Ticker

6/recent/ticker-posts

Karin Harshe Na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya

Baya ga karin harshen Hausa da ake samu a yankuna daban-dabam na ƙasar Hausa, haka ma ana samun karin harshe na rukunin al'umma daban-daban. Karin harshen rukuni kan samu ne, ko dai dalilin matsayi ko muƙami ko aiki ko jinsi ko addini ko ilimi ko kuma shekaru. Wannan bincike ya yi nazarin wani nau'in Hausa na rukuni wadda ake samu a shafin jaridar Aminiya, mai suna 'Shafin Makaranta Hausa’. Binciken ya yi ƙoƙarin fito da nau'in Hausar da shafin ke amfani da ita tare da ƙoƙarin kawo bambancinta da Hausar da aka saba da ita yau da kullum, wannan shi ya ƙara tabbatar da Hausar shafin makaranta Hausa a matsayin wani nau'in karin harshe na rukuni.

Karin Harshe Na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya

DAGA

Nazir Ibrahim Abbas
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Imel: ibrahimabbasnazir@gmail.com
 Gsm: +2348060431934

Aminiya

Gabatarwa


Karin harshe wani ɓangare ne na ilimin walwalar harshe a cikin kimiyyar harshe. Karin harshe ya danganci bambancin da ake samu na magana a cikin harshe ɗaya, wanda bai kai ga ya haifar da rashin fahimta kwata-kwata ba tsakanin masu magana da harshen, sai dai ga waɗanda na ‘yan rukunin da ake amfani da shi ba. Ana iya nazarin karin harshe ko ta ɓangaren yanki ko kuma rukuni. Karin harshe na yanki ya danganci bambancin da ake samu a cikin harshe dalilin yanki ko wurin da al'umma suke zaune. Yanki yana iya haifar da nau'in bambancin magana a cikin al'umma masu harshe ɗaya, wanda shi ne ake kira karin harshe na yanki ko nahiya.

Wani nau’in karin harshe, shi ne karin harshe na rukuni. Karin harshen rukuni shi ne wanda ake samu dalilin alaƙa ta rukuni a cikin al’umma. Alaƙar karin harshe na rukuni na iya kasancewa ko dai don shekaru ko matsayi ko ilimi ko addini ko jinsi ko aiki ko kuma muƙami. Wannan rukunin shi ma ya kan haifar da nau’in magana daban, daidai rukunan da muka ambata a sama.

A wannan takardar an yi bincike mai taken: ‘Karin Harshe Na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta na Jaridar Aminiya’, za a duba wani nau’in Hausa na rukuni wadda ake yi a wani shafin jaridar Aminiya mai suna ‘Makaranta Hausa’. Hausar shafin makaranta ta danganci wani rukunin al’umma keɓantattu da ke matsayin ɗaliban makaranta da malaminsu mai suna Ɗodo’. Ita wannan Hausa, ɗaliban da masu karanta shafin a kai a kai ne kaɗai ke iya fahimtar abin da take nufi kai tsaye. Kalmomin da ake amfani da su a shafin na Hausa ne amma rukunin ɗaliban makarantar da malaminsu ne suke tsara su, suna kuma amfani da su, kuma su ne suka fi sanin hanyar da suke bi wajen ƙirƙiro kalmomin da kuma jumlolin daga cikin Hausar da aka saba da ita.

Sha’awar Hausar shafin ta la’akari da hikimomin da ke ciki, shi ya sa na yi nazari a kan Hausar a matsayin wani nau’in karin harshe na rukuni.

Bayanan da za mu yi amfani da su mun tattara su ne daga cikin jaridu goma sha uku (na makawanni 13) da ke ƙunshe da shafin na ‘Makaranta Hausa’. Shafin yana fitowa a shafi na goma sha huɗu (14) na jaridar ta Aminiya wadda ake bugawa a kowane sati. Mun yi nazarin Hausar kowane shafi daga cikin waɗannan jaridun a lokacin da nake gudanar da wannan binciken.

 

Karin Harshe Da Nau’o’insa


Masana da dama sun bayar da ma’anar karin harshe da kuma nau’o’insa. Wasu daga cikin waɗannan masanan su ne:

Skinner (1977:6) Ya kalli harshe a matsayin – ‘Wani nau’in magana a cikin harshe ɗaya, wanda ba shi ne ainihin harshen ba’.

Crystal (2008:142) Ya bayyana - ‘Karin harshe ko dai na yanki ko rukuni, a matsayin wani nau’in magana na harshe wanda ake iya ganewa ta wasu kalmomi da tsarin harshe (nahawu). Y ace karin harshe mafi yawa yana da tsarin furuci ko nau’in magana da ya bambanta’.

Mathews (1977:56) kuwa ya bayyana: ‘Karin da duk wani nau’in magana na harshe musamman kuma wanda ake magana da shi a wani sashe na ƙasa’.

Sani (2009: 02) ya kawo ma’anar karin harshe a matsayin; ‘Nau’i ne daga cikin  nau’o’in harshe guda wanda ake amfani da shi musamman a wani sashe na al’umma’.

Adeyanju (1989: 39) kuwa ya kawo ma’anar karin harshe- ‘A matsayin yadda mutum ya saba yin magana a cikin gungun al’umma da yawa masu harshe ɗaya’.

Karin harshe ke nan yana nufin bambancin magana da ake samu tsakanin mutane masu harshe ɗaya wanda bai isa ya haifar da rashin fahimta tsakaninsu ba. Duk harshen da ya bunƙasa yana iya samun karin harshe a cikinsa.

Amfani (1993:02) ya bayyana: ‘Nazarin karin harshe (dialectology) a matsayin nazarin yanayin magana na harshen mutane ɗaya, waɗan da ke fahimtar juna, kuma suna da alaƙar hulɗa ta magana’.

 
Nau’o’in Karin Harshen Hausa

Karin harshe a Hausa yana da nau’o’i guda biyu; waɗannan kuwa kamar yadda malamai suka bayyana su ne; karin harshe na yanki da kuma karin harshe na rukuni. Karin harshe na yanki, shi ne wanda ake samu dalilin wurin zama ko yankin da al’umma suka fito. A irin wannan hali yanki ko wurin zama yana iya haifar da nau’in magana na daban ga al’umma.

A Hausa kuwa akwai kare-karen harshe na yanki, kamar yadda Bergery (1934), Ahmed Da Daura (1970), Liman (1978), Malka (1978), Amfani (1980, 1993), Zaria (1992), Sani (2003), suka bayyana waɗan da suka haɗa da: Kananci, Sakkwatanci, Dauranci, Zazzaganci, Bausanci, Zamfaranci, Adaranci, Damagaranci, Gobiranci, Kurfayanci, Canganci. Waɗannan kare-karen harshe kuwa ana samunsu ne a yankin Arewacin Nijeriya da Arewacin Jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin malaman sun rarraba su a matsayin na sashen gabas da yamma ko manya da ƙanana. Yayin da wasu suka kalle su a bisa tsarin tarihin Bayajida.

Ana iya ganin bambancin karin harshe na yanki a dukkan ɓangarorin nazarin kimiyyar harshe tun daga ilimin furuci har i zuwa ga ilimin ma’ana.

A ɓangaren karin harshe rukuni kuwa, Mathews (1977:344) ya bayyana cewa: ‘Nau’in magana ne, wanda ya danganci wani nau’in al’umma ko rukunin wata tawaga ɗaya a cikin al’umma’.

Fagge (2001) Ya yi nazarin karin harshen Hausa na rukuni, inda ya kawo Hausar da ta shafi rukunin al’umma daban-daban wadda ta haɗa da Hausar: ‘Yan siyasa da Hausar gardawa da Hausar ‘Yan ƙadiriyya da Hausar ‘Yan motocin haya da Hausar ‘Yan acaɓa. Bugu da ƙari ya kawo Hausar ‘Yan Sanda da Hausar Makanikai da Hausar Ƙungiyoyin addinai (Ɗariƙa, Izala, Shi’a) da Hausar ‘Yan mata dai sauransu.

Yakasai (2012), Shi ma ya kawo irin wannan Hausa ta rukuni wadda ta ƙunshi Hausar Kasuwanci da Hausar Sarakuna da Hausar Mawaƙa da Hausar Malamai da Hausar Dattijai da Hausar Samari da ‘Yan Mata da Hausar Matan Aure da Hausar Gidana Magajiya da kuma Hausar Wurin Zaman Makoki.

Karin Harshen Hausa na Rukuni

 


Karin harshe na rukuni, karin harshe ne wanda ya danganci bambancin magana da ake samu dalilin matsayi ko aji ko rukuni ko shekaru ko muƙami ko jinsi ko addini ko ilimi ko kuma tarayyar aiki iri ɗaya (a irin wannan yanayi ne ake samun kalmomin fannu, da suka keɓanta ga wani aiki ko ma’aikata).

Wannan nau’in karin harshe ya sha bamban da karin harshe na yanki domin ana iya samunsa a cikin al’umma ko tsakanin mutanen da suke da tarayya ɗaya daga cikin abubuwan da muka ambata a baya na shekaru ko matsayi ko aji ko ilimi ko jinsi ko aiki ko muƙami.

Bambancin da ake samu a irin wannan karin harshe na rukuni bai yi yawan na karin harshe na yanki ba, domin shi wannan ya fi shafar kalmomi ne da ‘yan guntayen jumloli waɗan da rukunin al’ummar da ke amfani da su, sun fi sauƙin fahimtar saƙon da suka ƙunsa.

 
Shafin Makaranta Ɗodorido na Jaridar Aminiya’.

 


Aminiya wata shahararriyar jaridar Hausa ce, wadda kamfanin ‘Media Trust’ da ke da babban ofishinsa a Abuja, ya ke bugawa a kowane mako, jaridar tana fitowa a ranar juma’a ta kowane sati. An fara buga wannan jarida ne, a shekara ta 2006 kuma tana da shafuka arba’in (40) a cikinta.

Kamar mafi yawan jaridu, wannan jaridar ta Aminiya tana da shafukan da suka ƙunshi labarai na gida da na waje da shafukan ilimantarwa da na tallace-tallace da na labaran al’ajabi da rahotanni da kuma shafukan nishaɗantarwa.

Shafin da za mu yi nazari a kansa, shi ne shafin ‘Makaranta Dodorido’ na jaridar Aminiya, wanda shafi ne na, faɗakarwa da ilamantarwa da ke zuwa cikin siga ta nishaɗi. Abin da ya ja hankalina akansa shi ne, Hausar da ake amfani da ita a shafin da yadda ake sarrafata da jujjuyata da ƙirƙiowa da kalmomi abun ban sha’awa, har ya kai ga wanda ba ɗalibin makarantar ba sai ya kasa fahimtar inda aka dosa.

Wannan shafi na ‘Makaranta Dodorido’ a kowane mako yana fitowa a shafi na goma sha huɗu (14) na jaridar Hausa ta Aminiya kuma yana da siga ta nishaɗantarwa da take gudana ta hanyoyi daban-daban. Sigar tana nuna cewa ana isar da wasu saƙonni ne, na ‘yan makaranta.

Tsarin shafin ‘Makaranta Dodorido’ yana tafiya ne bisa tsarin makaranta wadda ke da ɗalibai da malami ɗaya da suke kira Ɗodo’ , wannan ne, ya sa ma akwai surar wani hoto da ba a gane kowane ne ba a saman shafin, a gefen hagu, wanda ga dukkan alamu shi ne hoton Ɗodon’  da adireshinsa na email a ƙasa mai taken ‘turakundodo@yahoo.com’.

Shafin bugu da ƙari yana tafiya ne da tsarin ko dai dodon ya bayar da labari ko kuma saƙon wasiƙu daga ɗaliban makarantar daban-daban da ke jihohin ƙasar nan, waɗan da suke rubutawa don isar da  saƙonninsu. Kowace wasiƙa daga ciki tana ɗauke da take, wanda ke nuna saƙon da ta ƙunsa. Mafi yawan lokuta, shafin ya kan tattauna al’amurran da ake ciki a ƙasar nan a cikin gugar zana da nishaɗi da amfani da wasu kalmomi da jumloli na musamman.

Hausar shafin makaranta dodorido, Hausa ce ta rukunin al’umma wadda ta bambanta da Hausar da saba ji ko yi, yau da kullum. Hausa ce wadda ɗaliban makarantar da malaminsu da masu sha’awar shafin waɗan dake karanta shi yau da kullum kawai ne ke gane ta. A nan muna iya kallon Hausar shafin makaranta dodorido, a matsayin karin harshe na rukunin al’umma ɗaya  wanda kuma ake iya gane siffofin shi, a misalan da za mu bayar na Hausar malamin da ɗaliban makarantar da za mu fito da su a cikin aikin.

 
Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya

Hausar Shafin makaranta dodorido ta jaridar Aminiya, wata Hausa ce ta daban wadda kalmominta da jumlolinta suka bambanta da Hausar sauran rukunin al’umma. Hausar ta ƙunshi fassara wasu kalmomi da jumloli da sunaye kai tsaye tare da ƙirƙira sababbin wasu kalmomi cikin hikima da fassara wani tunanin al’umma ta hanyar ƙirƙira ta annushuwa da gugar zana. Daga cikin irin nau’in wannan Hausa ta rukuni ne ake samun irin waɗannan ƙirƙirarrun kalmomi da kuma jumloli kamar haka:
Lamba

Hausar Shafin Makaranta

Ma’anarta

1.

Direban Alli

Malami

2.

Zaman Lumana

Zaman lafiya

3.

‘Yan makaranta

Ɗaliban makaranta dodorido

4.

Watsattsakewa da buɗa wagegen littafi

Karatu da rubutu

5.

Taliyar indon-mami

Indomi

6.

Giz-baba

Malamin makarantar

7.

‘Yayan kaji waɗan da ba a ƙyanƙyashe ba

Ƙwayaƙwai

8.

Ƙaramin lauje

Biyu

9.

Masu hannun riga

Mahaukata

10.

Yaron Daku

Jami’in tsaro

11.

Haramta ƙwambo da bobon bokoko

Boko haram

12.

Ɗan bayan kango

Wanda ba ɗan makaranta ba

13.

ShuɗadƊ’iyar shekara

Shekarar bara

14.

Haurobiyawa

‘Yan Nijeriya

15.

Ankararwa

Faɗakarwa

16.

Mai-duka

Allah

17.

Jihar Jijjiga ciyawa

Jihar Jigawa

18.

Shugaba Mainasara

Shugaba Goodluck

19.

Ɗan tallafin suɗin gambiza

Kuɗaɗen rarar man fetur

20.

‘Yan hannu baka hannu ƙwarya

Talakawa

21.

‘Yan-sa-in-ɗauka-ba-tare-da-na-ajiye-ba

Barayin gwamnati

22.

‘Yan sa-mu-raba-da-shi

‘Yan kazagin gwamnati

23.

Tamola da ƙafafun Haurobiyawa

Wasa da hankalin ‘Yan Nijeriya

24.

Wasoson lalita

Satar kuɗin asusun gwamnati

25.

An yi walƙiya mun je gano

Mun gane gaskiya

26.

‘Yan Allah-ba-ku-mu-samu

‘Yan barandar siyasa

27.

Jatau mai-sa-in-sa

Jonathan

28.

Jan jinin Haurobiyawa

Satar dukiyar ‘yan Nijeriya

29.

Batu

Magana

30.

Jatau

Jonathan

31.

Jihar Barnawa

Borno

32.

Kwamin-titi

Kwamiti

33.

Kiran sallah da usur

Abin mamaki

34.

Direban mashahuriya makaranta

Malami

35.

Bijiro

Kawo

36.

Haurobiya

Nijeriya

37.

Niyar-jari

Nijar


38.

Yaren hau-hau wajen hawan sa

Harshen Hausa

39.

Bokan turai na makaranta

Malamin makaranta

40.

Yaren makaranta

Hausar shafin dodorido

41.

Damƙa shi

Kai shi

42.

Kurtun magana

Wayar Gsm

43.

Makaranta ta dodanni

Makarantar dodorido

44.

Saka-ka-tare

Sakatare

45.

Bututun batutuwa

Mai magana da yawun wasu

46.

Malam Dodo/Farfesa Dodo

Malamin makaranta

47.

Wurin ƙwadago

Ma’aikata/Wurin aiki

48.

Harubja

Abuja

49.

Manja

Manaja

50.

Masu hawa sa

Hausawa

51.

Gwamnan Dabawa

Gwamnan Kano

52.

Uwar kowa

Gwamnati

53.

‘Yan caɓawa

‘Yan acaɓa

54.

Romon makaranta

Ilimi

55.

Kwankwatsa-tsiya a birnin dabo

Kwankwasiyya a Kano

56.

‘Yan ƙolaye

Ɗaliban makaranta

57.

Walwalin waliyo a kan Babura

Gudu a kan babura

58.

Bagas

Garaɓasar dumokuraɗiyya

59.

Hana zaburar baburido

Hana acaɓa

60.

Na damo

Haƙuri

61.

Na mujiya

Idanu

62.

Saraf-na-saɗaf

Sanusi Lamiɗo

63.

Walata Ruɗani

Walter Rodney

64.

Kwasar gagarumar jar miya

Sata

65.

Fasko

Gano

66.

Jatau ya jona tantanin mulkinsa

Jonathan ya fara mulki

67.

Dama-dama da kurɗa-kurɗar siyasa

Hada-hadar siyasa

68.

Shekara dubu ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje

Shekara ta 2012

69.

Zagaye da madambaci da zagaye da manuniyar ƙasa, madambaci da madambaci da manuniyar ƙasa da manuniyar sama ƙaramin lauje da zagaye da manuniyar ƙasa

08098896209

70.

Kwashi-kwaraf

Satar kuɗin gwamnati

71.

Kawun Bararrajewa

Kawu Baraje

72.

Baban-gada-gada mai burga da baragada

Gwamna Babangida

73.

Gwamna mai sunan sulalla

Gwamna Sule Lamiɗo

74.

Gwamna mai kwankwatsa-tsiya a birnin dabo

Gwamna Kwankwaso

75.

Kassara al’umma

Wahalar da al’umma

76.

Ba-haurobiye

Ɗan Nijeriya

77.

Jihar Ni-na-ja

Jihar Niger

78.

Ku-zauna-a-zaure

Kazaure

79.

Garin-ja-haɗe

Garin Haɗeja

80.

Jam’iyya mai ɗan boto da sanda jirge

Jam’iyyar PDP

81.

Shekaru sili da ƙofar hanci

Shekaru 13

82.

Arewatawa

‘Yan Arewa

83.

Kadadawa

‘Yan kudu

84.

Makarantar masu dangwala tawada a kurtu da zayyana a kan allo

Makarantar almajirai

85.

Masu laluben ɗandago da ɗan ƙanzo

Almajirai

86.

Hauren haskaka Haurobiya

Kuɗin wutar lantarki

87.

Hauren-Danja

Niger Delta

88.

Jan linzamin tsuntsayen sama

Tuƙin jigin sama

89.

‘Yan dugwi-dugwi

Yara

90.

Huta-fara

Karatun Firamare

91.

Babban kusu

Barawo92.

Zagaye da kwanciyar magirbi da zagaye da manuniyar sama da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya

07067947944

93.

Loma-a-murɗe

Lamurde

94.

In-gwangwaje-in-wala

Ngozi Iweala

95.

Man tunkuza

Man fetur

96.

Ruɓaɓɓen-abban-titi

Reuben Abati

97.

Zage na ‘yan dambe

Zage damtse

98.

Kwana manuniyar ƙasa

Kwana tara (9)

99.

Jihar mu-muka-fara-sharia

Jihar Zamfara

100.

Kurtun baburido

Bayan babaur

101.

Kekerido

Keke

102.

Ranar da aka haifi Ɗanladi da ‘Yar ladidiya

Ranar Lahadi

103.

Mutum mai kallon alƙibla

Musulmi

104.

Amintattar jarida

Jaridar Aminiya

105.

Tunanin gizo da ƙoƙi

Ƙarya

106.

Wadatacciyar sallama

Sallama

107.

Masu bautar mahalicci sili

Masu bautar Sarki ɗaya

108.

Gardawan makaranta

Ɗaliban makaranta

109.

Dodo uban dodanni

Malam Dodo

110.

Romon makaranta/gishirin kyautata rayuwa

Ilimi

111.

Dubannin gaisuwa

Dubun gaisuwa

112.

Malam mai almajirai

Malam Dodo

113.

Bayan kada

Kaduna

114.

Jaridar ‘Yar yau

Daily Trust

115.

Jaridar Turanci ta Gadin yana

Jaridar Guardian

117.

Fura mai kyau

Firamare

118.

Malam Nasara El-rusau

Malam Nasiru El-Rufa’i

119.

Gudun loko

Boyo

120.

Batu na dokin ƙarfe

Batun gaskiya

121.

Jihar Bayasa

Jihar Bayelsa

122.

Janatantin

Jonathan

123.

Gazdawa

Ƙauyawa

124.

Man tunkuza

Ɗanyen mai

125.

Damin hauro

Kuɗi

126.

Barade

Sojoji

127.

Ƙarfe ƙofar hanci da ƙofar hanci da zagaye na yammaci

Ƙarfe 3:30 na yamma

128.

BauɗadƊ’en joji, Sissiliya, Gaulan Jatau

Bode George, Cesiliya, Gulak

129.

Waf-sayoyi

Websides

130.

Mafuskantar alƙiblar kaɗaita mahalicci da ibada

Masallaci

131.

Makarantar dodo uban dodanni

Makaranta dodorido

132.

Ranar da aka haifi Ɗanliti

Ranar litinin

133.

Uwar jiki

Lafiya

134.

Bututun batutuwan jatau mai-sa-in-sa

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Jonathan

135.

Shugaban masu ɗamara da launin faɗuwar rana a saman riga

Shugaban jami’an Civil Defence

136.

Shaƙulatin ɓangwaro

Riƙon sakainar kashi

137.

Gidan Bokan Turai

Makaranta

138.

Masu addinin Ɗan Amina

Musulmi

139.

Jihar Tumbin Giwa

Kano

140.

Sarki Sili

Sarki ɗaya

141.

Direban buzu da jan hanjin ligidi ana bugi dutsi kwas

Malamin tsibbu mai jan tasbaha

142.

Babban rumbun adana damin hauro na ƙasar Haurobiya

Babban bankin Nijeriya


143.

Garin Mugurgusa

Garin Gusau

144.

Masu fuskantar alƙibla

Musulmi

145.

Jar boto

Jar hula

146.

Tudun ba ceto

Halaka

147.

Kurtun magana na Halo-Alo

Telfon

148.

Jami’ar Dodorido

Makaranta dodo

149.

Na kuturu

Haƙuri

150.

Abun da ya fi hauka rashin magani

Jahilci

151.

Ci-ba-daɗi

Wahalar da jama’a

152.

Fasa balam-balam

Fasa bam

153.

Dakarun burga

Dakarun JTF

154.

Santala Ƙwaiduwa

Stella Odua

155.

Dokar duniya

Dokar hana fita (Curfew)

156.

‘Yan hana murƙushe gumin Ɗan Adam

Masu kare haƙƙin al’umma

157.

Shekara dubu ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje da sili da ƙofar hanci

Shekara ta 2013

158.

Bututun ‘yan kwakwazo da baza na mujiya

Kafafen watsa labarai na Rediyo da Talabijin

159.

Bala-lura

Bala’i

160.

‘Yan hana bokoko

‘Yan book haram

161.

Gwamnan asusun ƙarfanfana

Gwamnan babban bankin Nijeriya

162.

Mina-mina a jihar Ni-na-ja

Hada-hada a jhar Niger

163.

Tsomomuwa

Matsala

164.

Jihar Alan-goguro

Jihar Borno

165.

Ɗabi’ar kifi da kada

Wanka

166.

Kwana kwanciyar magirbi

Kwanaki bakwai (7)

167.

Takalmin malam mantau

Mantuwa

168.

Gagarumar garaɓasar dama-dama da kurɗa-kurɗar wasan Samson-siya-siya

Gajiyar Siyasa

169.

Garin gano

Ganewa

170.

Gusha-da-tsaf

Bula Tsaf

171.

Injinmiya

Injiniya

172.

Yaren kuci-kuci-hutawa

Indiyanci

173.

Turkewa a sunnar Manzo

Aure

174.

Birnin Zage-zage

Zaria

175.

Ɗan ku-ci-ku-ba-mu

Mai roƙo

176.

Masu roɗi-roɗin tufa

Sojoji

177.

Hannun zinari da ƙafar gwalagwalai

Masu kuɗi

178.

Mulkin mulaka’u

Mulkin wahalar da al’umma

179.

Shekara dubu ƙaramin lauje da kwanciyar magirbi

Shekara ta 2007

180.

Saɓi zarce na kusu

Sata

181.

Wasan Samson-siya-siya

Siyasa

182.

Unguwar zomo

Uzoamaka

183.

Masu ɗamara da ɗan taku da kulki

‘Yansanda

184.

Ƙaura

Canza wuri

185.

Laluban na koko

Neman abinci

186.

Hausam-fa

Shiyar Hausawa

187.

Gwarawan-fa

Gwarimpa

188.

Ɗunɗume ƙururu

Cin abinci

189.

Likimo

Kwana

190.

Karatun wasiƙar jakin dawa na da birni

Ƙaryar shugabanni ga talakawa

191.

Masu aika-aika

‘Yan ta’adda

192.

Kuturun hasashe

Tunanin banza

193.

Ranar da aka haifi Ɗanladi da Ladi ƙaramin lauje da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya

Ranar Lahadi 24 ga wata

194.

Rana ta ƙaramin lauje da ƙaramin lauje ga watan janye-wuri na shekara ta dubu ƙaramin lauje da sili da ƙofar hanci

22-01-2013

195.

Zagaye da madambaci da sili da manuniyar sama da sili da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da manuniyar sama da babban lauje da sili da babban lauje

08161946515

196.

Kamfanin cefanar da labarai

Kamfanin dillancin labarai

197.

Makon da ya arce

Makon da ya gabata

198.

Ɗoki-ɗora

Tsarin zaɓen Nijeriya

199.

Mai martaba babban mutum mai rawani

Sarki

200.

Dirshe

Tsaya

201.

Garin dama-tumatur a jihar Yawon-bebe

Damaturu a jihar Yobe

202.

Karɓar na koko

Karɓar cin hanci

203.

Mutum ƙaramin lauje

Talaka

204.

Ƙarfe ƙofar hanci da rabi

Ƙarfe 3:30

205.

Sana’ar zabarin baburido

Acaɓa

206.

Kumbon-tsotso

Kumbotso

207.

Taron-rauni

Tarauni

208.

Ƙurƙurido

A daidaita sahu

209.

Damo-da-kura-da-ɗiya

Dumokuraɗiyya

210.

Malala gashin tunkiya da ‘yan matsabbai

Da yawa

211.

Gandun aika-aika

Ganduje

212.

Hauro dubu ɗari babban lauje

Naira dubu ɗari biyar

213.

Damin hauro sili da zagaye da zagaye da zagaye

Naira dubu goma

214.

Babban lauje da zagaye da ƙaramin lauje da zagaye da sili zagaye da babban lauje

5020105

215.

Ƙasashen da jaɓa da gafiya da kusu ke wandaƙa

Ƙas ashen da ake satar dukiyar al’umma

216.

Takardun ƙwadago

Takardun ɗaukar aiki

217.

Ƙwadagon hana baƙin haure shige da fice

Immigration

218.

Tagadaz

Agadaz

219.

Jihar Ɗakin kara

Jihar Katsina

220.

Masu hawa sa

Hausawa

221.

Yaren Makaranta

Hausa

222.

Masu zama bisa buzu

Malaman tsibbu

223.

Gidan malam Tunau

Makaranta

224.

Gwamnan Dabawa

Gwamnan Kano

225.

Garin da ake sa dara

Kano

226.

Angwance

Aure

227.

Gidan gaskiya

Hanya

228.

Wa-zai-zo-ya-biya

Wazobiya

229.

Sumul

Ƙalau

230.

Ƙaramin lauje da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya

24

231.

‘Yan mai tako’ina

Masu hali

232.

Adon gari

Mata

233.

Ta ido

Kunya

234.

Halin amale

Handama

235.

Gobara

Lantarki

236.

In da masu yaen hau-hau wurin hawan sa suke zaune

Mazaunin Hausawa

237.

Wuri sili

Wuri ɗaya

238.

Elin-zubar

Elizabeth

239.

Farcen susa

Babu dama

240.

Masu ƙasƙantar da kai wajen gagara misali

Masu ibada

241.

Ta jiki

Shawara

242.

Sintirtir

Sintiri

243.

Rana ta ƙaramin lauje da manuniyar ƙasa ga watan mayun shekara ta dubu ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje

29 ga watan Mayun 2012

244.

Hauro tiren taliya madambaci da gashin balama sili da zagaye da zagaye

Kuɗi tiriliyon takwas da biliyan ɗari

245.

Tunar kilshi

Harakokin duniya

246.

Gaisuwa irin ta masu addinin Ɗan Amina

Sallama

247.

Baba manga

Bamanga

248.

Tada kan adda

Ta’addanci

249.

Jami’an asusun ilimi

Shugabannin Ƙungiyar ASUU

250.

Kamfanin dumdumdurundum

Kamfanin bayar da wutar lantarki

251.

Batu na ingarmar ƙarfe

Gaskiya

252.

Ranar ‘yancin rani

Ranar tunawa da samun ‘yanci

253.

Baba Ojo

Obasanjo

254.

Shugaba ‘Yar bishiya

Shugaba ‘Yar adua

255.

Zaman-takewa

Cutarwa

256.

Watan Noman-baba

Watan Nuwamba

257.

Doguwar dabba

Raƙumi

258.

Watan-dashen-baba

Watan Disemba

259.

Turken rayuwa

Aure

260.

Cefanar

Sayar

261.

Masanin sisi-da-sisi

Gwamnan babban bankin Nijeriya

262.

Zari-ruga

Satar kuɗin gwamnati a ɓoye

263.

Ma’aikatar kula da sufurin tsuntsayen sama

Ma’aikat kula da jiragen sama

264.

Mai gonaki otawa

Obasanjo

265.

Mace da zane

Ministar kuɗi Ngozi Iweala

266.

Lalita

Asusun ajiya (Accaunt)

267.

Tayar-ladan, Malalen-suya, Indon-isiya

Thailand, Maleysia, Indonisia

268.

Niyar-jari, Zaman-gidan-buwai

Niger, Zimbabwe

269.

Damisoshin Asiya

Ƙasashen Asia

270.

Zaɓi-sonka

Zaɓe

271.

Dama-dama-da-kurɗa-kurɗar wasan Samson-siya-siya

Siyasa

272.

Samartakar kusu

Satar dukiyar gwamnati

273.

Uban-mama

Obama

274.

Amari-kowa

Amurika

275.

Dalilin-taronsu

Jaridar Daily Trust

276.

Faffale-dalili

Jaridar Peoples Daily

277.

Balon-faranti

Jaridar Blue Print

278.

Gadin-yana

Jaridar Guardian

279.

Banda-da-gadi

Jaridar Vanguard

280.

Shugaba mai Gudun-loko

Shugaba Goodluck

281.

Uwargida Damo-haƙuri

Uwargida Patient

282.

Jami’an tsoratarwa

Jami’an tsaro na haɗin gwiwa

289.

Raɓaɓas

Rivers

300.

Mai ɗan taku da kulki

Ɗan sanda

301.

Tonon-Anini

Tony Anini


Matanin Wasu Labaran Shafin Makaranta

A wannan ɓangare zan kawo wasu labarai da na tsakuro daga wasu shafukan ‘Makaranta Dodorido’ da ke cikin jaridar Aminiya domin ganin yadda sigar Hausar shafin take.

‘Yar makaranta ki riƙa ɗumama ɗumame da ɗumi-ɗumi

ɓayan gaisuwa da fatar alheri ga babban direban alli na wannan makaranta da sauran ɗalibai, zan taya abokiyar watsattsakewa da buɗa wagegen littafi a wannan makaranta, wacce ta angwance da yaron Giz-baba da fatan Allah ya ba su zaman lumana, kuma muna so ki nuna masa irin horon da kika samu a hannun malam wajen ɗunɗuma ɗumame da ɗumi-ɗumi da kuma dafa taliyar indon-mami da ‘ya’yan kaji waɗan da ba a  ƙyanƙyashe ba’. Aminiya 2012, Febrairu, shafi na 14.

 
Hausam-fa ko Gwarawan-fa?

‘A shekara ta dubu ƙaramin lauje da kwanciyar magirbi kamfanin buga Amintattun jaridu ƙasar Haurobiya ya yi ƙaura daga unguwar Mawanawasa kan layin zaratan Zambiya zuwa garin Tako-tako, inda aka gina mana ɗakin katako, mu kuwa muke laluben na koko a ciki. Tun daga waccan shekarar zuwa yau nike ta neman inda Hausam-fa take, domin na san a Harubja da akwai rukunin matsugunnin al’umma mai laƙabin ‘Gwarawan-fa’. Don haka nike ta neman ina Hausawam-fa take, ko kuma rukunin matsugunnin al’umma da aka gina a wannan katafaren birnin inda masu magana da yaren Hau-Hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa suke bararraje’. Aminiya, 2012, Satumba, shafi 14.

  
Kada a rungumi ƙadandoniya

‘Assalamu alaikum ɗaliban wannan makaranta ta mu mai albarka ta Dodorido da ke farfajiyar jarida, sanin kowa ne a rayuwa karɓar abu mai kyau ko maras kyau shi aka fi so ga mutum mai kallon alƙibla, amma a wannan lokaci jama’a sun shiga ruɗani na rayuwa da kallon abin duniya da yin tunanin gizo da ƙoƙi, yawancin mutane zuciyar su ta ƙoƙe kamar ƙoƙiya maza da mata suna tafiya ba kai ba gindi a harkar zamantakewa, kasuwanci da ma sauran al’amurran yau da kullum dab a a faye ɗaukar ƙaddara ba. Kaico duniya rawar ‘yanmata na gaba ya koma baya. Hattara al’umma mu riƙa ɗaukar kaddara idan mun ƙi kuwa mu rungumi ƙadandoniya’.

Daga: Ɗalibar makarantar Tumbin giwa Jamila Ishak (Atinen Ziko) ta garinsu Munyi-jibir, kurtun mangana: zagaye da kwanciyar magirbi da zagaye da manuniyar sama da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya’. Aminiya, 2013, Afrilu, shafi 14.

1.6 Kammalawa


Wannan maƙala mai taken ‘Karin Harshe na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya’ ta yi nazari a kan Hausar shafin Makaranta na jaridar Aminiya a matsayin wani nau’in karin harshe na rukuni a Hausa, wanda ya danganci wasu rukunin al’umma da suka haɗu a sigar makaranta, wadda ke da malami da ɗalibai. Shafin kamar yadda muka bayyana a baya ya kan fito ne, ku san kowane mako a jaridar Hausa ta Aminiya kuma ya kan tattauna al’amurran yau da kullum da suke faruwa a cikin al’umma a ƙasar nan cikin nau’in wata Hausa ta daban.

Wannan Hausar kamar yadda misalan da muka bayar suka gabata, Hausa ce ta daban wadda ta keɓanta ga malami da ɗaliban makarantar kawai kuma tana tafiya ne ta sigar Hausantar da kalmomi da fassara wasu tare da amfani da ayyukan wasu mutane ko takensu maimaikon sunayensu. Bugu da ƙari ana kuma ƙirƙiro wasu jumloli da sassan jumlolin Hausa. Shafin musamman yana da tsarin da yake bi wajen bayyana lambobi, wanda sai ƙwararre a irin wannan Hausar ne zai iya fahmitarsu. A tunani na, wannan Hausa idan aka ƙara zurfafa bincike a kanta da wasu makamantanta za ta taimaka wajen samar da nau’in wani harshe na daban wanda zai iya taimakawa wajen sadarwa a keɓaɓɓun wurare, musamman wajen inganta sadarwa ta wasu ma’aikata na musamman ko kuma wurin ayyukan jami’an tsaro a ƙasar nan. Haka ma Hausar tana iya haifar da wani karin harshe babba, wanda za a iya faɗaɗa bincike a kansa.

Akwai buƙatar a yi amfani da basira da ƙwarewar mutane masu irin wannan baiwar ƙirƙira a harshe domin haɓaka harshen da duban yadda za su bayar da gudummuwa ga ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya. Wannan bincike ya nuna muna cewa harshen Hausa yana iya bunƙasa ta irin wannan hanya har a kai ya haifar da wani harshe a cikin al’umma, idan aka baiwa irin waɗannan mutane masu baiwa ta harshe goyon baya da taimakon da ya dace.
 

Manazarta


Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.