai ga samun nasarar komawa
kan abin da an ke furtawa a maimakon tsohuwar hanyar nan da aka fi rinjaya na a
maida hankali a kan duk wani abu da a ka rubuta mahimmanci. Wannan gagarumin
canjin ya auku ne a farkon ƙarni na ashirin ne (ƙ 20th C).
Hr-ila-yau a na cikn wannan halin sai wasu malamai suka fito da wani
ra’ayinsu akan nazarin harshe can kwatsam! Sai wani Ba’amerike (Bature), mai
suna Noam Chomsky. Chomsky ya fito da sabon ra’ayi game da nazarin
harshe, inda ya nuna bai kamata ba a riƙa nazarin harshe ta hanyar
nahawun gargajiya ko nahawun ƙwanƙwancewa ba. Wanna bayani da Chomsky ya yi
cikin fagen nazarin harsuna ya samu ɗaukaka fiye da sauran malamai manazarta
harsuna na wannan lokacin. Hasali ma ta kai kowa ya fito ƙokri ya ke ya
kwatanta kansa da Chomsky, ko kuma ya samo wani abin kushewa daga gares hi
(Chomsky). Chomsky ya bayyana ne a shekarar 1950, kuma a 1957, ya wallafa wani
littafi mai suna “styntsctic structure”. Wannan littafin ya kara
fitowa da Chomsky fili a idon duniya musamman a wajen ɗalibai da malamai manazarta
harsuna. A cikin wannan littafin ne aka samu wani sabon ra’ayi da ya
kira, “Nahawun Taciya” (Transformational Grammer). Bayan haka bisa
la’akari da irin halin ƙaƙa-ni-k-yi da nazarin harshe ya shiga a shekara 1950
. A wannan tsakanin sai da ta kai an sami kusan shekaru ashirin babu wani
canji na ku-zo-a-gani da aka samu dangane da nazarin harshe. Malaman da
suka cancanci su kawo wani sabon abu cikin nazarin ilimin harsuna, sai kuma
kowanne daga cikinsu ya kasance ya na da ra’ayinsa na son rai, da zargin juna a
tsakaninsu. |ullowar Chomsky ya sa an samu gagarumin canji Wanda a
ke kira “juyin-juya-hali” a cikin a cikin nazarin ilimin harsuna, bayan haka
nahawun taciya ba wani ra’ayi ba ne da Chomsky ya ƙirƙiro don ya kushe hanyoyin
da a ke bi wajen nazarin Nahawun taciya ko nahawun ƙwanƙwancewa.
Nahawun taciya hanya ce da Chomsky ya zo da shi ne don daidaita nazarin harshe
ya ta bai ɗaya kuma daidai da zamani. Bayan haka Chomsky ya bayyana wasu
hanyoyi da yake ganin za a samu gyra ga wasu ra’ayoyi na malamai waɗanda suka
gabata, kuma waɗanda a ganinsa waɗannan hanyoyi masu rauni ne kuma kuma wasu
daga cikinsu marasa makama.
Dalilan da suka ƙara ƙarfafa wa Chomsky ƙwarin guiwa har ya fito da wanna
ra’ayi, Wanda ya kira “Nahawun taciya” a na iya ganinsu a cikin
nazarce-nazarcen malamai na wannan ƙarnin da na wasu malaman da suka gabata.
Daga cikin rubuce-rubucen da Zelling, S. Harris ya yi, sun ƙarfafa
wa Chomsky tunaninsa. Haka kuma ayyukan Jacobson a koda
yaushe yakan yi tunanin tsarin sauti na bai ɗaya, ko kuma na gama duniya
(phonological universal). Ya yarda cewa bambanci da ke akwai na tsarin
furuci a cikin harsuna na duniya bambanci ne wanda malamai suka karkata a kan
ra’ayinsu. Shi ma, De-saussue ya na cikin waɗanda suka ƙarfafa tunanin Chomsky.
De–saussure kuma shi ma ya nuna cewa gina jumla ba ya cikin wani yanki na
tsarin harshe kamar yadda ya bayyana kamar haka” Harhaɗa kalmomi zuwa
jumloli abu ne wanda kowanne ɗan asali mai magana da harshe kan yi
a lokaci na musamman, ba abu wanda harshe kan yi gaban ɗaya ba.” Saboda haka
irin wannan rashin yarda da wasu abubuwa game da harshe da wasu malamai suka
nuna, shi ya ƙara ƙarfafa tunanin Chomsky wanda ya kai shi ga fitowa da wannan
ra’ayi nasa wanda ya yi wa suna da “Nahawun taciya”.
2.3 MATSAYIN AZUZUWAN KALMOMIACIKINJUMLAR HAUSA
A nan an dubi jumlar Hausa ne, da nufin fito da ire – irenta, don sanin yadda
fasalolinta suke a fagen nazari. A nahawun harshen Hausa a na da ire-iren jumla
guda huɗu ta fuskar zamantakewar azuzuwan kalmomin cikinta, waɗanda masanan
zamani suka tantance su a fagen nazari. Waɗannan jumlolin sun bambanta da rabon
farko da a ka sani, wato waɗanda masana suka samar da su ta fuskar yanayin
zubinsu. Wato kaso uku da masanan farko suka aiwatar, kason na masanan farko da
suka gudanar ya na da ire-iren jumla guda uku waɗanda suka haɗa da: sassauƙar
jumla da sarƙaƙƙiya da harɗadɗ’iya. Su kuma, masanan na ilimin ginin jumlar
harshen Hausa na zamani sai suka sake duba wannan rabon suka fito da ire-iren
jumloli har guda huɗu kamar haka:
(i) Sassauƙar Jumla.
(ii) Jumlar Tambaya.
(iii) Jumlar Umarni.
(iv) Jumlar Korewa.
Waɗannan jumlolin su masanan zamani suka tantance don sama wa ɗalibai da manazarta
ilimin ginin jumla sauƙin nazarin jumla da sassanta.Yanzu za a ɗauki kowace
jumla domin a nuna yadda tsarinta yake a fagen nazari.
Sassauƙar Jumlar Hausa
Sassauƙar jumla ta ƙunshi yankuna biyu manya. Bisa ra’ayin masanan farko,
sassauƙar jumlar Hausa tana da yankin suna (YSn) da yankin aiki (YA).
Amma a ra’ayoyin masanan zamani an sami bambancin ra’ayi dangane da yankin
aiki. Bisa fahimtar masanan zamani suna ganin cewa yankin da masanan farko suka
kira yankin aiki, sunan bai dace da shi ba, saboda yankin ya na iya kasancewa
ya ɗauki wasu zmahimman azuzuwan kalmomi na daban bayan ajin kalmar aikatau.
Sanin haka sai suka kira shi da yankin abin da aka faɗi a game da suna
(YAfgSn) maimakon yankin aiki (YA). Wannan batu a na iya taƙaita shi kamar
haka:
J
Suna aikau + Abin da aka faɗi a game da suna
Wannan yanki na abin da aka faɗi a game da suna (YAfgSn) ya ƙunshi kalmar
aikatau da kalmar karɗau (Aikatau + Karɗau) sannan ana iya samun wasu azuzuwan
kalmomin su fito a yankin. Ana iya samun kalmar bayanau da sifa da harafi.
Babban abin da ake son sassauƙar jumla ta ƙunsa a matsayin ginshiƙan tubalan
gina ta su ne, kalmar suna aikau ta zo a farkon jumlar, sai kalmar aikatau ta
fito a tsakiyar jumlar sannan kalmar suna karɗau ta zo a ƙarshen jumlar. Wannan
tsarin shi zai ba da fasalin nan na S.A.K a matsayin tsarin gudanar da sassan
sassauƙar jumla. Irin wannan gundarin tsarin na S.A.K shi ne ake samu a harshen
Ingilishi da wasu harsunan masu ɗimbin yawa. Wannan tsarin na S.A.K. shi ake
kira da S.V.O a harshen Ingilishi.
Ga Misali:
Hausa
Ingilishi
(a) Bala ci
abinci.
(b)
John eat food.
SnAikau Aik Snkaɗ
Subject noun Verb Object noun
1.
A.
K.
S.
V. O.
Jumlar Hausa tana buƙatar mafayyaciya (Maf) bayyananne, wanda zai fayyace suna
aikau ta fuskar jinsi da adadi. Wannan ƙwayar ma’anar ita ce, “ya” a wannan
misalin na (a).
Aikatau na jumlar “ci” ya na buƙatar a fayyace shi ta fuskar lokaci da taƙi
(Lokt). Ƙwayar ma’ana da ke gudanar da wannan aikin ita ce, “a”. Ƙwayar
ma’ana “a” ana kiranta da lokataƙ (Lokt) domin tana fayyace aikatau ne
dangane da lokacin da aka aikata aiki a cikin jumla da kuma kammaluwar aiki ko
rashin kammaluwar aikin.Shi ya sa jumlar ta koma kamar haka:
Sassauƙar Jumlar Hausa:
- Bala ya
a
ci
SnAikau Maf. Lokt
Aik SnKarɗa
S
A K
Ga hanyar nazarin li’irabi a zamanance. Jumlar Hausa tana ƙunshe da waɗannan
azuzuwan kalmomin kamar haka:
J
YSn
+ YAfgSn
YAfgSn
KN + YA
YA
Aik,
YSn
KN
Maf,
Lokat
YSn
Sn
Sn
Bala
Maf
ya
Lokat
-a
Aikatau
ci
Sn
abinci
J
YSn YAfgSn
Sn
KN
YA
Maf Lokat
Aik
Sn
Bala ya
-a ci
abinci
Sassauƙar jumlar Hausa tana ɗauke da ginshiƙai guda uku ne ƙwarara. Ginshiƙan
su ne: Suna aikau (Snaik), da aikatau (Aik), sai suna karɗau (Kƙb).
Jumlar Korewa
Jumlar Hausa ta korewa tana ɗauke da wasu kalmomi na musamman da harshen ya
tanada domin yin sharaɗi da su, kafin a gina ita wannan jumla ta amsu. Sannan
da waɗannan kalmomin ne za a iya nuna irin korewar zance da aka samu a cikin
jumlar. Kalmomin ana amfani da su ne wajen nuna korewar zance a cikin jumla ta
hanyar bin wasu ƙa’idoji da aka gindiya na amfani da su don nuna yadda korewar
ta auku. Shin korewar ta jumlar ce gaba ɗaya, ko korewar wani ɗangare ne na
zance a cikin jumlar. Misalin sassan jumlar korewa shi ne:
Rabi baa ta tafi kasuwa ba.
Masana sun fito da tsarin kalmomin korewa da fasalin da ake amfani da su a
cikin jumla, domin nuna irin korewar da aka samu. Ra’ayi ya bambanta a wajen
bayani dangane da korewa. Masana irin su Kraft C. H. da Kirk – Greene
(1973:37-40 da 61- 64) da Galadanci (1976:77- 83) da Skinner (1977:77 – 78), da
Zaria (1981:82 - 84) da Bagari (1986), duk sun bayyana korewa kaɗai ba tare da
sun nuna korewar yanki ce ko ta jumla baki-ɗaya ba. Yalwa (1995) da Newman
(2000) da Amfani (2006) da Muhammad (2010) da kuma Sani (2010) da
Umar (2012) duk sun yi bayani kan cewa ana samun korewa iri biyu, da ta yankin
jumla da ta jumla gaba ɗaya. Masana sun yi tarayya dangane da tsarin kalmomin
korewar. Ga yadda suke tare da misalan su :-
(i) Ba (bàà-----bá) = Bàà Ali ya sayaa bá.
(ii) Ba (bà-----bá)
= Rabi bà ta tafi makaranta bá.
(iii) Ba (báá----)
= Báá kuɗi a banki.
(iv) Ba (bâ….)
= agwagwa bâ ta tashi sama sosai.
(v) Ba (báábù----) = Báábù ruwa a
randa.
(vi) Ba-i (bà-i… bà) = bài dace a hana bara bá.
(vii) Káádà/Kâr------ = Káádà ka a tafi. Ko
kâr ka a tafi.
Abin lura a nan shi ne, fasalin ginin jumlar korewa yana ƙunshe da wasu mahimman
kalmomi da aka tanada don amfani da su wajen nuna korewa a jumlar Hausa.
Jumlar Tambaya
Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake ginawa don a yi tambaya. A Hausa ana da
jumlar tambaya kamar haka:
(a) Yàushéé Rabi za ta tafi?
(b) Wàà Isaa ya a mààráá?
(c) Mèè Musa ya káamaà?
Hausa tana da tsarin da take bi wajen ginin jumlar tambaya. Hanyar da Hausa
take bi wajen ginin jumlar tambaya ita ce, dole ne “kalmar tambaya,” ta zo a
farkon jumla. Haka kuma dole ne alamar tambaya ta zo a ƙarshen jumla. Amma ana
iya samun wani tsarin da Hausa take amfani da shi a maganganun yau da kullum.
Wasu daga cikin kalmomin tambaya da Hausa take amfani da su wajen ginin jumlar
tambaya su ne;
(i) Iná? = Ina Maryam ta a tafi?
(ii) Wàà? = Wàà za a aika?
(iii) Yàushéé? = Yàushéé za a dawo aiki?
(iv) Ƙàƙáá? = Ƙàƙáá za a yi?
(v) Yáyáá? = Yáyáá Audu ya a faɗi jarabawa?
(vi) Mèè? = Mèè Ali ya a saya?
Masanan da suka aminta da wannan tsarin sun haɗa da; Kraft C. H. da Kirk –
Greene (1973) da Skinner (1977) da Zaria (1981) da Jinju (1986) da Bagari
(1986) da Yalwa (1995) da Amfani (2005) Muhammad (2010) Umar (2012). Duk sun yi
bayani game da wannan tsarin na jumlar tambaya.
Jumlar Umarni
Jumlar umarni tana ɗauke da wani tsari da ya bambanta ta da sauran jumloli da
ake da su a Hausa. Jumlar umarni takan zo da kalma ɗaya rak, a matsayin jumla
cikakkiya, mai ma’ana. Kuma kalmar da take zuwa da ita, ita ce kalmar aikatau
(Aik). Ga misalin jumlar umurni;
(a) Tashi!
(b) Rubuta!
Abin lura a nan shi ne jumlar umarni koyaushe takan ƙare da alamar motsin rai.
Kamar yadda aka nuna, jumlar umarni cikakkiyar jumla ce, sai dai kuma ta ƙunshi
kalma ɗaya rak.
Masana irin su, Kraft da Kirk – Greene (1973) da Skinner (1977) da Zaria (1981)
da Bagari (1986) da Jinju (1986) da Yalwa (1995) da Newman (2000) da Jaggar
(2001) da Amfani (2006) da kuma Umar (2012) duk sun yarda da cewa wannan
bayanin da aka gabatar shi ne tsarin samar da jumlar umarni a Hausa
2.4 NAƊEWA
A babi na biyu shimfiɗa ce ta zo a matsayin gabatarwa, bayan nan sai bincike ya
yi waiwayen azuzuwan kalmomi na harshen Hausa. Inda ya bayyanansu tare da kawo
su daki-daki, wanda daga bisani nahawun taciya ya biyo baya tare da ra’ayin
masana ilimin taciya da nahawun harshen Hausa. Matsayin azuzuwan kalmomi a
cikin jumla ta zo a gaba wanda a nan ne a ka yi bayanan gamsassahe game
dajumlar Hausa. Wanda da ma nazarin shi ne hanyoyin nazarin jumla a nahawun
Hausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.