Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Lokacin Abu A Yi Shi

Amsoshi

DAGA


 


ALIYU MUHAMMAD BUNZA


Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya


Jami’ar Umaru Musa Yar’adua


Katsina, Nijeriya.


Takardar da aka gabatar a bukin k’addamar da Littafin Kyakkyawar Safiya Tarihin Mai Girma Sarkin Kabin Yabo Alhaji (Dr) Muhammadu Maiturare II, na Malami  Umar Torankawa, Ranar Asabar 31 ga Mayu, 2014 da k’arfe 11 na safe a d’akin taron makarantar tunawa da Sarkin Musulmi Muhammadu Maccid’o, Sakkwato.


https://www.amsoshi.com/2017/11/06/jiya-ba-yau-ba-farfesa-aliyu-muhammad-bunza/

Gabatarwa


Lokaci wani zamani ne. A hangen wasu masana wani zarafi ne da ba shi da bagiren da za a riske shi bayan an yi gaba da gaba da shi ya ba da baya. A ganin matasa, wani yayi ne da ke tashe sa’ar da aka mik’a wuya gare shi gadan-gadan. Idan aka ba shi baya ko ya ba da baya sai ya wuce kamar ruwan fak’o. A tunanin Bahaushe, komi na da lokacinsa, idan ba a yi katari da lokacinsa ba za a yi aikin banza wa kare wanka. Idan an dace da lokacinsa za a ga an yi dace tsintuwar guru a cikin  sud’i. Ashe gaskiyar masana da ke cewa, mutum uku suna cikin wahalar da ba ta da ranar hutawa. Na farko shi ne, wanda lokacin abu ya yi, ya k’i mika kai bori ya hau, wai shi bai yarda ba sai ya gani. Na biyu, wanda lokacin abu bai yi ba ya ce sai ya yi shi. Babban wahaltacce na uku shi ne, mai ba su shawara da su dage su sa k’wazo, har da fad’ar ba a san maci tuwo ba sai miya ta k’are. Kada in cika ku da gafara sa ba ku ga k’aho ba, ga bakin zaren tunanina.

Na Gaba Idon Na Baya


Mutumin da ya rasa tarihi an tak’aita masa sake jiki cikin masoya, an hana masa mik’e k’afafu cikin magabatansa. A kowace al’umma gabaci abin bege ne da tink’aho ga mamaya baya. A addinance gabaci abin koyi ne. A ilmance wata babbar madogara ce ga na baya. A tarihance, komai saurin Laraba tana barin Talata ta wuce. Sanin irin k’imar gabaci ya sa a tarihin duniya kowa k’ok’ari yake ya taskace gabacinsa ya zama furen kallo a kowane zamani ya rayu. Dalilin da ya sa ke nan takardun kud’ad’en duniya ke d’auke da hotunan magabatan k’asar. Wasu wurare a sassak’a surorinsu a matsayin gumaka da za a adana a gidajen tarihi. Wasu a kafa su a k’ofofin birane ko tsakiyar manyan wuraren shawagin jama’a a ji su, a gan su. Wasu a yi wa daularsu ko k’asarsu ko garinsu ko unguwarsu suna da sunayensu. Wasu a taskace tarihinsu a adabin bakan al’ummarsu. A ci gaban zamani, yau rubutu ne babbar hanyar adana tarihin magabatanmu. A nawa gani, ya yi kusan zama tilas ga ma’ilmantarmu su tashi tsaye ganin sun taskace tarihinmu domin sanin:

Fakon Kaya Ya Fi Ban Cigiya


A tarihin duniyar bak’ar fata, ba a ta’ba ba Turawan mulkin mallaka mamaki ba kamar yadda aka ba su a k’asar Hausa. Sun tarar da daulolinmu nagartattu girkakku. Sun sami mutanenmu amintattu fitattu ‘yantattu. Sun tarar da tsarinmu daidai da rayuwarmu. Sun sami k’asarmu da addinin da ya koro su daga k’asashensu. Sun tarar da tsarin dokokinmu da shari’armu ba su buk’atar gyaran fuska ga kowane mahaluki. Sun riske mu da ilmin da bai da k’ila-wa-k’ala kuma ba ya jin kunyar idon kowane masani. Babban abin da ya d’aure musu kai ya ‘batar musu da k’idaya shi ne, sun tarar da shugabanninmu ba su yarda a ci gajiyar talakka da su ba. Talakawa ba su yarda a ta’bi gabacinsu ba sai dai komi taka zama ta zama. Wannan dalilai suka tilasta Turawa d’aukar makamai na fuskantarmu da sarakunanmu gadan-gadan abubuwan da suka auku su auku.

Jin haushin haka ya sa masanansu ke ta rubuce-rubucen izgili a kan k’asashenmu da shugabanninmu. Wasu su ce, ba mu da tarihi. Wasu su ce, daga birai muka fara. Wasu su ce, rayuwarmu ta dabbobi ce. Wasu su ce, ba mu da tsarin shugabanci bale na siyasa da walwala, ga su nan dai. Abubuwan nan suna nan a rubuce a duniyar karatu kuma da su wasu takkwalan ‘yan boko ke cin abinci suna koyar da ‘ya’yanmu cewa kakanninmu dambalallu ne, mayaudara ne, fitinannu ne, wai don d’ai sun k’i magana da hanci da k’wambo da kirshe da ragama da soka alk’alami hagu zuwa dama. Wannan ita ce musibar k’arninmu. Don haka, duk abin da zai yi fito-na-fito da ita tilas mu ba shi goyon baya. Irin wannan aiki na daga cikinsu.

 

 

Lokaci Ba Ya Jira


Lokaci ya yi na a ce, a yau tarihin k’asarmu da na magabatanmu mu muka rubuta abinmu da kanmu. Manyan sarakunan daulolinmu mu tabbata suna cikin kundayen tarihin da ‘ya’yanmu ke karatu. Al’adunmu da harshenmu da adabinmu su taskace a d’akunan karatunmu. Yak’e-yak’enmu da sulhunmu da k’aurace-k’auracenmu da abubuwan da suka wakana a k’asashenmu mun san su mun taskace su da alk’alaminmu. Ku dubi shigen kutsen da bak’in al’adu ke yi muna suna son su rinjayi tantagaryar sahihin tarihinmu. Yau fitattun mawak’anmu na baka sai dai a garmahon k’auyawa. Cimakarmu ta gargajiya sai dai a cikin wasan kwaikwayo. Tsarin suturorinmu sai a bukin daba. Uwa uba, ladabi da biyayya da muka yi wa mak’wabta fintinkau a yau ya zama rashin wayewa da rashin sanin ‘yancin kai. Fito-na-fito da hukuma, gwada tsawo da mahaifa, cin zarafin gabaci, yin ido hud’u da kunya, yi wa k’arya cefane, bak’i ne a k’asarmu. Wanda duk ya ba su masauki Allah Ya isa muna. Idan muka sa wa lokaci ido zai kama musu gidan haya a k’ark’ashin ‘yancin demokrad’iyya. Don haka, za mu ce:

Da Abinmu Aka Gan Mu


Idan dai tsarin demokrad’iyya za a yi dodo-rido da shi a  yi wa tsarinmu idon marurugiya, a yi furjin mussa (mussa) da mu da sarakunanmu da shugabanninmu. To! Tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela tana da farinta. A irin tsarin sarautun k’asashenmu, demokrad’iyya wasan yara ce. Sarakunanmu ba dodanni ba ne irin sarakunan Turai da Asiya da k’asashen Larabawa. Kowane fanni na rayuwa yana da mai sa ido a kai. Kowace sana’a tana da jagora. Kowane jinsi yana da shugaba. Kowace fasaha tana da jagora. Kai! Hatta da nak’asassu da marasa galihu da ‘yan gudun hijira da tawagogin musiba ba a yi ko oho da su ba. Abin ban haushi, wad’anda suka saci tsarinmu, wai yau su ke da k’ima ga idon masu ilmin boko, kayansu ne na gaske namu ne jabu. Aka sace magungunanmu na asali aka bar bokaye bautar Iskoki. Aka rusa littattafan ak’ida na masu jihadi, aka raya na tsibbu. Aka haramta wa mak’eranmu fasahar k’era makamai, aka bar su da yuk’a da takubban fad’a da junansu. Aka rusa muna fasahar sak’a, aka cika mu da Osho. Haka ma tunanin kakanninmu na, in ka ci ya k’are, in ka ba wani ya k’aru, a yau, ya koma in ka ci ka k’oshi, in ka ‘boye, ka dad’e kana cin abinka. Idan dai an fahince ni, to za a ga, rubuta tarihin shugabanninmu da magabatanmu wani farfad’on tunatar da mu zancen Farfesa Ibrahim Narambad’a Tubali ne:

Jagora: Banza sharanin maras kare

Sai kuwwa, sai ko wanda yak kasa

Ya ce mishi anshi rataya

Gindi: Ya ci maza, ya kwan shina shire

Gamda’aren Sarkin Tudu Alu

 

Baya Ba Ta Da Kad’an


A yau jihadin Mujaddadi bai cika k’arni uku ba, har yanzu ba za a rasa tsofaffin da kakanninsu aka yi yak’in ba. Duk da haka, Turawa sun cika shi da k’ura da ature da zantukan ‘batanci irin: Jihadin Fulani, daular Fulani, daular Usmaniyya. Masu jihadi k’wacen mata suke yi (wato irin na ‘yan d’aukar amarya). Mujaddadi gabanin ya rasu ya samu motsuwar hankali a kan kashe mutane da ya yi. Mujaddadi ya raba k’asa biyu ta d’ansa da k’anensa. Jihadin k’abilanci ne. Domin tattalin arziki aka yi shi. Sarkin Musulmi Attahirun Amadu layar zana ya yi aka kamo shi aka kashe. Wanda duk ya ratsi ire-iren wad’annan sokiburutsu zai ga hikimar marubutanmu na gida da ke ta k’ok’arin taskace tarihinmu domin Kabawa cewa suka yi, ba don kifin da ya wuce akan yi saba ba, don mai shirin komowa. A kakka’be wundin jawabinmu ina son a lura da lokaci ka da mu yi:

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/gaskiya-tunanin-bahaushen-karin-magana/

Saki Zari Kama Tozo


Ga alama mun riga mun yi kamun gafiyar ‘Baidu. Take-taken da tsarin Turai ya yi wa magabatanmu na mulki da siyasa ya sagarta mu muka yi zaton jini a babe. Mun yi wa sarakunanmu da masarautunmu rik’on sakainar kashi. Mun yi wa addininmu dubin mai bisa ruwa. Muka yi wa al’adunmu kallon hadarin kaji. K’asarmu da yankinmu muka muzantar da su. Kaico! Wai duk irin wayonmu ya zama na banza, muka sayar da gona muka sayi kwasa. Muka sa gida kasuwa domin biyan dukiyan aure. Ni dai abin da ya fi ba ni takaici shi ne, mu sayar da jaki mu sayo mangala, kun ko san ko Buzu ya haukace ba ya sayar  da rak’umi ya sayo akala. Da gangan muka sa kanmu cikin k’uncin da babu lada babu la’ada. A gai da Narambad’a da ke cewa:

Jagora: Ko dauri kyawon k’unci

In da Musulmi ka zama

Ana ta saka kullum

Ana ta bautan Allah

Ana ta samun lada

Kun ji kyawon k’unci

Yara: Wani k’unci sai ja’ba

Sai karen daji

Sai K’adangare sai Tunku

Gindi: Sardauna kandaren Magajin Rafi

Na Baciri Baban Madaye mai ban tsoro

 

Kayya! Mun riga mun shiga wannan k’unci. Yanzu ina mafita? Ga nawa Basakkwacen tunani zan ce:

In Ba a ‘Datu da Yaro a ba shi Daddawarsa


          Sarakunanmu sun sa baki an yi biris da su. Da mu ake gama baki a ci musu mutunci saboda biyan buk’atun siyasarmu. Shugabannin addininmu an gano sirrinsu an yi musu takunkumi da ‘Dangote da taliya da kujerun Umura. K’ungiyoyin addininmu sun fi ‘Dank’wairo jiran tsammani. Limamanmu sun zama ‘yan kwangila masu wa’azi da nasiha su ne wakilan maza’bu. An yi tsaye an raba addini da siyasa a Arewa domin bai wa mak’iya k’arfin guiwa su karya ko babu ga’ba. Abokanin zamanmu addininsu d’aya, siyasarsu d’aya, yankinsu d’aya, ak’idarsu d’aya, da burinsu d’aya na ganin ba mu sake tasiri a farfajiyar k’asarmu ta gado ba. Gwannoninmu da suka hango wannan ta’asar suka riddance wa kowace irin hanya da za a yi muna kisan kashi a yi muna korar ‘barawo a k’asarmu ta gado. Kash! Sai wasu daga cikinmu suka fifita ak’idar siyasa sama ga ak’idar Laa’ilaaHa illal Laahu. Allah ka cece mu, ka da ka bari a cuce mu.

Nad’ewa


Duk mai karatun jaridun k’asar nan ya san Musulunci na cikin ta tsaka mai wuya. Wanda duk ke sauraren kalaman shugabanninmu ya san Musulmi sun shiga uku. Take-taken abokanin zamanmu na tarayya na a kashe mu ne a k’ona, ba na a hura wuta kowa ya ga rabonsa ba ne. In dai da demokrad’iyya muke tink’aho ta cece mu, to, mun nuta bai wuri. In da yawan k’uri’a muke zaton mu k’wato hak’k’inmu, ga irin abubuwan da muke gani an riga an gama k’idan k’uri’u tun bara tare da ‘yan’uwanmu (da za a kashe mu tare) abin da ya rage sanarwa. Cikin siyasar BOKO HARAM an yi muna taron dangi. Rugumutsin ‘ya’yanmu na Chibok fassararsa Arewa ta koma Iraqi da Siriya. Allah Ya isa.

 

Post a Comment

1 Comments

Rubuta tsokaci.