Email: dirindaji12aa@gmail
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR USMANU DANFODIYO, SOKOTO
DA
AHMAD RUFA’I DALIJAN
SAHEN HAUSA
KWALEJIN ILIMI TA ADAMU AUGIE, ARGUNGU
An dad’e ana yi wa mawak’an baka da wak’ok’insu kallon hadarin kaji a k’asar Hausa. An d’auke su a matsayin wani gungun mutane da ba su da wani matsayi da daraja ko wani muhimmanci a al’umma. Sau da yawa akan kalle su a matsayi maras darajja ko wani muhimmanci a al’umma. Wani lokaci kuwa a kalle su a matsayin cima-kwance marasa abin yi da suka wofintar da rayuwarsu ta hanyar dogaro da kwad’ayin abin wasu a cikin al’umma. Irin wannan matsayi kuwa ya yi daidai da abin da Bahaushe ke cewa ‘ Maso abin wani wawa’.
A yau abubuwa sun sauya, amma wani abin takaici shi ne, akasarin mutane sun jahilci wannan sauyi, manufar wannan k’asida ita ce fitowa da irin rawar da wad’annan makad’a ke takawa a rayuwar wannan al’umma a fili, da tunanin cewa yin haka zai taimaka wajen kawar da jahiltar su da aka yi. Domin kuwa ko ba komai, suna da rawar takawa musamman a wannan hali da k’asa take ciki na lalacewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ilimi da matsalolin siyasa da sauransu. Bisa ga wannan , k’asidar za ta yi k’ok’arin kawo wasu d’iyan wak’ok’i daga mawak’an baka daban daban domin tabbatar da muhimmancinsu a cikin al’ummar Hausawa.
https://www.amsoshi.com/2017/06/30/danmaraya-jos-jikan-umar-a-gaishe-ka/
Wak’ar baka dad’ad’d’iyar abu ce wadda ta wanzu tun wani lokaci mai nisa da ya shud’e tsawon zamanna. Bahaushe ya k’agi wak’a ne tun kafin ya yi cud’anya da wata al’ada da kuma jama’a na k’etare. (Fadama 2008:79)
Masana da manazarta adabin Hausa sun bayyana ma’anar wak’a ta fuskoki daban daban. Kad’an daga cikin wad’annan masana da manazarta da suka yi k’ok’arin bayyana ma’anar wak’a sun had’a da; A B Yahya wanda ke da ra’ayin cewa:
“ Wak’a tsararriyar maganar hikima ce da ta k’unshi sak’o cikin za’ba’b’bun kalmomi
da aka auna domin maganar ta reru ba fad’a kurum ba” (Yahya 1997:5)
Anan kenan, a wajen ‘yankallo, watau wanda ba mawak’i ba , ba kuma manazarci wak’a ba, yana kallon wak’a a matsayin maganar da ake rerawa wadda ke da dad’in ji har ga zuciya, kuma tana fayyace gaskiya da kawo nishad’i.
Haka Fadama (2008:80) ya rawaito Gusau (2003) cewa “wak’ar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa ga’ba-ga’ba bisa k’aidojin tsari da daidaituwa a rera cikin sautin murya da amsa amon kari da kid’a da ‘yan amshi”
Baya ga wannan, shima Birnin Tudu (2002:23) ya rawaito Dangambo (1982) ya bayyana ma’anar wak’a kamar haka:
“ Wak’a wani furuci ne ( lafazi ko salo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko k’a’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salo mai armashi” Birnin Tudu (2002:24) ya k’ara rawaito Umar (1980) ya ce “wak’a tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka wad’anda ake kira baitoci ko d’iyoyi kuma ake rerawa da wani sautin murya na musamman”
A wata ma’anar an dubi wak’a a matsayin “ Wata had’akar kalmomi da kid’a ne cikin tsari mai bayar da armashi ga mai sauraro, a inda shi mai sauraren zai iya tantance wannan had’aka ta kid’a da jerin kalmomin” (Mashi 1986)
Ta la’akari da ma’anonin da masana da manazarta suka bayar ana iya bayyana wak’a da cewa
tana zuwa a sigar gunduwowin sautuka wad’anda ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman
Kad’an daga cikin ra’ayoyin masana dangane ma’anar wak’a kenan. Mawak’an baka mutane ne masu basira da fasaha da ke aiwatar da wak’ok’i iri iri a fannoni daban daban na al’ummar Hausawa. Fahintar rawar da suke takawa ba zai kammalu ba sai fa idan an yi nazarin wasu daga cikin wak’ok’insu tare da la’akari da irin tasirinsu a fannoni daban daban na rayuwa. Yin haka zai ba da damar yi wa wad’annan gungun mutane da wak’ok’insu adalci tare da kawar da irin kallon-kallon da ake yi musu a matsayin marasa aikin yi a cikin al’umma. Wannan kuwa ita ce manufar wanna k’asida tamu. Don haka, k’asidar ta dubi wasu daga cikin muhimman ‘bangarori da suka shafi gina rayuwar al’umma mai nagarta domin samun bunk’asar k’asa.
Hausawa kan yi wa Ilimi kirari da cewa, shi ne gishirin zaman duniya, wanda sai da shi ne rayuwa ke inganta. Saboda muhimmancinsa ga rayuwa ya sa da wuya a iya tafiyar da komi sai da ilimi a cikin al’umma. Wannan shi ya sanya mawak’an baka aiwatar da wak’ok’i masu d’imbin yawa da suka taka muhimmiyar rawa wajen ilmantar da al’umma ta fuskoki daban daban . A cikin wad’annan wak’ok’i ko d’iyan wak’ok’in, mawak’an sun yi k’ok’arin fitar da matsayin ilimi da amfaninsa da kuma irin k’ima da daraja da matsayin duk mutumin da ya nemi ilimi ya same shi ya kuma yi aiki da shi a cikin al’umma. Ga dai abin da wani manazarci ke cewa dangane da wannan al’amari:
“ Kid’a da wak’a a k’asar Hausa wani ginshik’in
abu ne da ake aiwatarwa don ilimntarwa ko
sadarwa nishad’antarwa, ko bayar da wata
gudummawa ta musamman.
Kusan kid’a ya yi rawa ya yi tsaki , ya durmuya
sosai a cikin rayuwar Bahaushe,
Musamman rayuwar da ta danganci zamantakewa
da sana’o’i da bukukuwa da lokuttan shak’atawa.”
(Gusau, 2005)
Dangane da wannan , ga kad’an daga cikin abin da wad’annan mawak’an ke cewa:
Jahilci rigar k’aya ne
Yara mu je makaranta
Mu yi karatu
(Muhammadu Bello Gwaranyo: Wak’ar jahilci rigar k’aya)
A wani d’an wak’a, mawak’in ya ci gaba da cewa:
Wanda bai san nun ara ba
ABCD bai iya ba
Ka tabbata jakin duniya ne
A k’ark’ashin wad’annan d’iyan wak’a, mawak’in ya yi k’ok’arin bayyana matsayin ilimi da matsayin mutumin da ake ganin yana da ilimi a idon al’umma. Haka ya yi k’ok’arin nuna wa al’umma matsayin jahilci wanda yake kishiya ne ga ilimi da kuma matsayin wanda ba shi da ilimi a cikin al’umma. Ya kuma yi hakan ne ta hanyar siffanta jahilci da rigar k’aya , rigar da take mai matuk’ar k’unci wajen sakawa. Kenan , duk mutumin da ya kasa neman ilimi tamkar ya bar kansa cikin k’uncin jahilci. Kamar dai ya saka wa kansa riga ce ta k’aya mai bak’in k’unci da wuyar d’ebewa.
Haka kuma wani mawak’in ya k’ara karantar da mu wani abu mai muhimmanci game da ilimi inda yake cewa:
Makaranta uwar k’warai ta
Kuma mai rik’on d’iya
Ta rik’i d’anta
Ta yi mai sutura ya shigo
(Abdu Inka Bakura: Wak’ar mu d’au ilimi gaskiya)
A wannan d’iyan wak’ar, mawak’in ya bayyana makaranta a matsayin uwa wadda take shayar da d’anta, ta rene shi, ta kuma tayar da shi ya zama mai amfani ga al’umma. Kenan ya fito muna da matsayin ilimi a nan wanda yake tayar da mutum, ya d’aukaka matsayinsa, ya sanya shi cikin sutura ta d’aukaka. Haka dai mawak’in ya ci gaba da cewa:
Makaranta uwar k’warai ta
Kuma mai rik’on d’iya
Ta rike d’anta
Ta yi mai mota ya shigo.
(Abdu Inka Bakura: Wak’ar mu d’au ilimi gaskiya gwamnati horo ta kai)
Wannan ya k’ara fito mana a fili da yadda mawak’an baka na Hausa ke k’ok’arin karantar da al’umma matsayin ilimi da kuma amfaninsa ga rayuwa. A dubi yadda bayan makaranta ta raya mutum ta tarbiyyantar da shi ta kuma sanya shi mai matsayi abin yabo a cikin al’umma, ba ta tsaya nan ba, har da ba shi damar mallakar abin hawa watau mota. Kenan, mawak’in ya fito muna a fili da irin fa’idar da ake samu bayan samun ilimi. Sanin kowa ne, mota wata abu ce ta alfarma da ba kowane mutum ke mallakarta ba, sai fa wanda Allah ya d’aukaka.
Har wayau, mawak’in ya ci gaba da bayyana matsayin makaranta da fa’idarta tare da kira ga iyaye da a saka yara a makaranta domin su nemi ilimi. Ga abin da ya ci gaba da cewa:
A kai yara su koyi ilimi
Makaranta ta gyara d’anta
Ta hora maka shi
ta kuma shirya maka shiya

A karshe sai mawak’in ya bayyana muna matsayin mutumin da ya tashi babu ilimi inda yake cewa:
Ilimi uwa uba ne
Kwat tashi babu ilimi
Yag girma babu ilimi
Ko ya bid’a buk’ata
Yac ce a ba shi
Ba a kulawa shiya.

Bayan mawak’in ya fad’akar da al’umma matsayin ilimi da muhimmancinsa, tare da neman a saka yara makaranta domin su ci wannan gajiya, a d’aya ‘bangaren ya kuma fito mana da illolin da ke tattare da rashin ilimi ga duk wani mutum a al’amurransa na yau da kullum. Ya fito da wannan a sarari inda ya nuna cewa komin girman mutum ko matsayinsa ko kud’insa matuk’ar bai da ilimi, to kuwa kud’insa da girmansa ba su yi masa wani dogon amfani.
A nan za mu ga cewa. bisa ga wad’annan d’iyan wak’ok’i da muka yi nazari akai, mawak’an baka sun taka muhimmiyar rawa wajen ilimantar da al’ummar Hausawa ta wannan haujin. Don haka sun zama tamkar malamai a cikin alumma.
Wannan wani fanni ne da mawak’an baka suka taka muhimmiyar rawa a adabin Hausawa. Kamar yadda aka sani, yawancin Hausawa musulunci ne addininsu. Shi kuwa addinin musulunci addini ne da aka saukar wa Annabin k’arshe, watau Annabi Muhammadu d’an Abdullahi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Wannan addini yana k’unshe da karantarwa da wa’azi da gargad’i a kan fannoni daban daban na ibada da suka shafi rayuwar d’an Adam. Daga ciki akwai hukunce-hukunce da suka shafi tsalki da sallah da azumi da zakka da aikin hajji da aure da tsarin zamantakewa da sauransu
Su kuwa mawak’an baka, suna da wani matsayi na musamman wajen rera wak’ok’i daban daban da ke k’unshe da bayani da wa’azi da gargad’i da kuma yin hannunka mai sanda a kan wad’annan shika shikai na addini. Ba za a fahinci hakan ba sai idan an yi la’akari da wasu daga cikin wak’ok’insu da aka gina a kan wad’annan dasussa. Ga kad’an daga ciki kamar yadda wani mawak’in ke cewa:
Asalin addini sai Sakkwato hak’k’an
In ana batun gidan Shehu
Ba a batun kowa
Abin da anka hwaro
Shi na yad dawo
Jama’armu malikawa
Shi wat ta’ba ganin
Limamin Madina ya zo
Ba mu yada gani nai ba
Zamaninka Bubakar
Kai kas sa ya zo
Domin k’ulla zumnci.
(Salisu Jankid’i: Wak’ar ‘Dibgau Bajinin dole )
Haka ma wani mawak’in ya k’ara da cewa:
Da karatu da zuwa makka
Tsoron Allah shi anka bid’a
(Muhammadu Sani Ingawa: Wak’ar ‘Dibgau Mamman Jikan Usmanu Tsoron ka a kai in anka gamu)
Haka kuma, ta ‘bangaren d’a’a a matsayin koyarwa ta addini, wani mawak’in yana cewa:
Nijeriya at tamu
Kowa da babba da yaro
Mu tsare ladabi da biyayya
Komi yana yin kyawo
(Muhammadu Ango Mai Tabshi; Wak’ar kowa yana son d’a’a )
Dangane da koyar da addini kuwa, mawak’an baka sun taka rawa sosai wurin zaburar da jama’a da su tashi su nemi ilimin addini.Ga abin da wannan mawak’in ke cewa:
Rike talakkawanka da kyawo
Kai masu hairi
Ka sa su hanyoyin musulunci
In sun ham’bare ka tank’waso su
In ko sun k’iya ka ba su kashi
(‘Dankwairo: Wak’ar babban jigo na Yari tura haushi)
A nan za mu ga cewa, bisa ga wad’annan d’iyan wak’ok’i da ke sama , mawak’an baka na Hausawa sun taimaka ainiun wurin karantar da addini. Wannan kuwa ana iya ganinsa a fili idan aka yi la’akari da wak’ar ‘Dankwairo inda yake cewa:
------------------------------
Ka sa su hanyoyin musulunci
In su ham’bare ka tankwaso su
In ko sun k’iya ka ba su kashi
Talakka bai san talakka ne ba
Wannan ya nuna shugabanni na da alhakin tilastawa talakkawansu da su yi rik’o da adddini da kuma biyayya ga addini, domin yana haifar da tarbiya a cikin al’umma. A wak’ar Muhammadu Anga Tabshi inda yake cewa:
-------------------------------
Kowa da babba da yaro
Mu tsare ladabi da biyayya
Komai yana yin kyawo
---------------------------------
Babban abin da wannan mawak’i ke k’ok’arin karantarwa shi ne koyar da ladabi da biyayya a cikin al’umma. Domin sha’anin addini abu ne da ke tafiya tare da ladabi da biyayyar karantarwar wannan addini. Don haka, makad’an baka na da wani matsayi na musamman wajen karantar da al’ummar Hausawa addininsu.
Wani ‘bangare da mawak’an baka na Hausa suka yi fice da zarra shi ne ta gefen wayar da kai. Ta wannan ‘bangare mawak’an baka sun taka rawar gani wajen sanar da al’umma abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwa irin ta yau da kullum. Hatta gwamnatoci da hukumomi a wasu lokutta kan yi amfani da mawak’an baka da wak’ok’insu wajen wayar da kan al’umma. Ba kuma za a iya fahintar wannan gagarumin k’ok’ari na mawak’an ba sai idan an yi la’akari da wad’annan d’iyan wak’a da ke k’asa da abin da suka k’unsa. Misali wani mawak’in yana cewa:
Naira da kwabo sabon kud’d’i
Idan ba ka san su ba
Matso kusa ni zan bayyana
( Haruna Uje :Wak’ar Canjin Kud’in Nijeriya daga Fam zuwa Naira da kwabo .1973)
Haka wani mawak’in na cewa game da abin da ya shafi yak’i da rashin d’a’a:
Yak’i mukai da rashin d’a’a
( Musa Dankwairo: Wak’ar war Against Indiscipline)
Ta fuskar kiwon lafiya kuwa, nan ma ba a bar su a baya ba domin sun yi wak’ok’ i da dama da suka shafi wayar da kai dangane da kiyon lafiya a cikin al’ummar Hausawa. Ga abin da wani mawak’in yake cewa:
Na taho in gaishe ki
Lafiya uwar jiki
Babu mai fushi da ke.
(Idi Dangiwa Zuru: Wak’ar lafiya uwar jiki)
Ta fuskar wayar da kai a kan aikin gona kuwa domin samar da abinci ga ‘yan k’asa, wani mawak’in yana cewa:
Aikin gona mu kama
Gwamnati na da niyyar
Shirin kowa abinci
(Muhammadu Ango Mai Tabshi: Wak’ar Gona)
Idan aka yi nazarin wad’annan d’iyan wak’ok’i da ke sama, za mu ga cewa, mawak’an sun taimaka wajen wayar da kan al’umma. Wannan abu ne da za mu gani a fili idan muka dibi wak’ar Haruna Uje ta canjin kud’in Nijeriya daga fan zuwa naira.Wannan wak’ar ta yi tasiri sosai a idon Hausawa domin a cikinta ne mawak’in ya fayyace yadda sabuwar naira take domin al’umma su iya tantance ta . Muhammadu Ango Mai Tabshi kuwa ya yi k’ok’arin jawo hankalin al’umma ne a kan muhimmancin noma domin wadata k’asa da abinci.
https://www.amsoshi.com/2017/06/28/amadu-maradun-ko-gobe-alu-ne-gwamnan-sakkwatawa/
Sanar da tarihi ya k’unshi ambaton abubuwan da suka auku a rayuwar yau da gobe wad’anda kuma suka shud’e. Shi ma wannan wani ‘bangare ne da ya shafi al’umma mai kuma muhimmamci, mawak’an baka na Hausa sun shahara wajen gina wak’ok’i daban daban da suka yi tasiri matuk’a wajen koyar da tarihi a al’umma. Ga k’ad’an daga cikin abin da wasu mawak’a ke cewa:
Kwana lafiya mai Daura
Jikan Abdu gwabron Giwa
Duba can cikin tarihi
Duba asalin sarautar Daura
Tun Kan’ana tun Lamarudu
Hab bisa Umarun Bagadaza
Hag gun magajiya Daurama
( Alhaji Mammam Shata : Wak’ar Sarkin Daura )
A wannan d’an wak’a, mawak’in ya sanar da mu wani abu game da tarihin asalin sarauta a k’asar Hausa cewa daga Daura ne. A ra’ayi na biyu kuwa ya gaya muna cewa asalin k’asar Hausa daga k’asar Larabawa ne wanda ake dangantawa da wani mutum wai shi Umarun Bagadaza. Kenan ta wannan wak’a, al’umma ta k’aru da sanin tarihin asalin Hausa da Hausawa wanda yake ba k’aramin al’amari ne ba.
Dangane da wannan, wani mawak’in ya ce:
--------------------------------------------------
Gwarzon shamaki na malan toron giwa
Baban Dodo ba a tam ma da batun banza
Ahmadu Allah ya ba ka albarkar Bello d’an Shehu
Yadda yay yi zaman duniya da imani yak’ k’aura
Amadu Allah ya ba ka albarkar Mu’azu d’an Bello
----------------------------------------------------------
(Narambad’a : Wak’ar Gwarzon Shamaki Na Yari )
A cikin wannan d’an wak’a, mawak’in ya sanar da mu jerin sunayen wasu daga cikin shugabannin Musulunci da suka yi mulkin daular Musulunci ta Sakkwato da suka gabata.
A wasu lokutta, sau da yawa mawak’an baka kan karantar da dasussan da suka shafi siyasa da mulki a wak’ok’insu. Akan sami wak’ok’i da yawa da ke bayani a kan yadda ake jagoranci da shugabanci na gari da ba kowa hak’k’insa da adalci da kuma kwatanta gaskiya. A cikin wasu wak’ok’i sukan yi hannunka mai sanda da wa’azi da gargad’i ga sarakuna da shugabannin al’umma ta yadda ya kamata su gudanar da sha’anin mulki da rik’e amanar talakkawansu da kuma ladabtar da su idan sun k’angare. Wasu wak’ok’in sukan k’unshi yadda siyasa ke gudana cikin k’asa da bayyana yadda jam’iya ke kafuwa da manufofinta da sauransu. Ana iya fahintar haka idan aka fahinci abin da wad’annan mawak’a ke cewa cikin d’iyan wak’ok’insu. Misali Naranbad’a na cewa:
Amadu diba mazan gaba diba na baya
Ka duba dama ka duba hauni
Ka san jama’ag ga da an nan
K’auye da birni ba su da jigo sai kai
( Ibrahim Narambad’a: Wak’ar Gogarman Tudu jikan Sanda )
Ga kuma abin da wani mawak’in ke cewa:
Rike talakkawanka da kyawo
Kai musu hairi
Ka sa su hanyoyin Musulunci
In ko sun k’iya ka ba su kashi
( Alhaji Musa Dankwairo: Wak’ar Babban Jigo na Yari)
Harwayau, wani mawak’in na cewa:
Wada Mainasara ya yi k’ok’ari
Ko Ibrahimu ya yi k’ok’ari
An d’e’be k’asa zamaninsa
Ibrahim sa’akka an game ta dut
( Ibrahim Narambad’a : Wak’ar Ibrahimu Naguraguri)
Haka wani mawak’in na cewa:
Mu zo ga N . P. N matattara
Ba ta bambanci cikin k’asa
National party sai hamdala
( Muhammadu Ango mai Tabshi: Wak’ar N P N )
Hausawa na yi wa sana’a kirari da cewa “ sana’a sa’a rashin sana’a rashin sa’a” Wannan kuwa wani ‘bangare ne mai muhimmanci a rayuwar Hausawa da mawak’an baka suka taka wata rawa ta musamman. Sana’a dai ita ce duk wata hanya halattacciya da mutum zai nemi abin da zai ci da samun biyan buk’ata.
Hak’ik’a, duk al’ummar da ke gurin bunk’asa tattalin arzikinta, dole ta kama hanyar sana’a haik’an. Ganin irin wannan matsayi na sana’a ya sa mawak’an baka na Hausa ba su yi tuya suka manta da albasa ba. Domin kuwa sun aiwatar da wak’ok’i daban daban da ke tsintsar bayani game da sana’a. Ga kad’an daga cikin abin da wani mawak’i ke cewa:
--------------------------
Kuma akwai mak’era namu
Na gargajiya suna da sana’ar hannu
Kuma magina namu
Na gargajiya suna da sana’ar haunnu
Kuma da sassakawa namu
Na gargajiya suna da sana’ar hannu
Kuma akwai majema namu
---------------------------------
(Sarkin Taushin Katsina: Wak’ar aladun gargajiya)
A k’arshe wannan mawak’in ya yi k’ok’arin karkasa mana sana’o’in Hausawa har da ambaton jinsin mutane da suka shahara ko aka fi sani da aiwatar da wannan sana’ar.
Mawak’an baka sun taka rawar gani wajen koyar da harshe a al’umma. Akan sami wak’ok’i da dama da suka yi tasiri matuk’a wajen koyar da fannonin harshe daban daban da suka k’unshi nahawu da adabi da balaga da furuci da dai sauran maganganun hikima da sarrafa harshe. Babu shakka, ana fahintar wannan musammam idan an yi la’akari da d’iyan wak’ok’in da ke biye:
Haka Shata yana cewa:
Rak’umi girmanka na wofi
‘Dan akuya ya fi ka d’uwaiwai
(Alhaji Mamman Shata: Wak’ar ‘Dan dutse na Bilbis)
Wad’annan d’iyan wak’a da ke sama sun yi k’ok’arin kawo muna Karin Magana, wanda wani nau’i ne a ‘bangaren adabi.
Wannan wani ‘bangare ne da mawak’a ke k’ok’arin cusa wa jama’a ra’ayin k’aunar k’asarsu, da son ganin cewa ta bunk’asa ta kuma ci gaba tamkar kowace k’asa a duniya. A nan mawak’a kan yi amfani da tubalai daban daban wurin gina wannan jigo. Ire iren wad’annan tubalai sun had’a da gargad’i da fad’akarwa ko wayar da kai da sauransu. A wannan muhallin Shata ya k’ara cewa:
‘Yan Arewa ku bar bacci
Nijeriyarmu akwai dad’i
K’asar Afrika bak’ar fata
In ka yi yawo cikin nata duk
Ba kamar Nijeriya gidan dad’i
Balle Arewa uwad dad’i
( Alhaji Mamman Shata : Wak’ar ‘Yan Arewa ku bar bacci )
Har ila yau, wani mawak’in Dan ba’u na cewa:
Ina Yarbawa, Nufawa
Ina jama’ar Ibo
Da ku jama’ar Tibi
Duk ku taru mu je gaba d’ai.
(Musa ‘Dan ba’u: Wak’ar had’in kan k’asa)
A nan za a ga cewa, wad’annan mawak’a suna k’ok’arin kira ne ga jama’ar k’asar nan baki d’aya da su zama masu k’aunar juna domin k’asa ta samu ta ci gaba. Za a kuma yarda cewa, yin wannan kuwa ba k’aramar gudunmawa ne wad’annan mawak’a ke bayarwa ba domin samun cin gaban k’asa.
Mawak’an baka kamar yadda mak’alar ta bayyana k’arara ba abin wofintarwa ba ne ga jama’a domin d’aukacin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma musamman ta ‘bangaren ilimi da tattalin arzikin k’asa da zaman lafiya da sauransu. Bisa ga wannan ne muk’alar ta kawo shawarwari don ganin an k’arfafa ma mawak’an baka gwuiwa ta yadda za su k’ara dagewa wurin wanzar da kyawawan manufofinsu a cikin al’umma.
Cima kwance da aka d’auki mawak’anmumu na baka ba adalci ba ne gare su ba da ma wani Bahaushe, domin manufofin da suke iya yad’awa wanda duk ya shafi fannoni iri daban daban wad’anda suka had’a da na ilimi da wayar da kai da sana’a da addini da sauransu.
Duk wad’annan fannoni da aka ambata a sama an yi k’ok’arin kawo wasu d’iyan wak’ok’i wad’anda suke jaddada tasirinsu a cikin al’ummar Hausawa. Bisa ga k’warya-k’waryan sharhin d’iyan wak’ok’in da aka yi, za a ga cewa mawak’an baka sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar Hausawa musamman ta fuskar wayar da kai a kan abin da ya shafi zaman lafiya da tattalin arziki da siyasa da addini da kyawawan huld’od’i na zamantakewa a tsakanin al’umma da dai sauransu. Kenan mawak’an baka tamkar malamai ne a cikin al’umma, don haka ba abin wofintarwa ba ne idan muka yi la’akari da matsayinsu da irin gudunmawarsu ga jama’a.
https://www.amsoshi.com/2017/06/28/dan-shaaibu-sarkin-yamma-alu-wamakko/
MANAZARTA
Abba M , & Zulyadaini B. ( 2000) Nazari kan Wak’ar Baka ta Hausa. Zariya. Gaskiya Corporation LTD.
Birnin Tudu S Y (2002) “ Jigo da Salon RubutattunWak’ok’in Furu’a na Karni na Ashirin” Kundin Digiri na Uku. Sahen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Sakkwato.
Gusau S M .(2011) Makad’a da Mawak’an Hausa Littafi na ‘Daya. Kano . Usman Al-Amin Publishing Company.
Gusau S M (1993) Jagoran Nazarin Wak’a. Fisbas Media Service, Kaduna.
Mashi M B (1986) “ Wak’ok’in Baka na Siyasa” Kundin digiri na Biyu. Sashen koyar da harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero Kano.
Umar M B ( 2003) Tasiri da Yad’uwar Adabin na Hausa. A cikin Zaria Journal of Language Studies. Vol.1 No. 1 .
Yahya A B. (1999) Salo Asirin Wak’a. Kaduna : Fisbas Media Service.
Yahya A B. (1997) Jigon Nazarin Wak’a. Kaduna: Fisbas Media Service.
Gumi M F. (2008) “ Tsumagiyar Kan Hanya: Nazarin Wasu Wak’ok’in Yunwa na Baka a Sakkwato da Zamfara da Kabi”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijerya, Jami’ar Sakkwato.
Absract
Today in many part of the world, oral singers play a vital role towards the national development of many countries. They save as a means for expressing human feelings towards achieving greater height in the development of human mind. Today the position of the songs in modern and traditional political activities in Hausa communities can not be overemphasized. For instance, it is through these songs the Nigerian political parties are educating their electorate on their manifestors and other important things. It is in view of the above functions attached to the oral singers (songs) in Hausa communities; this paper intends to flash back on the role of these singers towards the national development in Hausa communities. As such,the paper intends to reviewed some areas of national development as sighted by many singers among which includeds: education,religious ,puplic awareness, history,administration,politics,accupation, languages among others.Tsakure
A yau, a mafi yawan sassan duniya, mawakan baka suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaban kasashensu ta fuskoki daban daban. Wadannan mawak’an baka, suna bayyana k’udurorin da ke zuciyarsu da na al’ummarsu ta yadda za su samu biyan buk’atocinsu. Don haka, a yau matsayin mawakan baka na zamani da na gargajiya musamman ta fuskar siyasa a bayyane yake ba sai an jaddada ba. Alal misali, ta hanyar wad’annan mawak’an bakan ne ‘yan siyasa suke tallata manufofinsu da sauran buk’atocinsu ga al’umma. A bisa ga irin wannan muhimmanci da mawak’an baka ke da shi a k’asar Hausa, wannan takardar ke da manufar waiwaye a kan muhimmancin wad’annan mawak’an wajen samar da ci gaban k’asa ga al’ummar Hausawa. Don haka, wannan takardar ta k’udurci waiwayen gudummawar wad’annan mawak’a ta fuskoki daban daban a bakin wasu mawak’a a ‘bangarorin ci gaban al’umma da suka had’a da: Fannin inganta ilimi da koyar da addini da wayar da kai da tarihi da sha’anin mulki da sana’o’i da harshe da kishin k’asa da sauransu.1.0 GABATARWA
An dad’e ana yi wa mawak’an baka da wak’ok’insu kallon hadarin kaji a k’asar Hausa. An d’auke su a matsayin wani gungun mutane da ba su da wani matsayi da daraja ko wani muhimmanci a al’umma. Sau da yawa akan kalle su a matsayi maras darajja ko wani muhimmanci a al’umma. Wani lokaci kuwa a kalle su a matsayin cima-kwance marasa abin yi da suka wofintar da rayuwarsu ta hanyar dogaro da kwad’ayin abin wasu a cikin al’umma. Irin wannan matsayi kuwa ya yi daidai da abin da Bahaushe ke cewa ‘ Maso abin wani wawa’.
A yau abubuwa sun sauya, amma wani abin takaici shi ne, akasarin mutane sun jahilci wannan sauyi, manufar wannan k’asida ita ce fitowa da irin rawar da wad’annan makad’a ke takawa a rayuwar wannan al’umma a fili, da tunanin cewa yin haka zai taimaka wajen kawar da jahiltar su da aka yi. Domin kuwa ko ba komai, suna da rawar takawa musamman a wannan hali da k’asa take ciki na lalacewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ilimi da matsalolin siyasa da sauransu. Bisa ga wannan , k’asidar za ta yi k’ok’arin kawo wasu d’iyan wak’ok’i daga mawak’an baka daban daban domin tabbatar da muhimmancinsu a cikin al’ummar Hausawa.
https://www.amsoshi.com/2017/06/30/danmaraya-jos-jikan-umar-a-gaishe-ka/
2.0 WAIWAYE KAN MA’ANAR WAk’A
Wak’ar baka dad’ad’d’iyar abu ce wadda ta wanzu tun wani lokaci mai nisa da ya shud’e tsawon zamanna. Bahaushe ya k’agi wak’a ne tun kafin ya yi cud’anya da wata al’ada da kuma jama’a na k’etare. (Fadama 2008:79)
Masana da manazarta adabin Hausa sun bayyana ma’anar wak’a ta fuskoki daban daban. Kad’an daga cikin wad’annan masana da manazarta da suka yi k’ok’arin bayyana ma’anar wak’a sun had’a da; A B Yahya wanda ke da ra’ayin cewa:
“ Wak’a tsararriyar maganar hikima ce da ta k’unshi sak’o cikin za’ba’b’bun kalmomi
da aka auna domin maganar ta reru ba fad’a kurum ba” (Yahya 1997:5)
Anan kenan, a wajen ‘yankallo, watau wanda ba mawak’i ba , ba kuma manazarci wak’a ba, yana kallon wak’a a matsayin maganar da ake rerawa wadda ke da dad’in ji har ga zuciya, kuma tana fayyace gaskiya da kawo nishad’i.
Haka Fadama (2008:80) ya rawaito Gusau (2003) cewa “wak’ar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa ga’ba-ga’ba bisa k’aidojin tsari da daidaituwa a rera cikin sautin murya da amsa amon kari da kid’a da ‘yan amshi”
Baya ga wannan, shima Birnin Tudu (2002:23) ya rawaito Dangambo (1982) ya bayyana ma’anar wak’a kamar haka:
“ Wak’a wani furuci ne ( lafazi ko salo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko k’a’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salo mai armashi” Birnin Tudu (2002:24) ya k’ara rawaito Umar (1980) ya ce “wak’a tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka wad’anda ake kira baitoci ko d’iyoyi kuma ake rerawa da wani sautin murya na musamman”
A wata ma’anar an dubi wak’a a matsayin “ Wata had’akar kalmomi da kid’a ne cikin tsari mai bayar da armashi ga mai sauraro, a inda shi mai sauraren zai iya tantance wannan had’aka ta kid’a da jerin kalmomin” (Mashi 1986)
Ta la’akari da ma’anonin da masana da manazarta suka bayar ana iya bayyana wak’a da cewa
tana zuwa a sigar gunduwowin sautuka wad’anda ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman
Kad’an daga cikin ra’ayoyin masana dangane ma’anar wak’a kenan. Mawak’an baka mutane ne masu basira da fasaha da ke aiwatar da wak’ok’i iri iri a fannoni daban daban na al’ummar Hausawa. Fahintar rawar da suke takawa ba zai kammalu ba sai fa idan an yi nazarin wasu daga cikin wak’ok’insu tare da la’akari da irin tasirinsu a fannoni daban daban na rayuwa. Yin haka zai ba da damar yi wa wad’annan gungun mutane da wak’ok’insu adalci tare da kawar da irin kallon-kallon da ake yi musu a matsayin marasa aikin yi a cikin al’umma. Wannan kuwa ita ce manufar wanna k’asida tamu. Don haka, k’asidar ta dubi wasu daga cikin muhimman ‘bangarori da suka shafi gina rayuwar al’umma mai nagarta domin samun bunk’asar k’asa.
3.0 Koyar da Ilimi da ‘Daukaka Martabarsa
Hausawa kan yi wa Ilimi kirari da cewa, shi ne gishirin zaman duniya, wanda sai da shi ne rayuwa ke inganta. Saboda muhimmancinsa ga rayuwa ya sa da wuya a iya tafiyar da komi sai da ilimi a cikin al’umma. Wannan shi ya sanya mawak’an baka aiwatar da wak’ok’i masu d’imbin yawa da suka taka muhimmiyar rawa wajen ilmantar da al’umma ta fuskoki daban daban . A cikin wad’annan wak’ok’i ko d’iyan wak’ok’in, mawak’an sun yi k’ok’arin fitar da matsayin ilimi da amfaninsa da kuma irin k’ima da daraja da matsayin duk mutumin da ya nemi ilimi ya same shi ya kuma yi aiki da shi a cikin al’umma. Ga dai abin da wani manazarci ke cewa dangane da wannan al’amari:
“ Kid’a da wak’a a k’asar Hausa wani ginshik’in
abu ne da ake aiwatarwa don ilimntarwa ko
sadarwa nishad’antarwa, ko bayar da wata
gudummawa ta musamman.
Kusan kid’a ya yi rawa ya yi tsaki , ya durmuya
sosai a cikin rayuwar Bahaushe,
Musamman rayuwar da ta danganci zamantakewa
da sana’o’i da bukukuwa da lokuttan shak’atawa.”
(Gusau, 2005)
Dangane da wannan , ga kad’an daga cikin abin da wad’annan mawak’an ke cewa:
Jahilci rigar k’aya ne
Yara mu je makaranta
Mu yi karatu
(Muhammadu Bello Gwaranyo: Wak’ar jahilci rigar k’aya)
A wani d’an wak’a, mawak’in ya ci gaba da cewa:
Wanda bai san nun ara ba
ABCD bai iya ba
Ka tabbata jakin duniya ne
A k’ark’ashin wad’annan d’iyan wak’a, mawak’in ya yi k’ok’arin bayyana matsayin ilimi da matsayin mutumin da ake ganin yana da ilimi a idon al’umma. Haka ya yi k’ok’arin nuna wa al’umma matsayin jahilci wanda yake kishiya ne ga ilimi da kuma matsayin wanda ba shi da ilimi a cikin al’umma. Ya kuma yi hakan ne ta hanyar siffanta jahilci da rigar k’aya , rigar da take mai matuk’ar k’unci wajen sakawa. Kenan , duk mutumin da ya kasa neman ilimi tamkar ya bar kansa cikin k’uncin jahilci. Kamar dai ya saka wa kansa riga ce ta k’aya mai bak’in k’unci da wuyar d’ebewa.
Haka kuma wani mawak’in ya k’ara karantar da mu wani abu mai muhimmanci game da ilimi inda yake cewa:
Makaranta uwar k’warai ta
Kuma mai rik’on d’iya
Ta rik’i d’anta
Ta yi mai sutura ya shigo
(Abdu Inka Bakura: Wak’ar mu d’au ilimi gaskiya)
A wannan d’iyan wak’ar, mawak’in ya bayyana makaranta a matsayin uwa wadda take shayar da d’anta, ta rene shi, ta kuma tayar da shi ya zama mai amfani ga al’umma. Kenan ya fito muna da matsayin ilimi a nan wanda yake tayar da mutum, ya d’aukaka matsayinsa, ya sanya shi cikin sutura ta d’aukaka. Haka dai mawak’in ya ci gaba da cewa:
Makaranta uwar k’warai ta
Kuma mai rik’on d’iya
Ta rike d’anta
Ta yi mai mota ya shigo.
(Abdu Inka Bakura: Wak’ar mu d’au ilimi gaskiya gwamnati horo ta kai)
Wannan ya k’ara fito mana a fili da yadda mawak’an baka na Hausa ke k’ok’arin karantar da al’umma matsayin ilimi da kuma amfaninsa ga rayuwa. A dubi yadda bayan makaranta ta raya mutum ta tarbiyyantar da shi ta kuma sanya shi mai matsayi abin yabo a cikin al’umma, ba ta tsaya nan ba, har da ba shi damar mallakar abin hawa watau mota. Kenan, mawak’in ya fito muna a fili da irin fa’idar da ake samu bayan samun ilimi. Sanin kowa ne, mota wata abu ce ta alfarma da ba kowane mutum ke mallakarta ba, sai fa wanda Allah ya d’aukaka.
Har wayau, mawak’in ya ci gaba da bayyana matsayin makaranta da fa’idarta tare da kira ga iyaye da a saka yara a makaranta domin su nemi ilimi. Ga abin da ya ci gaba da cewa:
A kai yara su koyi ilimi
Makaranta ta gyara d’anta
Ta hora maka shi
ta kuma shirya maka shiya
(Abdu Inka Bakura: Wak’ar mu d’au ilimi gaskiya gwamnati horo ta kai)
A karshe sai mawak’in ya bayyana muna matsayin mutumin da ya tashi babu ilimi inda yake cewa:
Ilimi uwa uba ne
Kwat tashi babu ilimi
Yag girma babu ilimi
Ko ya bid’a buk’ata
Yac ce a ba shi
Ba a kulawa shiya.
(Abdu Inka Bakura: Wak’ar mu d’au ilimi gaskiya gwamnati horo ta kai)
Bayan mawak’in ya fad’akar da al’umma matsayin ilimi da muhimmancinsa, tare da neman a saka yara makaranta domin su ci wannan gajiya, a d’aya ‘bangaren ya kuma fito mana da illolin da ke tattare da rashin ilimi ga duk wani mutum a al’amurransa na yau da kullum. Ya fito da wannan a sarari inda ya nuna cewa komin girman mutum ko matsayinsa ko kud’insa matuk’ar bai da ilimi, to kuwa kud’insa da girmansa ba su yi masa wani dogon amfani.
A nan za mu ga cewa. bisa ga wad’annan d’iyan wak’ok’i da muka yi nazari akai, mawak’an baka sun taka muhimmiyar rawa wajen ilimantar da al’ummar Hausawa ta wannan haujin. Don haka sun zama tamkar malamai a cikin alumma.
4.0 KOYAR DA ADDINI
Wannan wani fanni ne da mawak’an baka suka taka muhimmiyar rawa a adabin Hausawa. Kamar yadda aka sani, yawancin Hausawa musulunci ne addininsu. Shi kuwa addinin musulunci addini ne da aka saukar wa Annabin k’arshe, watau Annabi Muhammadu d’an Abdullahi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Wannan addini yana k’unshe da karantarwa da wa’azi da gargad’i a kan fannoni daban daban na ibada da suka shafi rayuwar d’an Adam. Daga ciki akwai hukunce-hukunce da suka shafi tsalki da sallah da azumi da zakka da aikin hajji da aure da tsarin zamantakewa da sauransu
Su kuwa mawak’an baka, suna da wani matsayi na musamman wajen rera wak’ok’i daban daban da ke k’unshe da bayani da wa’azi da gargad’i da kuma yin hannunka mai sanda a kan wad’annan shika shikai na addini. Ba za a fahinci hakan ba sai idan an yi la’akari da wasu daga cikin wak’ok’insu da aka gina a kan wad’annan dasussa. Ga kad’an daga ciki kamar yadda wani mawak’in ke cewa:
Asalin addini sai Sakkwato hak’k’an
In ana batun gidan Shehu
Ba a batun kowa
Abin da anka hwaro
Shi na yad dawo
Jama’armu malikawa
Shi wat ta’ba ganin
Limamin Madina ya zo
Ba mu yada gani nai ba
Zamaninka Bubakar
Kai kas sa ya zo
Domin k’ulla zumnci.
(Salisu Jankid’i: Wak’ar ‘Dibgau Bajinin dole )
Haka ma wani mawak’in ya k’ara da cewa:
Da karatu da zuwa makka
Tsoron Allah shi anka bid’a
(Muhammadu Sani Ingawa: Wak’ar ‘Dibgau Mamman Jikan Usmanu Tsoron ka a kai in anka gamu)
Haka kuma, ta ‘bangaren d’a’a a matsayin koyarwa ta addini, wani mawak’in yana cewa:
Nijeriya at tamu
Kowa da babba da yaro
Mu tsare ladabi da biyayya
Komi yana yin kyawo
(Muhammadu Ango Mai Tabshi; Wak’ar kowa yana son d’a’a )
Dangane da koyar da addini kuwa, mawak’an baka sun taka rawa sosai wurin zaburar da jama’a da su tashi su nemi ilimin addini.Ga abin da wannan mawak’in ke cewa:
Rike talakkawanka da kyawo
Kai masu hairi
Ka sa su hanyoyin musulunci
In sun ham’bare ka tank’waso su
In ko sun k’iya ka ba su kashi
(‘Dankwairo: Wak’ar babban jigo na Yari tura haushi)
A nan za mu ga cewa, bisa ga wad’annan d’iyan wak’ok’i da ke sama , mawak’an baka na Hausawa sun taimaka ainiun wurin karantar da addini. Wannan kuwa ana iya ganinsa a fili idan aka yi la’akari da wak’ar ‘Dankwairo inda yake cewa:
------------------------------
Ka sa su hanyoyin musulunci
In su ham’bare ka tankwaso su
In ko sun k’iya ka ba su kashi
Talakka bai san talakka ne ba
Wannan ya nuna shugabanni na da alhakin tilastawa talakkawansu da su yi rik’o da adddini da kuma biyayya ga addini, domin yana haifar da tarbiya a cikin al’umma. A wak’ar Muhammadu Anga Tabshi inda yake cewa:
-------------------------------
Kowa da babba da yaro
Mu tsare ladabi da biyayya
Komai yana yin kyawo
---------------------------------
Babban abin da wannan mawak’i ke k’ok’arin karantarwa shi ne koyar da ladabi da biyayya a cikin al’umma. Domin sha’anin addini abu ne da ke tafiya tare da ladabi da biyayyar karantarwar wannan addini. Don haka, makad’an baka na da wani matsayi na musamman wajen karantar da al’ummar Hausawa addininsu.
5.0 WAYAR DA KAI
Wani ‘bangare da mawak’an baka na Hausa suka yi fice da zarra shi ne ta gefen wayar da kai. Ta wannan ‘bangare mawak’an baka sun taka rawar gani wajen sanar da al’umma abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwa irin ta yau da kullum. Hatta gwamnatoci da hukumomi a wasu lokutta kan yi amfani da mawak’an baka da wak’ok’insu wajen wayar da kan al’umma. Ba kuma za a iya fahintar wannan gagarumin k’ok’ari na mawak’an ba sai idan an yi la’akari da wad’annan d’iyan wak’a da ke k’asa da abin da suka k’unsa. Misali wani mawak’in yana cewa:
Naira da kwabo sabon kud’d’i
Idan ba ka san su ba
Matso kusa ni zan bayyana
( Haruna Uje :Wak’ar Canjin Kud’in Nijeriya daga Fam zuwa Naira da kwabo .1973)
Haka wani mawak’in na cewa game da abin da ya shafi yak’i da rashin d’a’a:
Yak’i mukai da rashin d’a’a
( Musa Dankwairo: Wak’ar war Against Indiscipline)
Ta fuskar kiwon lafiya kuwa, nan ma ba a bar su a baya ba domin sun yi wak’ok’ i da dama da suka shafi wayar da kai dangane da kiyon lafiya a cikin al’ummar Hausawa. Ga abin da wani mawak’in yake cewa:
Na taho in gaishe ki
Lafiya uwar jiki
Babu mai fushi da ke.
(Idi Dangiwa Zuru: Wak’ar lafiya uwar jiki)
Ta fuskar wayar da kai a kan aikin gona kuwa domin samar da abinci ga ‘yan k’asa, wani mawak’in yana cewa:
Aikin gona mu kama
Gwamnati na da niyyar
Shirin kowa abinci
(Muhammadu Ango Mai Tabshi: Wak’ar Gona)
Idan aka yi nazarin wad’annan d’iyan wak’ok’i da ke sama, za mu ga cewa, mawak’an sun taimaka wajen wayar da kan al’umma. Wannan abu ne da za mu gani a fili idan muka dibi wak’ar Haruna Uje ta canjin kud’in Nijeriya daga fan zuwa naira.Wannan wak’ar ta yi tasiri sosai a idon Hausawa domin a cikinta ne mawak’in ya fayyace yadda sabuwar naira take domin al’umma su iya tantance ta . Muhammadu Ango Mai Tabshi kuwa ya yi k’ok’arin jawo hankalin al’umma ne a kan muhimmancin noma domin wadata k’asa da abinci.
https://www.amsoshi.com/2017/06/28/amadu-maradun-ko-gobe-alu-ne-gwamnan-sakkwatawa/
6.0 SANAR DA TARIHI
Sanar da tarihi ya k’unshi ambaton abubuwan da suka auku a rayuwar yau da gobe wad’anda kuma suka shud’e. Shi ma wannan wani ‘bangare ne da ya shafi al’umma mai kuma muhimmamci, mawak’an baka na Hausa sun shahara wajen gina wak’ok’i daban daban da suka yi tasiri matuk’a wajen koyar da tarihi a al’umma. Ga k’ad’an daga cikin abin da wasu mawak’a ke cewa:
Kwana lafiya mai Daura
Jikan Abdu gwabron Giwa
Duba can cikin tarihi
Duba asalin sarautar Daura
Tun Kan’ana tun Lamarudu
Hab bisa Umarun Bagadaza
Hag gun magajiya Daurama
( Alhaji Mammam Shata : Wak’ar Sarkin Daura )
A wannan d’an wak’a, mawak’in ya sanar da mu wani abu game da tarihin asalin sarauta a k’asar Hausa cewa daga Daura ne. A ra’ayi na biyu kuwa ya gaya muna cewa asalin k’asar Hausa daga k’asar Larabawa ne wanda ake dangantawa da wani mutum wai shi Umarun Bagadaza. Kenan ta wannan wak’a, al’umma ta k’aru da sanin tarihin asalin Hausa da Hausawa wanda yake ba k’aramin al’amari ne ba.
Dangane da wannan, wani mawak’in ya ce:
--------------------------------------------------
Gwarzon shamaki na malan toron giwa
Baban Dodo ba a tam ma da batun banza
Ahmadu Allah ya ba ka albarkar Bello d’an Shehu
Yadda yay yi zaman duniya da imani yak’ k’aura
Amadu Allah ya ba ka albarkar Mu’azu d’an Bello
----------------------------------------------------------
(Narambad’a : Wak’ar Gwarzon Shamaki Na Yari )
A cikin wannan d’an wak’a, mawak’in ya sanar da mu jerin sunayen wasu daga cikin shugabannin Musulunci da suka yi mulkin daular Musulunci ta Sakkwato da suka gabata.
7.0 Koyar da mulki da siyasa
A wasu lokutta, sau da yawa mawak’an baka kan karantar da dasussan da suka shafi siyasa da mulki a wak’ok’insu. Akan sami wak’ok’i da yawa da ke bayani a kan yadda ake jagoranci da shugabanci na gari da ba kowa hak’k’insa da adalci da kuma kwatanta gaskiya. A cikin wasu wak’ok’i sukan yi hannunka mai sanda da wa’azi da gargad’i ga sarakuna da shugabannin al’umma ta yadda ya kamata su gudanar da sha’anin mulki da rik’e amanar talakkawansu da kuma ladabtar da su idan sun k’angare. Wasu wak’ok’in sukan k’unshi yadda siyasa ke gudana cikin k’asa da bayyana yadda jam’iya ke kafuwa da manufofinta da sauransu. Ana iya fahintar haka idan aka fahinci abin da wad’annan mawak’a ke cewa cikin d’iyan wak’ok’insu. Misali Naranbad’a na cewa:
Amadu diba mazan gaba diba na baya
Ka duba dama ka duba hauni
Ka san jama’ag ga da an nan
K’auye da birni ba su da jigo sai kai
( Ibrahim Narambad’a: Wak’ar Gogarman Tudu jikan Sanda )
Ga kuma abin da wani mawak’in ke cewa:
Rike talakkawanka da kyawo
Kai musu hairi
Ka sa su hanyoyin Musulunci
In ko sun k’iya ka ba su kashi
( Alhaji Musa Dankwairo: Wak’ar Babban Jigo na Yari)
Harwayau, wani mawak’in na cewa:
Wada Mainasara ya yi k’ok’ari
Ko Ibrahimu ya yi k’ok’ari
An d’e’be k’asa zamaninsa
Ibrahim sa’akka an game ta dut
( Ibrahim Narambad’a : Wak’ar Ibrahimu Naguraguri)
Haka wani mawak’in na cewa:
Mu zo ga N . P. N matattara
Ba ta bambanci cikin k’asa
National party sai hamdala
( Muhammadu Ango mai Tabshi: Wak’ar N P N )
8.0 KOYAR DA SANA’A
Hausawa na yi wa sana’a kirari da cewa “ sana’a sa’a rashin sana’a rashin sa’a” Wannan kuwa wani ‘bangare ne mai muhimmanci a rayuwar Hausawa da mawak’an baka suka taka wata rawa ta musamman. Sana’a dai ita ce duk wata hanya halattacciya da mutum zai nemi abin da zai ci da samun biyan buk’ata.
Hak’ik’a, duk al’ummar da ke gurin bunk’asa tattalin arzikinta, dole ta kama hanyar sana’a haik’an. Ganin irin wannan matsayi na sana’a ya sa mawak’an baka na Hausa ba su yi tuya suka manta da albasa ba. Domin kuwa sun aiwatar da wak’ok’i daban daban da ke tsintsar bayani game da sana’a. Ga kad’an daga cikin abin da wani mawak’i ke cewa:
--------------------------
Kuma akwai mak’era namu
Na gargajiya suna da sana’ar hannu
Kuma magina namu
Na gargajiya suna da sana’ar haunnu
Kuma da sassakawa namu
Na gargajiya suna da sana’ar hannu
Kuma akwai majema namu
---------------------------------
(Sarkin Taushin Katsina: Wak’ar aladun gargajiya)
A k’arshe wannan mawak’in ya yi k’ok’arin karkasa mana sana’o’in Hausawa har da ambaton jinsin mutane da suka shahara ko aka fi sani da aiwatar da wannan sana’ar.
9.0 KOYAR DA HARSHE:
Mawak’an baka sun taka rawar gani wajen koyar da harshe a al’umma. Akan sami wak’ok’i da dama da suka yi tasiri matuk’a wajen koyar da fannonin harshe daban daban da suka k’unshi nahawu da adabi da balaga da furuci da dai sauran maganganun hikima da sarrafa harshe. Babu shakka, ana fahintar wannan musammam idan an yi la’akari da d’iyan wak’ok’in da ke biye:
Haka Shata yana cewa:
Rak’umi girmanka na wofi
‘Dan akuya ya fi ka d’uwaiwai
(Alhaji Mamman Shata: Wak’ar ‘Dan dutse na Bilbis)
Wad’annan d’iyan wak’a da ke sama sun yi k’ok’arin kawo muna Karin Magana, wanda wani nau’i ne a ‘bangaren adabi.
10.0 KISHIN K’ASA:
Wannan wani ‘bangare ne da mawak’a ke k’ok’arin cusa wa jama’a ra’ayin k’aunar k’asarsu, da son ganin cewa ta bunk’asa ta kuma ci gaba tamkar kowace k’asa a duniya. A nan mawak’a kan yi amfani da tubalai daban daban wurin gina wannan jigo. Ire iren wad’annan tubalai sun had’a da gargad’i da fad’akarwa ko wayar da kai da sauransu. A wannan muhallin Shata ya k’ara cewa:
‘Yan Arewa ku bar bacci
Nijeriyarmu akwai dad’i
K’asar Afrika bak’ar fata
In ka yi yawo cikin nata duk
Ba kamar Nijeriya gidan dad’i
Balle Arewa uwad dad’i
( Alhaji Mamman Shata : Wak’ar ‘Yan Arewa ku bar bacci )
Har ila yau, wani mawak’in Dan ba’u na cewa:
Ina Yarbawa, Nufawa
Ina jama’ar Ibo
Da ku jama’ar Tibi
Duk ku taru mu je gaba d’ai.
(Musa ‘Dan ba’u: Wak’ar had’in kan k’asa)
A nan za a ga cewa, wad’annan mawak’a suna k’ok’arin kira ne ga jama’ar k’asar nan baki d’aya da su zama masu k’aunar juna domin k’asa ta samu ta ci gaba. Za a kuma yarda cewa, yin wannan kuwa ba k’aramar gudunmawa ne wad’annan mawak’a ke bayarwa ba domin samun cin gaban k’asa.
11.0 SHAWARWARI
Mawak’an baka kamar yadda mak’alar ta bayyana k’arara ba abin wofintarwa ba ne ga jama’a domin d’aukacin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma musamman ta ‘bangaren ilimi da tattalin arzikin k’asa da zaman lafiya da sauransu. Bisa ga wannan ne muk’alar ta kawo shawarwari don ganin an k’arfafa ma mawak’an baka gwuiwa ta yadda za su k’ara dagewa wurin wanzar da kyawawan manufofinsu a cikin al’umma.
- Ya zama wajibi ga jama’a su fitar da irin kallon hadarin kajin da suke wa mawak’an baka a matsayin marok’a, a maimakon haka kamata ya yi su k’ara k’afafa masu gwuiwa su k’ara himmatuwa wajen wanzar da kyawawan manufofinsu.
- A manufofin Gwamnati musamman abin da ya shafi zaman lafiya da kiwon lafiya da muhimmancin ilimi da sauran wasu manufofi na hukuma da ake so jama’a su ba da goyon baya a kai.
- Kafafen watsa labarai su jawo su ga jiki domin samun sauk’in isar da sak’o ga jama’a.
- A kafa hukuma ta mawak’an baka na Hausa domin ‘bata gurbi
- A yanka ma duk wani fitaccecn mawak’i alawus-alawus. Domin wannan shi zai hana su yawan yin wak’ok’i barkatai don neman na goro.
12.0 KAMMALAWA
Cima kwance da aka d’auki mawak’anmumu na baka ba adalci ba ne gare su ba da ma wani Bahaushe, domin manufofin da suke iya yad’awa wanda duk ya shafi fannoni iri daban daban wad’anda suka had’a da na ilimi da wayar da kai da sana’a da addini da sauransu.
Duk wad’annan fannoni da aka ambata a sama an yi k’ok’arin kawo wasu d’iyan wak’ok’i wad’anda suke jaddada tasirinsu a cikin al’ummar Hausawa. Bisa ga k’warya-k’waryan sharhin d’iyan wak’ok’in da aka yi, za a ga cewa mawak’an baka sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar Hausawa musamman ta fuskar wayar da kai a kan abin da ya shafi zaman lafiya da tattalin arziki da siyasa da addini da kyawawan huld’od’i na zamantakewa a tsakanin al’umma da dai sauransu. Kenan mawak’an baka tamkar malamai ne a cikin al’umma, don haka ba abin wofintarwa ba ne idan muka yi la’akari da matsayinsu da irin gudunmawarsu ga jama’a.
https://www.amsoshi.com/2017/06/28/dan-shaaibu-sarkin-yamma-alu-wamakko/
MANAZARTA
Abba M , & Zulyadaini B. ( 2000) Nazari kan Wak’ar Baka ta Hausa. Zariya. Gaskiya Corporation LTD.
Birnin Tudu S Y (2002) “ Jigo da Salon RubutattunWak’ok’in Furu’a na Karni na Ashirin” Kundin Digiri na Uku. Sahen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Sakkwato.
Gusau S M .(2011) Makad’a da Mawak’an Hausa Littafi na ‘Daya. Kano . Usman Al-Amin Publishing Company.
Gusau S M (1993) Jagoran Nazarin Wak’a. Fisbas Media Service, Kaduna.
Mashi M B (1986) “ Wak’ok’in Baka na Siyasa” Kundin digiri na Biyu. Sashen koyar da harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero Kano.
Umar M B ( 2003) Tasiri da Yad’uwar Adabin na Hausa. A cikin Zaria Journal of Language Studies. Vol.1 No. 1 .
Yahya A B. (1999) Salo Asirin Wak’a. Kaduna : Fisbas Media Service.
Yahya A B. (1997) Jigon Nazarin Wak’a. Kaduna: Fisbas Media Service.
Gumi M F. (2008) “ Tsumagiyar Kan Hanya: Nazarin Wasu Wak’ok’in Yunwa na Baka a Sakkwato da Zamfara da Kabi”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijerya, Jami’ar Sakkwato.

2 Comments
[…] Waiwaye A Kan Tasirin Makad’an Baka A Cikin Al’ummar Hausawa […]
ReplyDelete[…] Waiwaye A Kan Tasirin Makad’an Baka A Cikin Al’ummar Hausawa […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.