DAGA


Abdulbasir Ahmad Atuwo
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
07032492269
atuwo@yahoo.com


Da


Dano Balarabe Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
07035141980
danobunza@yahoo.com


Takardar da aka gabatar a taron Ƙasa da Ƙasa kan Nazarin Harshen Hausa . Wanda aka gabatar a Jami’ar Bayero da ke Kano, daga Ranar 10-12 ga watan Nuwamba 2014.Tsakure


WaƘa na ďaya daga cikin abubuwan da ke bayyanar da abin da ke cikin rayuwar mawaƘi musamman abin day a shafi mu’amalarsa ta yau da kullum.Ilimin addini da na gargajiya na tasiri cikin rayuwar mawaƘi musamman dangane da abubuwan da ya rayu a kansu. Hausawa sun ce “Kowa da kiyon day a karƂe maƘwabcin mai akuya ya sayi kura”. Wannan takarda ta Ƙunshi bayanin luguden nassi Allah ta Maharazu Barmu Kwasare. Haka kuma wannan takarda na ďauke da taƘaitaccen tarihin Maharazu Barmu Kwasare da aka yi amfani da wasu baitoci daga cikin wasu waƘoƘinsa.

1.0 Gabatarwa


9. Ku bar Ƃata ku yi tcinka bayi,
Ku bar faďin wani bawa ya yi,
Ai ba a yi sai Allah ya yi,
Abin da duk kaka dubin ka yi
Shi yan nufe ka da yi nai Allah.

Marubuta waƘoƘin Hausa sun daďe suna rubuta waƘoƘi sai dai kowa da irin kiyon da ya karƂe shi, maƘwabcin mai akuya ya sayi kura. Wasu sun raja’a kan rubuta waƘoƘin addini, a yayin da waďansu suka yi wa na hululu bante daidai da kwankwasonsa. WaƘoƘin da wasu suka rubuta na gargaďi da wa’azi ne da sauran karantarwar addini, a inda za a sami waƘoƘin da wasu suka rubuta na shiryar da masu sha’awarsu kamar daga duniya sai Kaduna. Ma’ana, wasu waƘoƘi na shiryarwa ne ga jama’a, a inda waďansu kuwa, lamurran duniya kaďai suka fuskanta. Ganin kasuwar da marubuta waƘoƘin Hausa ke ci ta wannan fuskar da aka yi bayani a sama ya sa aka hango cewa waƘoƘin Maharazu na cikin waƘoƘin da ke jan hankalin al’umma kan nuni da a rinƘa sara ana duban bakin gatari. WaƘoƘi ne da ke tattare da rakiyar nafsoshin AlƘur’ani da Hadisai da kuma bayanin magabata, har ya kasance da wuyar gaske a ďaga waƘar Maharazu daga farko har zuwa Ƙarshe ba tare da an sami luguden nassi a ciki ba ko wuri ďaya. Ganin haka ya sa na Ƙudurci nazarin luguden nassi a cikin waƘoƘinsa domin ko ba komi an ce malami ya kasance rahama ga al’umma ba ya zama musiba gare su ba. Ganin ƘoƘarin da Maharazu ya yi a fannin amfani da nassoshi a cikin waƘoƘinsa tare da la’akari da alfanun da ake samu a ciki ya sa na ďauki wannan Ƃangare domin nazarinsa, domin Hausawa sun ce “Ana bukin duniya, akan yi na Ƙiyama”. Ganin salon luguden nassi a cikin waƘoƘin Maharazu na tabbatar muna da cewa akwai tausaya wa al’umma tare da lallashin zukatansu da cewa kowa ya shiga taitayinsa ga ayukan da yake aikatawa, su kasance na alheri tare da guje wa na sharri. La’akari da haka ya sa Maharazu ya ja kunnen al’umma a cikin wasu baitoci uku na waƘar Allah yana cewa:
55. Ni ban da ilimi balle jidda,
Hankali kurum in yo muku fa’ida
Ilmi kaďan na nir rida,
Na ji maza na nan su shidda,
Duk ba su ganin Manzon Allah.

56. Mai cin riba shi af farkonsu,
Da mai barin salawatul khamsu,
Gami da mai Ƙarya babbansu,
Ga uku nan wada munka faďe su,
Saurammu ukku da ikon Allah.

57. Mai yanke Ƙauna gun ‘yan’uwa,
Mai canye zakkatai shi Ƙi fissuwa,
Da mai barin mata tashi kassuwa,
Kun ji ukun suna bisa ďemuwa,
Gidansu nesa ga Manzon Allah.

Kafin shiga cikin wannan takarda ya dace a bayyana ma’anar nassi da luguden nassi tare da nau’o’insa tukuna.
2.0 Ma’anar Nassi
Kalmar nassi na ďauke da bayanin cewa kalma ce ta suna kuma mai jinsin namiji, kuma tilo. Jam’in wannan kalma shi ne nassoshi. Tare da haka kuma an ba da ma’anar nassi da cewa, (i) ayoyin Ƙur’ani ko Hadisi (ii) matani . Ita kuma kalmar matani an ba ta ma’anar littafin da ba a yi wa sharhi ba . A wani wuri kuma cewa aka yi nasi na nufin (noun, musculine). Any passage of the koran or other Arabic book. Ana iya fahimtar ma’anar nassi daga littattafan da aka kawo a sama da cewa madogara ce ko hujja ko dalili na faďar wata magana ko aikata wani aiki daga littafin Allah (AlƘur’ani) ko kuma daga maganar da fiyayyen halittu ya faďa ko aikin da ya aikata ko kuma aiki ko maganar da aka yi a gabansa bai ce komi ba (Hadisi/sunna).
Aro nassoshin Ƙur’ani da Hadisi da littattafan Furu’a da tarihi da adabi na Larabawa ana lugude bayan bayyanar Musulunci da samuwar karatu da rubutu, ake kira luguden nassi . Ana kiran sa “Iktabas” a cikin tsarin waƘoƘin Larabci ko a ce da harshen Larabci..

3.0 TaƘaitaccen Tarihin Maharazu Kwasare


Bayyana ko wane ne Maharazu baki ďaya ba zai yiwu a cikin wannan takarda ba. Akan iya yin tsakuren ko wane ne shi, sannan a ba da manazarta domin mai buƘatar haka. Za a sami gamsasshen bayanin Maharazu a cikin , da kuma littafin Ibrahim Yaro Yahaya za a sami sunansa ne na 12 a cikin marubuta waƘoƘi a jihar Sakkwato.
Duk da haka ya dace a ji wani abu dagane da Maharazu. An haifi Maharazu a garin Kwasare (wani Ƙauye kusa ga garin Acida da ke ƘarƘashin Ƙaramar Hukumar Mulkin Wurno, a shekarar 1916). Ya tashi gidan karatun addini ya kuma yi karatun sosai har ya kai an san shi a matsayin babban malami. Ɗankasuwa ne, mai sana’ar koli, ya yi saƘar hula Ƙube yana sayarwa. Allah ya yi masa baiwa a fagen rubuta waƘa sai dai da Ajami yake rubuta waƘoƘinsa, kuma bai yi karatun boko ba. Ya yi tafiye-tafiyen cin kasuwannin jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara. Idan aka sami waƘoƘinsa za a ga haka. Ya wallafa waƘa fiye da talatin.
Ba wannan kaďai ba, Maharazu ya kawo ďan bayanin kansa a cikin wasu bitocin waƘoƘinsa. Za a ga wannan a waƘar masallaci da kuma waƘar da ya yi ta ta’aziyyar Malam Babi. Ga abin da ya ce a cikin waƘar masallaci kamar haka:
Tammat daďa Barmu ya cika wanga littafi,
Sunansa Maharazu halshenai da Hausanci.

Garinsu Kwasare, nasbatai guda biyu ta,
Abbun Eulatiyyi, ummu haƘiƘa Gobarci.

A cikin waƘar da ke biye kuwa, Maharazu ya faďa da bakinsa domin ya kira kansa sha’iri, almajiri, da Ƙara nanata sunan garinsu. Ga baitocin da ke ďauke da zancen kamar haka:
Tammat daďa waƘa ta cika,
Daga Barmu, Mahrazu sha’iri.

Birnin Kwasare nan yaf fita,
Wani mai yawo almajiri.

Wada anka nufai da hususiya,
A nufai da zamowa ďahiri.

A cikin waďannan baitoci akwai abin riƘawa dangane da ko wane ne Maharazu. Ko ba komai, Hausawa sun ce “WaƘa a bakin mai ita ta fi daďi”. Haka kuma, sunan mahaifinsa AbdulbaƘi (Labbo Ɗanmariya), mahaifiyar sa kuma Rahamatu. Sunan Ƙanensa Malam Shehu. Maharazu ya rayu a duniya da shekara 63, sannan ya rasu a shekarar 1979. Ya shekara 36 da rasuwa a wannan shekara.

4.0 Nau’o’in Luguden Nassi


Kawo nassi a cikin waƘa nau’i-nau’i ne. Masana sun yi bayanin cewa akwai nau’o’in salon luguden nassi iri uku aƘalla. Gas u nan tafe kamar haka:
1. Jawo nassi (kawo nassi kai tsaye)
2. Fassara nassi
3. Ishara zuwa ga nassi.

4.1 Jawo Nassi:


Wannan na nufin marubuci ya kawo gundarin nassi daga AlƘur’ani ko Hadisi ko kuma littattaffan Furu’a kai tsaye cikin gundarin nassin asali. A nan ne za a ga aya cikakkiya ko sashenta domin kafa hujja ko yankar wani hukunci. A nan sai an kawo ayar ko haidisin da Larabci kai tsaye. Misali duk lokacin da ake son kawo nassin da ke tabbatar da kaďaitar Allah idan aka ce Allah ahad ko kuma Allah shi kaďai yake ba ya da abokin tarayya, sai an kawo su cikin nassi gundarinsa. Za a zo da wannan a cikin zuciyar takarda a Ƃangaren luguden nassin.

4.2 Fassara Nassi:


A nan ba jawo nassi ake yi ba tsagaronsa. Haka kuma ba ishara ake yi ba. Abin da ake nufi da fassara nassi shi ne, kawo magana wadda da mai karatu ko sauraro ya ji, zai gano bayanin ne kai tsaye daga Al’Ƙur’ani ko Hadisi ko kuma ijma’in da malumma masana suka yi a kan wata matsala domin samar wa alďumma mafita.. Haka kuma idan aka ce fassara ana nufin mayar da ma’anar wata magana daga wani harshe zuwa wani harshe. Yakan iya kasancewa daga harshen Larabci zuwa Hausa ko kuma daga wani harshe zuwa wani. Misali, Allah bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Kai tsaye akan iya gano fassarar ayar AlƘur’ani ce inda aka ce: (Lam yalid walam yulad) idan aka sami haka a nassin AlƘur’ani ko Hadisi ko kuma maganar magabata, shi ake nufi da fassara nassi.

4.3 Ishara zuwa ga Nassi:


Ishara zuwa ga nassi shi ne ambatar wata madogara ba tare da an jawo nassin ba. Idan marubuci ya ambaci sunan wani littafi kowane iri ne idan dai ya yi hakan ne domin kawo hujja to, ishara ce zuwa ga nassi. Misali duk marubucin da ke magana har ya faďi cewa a dubi AlƘur’ani ko Hadisi ko wani littafin Furu’a domin ganin hujja, ishara ce zuwa ga nassi. Aikin da wannan takarda ke buƘatar bayyanawa a nan shi ne ta ďauki waďannan nau’o’in luguden nassi da aka yi bayanin ma’anarsu a sama kuma, a ga yadda Maharazu ya yi luguden su a cikin waƘarsa mai suna ‘WaƘar Allah’. Ga abin nan zuwa kamar haka:

5.0 Luguden Nassi a Cikin WaƘar Allah Ta Maharazu Barmu Kwasare


Akan sami luguden nassi a cikin waƘoƘin waďansu marubuta da waďanda ba rubutawa suke yi ba sai dai, amfani da nassi da ake samu cikin waƘoƘin waďansu ya fi na waďansu yawa. Haka kuma akan iya tantance wanda yake almajiri daga wanda ya ďauki abin daga sama. Ko shakka babu, duk lokacin da aka ďaga waƘoƘin Maharazu aka duba za a tabbatar da almajiri ne ke magana kuma tare da tabbatar da cewa akwai albarkar almajirci a ciki. Idan aka dubi WaƘar Allah da ya rubuta za a fahimci cewa Maharazu ba ďan haye ba ne a wurin amfani da nassoshi a cikin waƘar ba. Duk wanda ya karanci WaƘar Allah la shakka zai fahimci malami ya yi wannan rubutu. Ga yadda abin ya kasance:

5.1 Jawo/Kawo Nassi:


Wannan ďaya ne daga cikin nau’o’in luguden nassi da wannan takarda ta duba. Bayanin ma’anarsa ya gabata sai dai abin da ya rage shi ne fitowa da shi a gan shi daga cikin WaƘar Allah. Ba kamar fassara nassi da ishara ba, jawo nassi na tabbata ne da kawo tsagaron aya ko sashenta, hadisi ko sashensa da kuma zance/maganar magabata kan wani abin da shari’a ke son yi wa matsayi.
Wata matsala da ke hana marubuta kawo tsagaron nassi a cikin waƘoƘinsu ita ce tsoron lalacewar karin waƘarsu da suke yi. Maharazu ma bai kawo nassoshi da yawa a cikin waƘarsa da yawa ba kamar yadda ya kawo luguden nassin ishara da fassara nassi ba. Duk da haka ba a rasa ďaya ko biyu da za a kawo a matsayin misali ba. Ga misalin jawo nassi/kawo nasis daga WaƘar Allah ta Maharazu Barmu Kwasare kamar haka:
23. Sarkin da anka yi ko na ina na,
Duk wanda anka naďa sarki na,
Allah gwani babban sarki na,
Don shi ka kama wata haka rana,
Shi ad da kunfayakunu Allah.

Za a iya fahimtar cewa, gutsuro nassi ne aka yi a cikin wannan baiti, domin ba aya ce gaba ďayanta aka kawo ba. Rashin kawo ayar baki ďaya kuma ba zai hana abin ya sake ďaukar wata fuska daga barin kasancewar sa jawo nassi ko kawo nassi ba. Yana nan zamansa kawo nassi/jawo nassi sai dai kuma a matsayin gutsurowa.
Maharazu ya yi amfani da sashen Ƙarshe na ayar ya kawo domin za a tabbatar da haka idan aka ga ayar baki ďaya. Yadda ayar take shi ne: Iza arada shai’an fa inna ma yaƘulu lahu kun fa yaku. Ma’ana Allah ya ce: Idan muka yi nufin wani al’amari ya kasance, abin da za mu ce shi ne zamo sai kawai ya zamo/kasance, sai ya kasance. Ga wani baiti da ke ďauke da jawo nassi, wanda wannan nassi ne na hadisi.
62. Ai mai kuďi in ba shi da fashi,
To ko batun nassi bai tashi,
La’anahullahu rashi wal murtashi,
In kun duba sai ku gane shi,
Cikin iziyya bayin Allah.

Marubucin ya kawo nassi tsagwaronsa a layi na uku. Za a Ƙara fahimta a nan cewa, jawo nassi ko kawo nassi shi ne ďauko hujja ko nassi a cikin kalmomin asali ba tare da an canza ko Ƙara komi ba, kuma idan aka koma ga tushe ya kasance an same shi hakanan babu ragi babu Ƙari. Misalan da aka kawo na jawo nassi da ke sama haka za a tarar da su idan aka dubi wuraren da suke tun asali, wato misalin farko an same shi cikin AlƘur’ani, na biyu kuma a cikin littafi mai suna iziyya.
5.2 Fassara Nassi:
Bayanin ma’anar fassara nassi ya gabata a sama wanda ke nufin abu ďaya idan aka ce kawo ma’anar nassi. Akwai wannan nau’in luguden nassi a cikin waƘoƘin Maharazu Ƙwarai, sai dai za a yi la’akari da waƘar da ake magana a kai wato WaƘar Allah. Maharazu na yawan fassara nassin AlƘur’ani a cikin WaƘar Allah, wanda sai dai a ba da misalai kaďan ba domin a kawo su duka ba. Idan kuma aka ce a kawo su baki ďaya abin zai yi yawa. Ga wasu misalai domin tabbatar da abin da ake magana a kai.
5.2.1 Kaďaitar Allah
Ko shakka babu Allah shi kaďai yake, ba shi da abokin tarayya, kuma bai yi kama da komi ba. Wannan na nuna Ƙarfin imanin bayi ne a fagen kaďaita Allah da suke da a cikin zukatansu. Dangane da haka ne ya sa Maharazu ya fassara nassoshi kai tsaye a cikin waƘarsa tare da tabbatar da kaďaitar Allah wanda duk wanda ya rasa wannan nau’i na imani sai dai a sake lale ďan caca ya ga an yi masa coge. Ga wasu baitoci tafe da ke nuna kaďaita Allah a wurin bawa:
4. In za ni yin abu in ce Allah,
In nig gama in gode Allah,
In niy yi samu in ce Allah,
In nir rasa kuma in ce Allah,
Don babu mai komi sai Allah.

5. Ya sahibina in hore ka,
Al’amari in ya same ka,
Ɗayanta Allah shi ka isak ka,
In ko mutum ya zalunce ka,
Sa mai ido da amanar Allah.

15. Allah guda na shi yay yo mu,
Ya san yinimmu da ko kwanammu,
Shina matsuwammu shi koma ji Ƙanmu,
Shina kashe mu shi ko tashe mu,
Sarkin da bai da magada Allah.

25. Sarki guda na ba shi da ďan’uwa,
Shi da kowa bai tarewa,
Tashi sarauta ba ta misaltuwa,
HaƘiƘa bai gada ba ga kowa,
Balle a yo gadon ta ga Allah.

Da za a nazarci baitocin da ke sama a natse, za a tabbatar da Maharazu ya yi amfani da nau’in fassara nassi daga cikin nau’o’in luguden nassi guda uku da aka ambata a sama. Ayoyin AlƘur’ani ne da kuma Hadisai zalla ya kawo idan aka tsaya aka tantance sosai. A baitin fakro, layi na farko Maharazu ya fassara Bismillahi ne da kuma hadisin da Annabi SAW ya ce, “Duk aikin da za a fara ba tare da an fara da sunan Allah ba, ya zan mai yankakken albarka”. Layi na biyu kuwa marubucin ya fassara alhamdu lillahi ne. Ga shari’a idan za a fara cin abinci an ce a kira/fara da sunan Allah. Idan aka Ƙare cin abincin kuma sai a gode wa Allah ta hanyar faďar alhamdu lillahi. Layi na uku da na huďu kuwa fassarar hadisin Annabi SAW ne hadisi na biyu a Ƃangaren bayanin abin da ake nufi da imani tare da ginshiƘansa. A nan Maharazu na fassara yin imani da Ƙaddara mai kyau da maras kyau ne. A layin Ƙarshen baiti kuwa ya Ƙara jaddada muna cewa yana da imanin komi da kowa na Allah ne. Duk abin da ka gani ga wani na Allah ne ya ba shi in kuma rashi ne, daga Allah yake.
A baiti na biye kuwa daidai layi na uku, Maharazu na fassara ayar nan inda Allah ya ce “Waman yatawakkal alallahi, fa huwa hasbuhu’. A baitin da ke biye da wannan kuma, layi na huďu fassara ce ta Yuhyi wa yumitu, a matsayin gutsuro sashen aya. A baitin Ƙarshe kuwa ya nuna Allah shi kaďai yake ba ya da abokin tarayya, tare da ba da tabbacin Allah bai gadi mulki ga kowa ba balle ya bar wa wani gado. Ba ya da farko kuma ba ya da Ƙarshe. A layin farko za a fahimci fassarar Ƙulhuwallahu ahad ce. Dangane da siffofin Allah kuma, Maharazu bai Ƙyale ba sai da ya kawo fassarar wata ayar da ke cikin suratul iklas a daidai layi na uku kamar haka:
29. Har abada shi ke ikon nashi,
Bai gado kuma ba a gade shi,
Bai haifi kowwa ba a haife shi,
Shi agazan kar in saƂe shi,
Ba mai Ƙidaye sarautar Allah.

A gundarin ayar ga yadda take:........................................... A wani baiti da Maharazu ya kawo na abin da ya shafi ayukan Allah, ya kawo cewa, Allah ke rayawa kuma shi ke kashewa. Maganar na nan daidai layi na huďu kamar haka:
15. Allah guda na shi yay yo mu,
Ya san yinimmu da ko kwanammu,
Shina matsuwammu shi koma ji Ƙanmu,
Shina kashe mu shi ko tashe mu,
Sarkin da bai da magada Allah.

Wannan ya yi daidai da wurin da Allah ya ce:...................................
Haka kuma akwai fassarar wata aya da Maharazu ya kawo a layuka biyu na Ƙarshen baiti na 30 wurin da ya fassara Lahaula wala Ƙuwwata illa billah. Ga baitin kamar haka:
Yawan tsaro da yawaita dubara
Duk ba su kauda mutum ga hasara,
Babban tsari na nan ga Tabara,
Babu tsimi kuma babu dubara,
Sai wadda yay yi ma bawa Allah.

5.3 Ishara Zuwa ga Nassi:
Akan sami marubuta waƘa na yawan amfani da ishara zuwa ga nassi domin yin nuni ga madogarar da suka gani kuma suka dogara a kai. Bayyana wurin da aka ga hujja tare da ambaton suna ake kira ishara zuwa ga nassi. Ba a kawo nassin gundarinsa sai dai a faďi sunan abin da nassin ke ciki domin mai buƘata ya je ya samu ya duba. Shi ma wannan nau’i na luguden nassi akwai shi a cikin waƘar Maharazu mai suna WaƘar Allah. Ga misalai kamar haka:
58. Ku hau batun ga Ƙwarai ku riƘe shi,
Ku tabbata ba ni na faďe shi,
Wada nig ganai haka niw waƘe shi,
Cikin hadisi nis same shi,
Zancen Muhammadu Manzon Allah.

A nan Maharazu ya yi ishara da nassin hadisi a cikin wannan baiti tare da nuna nan ne madogarar da ya laƂe gare ta. Idan aka kula sosai ishara ce ko nuni zuwa ga nassi kai tsaye, wato nassin hadisin Manzon Allah (SAW). Akwai wani baiti da ke ďauke da irin isharar da ta gabata, mai zuwa kamar haka:
33. Ni jahili nike ba masani ba,
Amma batuna ba Ƙarya ba,
Duk wanda ya ce ba hakanan ba,
To duk shi bar ratce shi bi turba,
Shi dubi AlƘur’anin Allah.

122. Uwat tawaye mil labari?
Aljanna kiy yi biďa ko nari?
Kina bara da ďiya jariri,
Batunki babu shi tun daf fari,
Da na ganai ga farillar Allah.

123. Cikin iziyya duk na duba,
Cikin Risala duk na duba,
Lawal da Sani duk na duba,
Kai! Had da Ƙur’ani na duba,
Duk ban ganai ba ga ayar Allah.

A baiti na 33 da aka kawo, layin Ƙarshe ne ishara zuwa ga nassi. Ya yi nuni da a dubi AlƘur’ani za a ga hujja a ciki. Ita kuma farillar Allah da ke Ƙarshen baiti na 122 na nufin abin da aka wajabta da a yi, idan ba a yi ba kuma, an yi laifi. Haka ma a baiti na 123, kawo sunan Iziyya da Risala da Lawali da Sani da Ƙur’ani da ayar Allah duk ishara ce zuwa ga nassi Maharazu ya yi. Ta kawo waďannan misalai da ke sama, ya yiwu a sami wani ya Ƙaru da abin ta hanyar fa’idantuwa.

6.0 Kammalawa


Yin la’akari da muhimmancin da salon luguden nassi a ickin rubutattun waƘoƘin Hausa ke ďauke da shi ya sanya aka duƘufa a wajen nazarin WaƘar Allah ta Maharazu Barmu Kwasare domin a fito da shi. An dubi ma’anarsa (luguden nassi) da nassi shi kansa. Haka kuma takardar ta zo da bayanin ko wane ne Maharazu, keƂance daga bakinsa cikin wasu baitocin waƘoƘinsa. Haka kuma akwai bayanan da aka samo daga waďanda suka san shi. har yanzu takardar na Ƙunshe da nau’o’in luguden nassi manya guda uku fassara nassi da ishara zuwa ga nassi da kuma jawo nassi kai tsaye, tare da bayanin kowane da misalai gwargwado ta yadda za a nazarci abin cikin sauƘa ba tare da samun ruďewa ba. hasali ma, za a tarar mafi yawan murubuta waƘoƘin da ke amfnai da salon sarrafa nassi cikin waƘoƘinsu almajirai ne. wanda ba haka ba kuma sai dai ya rubuta waƘarsa ba tare da ya taƂo assi ba balle ya yi lugudensa a cikin waƘarsa.

Karanta wani

https://www.amsoshi.com/2017/07/18/isa-rasco-dangoma-ayyukansa-duniyar-adabin-hausa/

Manazarta


Ainu, H. (2006), “Rubutattun WaƘoƘin Addu’a na Hausa”: Nazarin Jigogi da Salonsu”. Kundin digiri na Uku da aka gabatar a sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Birnin Tudu, S.Y. (2002), Jigo da Salon Rubutattun WaƘoƘin Furu’a na Ƙarni na Ashirin”. Kundin digiri na uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Birniwa, H.A. (1987), “Conservatism And Discent”. A Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Ca 1946-1988. Kudnin digiri na uku, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Birniwa, H.A. (2003), “Tasirin Matanin AlƘur’ani da Hadisi Cikin Trubutattun WaƘoƘin Ashirin da biyu na Marubuta goma sha huďu masu tsokaci daga ko dai Ayoyin AlƘur’ani ko kuma Hadisai.
Birniwa, H.A. (2002), “Salon Riwayar Hadisi a cikin Imfiraji na Dr. Aliyu Namangi, Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Amin M.L. (2001), ‘WaƘoƘin Jihadi Goshin Ƙarni Na 21’. Mujallar Hausa Studies Vol. II No 2.

Birniwa H.A. (1981), ‘The Infiraji of Aliyu Namangi’ Kundin digiri na biyu (SOAS), University of London.

Birniwa H.A. ( ), ‘Tasirin Matanin AlƘurani Da Hadisi Cikin Rubutattun WaƘoƘi Ashirin Da Biyu Na Marubuta Goma Sha Huďu, Masu Tsokaci Daga Ko Dai Ayoyin AlƘur’ani Ko kuwa Hadisai’.

Bugaje H.M (2010), ‘Wa’azi A Rubutattun WaƘoƘin Mata Na Ƙarni Na Ishirin’. Kundin Digirin MA Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Bunza A.M (2009), Narambaďa, Ibrash Islamic Publications center, Lagos.

Ɗangambo A. (1980), ‘Hausa Wa’azi Verse From Ca 1800-1970. a Critical Study of Form, Content, Language And Style’ Ph D Thesis, S.O.A.S, University of London.

Ɗangambo, A (1981), Ɗaurayar Gadon Feďe WaƘa.

Funtua, A.I. (30th June 2003 – 4th July), ‘The Contribution Of Abdullahi B. Fudi To The Development OF Hausa Verse. A Study Of Their Form, Theme And Stgle’. Being A Paper Presented At A National Conderence, Organised By School Of Arts And Social Sciences Federal College OF Education, Katsina.

Galadanci, M.K.M (1975), ‘The Poetic Marriage Between Arabic And Hausa’, MaƘalar da aka gabatar a cikin mujallar Harsunan Nijeriya V 1-16 CNHN Jami’ar Bayero, Kano.

Gummi, A.M. (Babu Shekarar Bugawa), AlƘur’ani Mai Girma Da Kuma Tarjamar Ma’anoninsa Zuwa Ga Harshen Hausa Wurin Da Aka Tanada Musamman Don Buga AlƘur’ani Mai Girma, Na Mai Kula Da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Fahad, Madina.

Hiskett M. (1969), ‘Hausa Islamic Verse: Its Sources And Development Prior To 1920’, Ph D SOAS. University Of London.

Hiskett M. (1975), A History OF Hausa Islamic Verse, University Of London SOAS. Malet Street,London WCIE 7HP.

Ibrahim A. (2005), ‘WaƘoƘin Kungiyoyin Mawallafa Bege Da Gargaďi Ta Birnin Sakkwato’.Kundin Digirin farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Jami’ar Bayero Kano (2007), Ƙamusun Hausa, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, B.U.K.

Ƙaura H.I (1994), ‘Ƙawancen Salo A Tsakanin Rubutattun WaƘoƘi’
. Kundin Digirin farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Maigandi A. (2009), ‘Sharhin WaƘoƘin Da Aka Rubuta A Kan Jigon Addini Da Muhimmancinsu’. Kundin digirin farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Malumfashi, A.I. (1983), ‘Wa’azi A Rubutattun WaƘoƘin Ƙarni na Ashirin’. MaƘalar da aka gabatar a taron kara wa juna sani da Hukumar Fasaha da Al’adun Gargajiya ta Jihar Sakkwato ta shirya a ƘarƘashin Ƙungiyar Manazarta WaƘoƘin Hausa.

Muhtar I. (1984), ‘Nahawun WaƘa: Yanaye-yanayensa Da Sigoginsa Cikin Rubutattun WaƘoƘin Hausa’. Kundin MA Jami’ar Bayero, Kano.

Omar, S. (1983), ‘Style And Theme in the Poems of Mu’azu Haďeja’. Kundin digiri na biyu, SOAS University of London.

Sa’id B. (2002), ‘Rubutattun WaƘoƘin Hausa na Karni Na IShirin A Sakkwato Da Kebbi Da Zamfara’ Kundin Digiri na uku, Sas
hen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Beyero. Kano.

SarƂi S.A (2007), Nazarin WaƘen Hausa Samarid Publishers A Division Of Samarid Ventures LTD Plot 326, Sallari, Babbangiji Kano, Nigeria.

Usman, B.B. (2008), ‘Hikimar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr.) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000) da WaƘoƘinsa’. Kundin Digiri na uku, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Usman B.B (1997), ‘Poetry As A Source Of Historical Records: Umaru. Wazarin Gwandu Poem Of Shago Famine’ Takardar Da Aka gabatar A Taron Na 41 Da 42 Na Congress Of The Historical Society Of Nigeria A Jami’ar Maiduguri, Daga 27 Zuwa 30 Ga Satumba.

Yahya A.B (1982), Jigon Nazarin WaƘa, FISBAS Media Service, Kaduna.

Yahaya A.B. (1995), ‘Kwatancen Jigo Tsakanin WaƘoƘin Sarauta Na Baka Da Rubutatun Cikin Harsunan Nijeriya’, 17.34-56. CNHN Jami’ar Bayero, Kano.

Yahya A.B (2001), ‘Dangantakar waƘa Da Tarbiyar ‘Ya’yan Hausawa’ Cikin Harsunan Nijeriya XIX” 94-108, CNHN Jami’ar Bayero, Kano.

Yahya A.B. (2001), Salo Asirin WaƘa, FISBAS Media Services, Kaduna.

Yahya A.B. (1983), ‘A Critical Anthology Of The verse Of Alhaji Bello Giďaďawa’ Kundin digiri na biyu, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Yahya A.B. (1989), ‘The Verse Category of Madahu With Special Reference To Theme, Style And Background Of Islamic Source And Belief’ Kundin digiri na uku, U.D.U. Sokoto.

Yahya A.B.( ), ‘Rubutattun WaƘoƘin Nasiha: Wani Ɓangare Ko Kuma Sauyin Salo A Cikin Rubutattun WaƘoƘin Hausa Na Wa’azi’ Cikin Algaita, Jami’ar Bayero, Kano.

Yahaya I.Y (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce A Cikin Hausa, NNPC Zaria.

Zurmi A.D (2006), ‘Tsoratarwa A Cikin WaƘoƘin Wa’azi Na Nana Asma’u ‘Yar Shehu, Usmanu Danfodiyo’ kundin digirin farko, U.D.U. Sokoto.

Zungur A.M.S (1976, 77,81, 2008), WaƘoƘin Sa’adu Zungur NNPC, Zaria.