In An Ci Moriyar Ganga A Ba Ta Tukuicin Girma: (Awon Nauyin Butulci A Duniyar Tunanin Bahaushe Tsakanin Adabi Da Haƙiƙa)

    Takardar da aka gabatar a babban taron ilimi na bukukwan sati ɗaya ƙarƙashin Score Card Committee na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua domin jinjina wa da ban kwana na ɗebe kewar Farfesa Mu’uta Ibrahim Mataimakin Shugaban Jami’ar mai barin  gado, 2015, a Babban Ɗakin Taro na Jami’ar, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami’ar mai karɓar ragamar mulki Farfesa Idris Isa Funtua, 2015

    In An Ci Moriyar Ganga A Ba Ta Tukuicin Girma: (Awon Nauyin Butulci A Duniyar Tunanin Bahaushe Tsakanin Adabi Da Haƙiƙa)


    Aliyu Muhammadu Bunza
    Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
    mabunza@yahoo.com
    0803 431 6508



    TSAKURE
    Tunanin Bahaushe da ke cikin karin maganar: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza”; wani sabon salon faɗa da ‘butulci’ ne a kaikaice. Don haka, wannan binciken ya yi shimfiɗa da ma’anonin da kalmar ‘butulci’ ke ɗauka ƙarƙashin harshe da adabi da al’adun Bahaushe. Don tsettsefe bayani, an gayyato Ƙamusoshin Hausa fitattu guda uku da na Turanci ɗaya. Wannan ya ba mu hasken fito da fuskoki goma na ‘butulu’ a Hausance. A duniyar Adabin Hausa, an ratsi karin magana 12, tatsuniyoyi 2, waƙar baka 1, kirari 11, jimillar taskokin adabin 25 ke nan a kan sikelin awon butulci. A haƙiƙanin al’amari, an waiwayi shari’o’i guda biyar na butulci da ke gaban kotunanmu masu jiran hukunci. A cikin kowacensu butulci ya haddasa kisan kai na gilla. A kwakkwafen shari’un aka waiwayi yadda addinin Musulunci ya harari butulci da butulai. A kakkaɓen buzun bincike, an gano sifofi 27 da kowane butulu ke iya siffantuwa da su. A ma’aunin al’ada, cutar butulci ta fi fitattun cutuka 10 ciwo a zuciyar Bahaushe. Bincike ya ci nasarar  ƙyallaro turakun butulci 6, wanda ya kira mashaƙatar butulci. A duniyar Bahaushe, an waiwayi barazanar butulci wurare 10 ga ci gaban ƙasarmu; kana aka  yi daddage na musamman a kan yadda butulci yake yi wa ilmi zagon ƙasa. A naɗe buzun karatu, an ayyana yadda za a magance cutar butulci da dambarwarta. A sakamakon bincike, an ƙyallaro muhimman abubuwa 6, duk da haka, ƙololuwar cutar butulci dai kashe wanda aka butulce wa. A ko’ina butulu yake, tare da mutuwa suke yawo. Kowace cuta butulu ya ɓarka, a saurari wata a gaba, in bai raba abokin adawa da ransa ba. Ba don butulci ba, da ƙasarmu ta cancanci ta limanci duniyar zamaninmu a kan kowane fanni na rayuwar duniyar mutane. 

    Gabatarwa:
              Tunanin Bahaushe da ke ƙunshe cikin karin maganar: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza” kukan kurciya ne. Zargin maciya moriya ganga ke yi, da baya su kushe ta, su jingine ta, har su kai ga cuta mata da bakunansu bayan sai da suka dafa kafaɗarta duniyar lokacinsu ta san da zubin tsawonsu.  A tunanin Bahaushe “ganga” ta wakilci duk wani abu da aka ci, ko ake cin amfaninsa aka more masa. Tunanin Bahaushe na sarrafa “ganga” a karin magana shi ne, ita ce muryar makaɗa, ba don ta ba da makaɗa ba kowa ba ne, don ita aka san da shi, ita ce tagomashinsa, da ita yake ci.[1] Abin da duk ya kasance wa mutum da irin wannan matsayi, ya cancanci ya gode masa, ya yi masa kariya iya ƙarfinsa. Bahaushe sakayawa ya yi da cewa: “Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza”, ni kuwa na sauya tunanin zuwa: “In an ci moriyar ganga, a ba ta tukuicin girma”. Da ma abin da Bahaushe ke kira shi ne, “Kada a ci moriyar ganga da baya a ce mata koren banza”. A wata fassara shi ne, idan an ci moriyarta a gode mata, don haka na fassara shi zuwa, “Yaba kyauta tukuici”. Abin da duk aka ci amfaninsa ya cancanci a girmama shi, a saka masa da kyautatawa, wannan shi ne “tukuici”. A taƙaice, muradin Bahaushe ga wannan karin magana shi ne, yi wa “butulai” tawaye da zanga-zanga da ature cikin ruwan sanyi. Ganin irin yadda “butulai” ke yawaita, “butulci” na ƙara tunzura, “butulcewa” ya zama ruwan dare, nake son in ɗora shi a faifan nazarin al’ada mu ga yadda Bahaushe ya harare shi. Haƙiƙanin wannan bincike a misalai na haƙiƙa da aka shaida aka ɗora shi an gayyato sassan adabi domin su mara masa baya kawai.

    Dabarun Bincike:
              Matsalar da nake son in waiwaya daɗaɗɗiya ce kuma babu al’ummar duniya da ta kuɓuta daga gare ta. Kimiyyar rayuwa ce da kowane ɗan Adam, na kowace ƙabila, da launi, da addini bai kuɓuta ba. A wata mahanga, matsala ce da ta dabaibaye halittu masu rayuwar dabbobinsu, ƙwarinsu, da tsuntsayensu. Don haka, dabara ta farko da na bi ta ita ce, yin nazarin ƙwaƙƙwafi na ratsin kalmar “butulci” cikin harshe da adabi da al’adun Hausawa. Mataki na biyu, tsura wa kalmar ido da faɗin ma’anarta a wasu harsuna na daban. A mahanga ta uku, na yi rangadin gani ga ido, da tattaunawa da jama’a, da waɗanda abin ya shafa, da ofisoshin wakilan tsaro ‘yan-sanda, da SSS, da kotunan shari’a domin tantance shari’o’in da suka shafi “butulci”. Na ɗan yi yunƙurin rairaye jinsi da shekaru da halayyar aukuwar butulci ga butulai, da dangantakar su ga abin da suka butulce wa. Wannan ta kai ni ga tantance waɗanda musibar butulai ta fi auka wa a al’adance. A dabarun bincikena, a kowane mataki Bahaushe ne bara ga binciken kuma babban buri a tantance sakamakon ƙarshe na butulci ga wanda aka butulce wa da wanda ya yi butulci. Ta haka kaɗai za mu iya fayyace sakamakon butulci ga ci gaban duniyar mutane a rayuwarsu ta haƙiƙa.

    Mene Ne Butulci?
              Kalmar “butulci” fitacciya ce kuma sananniya cikin kalmomin Hausa. Da wuya a samu harshen da ba ya da ita a kalmominsa wadda ruhin ma’anarta ya yi kusa da na Hausa. A fassarar Reɓ. G. P. Bargery ya harari kalmar da cewa:
    Kalmar “butulci’ na da ma’anar “rashin godiya’. Namiji da macen kalmar ita ce “butulu” jam’inta shi ne “butulai’. A Hausar Kabi, ana ce wa jakar ɗura shinkafa “butulu”.[2]

    Irin kallon da Ƙamusun Hausa ya yi wa kalmar bai  butulce wa Bargery ba, domin cewa ya yi:
    Butulu suna ne na jinsin namiji da mace, wadda jam’insa ita ce “butulai” dukkaninsu na ba da fassara “mutum maras godiya’. Butulci kuwa yana nan a matsayinsa na “rashin godiya”.[3]

              Sanin irin makusanciyar dangantakar da ake iya samu tsakanin harshen Larabci da Hausa na tuntuɓi masana Larabci domin ƙarin bayani. A wajen Larabawa ma’ana ko kwatancin kalmar “butulu/butulci” ita ce “kufrun” wato “Kafirci”.[4] Da wannan sunan kulkin nassin Ƙur’ani ya ambace ta tun daga ƙissar Shaiɗan da Adamu har yanzu zuwa bayin da suka biyo baya.
              Duk da yake nason da harshen Larabci ya yi cikin harshen Hausa Turanci bai samu wannan gatar ba.[5] Amma yadda suka kalli kalmar da sunan ‘betray/betrayal”, biri ya yi kama da mutum. A fassarar sun ce:
    A doguwar fassara “butulci” na ɗaukar ma’anar zamba cikin aminci, rashin imani, saɓa alƙawali, tona asirin wani abu, yaudara, zamba, ga su nan dai. Butulci na ɗaukar ma’anar nuni ko bayyanar da wani abu da ke ɓoye; butulce wa wuta da hayaƙi ya yi shi ke bayyanar da ita a gane wurin da take.[6]

    Yunƙurin Roɗana Ma Newman a Ƙamusunsu akwai ƙarin haske; domin cewa suka yi:
    Kalmar ‘betrayal’ wadda za a zuba a jimla a matsayin ‘betray a trust’ sun fassara shi da ‘Ci amana’. “He bretrayed his country” - “Ya ci amanar ƙasarsa”. Idan kuwa ta sauya zuwa: ‘betray’s confidence’ ta koma, tona asiri.”[7]

              Wurin da na ga fassararsu ta ɗan soma ba su ruwa da na koma ga kalmar ‘treason’ suka fassara ta da ‘cin amanar ƙasa’ sai ma’anar ta yi tangam da wadda suka ba ‘betrayal’. Betray ta ɗauki ‘butulci’ ya fi fito da ita ƙuru-ƙuru, ita kuwa treason ta yi zamanta na ‘cin amanar ƙasa’, sai karatun ya fito a bayyane.

    Tsettsefe Ma’ana:
              Wannan binciken gaba ɗayansa a kan kalmar ‘butulci’ aka ɗora shi, don haka nake ganin dole sai an yi tankaɗe da rairayar kalmar an kai ga haƙiƙanin ma’anar da bincike zai dafi kafaɗarta ya tsayu da ƙafufunsa. A ganina, gudummuwar Bargery tana ɗingishi domin taƙaita ma’anar ‘butulci’ ga ‘rashin godiya’ kawai bai yi wa Bahaushe susa gurbin ƙaiƙai a kan yadda yake kallon ‘butulu’ da ‘butulci’ ba. Irin masassarar da ta kama ma’aunin Bargery ita ta kama ta Ƙamusun Hausa. Yadda Ƙamusun Websters ya fuskanci kalmar akwai wuraren da suka yi canjaras da Bahaushen tunani musamman da ya kalle ta da ma’anar ‘rashin imani’ da ‘tona asiri’ ko ‘zamba cikin aminci’.
              Waɗannan ma’anonoin duk suna iya bayyana cikin ƙunshiyar ma’anar butulci amma ba su Bahaushe ke ce wa “butulci’ ko “butulu” ba.  A ganin Bahaushe, butulci na da fuskoki goma da ake iya rarrabe shi da sauran miyagun halaye:
    1.     Ba a samun sa sai bayan an zauni abu zaman aminci da buƙata zuwa gare shi, ba shi ke da buƙata ga mazauninsa ba.[8]
    2.     A samu cin amfaninsa sosai da sosai har wani ba maciyi amfanin ba ya shaida.[9]
    3.     A ribaci amfanin, a yi zara da shi, a yi fice na a zo a gani, wato an kai ga buƙatar kusantar shi.[10]
    4.     Maciyi moriyar ya ga ya cika da wanda ya more wa, ko ya yi kusa ya cika da shi, ko ya cika har ya ga rinjaye a kansa.[11]
    5.     Samun tabbacin cikawa ko zaton rinjaye sai a fito gaba da gaba da shi, a yi kirarin ƙarfi ya kawo tsoro ya ɗebe, ko maraƙi ya cika da manyan shanu.[12]
    6.     Ba a kan kirarin kawai za a tsaya ba, sai a yi tsaye a kushe shi, a ɓata shi, ko a cutar da shi ta hanyar amfanin da aka samu gare shi.[13]
    7.     A ƙara matsa lamba a kafirce masa a yi masa fito-na-fito irin na zanga-zanga a shuka ƙiyayya da shi.[14]
    8.     A yi kunnen uwar shegu da dukkanin amfaninsa da aka ci, a mara wa masu adawa da shi baya, in an ga ya gagara, a ci zarafinsa da zuƙuƙunsa.[15]
    9.     A tsiri aƙidar sa ƙafan wando ɗaya da shi a kowace rawa zai taka.[16]
    10. Babbar buƙata ko buri a gusar  da martabar da aka san shi da ita ko ɗaukakar da ya yi ko amfanar jama’a da ya yi ko baiwar da jama’a ke ganin yana da, a maye gurbinsa da abin da ya shuka, a ga baya gare shi, a yi masa fitsari a kan kabarinsa.[17] Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu. Waɗannan ma’aunai goma za mu iya takura su da faɗar:
    Butulu shi ne, maras godiya ga amfanonin da ya ci ga kowane irin abu. Mai tsananin wutar zuci ta tukuicin sharri ga kyautar alfarma da gatar da aka yi masa. Mai tsananin son kai da kishin zucci ga duk wani ba shi ba, sakayyarsa ga kowa ita ce, a ɗeɓe idon sani a sa na mugunta. Zama lafiya da shi, ba a taimaka masa ya kai ga buƙatarsa ba, da ya kai ga burinsa, babban maƙiyinsa shi ne, wanda ya dafi kafaɗarsa ya kai ga buƙatarsa. Tukuicin da zai yi wa macecinsa na fito-na-fito da adawa da gaba da takaici da cin zarafi da cin dugadugai na ƙurewa da ƙin ƙarawa cikin makirci da yaudara, na ganin iyaka da ganin bayan macecinsa, shi ake cewa “butulci”. Assha! An butulce wa: yaba kyauta tukuici.

    Butulci a Farfajiyar Karatun Adabi:
              Duniyar adabi ƙawatacciya ce gewaye da abubuwa na haƙiƙa, ƙunshe da waɗanda ba su ba, taskace cikin ƙawataccen harshe da aka sarrafa a baka ko a rubuce ko a aikace irin na wasan kwaikwayo da wasannin gargajiya. A cikin kowane salo na adabi ana iya cin karo da saƙon “butulci” ko aikin ‘butulu”. Abin sha’awa, a kowane sashe na adabi “butulu” da ‘butulci” abin kushewa ne na ƙarshe. A cikin taskokin karin magana da kirari da shaguɓe waɗannan ‘yan misalai suna  ba da haske a kan hoton ‘butulci” da ayyukan ‘butulci’.

    Butulci Cikin Karin Magana, Kirari, Salon Magana da Shaguɓe:
    (i)               Sai an ci moriyar ganga a ce mata koren banza.
    (ii)             Tuwon girma miyarsa nama.[18]
    (iii)          A ci gari da kai a ba ka kuturun bawa.[19]
    (iv)           Kura da shan bugu Gardi da karɓe kuɗi.[20]
    (v)             Godiyar Maye.[21]
    (vi)           Godiyar ‘ya’yan kunama.[22]
    (vii)        An haife ka ka ƙi haihuwa don ƙeta.[23]
    (viii)      Mugun maƙwabci ba ka da mata ana haihuwa ɗiya da kamarka.[24]
    (ix)           A ja mu a kai mu an doki uwar makaho.[25]
    (x)             Wallahi kada a ƙara, an yi wa uwar raggo duka.[26]
    (xi)           Mutum ba ya nunin gidansu da hannun hagu. [27]
    (xii)        Bakin da ya ci ya gode in ba na kaza ba ne.[28]

    Butulci Cikin Tatsuniya da Labaran Gargajiya:
              Yadda tatsuniyoyi da labaran gargajiya da almara da ƙissoshi suka fito ƙuru-ƙuru ga tona asirin butulu da butulci sassan adabi na karin magana da sauran zantukan hikima ba su kai can ba. Mu tsura wa wannan tatsuniya ido sosai mu gani:

    Tatsuniyar Yaro da Maciji da Zarɓe da Maharbi:
              Wani yaro yana cikin daji ya ji kururuwar wasu mutane sun koro maciji suna neman su kashe shi. Da macijin ya zo wurin yaron ya nemi ceto. Yaron ya kwanta, ya buɗe bakinsa ya ce wa maciji: “Shiga cikin cikina, in sun wuce ka fito ka tafi abinka.’ Da suka wuce, ya ce wa maciji: “Bawan Allah fito sun wuce”. Maciji ya ce: ‘Ina! Ni na samu wurin zama, kayan cikinka su ne abincina har sai ka mutu.” Yaro ya dinga kukan fitan rai. Yana cikin kuka, ya gamu da zarɓe, zarɓe ya tambaye shi abin da yake yi wa kuka, ya kwashe ya gaya masa. Zarɓe ya ce: “Ka je ka kwanta a rana ka buɗe baki, in ya ji zafin rana zai turo kansa waje shan iska in cire maka shi.” Yaro ya bi umurni, maciji na jin zafin rana ya zaro kai waje zarɓe ya cafke ya zaro shi waje, ya wurgar. Yaro na mirmijewa ya cafke zarɓe, zarɓe ya ce wa yaron; ‘Me ke faruwa?” Yaro ya ce: “Ai na samu naman da zan warke mikin da maciji ya yi mini. Da na sha romonka ai sai in mirmije.” Zarɓe ya koma kuka, suna cikin taƙaddama sai ga wani maharbi ya zo. Ya tambaye su matsala, zarɓe ya kwashe ya gaya masa. Maharbin ya fanshi zarɓe ga hannun yaro. Ya karɓi zarɓe ya sake: zarɓe na jin ya fita hannun yaro ya faɗa hannun maceci, maceci (maharbi) na sake shi, sai ya yi caraf! Da idon maharbi ɗaya ya yi sama da ita, ya kai maharbi durƙushe da ido ɗaya kogon idon ɗaya na zubar jini.[29]

    Labarin Wani Makaho da Wani Mai Doki a Zangon Fatake:
              Wani mutum ne mai tsananin tausayi ya tarar da wani makaho shi kaɗai a zangon fatake ruwan sama na duka ba kowa. Ya je ya ɗora makahon a kan dokinsa ya ɗora babbar malfa a kan makaho maganin ruwa. Suna cikin tafiya, labari ya yi labari, sai makahon ya tambayi sunan dokin, wanda ya taimake shi ya gaya masa sunansa. Ya tambaye shi kuɗin da ya saye shi, da wurin da ya saya, da la’adar da aka yi, da dillalan, duk ya kwashe ya gaya masa. Shigarsu gari ke da wuya, sai makaho ya aza kuka da ihu! Da kururuwa cewa, ga mai ido zai ƙwace masa doki. Aka je fada, sarki ya binciki makaho, ya kawo duk abubuwan da macecinsa ya gaya masa ya faɗa. Aka karɓe doki aka ba shi. Aka kai makaho gidan baƙi aka sauke, mai doki kuwa aka kai shi gidan Yari saboda laifin sata. Makaho na cikin holewa cikin dare bayan kalaci, sai ga bayin Sarki na amana sun zo rangadin gidan.  Da shiga gida, suka riske shi yana kewar samu, yana cewa: “Na samu doki da malfa da wurin kwanciyar sarauta a banza.” Suka koma suka ba Sarki labarin abin da suka tsinta. Sarki ya karɓe doki ya ba mai abu, ya kori makaho daga garinsa. [30]

    Butulci a Rayuwar Mawaƙa:
              Mawaƙan baka da rubutattu ba su tsallake farfajiyar adabi ba ta fuskar karatun “butulci” da “butulu”. Makusanci daga cikin misalan da zai wakilci mawaƙan baka da rubutattu shi ne wanda malamin kiɗi Narambaɗa ya ambata a cikin ‘Waƙar Ya Ci Maza” ya ce:
    Jagora:        Sarki! Ka ga mutum shidda,
    Yara:           Babu mai zaunawa lafiya da su.
    Jagora:        Wanga “azuji” wanga “butulu”
    Yara:           Guda “ashararu’ guda “maɓannaci”
    Jagora:        Wanga guda “tsohon munafuki”,
    Yara:           Akwai wani na nan “mai ƙure mutum”
    Gindi:          Ya ci maza ya kwan shina shire
                       Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.[31]

              Idan muka waiwayi abubuwan da suka auku tsakanin yaro da maciji da zarɓe da maharbi dole mu gaskata makaɗa Narambaɗa. Babu wanda zai zama lafiya da shi. Darasin da ke cikin labarin makaho, da mai doki, wata babbar ishara ce ta duk wata rigar mutunci da butulu zai saka domin ya samu wurin zama cikin mutane. Haƙiƙa, wanda duk ba a wa butulci ba, bai san ciwon batulci ba labarin butulci yake ji. Wanda ya ɗanɗani azabar butulcin butulu zai ci Narambaɗa gyara ya ce. “Makaɗa lalurar waƙa ce ya sa, ya saka “azuji” na farko domin su duka shida butulu ne kakansu, azuji da ashararu jikoki, maɓannaci kama kunne, tshohon munafuki, tankaɗa hauɗi, mai ƙure mutum taka kusheyinsu ne”.Yanzu bari mu waiga kan awon butulu da butulci a duniyar haƙiƙa kamar yadda bincike ya kalato muhimman shari’o’i biyar kamar haka:        

    Abdulƙadir Usman S. Ɗori Alero A Garin Kwaifa:
              Wannan yaro ma’aikaci ne a Jihar Kabi a ma’aikatar Kiwon lafiya. Yana sana’ar sayar da kayan masarufi da tufafi. Yakan shiga ƙauyuka ya ba da bashi, in wata ya yi, ya je ya karɓo kuɗinsa ya ƙara ba da wani. A garin Kwaifa yana da abokan ciniki da yake ba bashi, aka yi ɗiban wa’adi ba su biya ba. Don haka, da ya je ƙauyensu suka nemi ya ba su kayan sallah, ya nemi su biya tsohon bashin da ya ba su. Suka kasa biya, ya ƙi ya ƙara musu. Bayan da  da ya gama abin da yake a garin, ya yi wa mai masaukinsa goma sha na arziki, sai masu bashin suka game kai da mai masaukinsa ya gaya musu lokacin da zai bar  garin. Da ya kama hanya, suka bi shi suka kama, suka ɗaɗɗaure shi a kan babur nasa suka sassare shi sai da ya mutu. Suka jawo fetur daga babur nasa suka zuba masa, da shi da babur duka suka ƙona su ƙurmus! Sai bayan ‘yan kwanaki aka gano (I.D. Card) nasa da bai ƙone ba a dajin da suka butulce masa. Yanzu haka butulan na gidan Yarin Birnin Kabi fiye da shekara uku babu hukunci. ‘Yan’uwan mamaci sun gaji da kai da kawo kotu sun sa ido.[32]

    Alhaji Yahaya Sa’idu Andarai da Bello Uban Dawaki Ƙwannawa:
              A shekarar 2014 wani babban ma’aikaci (Director Finance) Local Goɓernment Commission a gwamnatin jihar Kabi, mutumin garin Andarai ta Maiyama Local Goɓt, mazaunin Sokoto a gidajen gwamnatin jiha. Yana da yaro mai suna Bello Ubandawaki Ƙwannawa ɗan wani hakimi a Unguwar tsohon filin jirgin sama. Ya yi wa yaron aure, ya gina masa gida, a aurensa naira N300,000 ya ba shi na hidimar buki, yana sana’a da shi ta gidaje da filaye. Ya ba yaron wasu kuɗi na sana’a, yaron ya kira shi cewa ya zo an sayi fili. Gabanin ya zo, yaron ya yi hayar makasa, aka kashe shi cikin gidan yaron. Aka gina rami tsakiyar falon yaron.  Aka saka gawa a ciki ba sallah balle wanka, aka rufe, aka nemo magina suka shafe wurin da siminti aka saka babban kafet (darduma) na ɗaki kamar ba a yi komai ba, aka kawo kayan kaɗe-kaɗe aka ɗora aka ci gaba da shaƙatawa. Yaron da waɗanda suka karɓi jingar kisan duk suna gidan Yarin Sakkwato, babu labarin kowane irin hukunci.[33]
    Wasu Yaran Bunza da Maigidansu Igbo a Bunza 2014:
              Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito wasu yara da wani Igbo ke hulɗar cinikin magani da su na tsawon shekaru. Yana bin su bashi sun kasa biya. Da ya zo karɓar bashi suka lallaɓe shi ya je gidan ɗaya daga cikinsu har ɗakin uwarsa suka riƙe shi suka yi masa yankan rago. Suka ɗauki gawar suka kai wajen gari a wata ƙaramar hukuma suka yar. Asirinsu ya tonu ta hanyar motar da suka ɗauka haya domin su kai gawar daji. Wannan musibar ta auku garin Bunza, jihar Kabi. An ce shari’ar tana gaban ‘yan sanda ana bincike kamar yadda aka saba.[34]

    Lawwali Gandi da Maƙwabcinsa 2013:
              A jihar Sakkwato a ƙaramar hukumar Raɓah wani Cashier na Ƙaramar Hukumar Raɓah ya gamu da ajalinsa ta hannun yaransa da yaran da ke koyar da ‘ya’yansa karatun Islamiyya. Sun shiga gidansa suka kashe shi, suka banka wa gidan wuta, suka ɗauki abin da suke so suka tafi abin su. Yanzu haka suna gidan Yarin Sakkwato jiran hukunci tun shekarar 2014.[35]

    Tsohon Shugaban Jami’a (ƁC) da Yaransa, 2015:
              Wani tsohon mataimakin Jami’ar… ya gamu da ajalinsa ta hannun yaran gidansa da ya riƙe ya ɗauki nauyin karatunsu su biyu. Da suka buƙaci kuɗin da suka gani gare shi, suka bi dare suka kashe shi, suka ɗauke motarsa da kuɗin da ke ciki. Da bakinsu suka tabbatar da cewa, shi ya ɗauki nauyin karatunsu kuma saboda kuɗi suka kashe shi. An yayata a kafafen yaɗa labarai an nuno su a hannun wakilan tsaro. Zancen hukunci kuwa, shiru ka ce, an aiki bawa garinsu.[36]

    Duniyar Butulci a Ma’aunin Siyasar Duniya:
              Misalan biyar da suka gabata na haƙiƙa ne da wataƙila ina kusa da su don haka na shaide su. Waɗansu misalai kuwa duniya ta shaide su a zahiri, sai dai, wataƙila ba a yi tunanin aza su a sikelin butulci ba. Gabanin mu kwakkwahe batu ya kyautu mu ƙyallaro irin butulcin da Kampore ya yi wa Thomas Sankara. Abokan zahiri, Thomas ya jawo Kampore ya yi masa mataimaki ya sake komai a hannunsa. A cikin wasu jawabansa yana cewa: “Kampore will be the last man to betray me and our country.”[37] Me ya wakana? Kampore ya kashe shi ya hau karaga. Irin kusancin Saddam Hussaini da Tarikh Azeez ya isa misali. Masu addini irin na Tarikh a ƙasar Iraƙ ‘yan tsiraru ne,[38]  amma Saddam ya yi tsaye ya yi masa mataimakin shugaban ƙasa. A ƙarshe, ta hannunsa aka kama Saddam aka kashe aka tarwatsa ƙasar. Dangantakatar Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Nzegu abin misali ne. Nzegu ta hannun Sir Ahmadu Bello ya samu ci gaba gidan soja. Da guguwar butulci ta murɗi zuciyarsa, shi ya je har ɗakinsa ya bindige shi, ya mutu, ya jawo gawar ƙasa giriri har wajen gidan.[39]  Mafasa baƙin tarihi sun ce, da Bisalla da William Sirry da Bukar Suka Dimka a ƙarƙashin General Murtala suka samu ƙarin girma. Saboda kusanta, Bisalla da Murtala, kotun soja ta bi duk yadda za a yi a kuɓutar da shi ga butulcin da ya wakana, an kasa samun kafar yin haka. Yayin da za a bindige Bisalla ya furta cewa: “Yesterday I was about to be free, but today for this boy Dimka, Allah Sarki.” Kisan gilla da Dauda Malam Wanke ya yi wa Ba’are Mainasara butulci ne. Ku tambayi ƙarshen Wanke![40] Kaico! Butulci ya fi sharri gaggawa, da saurin tafiya, da mayar da gami, da ɗaukar fansa, da dogon shaƙo da sha yanzu magani yanzu. Wace cuta ta fi butulci? Tashi tsaye ka nemi maganinta.

    Butulci a Ma’aunin Addini:
              A ko’ina mutum yake yana tare da al’adarsa. A doguwar fassara, al’ada ita ce aƙidar da mutum yake a kai, ta hani da horo. A buɗaɗɗiyar fassara ƙangin doka ta hani da horo da samun sakamako ita ce “addini”. Bahaushe ya rayu a tsakanin aƙidun addinai huɗu: addinin gargajiya, addinin Yahudu, addinin Nasara da addinin Musulunci. A ƙasar Hausa addinin Musulunci ya fi kanta da amo da rinjaye da yawa da masu aiki. Don haka, da an ce addini a ƙasar “Musulunci” zai fara zuwa a zuciyar kowane adilin mai bincike. Addinin Musulunci da Bahaushe ya runguma ya yi wa butulci suna da “kufurun” wato kafirci. Na kalli abubuwan ta fuskoki kamar haka:
    i.       Da Allah Ya halicci Mala’iku, da Adamu, da sauran abubuwa, ya umurci a yi wa Adamu sujuda a matsayin tukuici ga baiwar da ya yi musu. Nassi ya ce: “Shaiɗan ya yi girman kai ya ƙi.” Ƙin bin umurni, da takin saƙa da Mahaliccinsa, da butulce wa ni’imar da aka yi masa Allah Ya ce: “Wa kaana minal kaafiriina.[41]
    ii.     Halittar Annabi Isah (AS) ta jefa Yahudawa da Nasara cikin ɗemuwa, don haka suka ƙirƙiro aƙidar ukuntawa (doctrine of trinity). Raba Allah gida uku ya sa, nassin Alƙur’ani ya ce sun kafirta. Ashe ƙoƙarin takin saƙa da Allah da sama masa kishiya da yin fito-na-fito da iradarSa ya sa aka kira su “butulai”.[42]
    iii.     A hadisi an ce, wasu bayin Allah mahaifinsu ya mallaki taguwa da ita aka ɗauki nauyin gidan duka. Da ita aka yi ɗawainiyoyin Hajji da Umura da sama wa yara abinci. Bayan rasuwar mahaifinsu suka je da ita Hajji za su yi hadaya da ita, suka kasa rinjayarta su kayar su yanka. Matsalar aka kai ta gaban Manzo (SAW) ta bayyana wa Manzo irin butulcin da suke son yi mata, bayan sun gama cin moriyarta su yanke ta. An ce, Manzo (SAW) ya umurce su da su sake ta, kuma kada a yi murai a yanka ta har abada.[43]
    iv.   A addinance, idan ɗa ya kashe uba za a kashe shi, a hana shi gado, saboda tsananin butulcinsa. Idan uba ya kashe ɗa, ba a kashe shi domin nassi bai yarda akwai butulci a nan ba.[44]
    v.     A fagen yaƙi na kowane irin jihadi, a kowane hali mahaifa suka shigo hannun ɗa a matsayin bayi sun ɗiyauta saki ba ƙaidi. Ɗa ba zai auri mahaifiyarsa ba da matar mahaifinsa da wadda ta shayar da shi nono addinin Musulunci bai yarda a butulce wa kowa ba.[45]

    Ma’aunin Tantance Butulci Ga Butulu:
              Kwakkwahe bakunan waɗannan misalai da muka gabatar kan butulci suna buƙatar a ɗora su a kan wani ma’auni da za a tantance mai butulci. Ga ɗan abin da muka gani a kan butulu, za mu tantance butulci da sifofi kamar haka:
    i.                   A kuɓutar da shi daga wuya ya saka macecinsa ciki.[46]
    ii.                 A ceto ransa, ya yi sakayya da kashe maceci.[47]
    iii.              A sanar da shi abu ya ƙulla adawar ja-in-ja da masanin da ya sanar da shi abin, ya yi gagarumar adawa a kushe shi.[48]
    iv.               A taimake shi, ya tushe ƙofar sake taimaka wa kowa, bisa ga cutar da mai taimakon da ya yi.[49]
    v.                 Idan aka kuɓutar da shi tarko ya shigar da wuyan macecinsa, ya tsallake, ya hau bakinsa da kirari.[50]
    vi.               Idan aka suturtar da shi, ya cire suturar mai sutura da ya ba shi, ya ƙara da nasa, ya bar maceci tsirara, ya sa a yi masa ature da gayyan wayyo![51]
    vii.            Godiyarsa a koyaushe in ya yi ta, yaudara ce, domin tukuicin da zai bayar muninsa ya yi muni.[52]
    Babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa bakwai da butulu ya rage. Da za a ɗora shi a kan kalmomin al’ada na hukunta halayyar masu munanan halaye, bisa ga bitar abubuwan da suka wakana na misalan adabi da zahiri za mu ce, butulu dai:
    1.     Mayaudari ne - nisanci ba shi amana domin duk yadda ya san mutum yana yi masa aibi.
    2.     Maƙaryaci ne - ba a shiga ɗaki da maganarsa.
    3.     Macuci ne - kiyayi dukiyarka da irlinka.
    4.     Mahassadi ne - bai taɓa ɓoye jiyewarsa ba in ya samu tazara.
    5.     Munafuki ne - kada ka yarda ka sake jikinka da shi.
    6.     Ɗan’ta’adda ne - nisanci kaɗaita da shi.
    7.     Maras tausayi ne - ba su taɓa haɗa hanya ɗaya da imani ba.
    8.     Maƙiyi ne - komi ya yi maka shigo-shigo ba zurfi ne.
    9.     Mugu ne - bai taɓa yi wa sabo da kusanci ragowa ba.
    10.  Annamimi ne - duk abin da kuka yi tare, ba shi yake nufi ba.
    11.  Mutakabbiri ne - bai taɓa jiran lokacinsa ba, idan ya ga an ba shi tazara.
    12.  Ɗan jidali ne - babu mai zaunawa lafiya da shi.
    13.  Jahili ne - bai taɓa tunanin komai ya ruɓa yana wari ba.
    14. Wawa ne - mai ganin kowa wawa a irin wayonsa na wauta.
    15.  Matsoraci ne - bai gaba-da-gaba sai dai sari ka noƙe.
    16.  Raggo ne - bai taɓa ɗebe wa kansa takaici ba sai ya gayyato abokan kunyata.
    17.  Maras haƙuri ne - bai taɓa yarda da rabon kwaɗo ba ya hawa sama ba.
    18.  Maras dangana ne - bai taɓa sake wa Allah abin da ya rinjaye shi ba.
    19.  Marowaci ne - bai yarda da cewa, yaba kyauta tukuici ba.
    20.  Makwaɗaici ne - ko wuta yana lasawa in bai kai ga masƙin da ke kanta ba.
    21.  Maras kunya ne - bai taɓa aikin da sakamakonsa ya kasance madalla ba.
    22.  Maras gaskiya ne - zantukansa da ayyukansa ba su taɓa yin daidai da niyyarsa ba.
    23.  Sakarai ne - kowa ya san halinsa, shi ko Allah bai ba shi hankalin sanin halin kowa ba.
    24.  Baƙauye ne - na ƙarshe, ƙyasuwa da sabara albarka!
    25.  Makiri ne - komai ya faɗa ko ya aikata, da lauje cikin naɗi.
    26.  Tabanjama ne - bai taɓa kunyar kunya ba, sai dai kunya ta kunyace shi.
    27.  Butulu ne - sai ya ci moriyar mutum ya ƙunduma masa sharri.

    Tirƙashi! Butulu ya cancanci kowane irin kirari na muzantawa da tonon asiri. Me za ka ce, in na yi masa kirari da:
    ·        Bunguli shigan mai ila
    ·        Talallabiyar kashi, ba a faɗi ba rai ya ɓaci
    ·        Mugun maƙetari ci baƙi
    ·        Tsululu mugun zawo ana karta kana biyar ban hannu
    ·        Sharri gaba aka sa ka, kowa ya sa ka baya cim mai kake yi
    ·        Gizago ba ka da sabo
    ·        Ciwon ciki babu nasiha
    ·        Cinnaka ba ka san na gida ba
    ·        Hannu na gaisuwa ƙafa na sata
    ·        Gatari faɗan kusa da kusa
    ·        Mugun tuwon da bai kashe yunwa ana kwalfarka maigida na mutuwa

    Kowace sifa daga cikin sifofin nan 27 aka bi a hankali a cikin adabin baka da rubutacce na Bahaushe za a fitar da hoton butulu a ciki. Idan aka nuta cikin bincike ga abubuwan da ke bayyana na haƙiƙa, za a ci karo da su daɓa-daɓa a fuskar butulu. Waɗannan musibun suka sa a Bahaushen tunani cutar butulu ta fi ta komai ciwo domin a ɗan awona:
    1.     Ta fi sata ciwo ga mai dukiya.
    2.     Ta fi ƙarya ciwo ga mai hankali.
    3.     Ta fi duka zafi a mutunci.
    4.      Ta fi yaudara cin rai ga mai zuciyar taimako.
    5.      Ta fi ƙazafi ɓata suna ga ƙarshen sakamakonta.
    6.      Ta fi munafunci ciwo ga mai imani.
    7.      Ta fi cin nama zafi ga kamilin mutum.
    8.      Ta fi zamba cikin aminci ga amintacce.
    9.      Da ita da mutuwa tangam suke ga misali na zahiri.
    10.  Ta fi ƙaddara raɗaɗi da zogi domin ƙaddara ta kowa ce, ita ko ta masu yaƙi da ƙaddara ce.

    Mashaƙatar Butulu
              Ga alama, mun bi ko’ina mun daddage domin hana wa butulu da butulci mazauna. Duk da haka, a duniyar tunanin Bahaushe akwai wuraren da butulci ke shaƙatawa idan an yi la’akari da cikakkiyar ma’anarsa da aka rairaye. A kowace zamantakewa da za a ɗan jima ana amfanin juna nan ne butulci ya fi shaƙatawa. A koyaushe Bahaushe ya yi tunanin butulci a zamantakewa yakan hango zama irin na:
    1.     Mahaifa da ‘ya’yansu.
    2.     Ma’aurata (mace da miji).
    3.     Maigida da yaronsa (ko a sana’a ko a ilmi ko a mulki)
    4.     Zumunta ta jini.
    5.     Zaman abokai (na soyayya).
    6.     Baƙo da mai masaukinsa.

    Irin kusancin da ke cikin waɗannan wuraren zumunci shida za mu ga, akwai sakewa da imani da juna, da miƙa al’amari ba da mugun zato ba, da yin hidima ta tsakani da Allah, da wahalar da jiki da samu da lokaci da basira domin a amfani juna. Ba a zaton a yi wata hidima da zato irin na ‘yan adashi ko ‘yan biki ko ‘yan ga-aiki. Duk wata amfanar juna da aka yi, ana yi domin ta cancanta a yi ta, shi ma wanda ake yi wa, haka zai ji a ransa idan yana da sukuni fiye da haka zai saka. To! Idan aka yi rashin sa’a ganwo ya birkice da dami, wutar hasada da mugun zama ta ruru, wani ya fara yi wa ganga kallon koren banza, kai tsaye Bahaushe zai ce; “An yi “butulci”, mai halin a kira shi “butulu”. A ko’ina batulci ya bayyana, yawo ya tafi wuraren  nan shida nan ne mashaƙatarsa ta al’ada da aka saba jin zarmoɗansa. A irin wannan kusanci an fi saurin hango rashin godiya, da cin amanar zama, da butulce wa mafari, da cin zarafi, da rashin ragowa, da jiyewa, da tozarta mafari, da rashin ragowa da tausayi irin ta wagilin baligi da iskan hunturu ke ratsawa, kamar yadda makaɗa Gambo ya sifanta kansa lokacin da yana matashi, wagili ya ce:
    Jagora:San da ba ni da tsinka ban da lura
                       :Ban da ragowa ban da sabo
                       :Ba ni da imani sa’annan/ ga raina.

              Idan dai ba a ga butulci cikin waɗannan wurare shida da aka ambata ba, a ko’ina aka gan shi zai iya ɗaukar wani suna ko sifa daga cikin sifofi (27) sai sunan ya ɗan sha barafasa. Idan ana neman wuta maƙera ba a same ta ba, aka ci karo da ita masaƙa aka ɗiba, duk dai sunanta “wuta” sunan muhallin da aka same ta ne kawai ya bambanta da irin mamakin da ta bayar.

    Barazanar Butulci Ga Cigaban Al’ummarmu A Yau:
              Illolin butulci  ba  ga rayuwa da dukiya kawai suka tsaya ba. Ga dukkanin alamu, abin ya ci zarafin ci gaban zamaninmu da zamantakewarmu wanda ke buƙatar kulawarmu ta gaggawa domin Gumi ta riga ta gamu da Anka. A dubi ‘yan waɗannan ƙorafe-ƙorafe na mai bincike a kan rutsin butulci da ke yi wa zamantakewar Hausawa barazana a yau.

    Malamai Da Makarantu:
              Yadda waɗanda suka ci moriyar ilmin zamani na farko tun yana da guiɓinsa, ya yi musu goma na arziki, suka sa ido makarantun na lalacewa babu kowace irin kulawa. Yadda duniyar zamaninmu ta sa wa fitattun malaman da aka ci amfaninsu ido da tsufa na wahalar da su ka ce, ba kafaɗarsu aka dafa aka zama abin da aka zama ba. Wannan butulci ne ko da ba a ce wa gangar ‘koren banza’ ba, domin an sa mata ido da tsufa da talauci su ƙarasa ta. Assha! Tir! Haba! Malami uba ne mai siffar uwa ma ba ɗa nono.

    Zaman Karkara:
              Yadda ƙauyawan da rayuwar ƙauye ta nagartar musu da rayuwa da tarbiya da ƙwazo, ta ba su damar cin moriyar zama birni. Yau su da ‘ya’yansu ke kafirce wa zama ƙauye, an yi kaka-gida birane an sauya suna an sake jiki birni ƙauyuka na zama kangaye.[53] Sakamakon wannan butulci kunya ta ƙaurace birane ta sa muna ido da halinmu, zama lafiya ya gagara. Wannan butulci ne na ƙin ƙarawa.

    Tsufa:
              Yadda muka sa wa gabaci ido su yi yaƙi da tsufa butulci ne babba. A kowace duniya da wayewar kai ya ratsa, tsofaffi magabata maza da mata da suka makaro suna da ma’aikatar da ke kula da su, da yi musu hidima na har abada, har sai lokaci ya yi halinsa. A irin fahimtarmu a sa wa tsufa ido da gabaci, mai rabon ganin baɗi ya gani. Barin gabaci da tsufa dambe babu mai rabo babban butulci ne.[54] Me ya durƙusar da tattalin arzikinmu da rashin tsaro ba wannan ba?

    Zumunta:
    A da, zumunta ita ce madafa ga maraya da marashi da gajiyayye da wanda ya hau dokin ta tsaka mai wuya da kowane irin mabuƙaci. A yau, an sa ƙafa an shure ta, matuƙar ba ka da, ba ka da ɗan’uwa, da rashi ya riske ka in kun fi tururuwa zuri’a kai ne ɗan’uwan kanka. In ka ji kalmomin zumunci na kai da kawo irinsu baba, babban ƙane, taubashina da dai makamatansu mai furta su mabuƙaci ne, wanda ake furta wa su yana kan ƙarfen Nasara. Sau nawa ake tsintar jinjirai a kai su gidajen marayu su rayu a can, alhali suna da iyaye da dangi kowa ya sa gabansa inda ya dosa, ba ya da wani ɗan’uwa daga matarsa sai ‘yan’uwanta. Me ya taɓarɓare muna tsaro da taɓarɓarewar tarbiya ba wannan ba? Sau nawa ana aikata fashi da makami da zai ci rayuwar waɗanda aka yi wa, kuma a tarar da ‘yan’uwa cikin ta’asar? Ka ce, ɗan’uwanka abinka, su ko ‘yan’uwa su ce, halinka shi bi ka

    Abota:
              Ko ba a ce uffan ba, zamanin abota da miƙa amana gare ta ya fara wuce wa in bai zurare ba gaba ɗaya. Irin hidima da kusanci da ɗaukar wa rai da danƙon zumuncin abota na mutanen da, a yau sai dai a tsince shi cikin adabi don a karanta a yi kewar tunanin gabaci. Sau nawa abotar soyayya ko ta siyasa ko ta addini ko ta wasa ko ta sana’a ke haddasa kisan kai na butulci domin wani tsohon bashi ko wata buƙatar da ake son a yi bayan aboki ya mutu? Wane butulci ya fi haka a duniya? Ina za mu je da irin wannan tunani? Yaya za a samu cigaba aminci bai gabaci zamantakewar abota ba? Butulcinmu ya haifar da wannan.

    Taimako:
              A da, a addinance da siyasance, taimako wata babbar gada ce ta ƙarfafa danƙon zamunci da son juna.[55] Tsananin butulcinmu ya sa a yau, da taimako ake garkuwa a yi cuta, da zamba cikin yarda, da 419, da kai hare-haren ƙunar baƙin wake. Da wuya ka ji an ɓarka wata gawurtacciyar sata ko ƙasaitacciyar damfara ga mai hannu da shuni ba da hannun waɗanda ya taimaka ko yake taimakawa ba. Wane butulci ya kai, sai an yi maka agaji, ka gode, an gode, ka biyo baya da bi-ta-da-ƙulli na kashe wanda ya taimake ka, ka yi awon gaba da dukiyar da yake agaji da ita, a bar iyalai cikin rashi biyu, an yi haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance. Butulcinmu ya haifar da yawan marayu da naƙasassu da gwagware da marasa galihu. Anya kuwa allonmu bai cike da rubutu ba?

    Sana’o’in Gargajiya:
              Matakan da magabata suka bi na kashe fatara da talauci da zauna-gari-banza da ci-ma-kwance da roƙo da bara da raraka da ci da ceto da ci da addini da mutuwar zuciya ita ce ta ƙarfafa sana’o’in gargajiya. Yau da noma da wanzanci da kamun kifi da ƙwadago da ujule da fatauci da sauransu ga matasanmu sun zama ƙauyanci. Waɗanda aka yi sadakin kakannninsa da iyayensu da wata sana’a ta gado sun yi watsi da ita, sun wofintar da ita sun shiga cikin masu yi mata shaguɓe da ature.[56] Mene ne butulci in ba haka ba? Ina ta kai mu yau, in ba sace-sace da ƙwace da ƙeƙeshewar kunya ga idanunmu ba? Kowace al’umma ta bai wa butulu masauki sai ya yi mata butulci ci gabanta ya dabirce.

    Gaskiya:
              Idan ba a manta ba, Bahaushen asali babbar suturarsa ita ce “gaskiya”. A namu zamani, wayonmu ya muzanta ta. Ta kasa samun wurin miƙe ƙafafu a gidajenmu da ma’aikatunmu da masallatanmu da zamantakewarmu. Wannan ya haddasa sai gaskiya ta ceci mutum ya hau tudun-mun-tsira ya gayyato ƙarya a yi mata kisan mahaukacin kare. Duk al’ummar da gaskiya ta ƙaranta dole butulci ya yawaita. Da butulci ya kafa gwannati ƙasa ta gama durƙushewa komai ƙarfin tattalin arzikinta da ilminta da ƙarfin sojanta. Ƙasarmu ba ta da ciwon da ya fi na butulci. Ku sa ido ku ga yadda mai gaskiya ɗaya, talaka, ya karɓe mulki ga hannun hamshaƙan jigajigan masu abin duniya fiye da miliyan ɗari biyu. A cikin duniyar da ake ciki yau 2014/2015 babu wanda ya kai ɗan Nijeriya sanin amfanin gaskiya da daɗinta da ƙarfinta da tagomashinta.[57] Ƙasar Amerika da Ingila da Faransa da Jamus da Rasha su ne shaiduna a kan wannan iƙirari.

    Tsarin Siyasa:
              Tsarin siyasa ta demokraɗiyya a kan butulci butulai suka ɗora shi. Tsarin ya yi takin saƙa da duniyar tunaninmu ta gargajiya da saukakkin addinai da ya taras na Yahudu da Nasara da Musulunci, aka aminta Allah bai san matsalolinmu ba, muka shata wa kanmu tsarin da ya dace da tunaninmu.[58] A koyaushe tunaninmu ƙaruwa yake yi, matsalolinmu na nunka su, tsarinmu ya kasa yi muna susa gurbin ƙaiƙayi. Idan ba a manta ba, butulcinmu kwatankwacin abin da ya auku tsakanin Shaiɗan da Ubangiji ne bayan an halicci Annabi Adamu (AS). Akwai ƙasashen da ba su kai mu arziki ba a da, da suka bar wa mai komai mai kowa dabara, yau su ke rungume da kwankwason tattalin arzikin duniya. Ko yanzu ba mu makara ba, mu dai sallami “baba butulu” ya koma ƙauyensu. Babu wai, hatta da wasan bori da tauri ya fi tsarin da muke a kai daidaitacciyar manufa ta kare rayuwar jama’a da dukiyoyinsu da mutuncinsu.

    Gaba Ta Koma A Baya:
              Tunanin tsantsame hannu gabaci ga shugabancinmu a sake ragama ga matasa wata alamar taɓuwar hankali ce da butulcin da muka yi wa gabaci ya haifar.[59] Kushe hasashen gabaci na faɗar, komai saurin Laraba tana barin Talata ta wuce, wauta ne. Ko hankalin tuwo ya san, da jiya, da shekaranjiya, da shekaranjiya ban da jiya duk jiya ce gabansu. Wa zai musunta cewa, da gobe da jibi, da gata, da citta, duk daga yau aka fara ƙidayar su? Me matashi ya sani bayan kece raini ya shiga tsara a dama da shi komai ta banjama, banjam? Su wane ne ‘yan ƙunar baƙin wake, mai rabon ganin baɗi ya gani? Waye ke kirarin ƙarfi ya kawo tsoro ya ɗebe? Wane rashin hankali ya fi abokin yaƙi ya yi iƙirarin, “a mutu duk har liman!” Ai Bahaushe cewa ya yi: “Abin da babba ya hango a zaune yaro ko ya daka tsalle ba zai hango shi ba”. Don me ake cewa, “Ana barin na zaune domin na tsaye?” Wane ne na zaune? Yaro. Wane ne na tsaye? Babba. To, wace dambala ta kai ga barin na zaune domin na zaune? Ban ga wata basira cikin faɗar; ana barin na tsaye domin na tsaye ba. Ƙasashen da ba su butulce wa al’adunsu ba, zancen sa wa matasa ido da rayuwar al’ummarsu ba ta taso ba.

    Nauyin Butulci A Sikelin Ilmi Da Cigaban Ƙasa:
              Ɗan abin da na rego gabanin wannan ɗan bincike shi ne, yadda butulci ya taka rawa wajen rusa ƙasarmu a yau. Na so a nan, in ɗan yi tsakure a kan dangantakar butulci da taɓarɓarewar ayyukan ci gaban ƙasa. A tunanina, dukkan ayyukan ciyar da ƙasa gaba “ilmi” ne cibiyarsu. Idan butulci ya rasti wurin da ake bayar da ilmi, ba zai ƙyale masu bayar da shi ba. Idan masu bayar da shi suka shaƙi gubar hayaƙinsa za su sunsuna wa masu karɓarsa (ɗalibai), daga nan kuma ƙasa ta kai sin waw raa takuri sai durƙushewa.
              Ƙololuwar sirrin ilmi ita ce nagartattun kayan aiki da ƙwararrun masu bayar da shi amintattu. Matuƙar an samu haka komai ya yi an ba gwauro ajiyar mata. Nagartattun kayan aikin ilmi ba su kai ƙwararrun masu bayar da shi muhimmanci ba, a ƙa’idance. Butulcin da ya shiga cikin ilmi shi ne “Maguɗin Jarabawa”. Babu butulcin da ya kai malamin da aka koyar, ya gane abin da aka koyar da shi, ya karɓi takardar shaidar ya cancanci ya koyar ko ya yi aiki a kan abin da aka koyar da shi, ya dawo yana yaudarar al’umma yana bayar da takardun shaida ga waɗanda ba su cancanta ba, ya saka al’umma gaba ɗaya cikin hasara. Idan butulci ya ratsi gandun ilmi an gama da ƙasa gaba ɗaya domin:
    (i)               Tattalin arzikinta gaba ɗaya ga ilmi ya dogara.
    (ii)             Makarantun koyar da kowane irin aiki ilmi ne jigonsu.
    (iii)          Kiyon lafiyar ƙasa ƙashin bayansa ilmi.
    (iv)           Fasaha da kimiyya da ƙere-ƙere ilmi ne tsarinsu.
    (v)             Tsaron ƙasa da gudanar da tsare-tsarenta ilmi ke tsare da shi.
    (vi)           Kowace musiba ta shafi al’umma da ƙasa da ma’ilmanta za a fuskance ta, idan ta buwaye su sai a sa wa mai yi ido.
    Wataƙila don ganin ɗan biyan da ake yi wa masu bayar da ilmi bai taka kara ya karya ba, ko kuma ganin garaɓasar wasu wuraren aiki saɓanin nasu sai butulci ya shige su. Illar da wannan butulci ya yi ƙasashenmu na da yawa. Daga cikinsu akwai:
    (i)               Taɓarɓarewar shugabanci na gaba ɗaya daga sama har ƙasa, ka ce ba a taɓa shaƙa ƙurar allin karatun boko ba.
    (ii)             Fasahar rubutu da karatu an yi kusan rasa ta ga waɗanda ke da shaidar ƙare karatun firamare da gaba da firamare.
    (iii)          Takardun shaidar digiri ba su kai nauyin na makarantun sakandare ba.
    (iv)           Manyan takardun digirin MA, MPhil, PhD a yau da wuya su gwada tsawo da takardun shaidar digiri na magabatansu.
    (v)             Shaihunan masana sun yawaita an kasa fitar da suhe wuta a kowane fanni na bincike, domin kama da wane ba wane ba ne.

    A taƙaice yau, butulcinmu ya kai ga takardun shaidar ƙare karatu ke da muhimmanci ba karatun ba. Kwalayen digiri nawa na ƙarya ake fasa ƙwaurinsu zuwa ƙasarmu a cutar da mu da al’ummarmu mu sa ido? Likitocin ƙarya da lauyoyin ƙarya da injiniyoyin ƙarya da masanan ƙarya da kwalayen digirorin PhD na ƙarya da ke cikin ma’aikatunmu da jami’o’inmu kaɗai sun isa su durƙusar da ƙasar nan. Yayin da mai koyo da wanda ke koyarwa duk jigonsu wanda bai koya ba, yaya za a yi a gano abin da ake son a koya? Sa wa wannan ido ba taimakon ƙasa ba ne, tsayin daka a tantance takardun kowane irin mai aiki ba ƙulla sharri ba ne, kwance sharri ne, domin maganin sharrin da aka tanka/ƙulla. Butulcin da ke a nan shi ne, waɗanda ya kamata su yi tsaye a yi bincike, su ke ba da takardun na ƙarya. Waɗanda za a su yi binciken takardunsu ne ake son a yi bincike. Masu ba yara takardun shaidar karatu ba su da takardun shaida. To! Mai sahihiyar takardun shaida ya sa ido a ci gaba da aiki da takardun ƙarya, ya yi butulci. Dole mu yi wa kanmu adalci, in muna son adalci ya gudana ƙasarmu.

    Tanade-Tanaden Al’ada Na Kare Butulci:
              Haƙiƙa babu al’ummar da ba ta da butulu. A kowane wuri aka samu butulu dole butulci ya bayyana. A ma’aunin bincike, da za a magance butulci gaba ɗaya da duniya ta zauna lafiya. A irin rutsin da na ƙyallaro butulu da ire-iren musibunsa, hanyoyin da za a bi a narka gubar ƙullun butulci a zukatan waɗanda ake butulce wa su ne:
    (i)               Mutane su ilmantu da cewa, akwai butulu, akwai butulci, kada a yi sakaci da sanin haka cikin kowane irin al’amari na duniya.
    (ii)             A cikin kowace hulɗa da zamantakewa ta duniya mai hankali ya yi shirin ko ta kwana ga kutsen butulcin butulu.
    (iii)          Kada tunanin butulu da butulci ya zama sanadin barin taimako da kusantar mutane, a dai yi taka tsantsan da sanin akwai su. Kada cutarsu ta hana a ceci wani.
    (iv)           A al’adance, komai za ka yi ka san dalilin da ya sa za ka yi shi. Dalilin ka shi ne maganin dahin da butulu zai harba domin ba don shi aka yi ba, butulcinsa shi zai cutar ga sakamakon da zai riska.  
    (v)             Masana sun ce, yana da kyau mai wayo da hankali a koyaushe ya saɓa wa tunanin masu ganin sun san shi ga abin da suke ganin yana iya yi ko zai yi. Idan katawar ‘yan-sa-ido ta kasa samun makarin wurin kamu ga ƙafafunka ka sha maganin batulcinsu.
    (vi)           A gudunmuwar adibban Larabawa cewa suka yi: “Abubuwa uku korarru ne a duniya babu su: Dodo da Hijilma da aboki na har abada (wato amini na ƙarshe)”. In an sha wannan ɗan magani wataƙila a samu riga-kafi.

    Sakamakon Bincike:
              A rayuwar ɗan Adam, komai zai aikata yana son ya ga sakamakonsa domin tantance shi sosai. Dalilin da ya sa na yi wannan bincike shi ne, ɗora duniyar almara da ta zahiri domin a kyautata zaman ta zahiri soasai, a samu ci gaba ciki. A ɗan abin da na hango a wannan bincike na lura da cewa:
    1.     Butulci ya fi amo sosai a duniyar siyasa musamman ga masu mulki da aminansu na tsaro ko tafiyar da mulki. Butulcin da ke bayyana a nan bai taɓa barin mai mulkin kan karaga ba, bale rayuwarsa. Idan ba a kashe su ba, sai bayan sun sauka kujera butulcin butulai ya bayyana.
    2.     Butulcin da ke aukuwa a abota ya fi na ɗa da uba da mahaifa ko mata da miji ko mai masauki da baƙonsa muni. Abotar ƙarshen zamani tana cike da matsalolin da sun fi gaban hankali ya yarda da aukuwar su. Butulci tsakanin iyaye da ɗa, ɗa ne mai laifi. Tsakanin miji da mata raba aure na maganinsa. Tsakanin baƙo da mai masaukinsa na ɗan lokaci ne. To! Na abota ya fi muni domin shi ake kira da ta ciki na ciki, da lauje cikin naɗi, zama da kusurwa, zaman ‘yan marina, ba a iya saurin tantance shi sai ɗaya ya zama sanadiyyar mutuwar ɗaya bisa ƙyashi da jiyewa.
    3.     Babu cigaban da butulci ba ya rusawa domin shi ke tarwatsa haɗin kan jama’a kowa ya sa kansa daban. Wannan ne dalilin da ya sa dokokin ƙasashen duniya suka saka masa hukuncin kisa ga mai shi kai tsaye babu tara balle ɗauri (treason).
    4.     Butulci karatunsa na tushe ƙofar taimako da agaji ga mutane. Gajiyayyu da marasa galihu da mabuƙata da marayu dalilin tagayyararsu a duniyar zamaninmu shi ne butulci. Wanda duk ya karanci butulci sosai da sosai yana jin tsoron ya je taimako sai an nemi taimakon a taimako shi.
    5.      Butulci na sa rashin yarda da rashin natsuwa da tsoro a zukatan jama’a. Wannan zai rarraba haɗin kai, da zarar haɗin kai ya wargaje ƙarfin jama’a ya ragu.
    6.      Butulci na haifar da mummunan ƙarshe da ɓata zumunci da ɓata zuri’a gaba ɗaya domin a al’ada cutar butulci da wuya a manta da ita a rayuwa.
    7.      Bala’in butulci ya fi auka wa masu hannu da shuni da masu tausayi ga musibun da ke auka wa jama’a. Wanda duk belar ta rutsa da shi, an ba shi tsoron sake tunanin sake jiki da abin hannunsa ga jama’a. A koyaushe tunaninsa sau ɗaya gyaɗar makaho ke ƙonewa.
    8.     Bisa ƙiyasi, jinsin mazaje sun fi mata butulci, kuma matasa sun fi yawa a ciki, haka kuma sai hasken ilmi ya bar farfajiyar tunani ake auka wa butulci.

    Naɗewa:
              Ba taimako ke da ciwo ba, tukuicin butulci ke da ciwo. Ciwon butulcin butulu na ɗan lokaci ne, don haka kada ya rafashe ka ga taimakawa. Da ɗai butulu zai tuna da: Ba ka tunɓuke sarki ka yi Sarki, zai tabbatar da ƙarshen ƙaiƙayi kan masheƙiya yake komawa. Rashin tunawa da akwai ranar ƙin dillanci shi ke sa a manta da cewa, ba a san tabkin da ke makara da ruwa ba. Karatun da ke cikin saƙon munafucin Dodo yakan ci mai shi, shi ya tabbatar da abin da duk ka shuka shi za ka girba. Dole mai samu ya kawar da kai ga rama cuta ga macuci ibada, domin faɗar kowa ya yi zamba kansa ya yi wa ya share wancan nassin. Kai dai a matsayinka na mai hankali da wayo, ka riƙa sara kana duban bakin gatari. Duban bakin gatari shi ne, a gyara yau don gobe. Da butulci wata hajar talla ce, da sunansa ya yi tagomashi cikin taskokin adabi da al’ada. Mai wayo a koyaushe ɓoye tunaninsa yake sai ya ga na sauran abokan tafiya, domin ya san gaggawa ba ta kunu. Ilmin da muke da shi na ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, shi ya sa muna natsuwar hango komai nisan dare gari zai waye, sai gari ya waye za a fara ƙyarga sunan ranaku, don haka butulu ka sani komai saurin Larba tana barin Talata ta wuce. Wannan lisafin haka yake a garin kowa sai garin da baba Litinin da Talata. Bisa ga darzajen karatun da muka yi, za mu iya taƙaita taƙaitaccen sakamakon butulci da cewa idan za a naɗe nazarin bitar karatun sakamakon nazarin butulci a ce:
    Butulci ƙololuwar hasada ce da wauta ta ƙiyayya da ƙyashi da son kai suka haifar. Musibarta idan ta shafi mahaifa tana da alaƙa da taɓuwar hankali ga mai ita. Ga masu tausayi da ba da agajin gaggawa, ganwo kan birkice da kaya. Ƙarshen sakamakonta ga masu hali da abokai da masu mulkin da masu gida da yaransu, ta fi haifar da ruɓushin dukiya da rayuwa cikin ƙazantaccen artabu na rashin tausayi da nuna rashin sani da sabo da ragowa. A zamaninmu, ba ta taɓa kai hari ba ta risga da rayuwa da dukiya gaba ɗaya ba. Haka kuma, taurarin butulci su ne waɗanda ake amincewa tare da dogon zamani na zamantakewar kyautatawa.    


    MANAZARTA
    Abraham, R. C. 1946. The Dictionary of the Hausa Language. London: Hodder and Stoughton.
    Awde, N. 2006. Hausa-English Dictionary. Longman, reprinted.
    Bargery, G. P. 1933. A Hausa-English Dictionary and English Hausa Ɓocabulary. Zaria: ABU Press.
    Bunza, A. M. 2009. Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Center.
    Bunza, A. M. 2014. In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo, Egypt: Elkods Printing House.
    Bunza, A. M. and Nofal, M. A. (ed.) 2013. Ruwan Bagaja In Perspesctiɓe: Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose 1933-2013. Published by Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity, Katsina and Uniɓersity of Cairo, supported by Tertiary Education Trust Fund (TETfund) Nigeria.
    Bunza, A. M., Gobir, Y. A., Sallau, B. A. (eds.) 2013. Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa (The Detrioration of Hausa Culture). Published by History and Culture Bureau, Katsina State, and Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity, Katsina.
    Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. 2006. Ƙamusun Hausa. Wallafar Jami’ar Bayero Kano.
    Gummi, A. M. 1979. Alƙur'ani Maigirma Da Kuma Tarjamar Ma'anoninsa Zuwa Ga Harshen Hausa. Wurin da aka Tanada Musamman na Sarki Fahad don buga Alƙur'ani mai girma, Saudiyya.
    Hubbard, P. J. 1973. “Education under Colonial Rule: A History of Katsina College 1921-1942”, PhD Thesis, Madison: Uniɓersity of Wisconsin.
    Magaji, A. 1999. “Kunya da Mutunta Mutane a Al’ada.” cikin Hausa Studies. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
    Mani, A. 1966. Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa. Zaria: NNPC.
    Mashi, A. A. 2000. “Zama da Maɗaukin Kanwa: Tasirin Zamananci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin digirin MA, Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
    Nduka, O. 1964. Western Education and the Nigeria Cultural Background. Ibadan: Oɗford Uniɓersity Press.
    Newman, R. M. 2003. An English-Hausa Dictionary. Longman, reprinted.
    Rimmer, E. M. 2009. Zaman Mutum Da Sana’arsa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
    The New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of English Language: Deluɗe Encyclopedic Edition. Trident Press, International Edition (1996).
    Yahaya, I. Y. 1971/72. Tatsuniyoyi da Wasanni Juzu’i na 6. Ibadan: Oɗford Uniɓersity Press.


    [1] Abin mamaki a nan shi ne, a cikin Hausawa makaɗa ‘yan tsirarru ne amma ga fitattun karin maganganu da suka shafi kayan kiɗa suna fitar da duniyar tunanin Bahaushe. Daga cikinsu akwai: Ganga ba ki asiri; tambarin talakka cikinsa; da gangan kiɗin ganga da lauje; gyaran gangar Azbinawa; ba gyaran-gyaran a yi mai kura ta sato ganga; shiru mai kiɗin kalangu ya faɗa rijiya; ga su nan dai. Don haka, ƙunso muhimmin saƙon Bahaushe cikin kayan kiɗan Bahaushe ba baƙo ba ne.
    [2] G. P. Bargery, A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Ɓocabulary. ABU Press, 1993.
    [3] CSNLF, BUK, Ƙamusun Hausa. Kano, 2006.
    [4] Hira da Dr. Abdulƙadir Sani, Shugaban Sashen Larabci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto (da ya gabata) Litinin, 2015.
    [5] Turanci ya zo ta fuskar ci da ƙarfi ta fuskar mulkin mallaka na indirect rule a arewacin Nijeriya da assimilation a ƙasar Jamhuriyar Nijar wanda ya haifar da yaƙe-yaƙe da gaba. Bugu da ƙari, ya zo da baƙon addinin Mishon da ke takin saƙa da aƙidar addinin Musulunci da ya tarar. Waɗannan abubuwan tarihi suka rage wa Turanci tagomashi a zukatan Hausawa ko lokacin da Turawa na kan danniyar mulkinsu haiƙan.
    [6] The New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of English Language: Deluɗe Encyclopedic Edition, Tredent Press, International 1996 Edition.
    [7] Roɗana Ma Newman, An English Hausa Dictionary. Longman, 2003.
    [8] Dubi irin zaman da Saƙimu agolan Malam Nabakin Kogi ya yi da Malam, kuma ya zama ajalin Malam da matansa huɗu duka. A dubi, A. Imam, Ruwan Bagaja, NNPC, 1933.
    [9] Irin zaman mata da miji a daɗe ana tare ana cin arzikin miji ana cikin daula, da ɗan abin ya ƙare ta tayar da jidali dole sai an sake ta. In ba a yi ba ta kai kotu, wannan shi ne butulci.
    [10] Yadda ɗalibi zai karɓi takarda daga hannun malaminsa. Idan ya ga ya kai ga karɓar manyan takardun shaidar MA, MPhil, ko PhD ko ya ga ya kai Shaihin masani ya fara raba ruwa rana da malamansa, wai ya ga ƙafafunsa sun kama ƙasa. Tir! Ai babban butulci ne a manta da cewa, sai an yi shuka ake zancen tumu.
    [11] Tarihin wani malamin kokuwa da ɗalibinsa ya isa misali. Bayan an tabbatar masa da ƙwarewa ga kokuwa, ya gama da kowa a garin bayan malaminsa. Aka zuga shi da turu ya ce, malamin ya zo a taka. Malam ya ƙi, ya matsa dole sai an yi, aka taka aka kayar da ɗalibin kamar bugun ashana. A dubi, A. M. Bunza, “Baki Abin Magana” wallafar Association of Nigerian Languages Teachers of Nigeria.
    [12] Wannan ana iya kwatanta shi da sakayyar shugaba Jonatahan na PDP da shugaba Buhari na APC. Buhari ya gyara Nijeriya tun ba a ko san da Jonathan ba. Ya daidaita tattalin arziki, da tsaro, da siyasa, da kawar da zalunci. A cikin wannan gagarumin aiki Jonathan ya rayu ya zama abin da ya zama. Yau don ya samu riƙa ƙasar na wucin gadi yake ta yin kirari na rinjayar Buhari cikin arzikin da Buhari ya shimfiɗa. Wannan butulci ne.
    [13] Kamar mutum ne ya saya raƙumi ko sa ya dinga yin ƙwadago da shi. Raƙumin ya sama masa dukiya da zai saya abinci ya rayu. Ya sama masa wata dukiyar ya saya filin gida ya gina shi. Yana samun gida, ya ci gaba da neman kuɗi, ya tara jallin aure. Ranar da za a yi walimar aurensa, ya yanka raƙumin a yi liyafar walimar aure da shi. Wannan shi ne misalin wannan ɓangare na butulci.
    [14] Tamkar dai yadda ɗan Adam yake, bayan Allah Ya halicce shi an ganar da shi Mahaliccinsa. Da ya girma, ya kama tsafi da shirka, ya yi fito-na-fito da Mahaliccinsa da ya ce ba ya gafarta wa shirka da Shi. Wannan kafircin shirka da yake yi shi ne kafirce wa Allah da butulce maSa.
    [15] Irin yadda makaɗa Gambo Fagada yake yi wa masu gidajensa ɓarayi da shi da makaɗa Kassu Zurmi. In an koro ɓarawo su shiga cikin ‘yan kuwa alhali in ya ci nasara su ke shan daɗi. A wani ɗan waƙa Kassu na cewa:
    Jagora:          In an samu a ishe mu
    :In ku tas samu ku yi yamma (Sakkwato)
    :Sai an dawo

    Wai abin nufi shi ne:
    In sun sato su zo a ci tare
    In ko su aka kama su tafi Sakkwato hursuna!
    [16] A ganin mafi yawan mafasa baƙin zamantakewa wannan ita ce ƙololuwar butulci a rayuwar ɗan Adam. Wanda duk ke da hannu na sanadiyyar kasancewarka wani abu a duniya ta kowace fuska ka kasance, a koyaushe yana gabas kana yamma, a koyaushe kana bayan akasin tunaninsa da manufarsa da ra’ayinsa hasadar ta kai matuƙa. Babban burinka kada sunansa ya yi fice a kan naka.
    [17] Butulu ba ya da kai sai na ɗaukar kaya. Ba ya da hankali sai na cin tuwo. A ko’ina yake babban burinsa ganin bayan wanda ya yi wa butulci. A bisa wannan tunanin, da duk gubar butulci ta yi turnuƙu sai ya zama sanadiyyar mutuwar wanda ya yi masa tsani.
    [18] Wanda duk ya kyautata maka ka kyautata masa fiye da yadda ya yi maka. In ka cuta masa ka yi butulci.
    [19] A wahala tare da kai buƙata ta biya, a yi rabon ƙeta da son kai butulci ne.
    [20] A yi garkuwa da abu, a kai ga buƙata, a kasa yi masa tukuicin girma an butulce masa.
    [21] Tukuicin cuta ga wanda ya kyautata. Godiyar Maye ga wanda ya kyautata masa shi ne ya kama shi ya cinye.
    [22] Idan sun girma ga mamarsu suke koyon harbi, zama ɗaya su kashe ta.
    [23] A taimake ka, ka ƙi taimakon waɗanda suka taimake ka butulcin buga misali ne
    [24] Zaman maƙwabta ta cuɗe ni in cuɗe ka ce; wanda aka cuɗa ya biyo da bi-ta-da-ƙulli butulu ne.
    [25] Sakayyar da ake so ga ɗa ke nan, in ya kasa yin ta ya yi butulci.
    [26] Haugen banza butulun wofi, to madokin ya sha ke nan? Allah Ya wadaren butulu.
    [27] Gidan gado ya amfani ɗa, ya sani ko bai sani ba, nunin gidan da hagu ko cikin kure butulcewa ne.
    [28] Goge baki ga ƙasa da kaza ke yi bayan ta ci abinci ya sa Bahaushe na zarginta da rashin godiya irin ta butulu.
    [29] Butulcin maciji ga yaro neman rayuwar yaro, bayan yaro ya kuɓutar da shi daga makasa. Butulcin yaro ga zarɓe neman kashe zarɓe, bayan zarɓe ya ceto ransa daga maciji. Butulcin zarɓe ga maharbi nakkasar da maharbi na har abada, bayan an kuɓutar da rayuwarsa daga yaro. Wannan shi ne misalin ƙaramin butulci na cuta wa maceci. A ƙarshen wannan ƙissar, mutum aka fara yi wa butulci kuma mutum aka yi wa butulcin ƙarshe. Don haka, mutum ya fi kowace halitta ƙiyayya da butulci. Wannan ƙissar sananniya ce a tatsuniyoyin Hausawa amma ni na karance ta a rubuce-rubucen darussan adabi na Dr. Ibrahim Sarkin Sudan Kwantagora, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato wajajen 1999/2000.
    [30] Na samu wannan ƙissar ga Alhaji Muhammadu Ɗanɗa Hamma Ali, Principal Goɓt. Technical Secondary School Farfaru Sokoto a wata hira ta musamman wajajen 2013/2014. Wannan ƙissar ta tabbatar da kasancewar butulu maƙaryaci kuma azzalumi, makunyaci, mayaudari. Kasancewarsa wawa ya sa aka tarar da shi yana kirarin zambar da ya yi. A kula, butulci ba ya da bambanci tsakanin lafiyayyu da marasa lafiya domin makaho ne aka taimaka ya yi butulci.
    [31] Don ƙarin bayanin wannan waƙar a dubi A.M. Bunza, 2011 Narambaɗa. Ibrash Publishers, Lagos.
    [32] Na bi diddigin wannan shari’ar ta hannun abokina Dr. Ibrahim Sarkin Sudan Kwantagora, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato shi kuwa abokin yayan Marigayi Abdulƙadir S. Dori ne, wato  Dr. Haruna Alero na Economics Dept. UDUS. Na je ta’aziyyar Alero tare da Dr. Ibrahim da misalin ƙarfe 9:30 na dare a garin Alero. Abin lura a nan shi ne, taimakon da ya yi wa butulai shi ya zamo sanadiyyar hasarar rayuwarsa da dukiyarsa. Wannan shi ne ƙarshen yaudara. Idan naka butulu ya bar ka da ranka ka kwana da kariyar bai manta ba.
    [33] Yahaya Sa’idu Andarai maigidana ne a Goɓernment College Sokoto (Nagarta College Sokoto) yana aji biyar 1977 ina aji 3. Musibar ta auku a garin Sakkwato ina cikin garin. Yayin da musibar ta auku yana Director Finance Local Goɓernment Serɓice Commission Kebbi State. An kashe shi ranar 15/09/2014. Wanda ya kashe shi yaronsa ne kuma abokin sana’arsa, mai kula masa da ‘yar sana’arsa ta filaye. Shi ya yi wa yaron aure, ya gina masa gida, a hidimar auren naira dubu ɗari uku ya ba yaron na shagalin biki. Wannan duk ba ta sa ya gode ba, don haka ya gayyato ƙatta ya biya su, suka kashe shi. Kisa shi ne mataki na ƙarshe na butulci. Me kake zaton za ka yi wa butulu bai nemi ya gama da rayuwarka ba?
    [34] Ba ni cikin garin Bunza ko da abin ya auku amma ranar na shigo garin. Matsalar ta auku a shekarar 2014. Yaron Igbo, yana da babban chemist a garin Koko ƙaramar hukumar Koko-Besse, Jihar Kabi. Sunan maigidansa Emeka. Yaran da ake zargi ɗaya ya tsere ɗaya an sako shi. Da wannan matsalar da ta garin Kwaifa duk ɗaya ce, bashi ya haddasa kisan kai. A ko’ina aka ga butulci ya haifar da kisa wani abu ake son a ɓoye kada ya bayyana a jiya, musamman matsala irin ta bashi idan ya yi yawa kuma ya tsawaita (bad debt).
    [35] Lawwali Gandi Cashier ne a Ƙaramar Hukumar Raɓah ta jihar Sokoto. Waɗanda ake tuhuma har da maƙwabcinsa ciki. Kisan ya biyo da ƙuna irin na Abdulƙadir S. Ɗori Alero. An san ya san makasan nasa, kuma saboda irin tsananin kusancin da suke da shi ya sa suka ƙona gidan gaba ɗaya kada a kama su butulcinsu ya bayyana su tozarta.
    [37] Yayin da ya kashe Thomas Sankara an yayata wannan jawabi a gidan Rediyon BBC da ƁOA da CNN da Radio Faransa sosai. Kusancin Sankara da Campore da ya kashe shi irin na Ba’are da Wanke ne a Jamhuriyar Nijar. Ya yi wannan jawabin ne lokacin da jami’an tsaro na ciki (SSS) suka yi masa hannunka-mai-sanda kan take-taken Campore.
    [38] A ƙasar Iraƙi Yahudu da Nasara in ma akwai su ‘yan tsiraru ne. Tarikh Azeez Kirista ne (Masihi) amma aka ba shi mataimakin shugaban ƙasar tare da sanin masu addinin Masihi a ƙasar ba su da ko kaso ɗaya bisa ɗari na jama’ar ƙasar Iraƙi. Gabanin da a auka wa ƙasar da yaƙi, aka tilasta a yi ƙuri’a ta a je yaƙi ko kada a je tare kuma da nuna yarda da gwamnatin da ke ci. Duk faɗin majalisar Iraƙi kowa ya yarda ƙuri’ar Tarikh kaɗai ce aka samu ta nuna rashin yarda. Da za a kai musu babban hari na farko Tarikh ya gaya wa UN/Amerika wurin da za a yi taron majalisar ƙoli ta Iraƙi, da lokacin da za a yi, da lokacin da manyan ƙasa za su shiga ɗakin taro. Daidai lokacin jiragen yaƙin Amerika suka kai hari wurin zaton Saddam na ciki. Duk da wannan bai sa Saddam ya fitar da shi ba ko ya ɗaure shi ko ya kashe shi. Da yake butulu maras kunya ne, maras sanin ya kamata, wawa, maƙetaci bai ja da baya ba sai da aka kashe Saddam. Me kake zaton ka yi wa naka butulu ku zauna lafiya? Idan butulci ya haɗa da siyasar mulki sai ya ci rayuwa yake ƙarewa.
    [39] An ce da Sir. Ahmadu Bello ya tabbata kashe shi za a yi, ya gaya wa Nzegu cewa: “Abin da ya kawo ka gidana ba za a ci nasararsa ba ko da kun kashe ni.” Wane takaici ne, na jan gawar maigidanka ƙasa giriri bayan ka kashe shi? Halin butulci ke nan, ko an mutu dafin gubar na nan ba ta gushe ba. Dubi yadda mutanen Kwaifa suka ƙona gawar maigidansu Abdulƙadir Usman S. Ɗori Alero.
    [40] Wai: “Jiya kaɗan da an kuɓutar da ni, amma yau saboda wannan yaro Dimka Allah Sarki!” A koyaushe butulu ganin yake yi in ya yi ta’adi yana iya kuɓuta. Abada wanzan ne ba ka so ga jikinka. Da zai samu ya kuɓuta sai ya aikata wadda ta fi wannan muni. Ku tambayi Zarɓe da ya cire wa yaro maciji.
    [41] Suratul Baƙara.
    [42] Suratul Ma’ida: “Laƙad kafaral laziina ƙaluu innal Laaha saalisu salaasa”.
    [43] Hira da Malam Mas’udu a makarantarsa ta zaure da ke masallacin Yarbawa Sokoto shekarar 2011.
    [44] Haka fassarar nassin ƙissar yake a fassarar magabatan farko. A Saudiyya shekarar 2014 wani ya doki ‘yarsa har ta mutu, aka yanke masa hukuncin bulala ɗari da ɗaurin shekara (biyar), dogaro a kan ba a kashe uba saboda ɗa.
    [45] A cikin babukan yaƙi na Risala da Mukhtasar Khalil an ambaci haka. Sheikh Ibn Ishaƙ a cikin littafinsa Sullamul Gawaamidi Fi Ilmi Rasaa’idi ya ambaci haka, wallafar Ɗan’ige Tsamiyar Dila, Sakkwato.
    [46] Haka yaro ya yi wa zarɓe, sai da maharbi ya cece shi.
    [47] Haka maciji ya so ya yi wa yaro, sai da zarɓe ya cece shi.
    [48] Irin haka ta auku tsakanin Annabi Musa (AS) da Malam Bil’amu Ɗanba’ura. Duk ɗalibin da ya butulce wa malaminsa sunansa Bil’amu.
    [49] Wane tsuntsu maharbin da ya ceci zarɓe zai sake taimaka wa a duniya? Ai zarɓe ya rufe ƙofar ceto.
    [50] Haka makaho ya yi wa mai doki da ya taimake shi.
    [51] Butulcin da maciji ya yi wa yaro ya yi kusan haka. Butulan Abdulƙadir S. Ɗori Alero sun fi fito da wannan maganar a fili ƙarara.
    [52] Dangantakar Bello Ubandawaki da Yahaya Sa’idu Andarai babbar hujja ce.
    [53] Da yawa daga cikin fitattun shugabannin duniya a ƙauye suka tashi suka amfana da nagartacciyar rayuwa irin su Mammar Gaddafi da Nelson Mandela da Saddam Hussaini da Shehu Shagari da Nnamdi Azikiwe da Yakubu Gawon da Dauda Malam Wanke da Ba’are Mainasara da sauransu.
    [54] Tilas a buɗe wata gagarumar ma’aikata da za ta kula da gabaci in ba haka ba butulce wa gabaci ya gama da mu.
    [55] Yanzu an manta da ajo da karo-karo da ɗegiya da tukuici da kyauta da biki da ɗauke da rance da bashi da jingina da tugu da sauran nau’ukan taimako.
    [56] A iya sanina, yau sana’ar ƙira da rini da kamun kifi da wanzanci sun shiga cikin haɗarin lokaci na yau ciwo gobe lafiya jibi masassara.
    [57] Don ƙarin bayani a dubi, M. Safana, “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, kundin MA, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
    [58] Tsarin sarauta irin ta addininmu ta dace da tunaninmu.
    [59] Yau 2015, ƙasarmu ta fi kowace ƙasa maguɗi da cin hanci da ta’addanci sanadiyyar miƙa ragama ga baya a manta da gaba.
    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.