Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ke Yin Amali Ko Cikin Raƙumi: Nazari Da Sharhin Jigo Da Salon Waƙar Ɗanƙwairo Biu Ta Dokta Bukar Usman Biu

DAGA

DANO BALARABE BUNZA
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO.
Email: danobunza@yahoo.com
Phone number: 07035141980

www.amsoshi.com

Tsakure


Waƙoƙin bakan Hausa na ɗauke da turaku daban-daban, wasu na ɗauke da yabo a inda ake samun wasu ƙumshe da habaici da zambo da ire-irensu da dama. Wannan takarda ta ƙunshi nazari tare da sharhin waƙar Ɗanƙwairon Biu a kan jigo da salo wadda ya yi wa Doctor Bukar Usman Biu. An tattauna abubuwa masu dama da suka haɗa da maanar kalmar amali da kirarin amali. Abin da ya biyo baya shi ne, an nazarci turakun da ke cikin waƙar da suka shafi yabo da ilimi da halayen kirki irin mutunci da riƙon amana da taimakon jama’a da kuma kyauta. Biye da wannan kuma shi ne nazarin salailan da suka fito cikin wannan waƙa da aka yi nazari da suka haɗa da salon kamance. An sami kamancen fifiko da salon kinaya da kuma na kambamawa. A ƙarshe kuma, an rufe takardar da kammalawa.

1.0 GABATARWA


Masana da manazarta adabin Hausa musamman na fannin rubuttun waƙoƙi da na baka sun daɗe suna bayar da gudummuwa ta hanyar nazarin waƙoƙi daban-daban. Sun sha gudanar da nazarce nazarce, kan jigo da salo da kuma zubi da tsarin waƙoƙin Hausa da marubuta suka rubuta da kuma waɗanda makaɗa suka rera. Waɗansu kuma kan sami wasu abubuwan da waɗannan su yi nazarin su Maƙasudin nazarin kowace waƙa shi ne fitowa da abin da ake buƙata a wannan ɓangare. Nazarin waƙa ba karamin aiki ba ne saboda manazarta na matuƙar burge makaɗa da marubuta kam ganin yadda suka tona asirin abubuwan da suke faɗa da ba su tsammanin a fahimta, idan aka warware zare da abawa, sai mamakin yin hakan ya kama su tare da sanya su a cikin gulbin tunanin yadda aka yi manazartan suka gano haka ba tare da sun tambaya an gaya musu ba. Abin da ya kawo wannan shi ne, baiwar da Allah ya yi wa al’umma mai yawa ce, kuma kowa da irin baiwar da aka yi masa. wasu masana an hore musu baiwar nazarin rubuttun waƙoƙi, wasu kuma an azurta su da baiwar nazarin na baka. kamar yadda Bahaushe ya ce, “Buƙatar dara a kasa. Ke nan, kowane fanni na da ƙwararrin sa. A kan haka ne aka sami ɗaliban waɗannan masana suna koyi da abin da aka koyar da su a ɓangarorin da aka ambata a sama, suna rawa da bazar malamansu. Wannan ne ya sanya da aka ƙyallaro waƙar da Ɗankwararor Biu ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu, sai aka aza ta a sikelin nazari gwargwadon hali.

2.0 MA’ANAR KALMAR AMALI


Asali kalmar ‘amali” ba Bahaushiya ba ce, Balarabiyar kalma ce da ake kira ‘Amal; Da Bahaushe ya are ta sai ya yi mata ƙarin wasalin i ta koma Amali yadda zai ji daɗin faɗar ta. Kalmar amal na nufin aiki a cikin harshen Larabci . Su kuma Hausawa suka ɗauke ta suna amfani da ita a matsayin mai yin aiki. A Larabci kalmar amal na matsayin aiki (verb), a inda a Hausa take matsayin maaikaci, wato subject da Turanci. Idan aka ce amali a Hausa, ana nufin raƙumin da yake gwarzo ko mai juriyar aiki fiye da sauran raƙuma. Wannan ne dalilin da ya sa aka ba gwarzon raƙumi sunan amali. Sai dai waɗansu kan kira shi amale, wanda yake duk abu ɗaya ake nufi.
Akwai wasu ma’anoni biyu da aka kalato daga wasu ƙamusan Hausa da suka ba da ma\anar kalmar amali/amale kamar haka: ƙamusun Bayero University Kano ya tayar da maanar kalmar haka:- Amaale: Su, nj. Mc-amaliya. Jam-amaalai riƙaƙƙen mahaukacin raƙumi, kirari, wani kaya sai amale, wace Ayagi mai ɗan doro? (pg:15).
A ƙamusun Bargesry kuwa, ga abin da aka ce: A.M Fem. Amaliya, plural amalai of ahoda; 1. (a) A full.grown Camel (-amali) (b) Salutation to a Madaki 2.Full-grown donkey 3. Largest of the three trings of instrument called molo .
A ma’anar ƙamasun Jamiar Bayero, Kano amale har ya kai a kira shi mahaukaci domin ƙosawarsa. Idan aka dubi maanar ƙamusu na biyu kuma, za a tarar duk abu ɗaya ake nufi da maanar Kamansun farko da aka ambata. (A Full-grown camel).

2.1 KIRARIN AMALE/AMALI


Ba amale kaɗai ke da kirarin a cikin dabbobin gida ba. Akwai dabbobin da ke da kirarin da ake yi musu na gida da na daji. Jaki da kare da sa da rago da akuya na da kirarin da ake yi musu kasancewar su dabobin gida. Idan aka yi zancen kirari, dabbobin daji ma ba a bar su a baya ba.
Ba da nisa ba, akwai kirarin da ke cikin kamusun Hausa na Jami’ar Bayero a daidai shafi na 15 inda aka ce kirarin amale shi ne:-
‘Wani kaya sai amale, wace Ayagi mai ɗan doro?”.
Bayan wannan kuma, akwai wani kirarin da aka yi wa amale inda ake cewa:-
Amale ka fi gayya aiki:- Ma’anar da wannan kirari ke nunawa ita ce, aikin da amalen raƙumi ke yi ya fi wanda taron mutane za su yi. Abin da yake gaskiya cikin wannan magana shi ne, amalen raƙumi na iya fara aiki tun fitowar rana har zuwa faɗuwarta ba tare da yin raki ko nuna kasawa ba. Ita kuma gayya, ba yadda za a yi a fara ta, ba a kare ba ko a daina aiki ba har faɗuwar rana.
Akwai kirarin amali a cikin wata takardar Aminu 2012, da yake kirarin amale ya shafi madugun da ke tare da shi, shi ma na madugu ya shafi amale. Ga kirare-kiraren kamar haka: -
“Wada nika dubin masu biyar raƙumma,
Kamar kwatancin soja,
Don kullum cikin shiri suka kwana,
Makiyayin amali ba shi da kwana,
Makiyayin amali ba shi da hutu,
Makiyayin amali ba shi tsoron yaƙi,
Ko da bindigogi aka yi,
Maza ana son sayen amali,
Wai mutuwa aka tsoro,
Na tambaye ku shin dai jama’a,
Kwam mace cikin duniyag ga,
Halama raƙumi yac ci shi?
Ai mutuwa ko kan gado tana iske mutum”.

Mai yin wannan kirari shi ne Illon Geza, sananne a fagen yi wa maduggai kirari tare da rakumman da suke tu’ammali da su. Ga wani kirari kamar haka:-
“Jaji so nikai in ji amali shina hidda ƙoƙiya shina ɗibga cida, ya ɗora hiƙar hauru, ya ɗora hidda kunfan baki.
Rannan ko ka ci magani ɗari kana katse mai,
Maza kowas sai amali ya sai mutuwa,
Matar mai amali ba ta nesa ga wanka,
Maganin amali Allag gyara,
Allah shi kiyaye ‘yan maza ga bakin mugu”.

Haka kuma kirare-kiraren amali bai tsaya a nan ba kurum. Akwai su da dama sai dai a kawo kaɗan don kar misalan su yi yawa.
Ga wani kirari da aka yi wa amali:

‘Garagiji fataken Allah,
Masu gardama suna maikaiwa,
Ku ka sa ma’auniya ta yi guɗa,
Kwanon tsaba ko shina sule shi komo ahu,
Maza majaya amali ko da kwanan hwarin’.

‘Masu biyar raƙumma,
A ba da mugun sassaƙe ida turewa,
Kyawon mahaukaci ya ida turewa,
In dai ɗaki na ruwa, awaki ka hwaɗi,
Ko an rufe ɗaki da mahaukaci ana buɗewa’.
‘Ina masu cewa,
Rikon amali ba duk magani ba ne, sabo ne?
Ai da rakumi da damisa da kura da kada,
kowa kag ga sun bari tsarin Allah na’.

3.0 NAZARI DA SHARHIN JICO DA SALON WAƙAR ƊANƙWAIRON BIU TA DOKTA BUKAR USMAN BIU.


Makaɗa da mawaƙan Hausa na matuƙar ƙoƙari domin ganin sun yabi waɗanda suke buƙatar yi wa hakanan ta fuskar asali da kyauta da iya gudanar da mulki da ilmin da Allah ya azurta wani da shi da abubuwan da suka yi kama da haka. Alal haƙiƙa an sami makaɗi mai suna Umar Idris (Danƙwairon Biu) ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu waƙa tare da yaba shi ta fuskoki da dama. Za a dubi fuskokin da makaɗin ya yabi wannan bawan Allah a cikin nazarin wannan waƙa tare da yin sharhin abubuwan da aka gabatar. Da farko, za a ɗauki jigon wannan waƙar ya zama soma-taɓi kafin abubuwan da za su biyo a baya. Ga yadda nazarin waƙar zai kasance:-

3.1 TURKEN WAƙAR:


Hausawa na cewa, “Nashin ƙasa, babu kure:. Masana sun bayyana cewa duk waƙar da aka yi, rubutacciya ce ko ta baka, ko ana rasa komi a cikinta dole ne a same ta da muhimmin saƙon da aka gina ta a kansa. Ana kiran saƙon jigo a rubuttun waƙoƙin Hausa, a inda sunan yake turke a waƙoƙin baka na makaɗan gargajiya. Waƙar da ake nazari a nan na ɗauke da babban turken yabo. Sai kuma saƙon ya kasu daban-daban kamar yadda nazarin zai nuna. Ga alada waƙar baka na tare da amshi wanda ita ma wannan waƙar da Ɗanƙwairon Biu ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu tana tare da wannan amshi daga bakin yaran makaɗin.

3.1.1 TURKEN YABO A CIKIN WAƙAR DR. BUKAR USMAN BIU


Soyayya ko kuma so a taƙaice ke sanya makaɗi ya yabi wani ko wasu a cikin waƙarsa. Akan yi yabon da ba na gaskiya ba bale wanda aka taki dahir? Hausawa sun ce So hana ganin laifi Duk mai son ka da wanda kake so ba ku laifi ga junanku. Umar Idris (Danƙwairon Biu) ya nuna soyayya matuƙa ga Dr. Bukar Usman a cikin waƙarsa, da yake ɗiyan waƙoƙin da za a kawo ke tabbatar da haka ba faɗa kawai ba. Idan aka dubi amshin waƙar da makaɗin ya ba yaransa, ya isa a gano cewa saƙon waƙar yabo ne. Ga amshin waƙar kamar haka:

Dokta Bukar Usman Biu Jarumi,
Malaminmu kuma babanmu ne,
Mazan ƙwarai, ku bar kaura da shi.
Da za a dubi kalmomin jarumi da malami da baba da mazan ƙwarai da aka ja wa layi a ƙarkashi, wannan kaɗai ya isa a fahimci mai adawar mutum ko wanda ke kushe shi ba zai kira shi da su ba sai dai ya kira shi da wasun waɗannan kalmomi domin abin ya koma suka. Kalmomin suka da ke waƙiltar na yabon da aka ja wa layi a sama su ne, raggo da jahili tare da faɗar babu haɗi tsakanin kifi da kaska bale ma a kawo alaƙar haihuwa da za a kira sunan baba. A maimakon mazan ƙwarai kuma akan iya amfani da mutumen banza duk dai domin nuna akasin yabo, wato zagi. Wannan amshi da ke sama yabo ne na ƙoli a idon wanda aka yi wa shi da manazarta su kansu. Saƙon wannan waƙa na ƙoli shi ne yabo. Shi kuma yabo masana sun faɗi cewa ya kasu zuwa gidaje da dama, kamar yadda za a gani cikin bayanan da ke tafe kamar haka:

3.1.2 ILIMI SUTURAR ALLAH


Ilimi na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ɗaga darajar mutum a san shi kuma a ji shi ko’ina. Dokta Bukar Usman Biu na ɗaya daga cikin waɗanda Allah Ya ɗaga darajarsu a fannin ilimi. Za a zo da ɗiyan waƙan da suka tabbatar da haka nan gaba kaɗan. Abu na farko da ke tabbatar da Bukar Usman ya sami ɗaukaka a fannin ilimi shi ne matsayin (Dr.) da yake karɓawa a halin yanzu. Ba mamaki a kira shi shehin malami nan gaba domin rabo daga Allah ne.
Dr. Bukar Usman Biu ba kanwar lasa ba ne idan aka yi zancen ilimi, kamar yadda wasu ɗiyan waƙa suka tabbatar. Bayan wannan ma mutane sun tabbatar da haka domin abin a fili yake ba a fake ba, abin da Hausawa ke kira filin wuri dabon ɗan kama. A taƙaice Dr. Bukar Usman ya rubuta littattafai sama da ashirin. Daga cikin waɗanda suka bayyana akwai, Taskar Tatsuniyoyi da na Turanci mai suna My Literary Journey da sauransu. Ga waɗansu ɗiyan waƙa da ke tabbatar da Dr. Bukar Usman mailmanci ne kamar haka:
Gabar da yamma dama da hauni,
Nijeriya, ƙasashen Turai,
Sun san halinka ka san nasu,
Dokta Bukar Usman Biu,
Sun san ka ne dalilin ilimi.

Yau ga Ɗanƙwairon Biu,
Umar Idrisa a zahiri,
Dokta Bukar Usman Biu,
Umar ni na san da kai,
A zahiri fa kai ba ka san ni ba,
Ya zan dole na san da kai,
Tunda kai ka rubuta a san da kai.

Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babanmu ne,
Dokta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani.

Ina marubutan zamani?
Ku zo mu taru don ga malami,
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babanmu ne,

Rimi mai faɗin gari,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka zama teku a fannin ilimi,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka riga su ka ce Allah,
Mai ilimin da babu iyaka,

Turawan duka duniya,
Su jinjina maka dole ne,
Giwa ba ta gudu don harbi,
Ka san Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu ne fa ta ko’ina,

Shi Dokta Bukar Usman Biu,
Yana aikinsa da ilimi,
Kuma yana aikinsa da hankali,
Wanda ya wuce a yi da lokaci.

Idan aka kula da ɗiyan waƙar da ke sama za a tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Bukar Usman suturar ilimi. A ɗan waƙa na farko da aka kawo, mawaƙin ya tabbatar wa jamaa da cewa, duk kusuruwowi huɗu na duniya (Gabas, Yamma, Kudu da Arewa) da gida Nijeriya da kuma ƙasashen waje tattare da sanin halinsa da suka yi da kuma nasu da ya sani, ba abin da ya haddasa hakan face ilimin da yake da shi. A hankalin tuwo ma, me ya dami Turawa da baƙar fata in ba shaanin ilimi ba? Ta yaya za su san wani har a ce hulɗa ta shiga tsakani in ba saboda ɗaukakar ilimi ba? Sanin muhimmancin ilimi ne ya sanya Allah Ya yi umurni da a neme shi, kuma Manzon Allah ya tabbatar da hakan a inda ya ce “Neman ilimi farilla ne ko da ya kai birnin Sin”. Daga cikin hulɗar da aka samu tsakanin Bukar Usman da mutanen ƙasashen waje akwai ta ilimi. Ke nan, ilimi na cikin abubuwan da ke ɗaukaka darajar mutum har a ji shi kuma a san shi nesa ba kusa ba, kamar yadda Allah Ya yi wa Bukar Usman sutura da shi.
A ɗan waƙa na biyu da aka gabatar, makaɗin na faɗar cewa, shi ya san Dokta Bukar Usman, sai dai Bukar bai san shi ba. Ya ƙara da cewa ba dole ne Bukar ya san shi ba sai dai shi ya san shi ne a tilas. Dalilinsa na faɗar haka kuwa shi ne cewar da ya yi a ƙarshen ɗan waƙar,
Tunda kai ka rubuta a san da kai.
Sanin kowa ne jahili ba ya rubutawa bale ya karanta. Sha’anin rubutu da karatu na mai ilimi ne don haka, Allah Ya tufatar da Bukar Usman da wannan tufa na ilimi har aka ji shi kuwa aka san shi ciki da wajen Nijeriya.
Ɗan waƙar da ke biye ma ya nuna cewa bayan ilimin addini da Bukar ya tashi da shi an ƙara ɗaukaka darajarsa ta ba shi ilimin zamani. Abin da ke ƙara tabbatar da wannan shi ne rubuce-rubucen da ya yi. Ilimin rubutu babbar ɗaukaka ce ga ɗan Adam. Tabbacin haka kuwa shi ne, akwai masu buƙatar su iya karatu da rubutu amma, kuma ba su sami hakan ba. Ashe duk wanda aka yi wa baiwar iya karatu da rubutu, an ɗaukaka darajarsa ta wannan fanni. A kan haka ba abin da ya rage wa Dokta Bukar Usman sai ƙara godiya ga Allah kan ni’imomin da aka yi masa. maganar na cikin ɗan waƙar wurin da aka ce:
Dokta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani,
Kuma riƙon amana naka ne.

A ɗan waƙan da ke biye da na sama kuma, ya ƙara fitowa da darajar ilimi a fili inda makaɗin ya nuna cewa:
Ku zo mu taru don ga malami,
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babanmu ne.

A fahimtata wannan ɗan waƙa na iya fassara taron da aka yi don girmama Dokta Bukar Usman sanadiyar littafin da ya rubuta na Taskar Tatsuniyoyi. Haka kuma an sami marubuta da yawa da suka rubuta maƙalu daban-daban kuma duk domin karrama Bukar Usman. An gudanar da wannan taro a mazaunin Jamiar Bayero ta Kano na dindindin. Haka kuma, duk wanda ya jiɓinci mai ilimi, zai amfana da iliminsa kamar yadda ɗimbin jamaa suka amfana da Bukar a cikin rubuce-rubucensa na ilimi.
A ƙarshen kuma, akwai ɗan waƙan da makaɗin ya yabi Bukar Usman inda ya nuna taska ne na ilimi da kowa ke amfana da shi dare da rana. Wannan ɗan waƙar shi ne kamar haka:

Rimi mai faɗin gari,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka zama teku a fannin ilimi,
A gaishe ka na Dokta Shema,
Dokta Shema na fannin magani.

Idan aka yi zancen ilimi Dokta Bukar Usman rumbu ne sha ɗiba. Za a fahimci haka tare da aminta idan aka yi la’akari da taron karramawar da aka yi masa a Kano. Da wuyar gaske ake samun wanda ya rubuta takarda a wannan taro da bai sanya littafin Taskar Tatsuniyoyi a manazartarsa ba. Ke nan kowa ya amfana da ilimin Dokta Bukar . Wannan ne dalilin makaɗin a kan cewa Bukar Usman Biu ya zama teku a fannin ilimi.

3.1.3 NAGARI NA KOWA, MUGU SAI UWAR DA TA HAIFE SHI


Ba shakka Hausawa sun faɗi gaskiya a kan faɗar wannan magana. Duk mutumin da ke da kirki za a ga koyaushe yana tare da jama’a. Shi kuma maras kirki koyaushe neman jama’a yake yi suna nisantar sa. Dokta Bukar Usman Biu mutum ne mai son jama’a tare da taimaka musu iya gwargwado. A halin yanzu shi kansa bai san iya jama’an da yake hulɗa da su ba kuma ba wanda zai gaya ma adadinsu. A ƙarƙashin wannan za a dubi abubuwan da suka haɗa da:

3.1.3.1 Halayen Kirki

Bukar Usman Biu mutum ne mai kirki matuƙa. An ga haka tsakaninsa da mutane daban-daban na gida da waje. Halayen kirkin da Bukar Usman ya mallaka masu yawa ne. Daga cikin halayen kirkin da makaɗin ya kawo na Dr. Bukar Usman akwai, mutunci da riƙon amana da taimakon alumma da kyauta da aiki da ilimi kuma ga hankali da sauran kyawawan halayen da wannan takarda ba za ta iya ƙunsa ba, domin ba dukkan halayensa na kirki makaɗin ya sani ba. Ya dai faɗi waɗanda suka sami shiga cikin waƙar domin ba a zube komi a lokaci ɗaya. Ga yadda makaɗin ya kawo halayen Bukar Usman a cikin ɗiyan waƙar:

3.1.3.2 MUTUNCI

A lokacin da Ɗanƙwairon Biu ke lissafo halayen Dr. Bukar Usman Biu na ƙwarai ga abin da ya ce dangane da mutunci:
Dokta Bukar Usman Biu,
Malaminmu kuma babbanmu ne,
Dokta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani.

Dangane da wannan hali na mutunci ana ji daga masu hulɗa da shi cewa, mutum ne mai karimci ƙwarai da gaske. Yana girmama jamaa yadda ya kamata, har ma idan ba ka san shi ba, aka nuna maka shi, za ka ji mamakin yadda yake karrama mutane su ma suna girmama shi.

3.1.3.3 RI
ƙON AMANA

Hausawa sun ce; “Riƙon amana sai ɗa. A nan, ba kowane ɗa ne ake nufi ba. An san duk wanda aka haifa namiji, ɗa ne. Haka kuma ba irin kasancewa ɗa kamar shayi ɗan gidan Labbo ba wanda Kassu Zurmi ya kawo a cikin waƙarsa. Abin da ake nufi a nan shi ne ɗan da ya kasance son kowa, ƙin wanda ya rasa. Idan aka ce son kowa ƙin wanda ya rasa, ana nufin mutumin da ke da alheri a cikin rayuwarsa zuwa ga mutane tare da nisantar su da sharri komin ƙanƙantar sa. Dokta Bukar Usman Biu ya kasance son kowa ƙin wanda ya rasa musamman idan aka yi la’akari da hulɗar da ke tsakaninsa da jama’a. Za a tabbatar da haka idan aka yi la’akari da abin da makaɗinsa ya faɗa a wani ɗan waƙarsa. Ba shakka duk wanda aka samu da riƙon amana ne halinsa, to tabbas ya zama ɗa irin wanda Hausawa ke nufi a wannan hauji. Ga abin da Ɗanƙwairon Biu ya ce:
Dakta mutunci naka ne,
Kuma kana da ilimin zamani,
Kuma riƙon amana naka ne,
Hadari kashe kaifin rana,
Birni da ƙauye ba ka da zallumi.

Layin da aka ja wa layi ƙarƙashinsa ne abin yin laakari dangane da riƙon amanar da ake bayani na Dokta Bukar Usman Biu. A nan za a iya cewa, Bukar Usman ya san amana, ya san muhimmancinta, ya san munin rashin yin ta, shi ya sa ya zaɓi ya kasance mai riƙon ta tsakaninsa da Allah da kuma kiyaye wadda ke tsakaninsa da jamaa. A nan, makaɗin na sanar da jamaa cewa Dokta Bukar Usman dattijo ne a ɓangaren amana, riƙon ta da kuma bayar da ita, musamman waɗanda ba su san shi ba.

3.1.3.4 TAIMAKON JAMA’A

Taimakon al’umma na cikin kyawawan halayen Dokta Bukar Usman Biu da aka shede shi da su tun kafin makaɗin ya faɗa. Sai dai ba abu ne da za a fito a faɗa a rubuce ba kurum, har sai wani sanadi ya faru irin wannan waƙar da aka yi masa, sai kuwa idan an sami yin hira da wani mutum a cikin kafafen yaɗa labarai kan halayensa. Da yake abin da waƙar Ɗanƙwairon Biu ta ƙunsa aka magana ga abin da ya sami faɗa dangane da taimakon alumma:
Dokta Bukar Usman Biu,
Kana da taimako fa ta ko’ina,
A ƙasar nan duk an san da kai,
Baba da ku aka damawa gida,
Kuma da ku aka damawa waje.

Ba shakka ga maganar da aka faɗa ta cewa Bukar Usman na da halin taimaka wa al’umma, domin ga shi nan a fili makaɗin ya kawo a cikin ɗan waƙa na sama. A layuka biyu da aka ja wa layi makaɗin ya tabbatar da Dokta Bukar Usman Biu na da taimakon jamaa kuma ta koina. Kalmar koina da makaɗin ya yi amfani da ita na nuna duk inda mutum ke tunanin taimakon da yake yi ya kai, to ya hurce nan. Saboda yawan taimakon da Bukar ke yi wa jamaa ya sa makaɗin ya ƙara fayyace ma jamaa da cewa, an san da haka a ƙasa baki ɗaya a cikin layi na biyu da aka ja wa layi. Halin da ake ciki ni ma ina matsayin sheda a kan wannan maganar cewa yana da taimato ta ko’ina. A taron da aka yi a ƙasar Nijar na karrama Marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju a ranar 19th 21st February, 2014 a garin Niamey a ɗakin taro na Salle Sani Baƙo, ministere des Affaires etrangeres Niamey, ya taimaka ya biya wa duk mai gabatar da takarda kuɗin rajista naira dubi biyar. Saboda wannan taimako da ya yi ya sa wani ya nemi a gwada wa jamaa Dokta Bukar Usman Biu, a inda aka nemi ya tashi tsaye domin kowa ya gan shi, kuma haka aka yi. Ba wannan taro kaɗai ba, a taron da aka yi na Nigerian Folklore Society a Jami’ar Bayero Kano, taro na 11 da aka yi a ranar 2-4 ga Afrilu, 2014, Bukar Usman Biu ya ba da kyautar littafinsa mai suna ‘Taskar Tatsuniyoyi” ga kowane mahalarcin taro day a gabatar da takarda. Ba da kyautar littafin taimako ne babba ga kowane mutum domin na tabbatar ba ni kaɗai na ji daɗin wannan taimako da ya yi ba. Idan aka yi la’akari da waɗannan abubuwa da aka kawo a sama zancen taimakon jama’a ba sai an nanata ba da Dokta Bukar Usman Biu ke yi. Allah Ya saka da alheri.

3.1.3.5 KYAUTA

Yin kyauta na daga cikin halayen kirki da aka yi bayani, har a addinin Musulunci. Abin da duk ya dace a faɗa dangane da halin Bukar Usman da ya shafi kyauta an faɗa a sama, sai dai a ƙara. Ba dogon bayani za a yi ba na abin da ya shafi kyautar da Dr. Bukar ke yi. Akwai daga cikin wani ɗan waƙa da makaɗin ke cewa:
Hadari kashe kaifin rana,
Birni da ƙauye ba ka da zallumi,
Balbela ki bi saniya,
In kin bi kare me za ki ci?

Hausawa sun ce, “Nuni ya ishi mai hankali”. Ita dai balbela sanannar tsuntsuwa ce da ke kiwo cikin shanu domin samun abinci. Haka kuma ba ta da wata alaƙa da kare bale ta bi shi don neman abinci. Idan ma ta bi shi, wahalar banza ce take yi ba samu za ta yi ba. Hasali ma idan ba ta ci saa ba, ita za ta zama abinci ga wani kare ba maganar ta samu abincin ba. A taƙaice wannan nuni ne na cewa, Bukar Usman mai kyauta ne ga na bayansa da na tare da shi,wanda ya sani da ma wanda bai sani ba.Jamaa na amfana da wannan bawan Allah matuƙa, kamar yadda balbela ke kama fari da ƙwari a lokacin da take tare da shanu a daji wurin kiwo.

4.0 SALO A CIKIN WAƙAR BUKAR USMAN BIU TA UMAR IDRIS (ƊANƙWAIRON BIU)


Masana sun bayyana ma’anar salo a cikin rubuce-rubucensu da suka yi. Za a kawo ma’anar da Abdullahi Bayero Yahya ya bayar kamar haka:
“Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar.

Daga bayanin ma’anar da ke sama za a fahinci salo hanya ce ko dabara ko wayo da marubuci ke bi domin isar da saƙon da ke cikin rubutunsa, ko maganarsa ko waƙarsa ta baka. Akwai wasu salailai da suka fito a cikin waƙar Dokta Bukar Usman Biu wadda Umar Idris ya yi masa kamar haka:

4.1 SALON KAMANCE


Salon kamance ɓangare ne na babban salon siffantawa. Salo ne wanda ke bayyana sifar wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu daban tare da amfani da kalmomin da za mu ba suna mizani. Salon kamance zai siffanta mutum da cewa ya yi kama da wani abu amma ba shi ne abin ba. Salon kamance kamar wada muka ambata yakan yi amfani da kalmomin da muka kira mizani. Kalmomin kuwa sun kasu gida uku akwai na daidaito, akwai na fifiko sannan akwai na kasawa. Kalmomin mizani su ke yi mana jagora wajen gane salon kamance a cikin waƙa. Saboda haka bari mu kawo misalai na kowane rukunin mizani:
1. Mizanin daidaito: Awa, kamar, wa, i, ƙoƙa, ya, ce kake da kuma daidai da.
2. Mizanin fifiko: Wuce, zarce, fi, take, gota, furce, tsere, da kuma ɗara.
3. Mizanin kasawa: Kasa, gaza, wane da kuma kalmomin masu soke samuwa kamar bai..... ba.

4.1.1 KAMANCEN FIFIKO

Ɗanƙwairon Biu ya yi amfani da salon kamancen fifiko a cikin waƙar da ya yi wa Bukar Usman Biu. Ya yi amfani da wannan salo domin nuna irin ratar da ke tsakanin Bukar Usman a matsayinsa na malami da kuma waɗanda ke a matakin jahilai a inda ya ce:
Dokta Bukar Usman Biu,
Umar na zo domin in gai da kai,
Malami fa ka wuce jahili,
Wajen hali kana da tawakkali,
Allah Ya yi ma sutura,
Ga ƙarfi da arziki babban rabo.

A layi na uku da ke cikin ɗan waƙan da aka kawo a sama inda makaɗin ya gwama malami da jahili ta fuskar kamance, a inda kowa ya tabbatar da malami ya fi jahili amfani ga jamaa ta kowace fuska. A wannan wuri makaɗin ya kawo cewa akwai bambanci mai yawa tsakanin masani da wanda bai san komi ba. An tabbatar da cewa malami na a matsayin haske jahili kuma na a matsayin duhu kamar yadda aka kamanta tsakanin shiriya da ɓata. Wannan ya yi daidai da maganar masu tallar hajojinsu a kafafen yaɗa labarai inda suke gwama nasu kaya da na wasu inda suke cewa: “The difference is clear” domin nuna nasu kaya ya fi na saura, wato da gani ba tambaya. Irin wannan ne makaɗin ke nunawa, har aka sami wannan salon kamancen fifiko.

4.1.2 SALON KINAYA

Kamar yadda aka sami kamancen fifiko a cikin wannan waƙa, haka ma akwai na kinaya a ciki. Kinaya na nufin kiran abu, musamman mutum da sunan da ba shi ne nasa da aka san shi da shi ba, domin wannan suna ya bayar da maanarsa da kuma tunanin da wannan suna. Salo ne wanda ake yin amfani da kalma ko kalmomi domin tunanin da suke sa mutum ya yi game da maanoninsu ya nashe ko ya lulluɓe wani abu ko mutumin da aka danganta kalmomin gare shi. A kan wannan bayani ne aka fahimci akwai wannan salo a cikin waƙar Dokta Bukar Usman Biu wadda Ɗanƙwairon Biu ya yi masa. Za a ga hakan a cikin ɗiyan waƙar kamar haka:
Rimi mai faɗin gari,
Dokta Bukar Usman Biu,
Ka zama teku a fannin ilimi,
A gaishe ka na Doctor Shema,
Doctor Shema na fannin magani.

Ina Bukar Usman Biu?
Karo da kai maza suka shan wuya,
Gwanki sha bara na mai Umai,
Allahu Ya yi ma sutura,
Da ƙarfi da arziki babban rabo.

Ina kada hana wanka?
Dokta Bukar Usman Biu,
Malami a fannin Adabi,
Alfijir Bukar Usman Biu,
Ka fito gari ya waye,
Mujaddadi ina masaninmu ne?
Hadari kashe kaifin rana.

Duk kalmomin da aka ja wa layi ƙarƙashi kinaya ce aka yi zuwa ga Dokta Bukar Usman Biu. Haka kuma kowace kalma na ɗauke da wata maanar da makaɗin ke nufi. Akwai kalmar Rimi da Teku da Gwanki da Kada da Alfijir da kuma Mujaddadi da kuma hadari.
Rimi sunan gari ne da makaɗin ya kira Bukar Usman da shi saboda yawan garin. A nan yana nufin yadda garin Rimi ke da yawa haka ilimin Bukar Usman ya yawaita. Ya ƙara bayyana ilimin Bukar Usman da cewa ai Bukar Usman ya zama teku a fannin ilimi. Yadda ba a san iyakar teku ba haka ma ba a san iyakar ilimin Dr. Bukar ba. A wani ɗan waƙar kuma makaɗin ya kira Bukar Usman da sunan gwanki. Gwanki a nan dabba ne kuma sananne a cikin dawa. Ko a bayanin masana kaɗai aka tsaya na maanar kinaya, cewa kiran wani mutum da sunan da ba nasa ba, ya isa ya zama hujjar cewa kinaya ce.
A wurin da aka kira Bukar Usman kada kuwa, makaɗin na nufin yadda kada yake babba a ruwa haka Bukar yake a lamurran da suka shafi jama’a a matsayin babba wanda Allah Ya ɗaukaka sosai. Kalmar alfijir kuma a nan an yi amfani da ita domin a nuna duk wurin da Dr. Bukar yake yana tare da jama’a domin da safiya ta waye mutane fitowa suke yi domin hidimominsu na rana. Kalmar mujaddadi a nan na nufin mai ƙarfafa wani abu. A fahimtar manazarta Bukar Usman mujaddadi ne a fannin adabi kuma ba za a musanta haka ba. Haka ma kiran da ya yi wa Bukar Usman da sunan hadari a wani wuri. Ko ba komi wannan kirarin hadari ne da ake yi masa da cewa: “Hadari mai kashe hasken rana”. A nan makaɗin na nufin Dr. Bukar Usman Biu na da ficen day a kai idan yana cikin jama’a ya fi fice idan aka yi zancen halayen kirki da ƙwarjini ga jamaa.

4.1.3 SALON KAMBAMAWA
Masana sun ce, idan mawaƙi ya yi zuƙu cikin magana, wato ya ƙara mata gishiri, a taƙaice ya bayyana abu fiye da yadda yake a haƙiƙani, za mu ce wannan mawaƙi ya yi amfani da salon kambamawa. Akwai irin wannan salo a cikin waƙar da Ɗanƙwairon Biu ya yi wa Dokta Bukar Usman Biu a wurin da ya kawo kamar haka:
Dokta Bukar Usman Biu,
Kai ka riga su ka ce Allah,
Mai ilimin da babu iyaka,
Turawan duka duniya,
Su jinjina maka dole ne.
- - - -
- - - -
A sha’anin nazari da sharhin waƙa wannan ɗan waƙa da aka kawo duk layukan da aka ja wa layi kambamawa ce makaɗin ke yi wa Bukar Usman. Ga alama, idan abin a yi wa makaɗi gyara ne, ko Bukar Usman na iya faɗa wa makaɗin cewa ya yi ƙarin gishiri ga abin da ya faɗa. Duk da yake shi makaɗi ya dai sami buƙatarsa ta biya, wanda ana kyautata zaton ta ma biyan.

5.0 KAMMALAWA


Waƙa ce ƙololuwar tunanin ɗan Adam kuma a cikin ta ne mawaƙa ke ɓarje guminsu domin su yabi wanda suke raayi kuma su kushe abokan gwada tsawo da masu gidajensu ko su kansu. A cikin wannan takarda, makaɗa Umar Idris (Ɗanƙwairon Biu) ne ya yi yabo da gaisuwar ban girma ga maigidansa Dokta Bukar Usman Biu. Na ce maigidansa saboda a bakinsa na tsinta a wurin da yake cewa:
Dokta Bukar Usman Biu,
Baba ni kai ne fa gwanina,
Gwanin wani ba gwanina ba ne,
Amma nawa gwani kuma,
Shi ne Dokta Bukar Usman Biu,
Dokta ga Umar Ɗanƙwairo,
ƙwairon Biu na wannan zamani.

Umar Idris ya ɗaga Dokta Bukar Usman Biu da hannu biyu a sama ya nuna wa jama’a tare da bayyana ɗaukakar da Allah Ya yi masa a ɓangarorin rayuwa daban-daban. Ya yaba shi a fagen ilimi a inda ya kira shi malami kuma marubucin da ya yi fice a fannin Adabi. Haka ya bayyana halayensa na kirki masu yawa. Kai! Umar ya faɗi alkhairori masu yawa da Bukar Usman ke yi sai abin da mantuwa ta hana a faɗa. Da yake baƙin ciki ba baƙon uwar ɓarawo ba ne, an sami wasu salailai kaɗan a cikin waƙar kuma aka nazarce su, domin ba yadda za a yi waƙa ba tare da an tsinci wani salo a ciki ba. Idan ma aka rasa salo a cikin waƙa, to ba waƙa ba ce. Ai maganar da Hausawa suka yi ce cewa Gaskiyar biki jariri. Idan babu jariri, babu buki. Don haka idan babu salo an rasa waƙa.
Dokta Bukar Usman Biu jarumi ne kamar yadda Ɗanƙwairon Biu ya faɗa. A raayina na ɗalibin nazarin waƙa na ga ya fi dacewa Umar Idris ya mayar da laƙabinsa Ɗanƙwairon Dokta Bukar Usman Biu, mamakon Ɗanƙwairon Biu. Dalilina a nan shi ne, da wuyar gaske ya yi wa wani waƙar da ta kai ta Dokta Bukar Usman bale ma ta hurce ta. Shi kuma Dr. Ya riƙi makaɗinsa matsayin yaro kamar yadda ya riƙe shi maigida. Hausawa sun ce Soyayya ta fi kuɗi. Shi kuma Sani Sabulu na kanoma cewa ya yi ƙauna ba ta ganin wahala Sani. Wannan ya faru ne a inda yake nuna hulɗarsa da mutanen ƙauye. Haka kuma kowane birni da zama ƙauye ya fara. Kowa ke ganin tausayi ya kasance lokacin da ake tausan sa.

Karanta wannan



MANAZARTA


Alƙurani Mai girma da Hadisin Manzon Allah S.A.W. da suka yi bayani kan neman ilimi
Abba & Zulyadaini (2000), Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Gaskiya
Corporation Ltd, Zaria.
Aminu N. (2012), “Nazarin Kirarin Madugan Raƙuna na Ilon Gezo In
Dunɗaye Journal of Hausa Studies, Department of Nigerian Languages, UDU, Sokoto vol.1 No. 4 pg 154-174.
Bargery, G.P. (1933), A Hausa-English Dictionary and English-Hausa
Vocabulary, A.B.U. Press Ltd Zaria-Nigeria.
D. Muhammed (1990), Hausa Metalanguage (ƙamus na keɓaɓɓun
Kalmomi). Volume 1, University Press Limited, Ibadan.
Dangambo A. (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari) Amana
Publishers Ltd New Kano Road. P.O. Box 1265, Zaria, Kaduna-
Nigeria.
Gusau S.M. (1996), Makaɗa da Mawaƙan Hausa Benchmark Publishers
Limited, Kano-Nigeria.
Gusau S.M. (2008), Waƙoƙin Baka A ƙasar Hausa: Yanayi-Yanayensu da
Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited, Kano-Nigeria.
Gusau S.M. (2009), Diwanin Waƙoƙin Baka (Zaɓaɓɓun Matanoni na
waƙoƙin Baka na Hausa), Century Research and Publishing Limited, Kano-Nigeria.
Jami’ar Bayero Kano, (2007), ƙamusun Hausa, Cibiyar Nazarin Harzunan
Nijeriya, B.U.K.
Sarɓi S.A. (2007), Nazarin Waƙen Hausa, Samarib Publishers, A Division
of Samarib Ventures Ltd.
Yahya A.B. (2001), Salo Asirin Waƙa, Sisbas Media Services Kaduna.
Yahya A.B. (1997), Jagoran Nazarin Waƙa. Fisbas Media Service, Kaduna.
Yakasai, S. A. (2012), Jagoran Ilimin Walwalar Harshe, GARKUWA Media Services, Kaduna.
WAƊABDA AKA YI HIRA DA SU
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, 2014.
Farfesa sAlisu Ahmaed Yakasai na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, 2014.
ABIN DA AKA SAURARA
Kaset na rakoda mai ɗauke da waƙar Dr. Bukar Usman Biu ta Umar Idris Ɗanƙwairon Biu, 2014

Post a Comment

3 Comments

  1. Auwal Abdulganiyyu20 July 2017 at 15:54

    Ina son abani email ne ɗalibi daga A.b.u zaria

    ReplyDelete
  2. Abu-Ubaida Sani21 July 2017 at 09:46

    Za ka iya yin amfani da d'aya daga cikin wad'annan:
    abuubaidasani5@gmail.com
    amsoshi2017@gmail.com
    Mun gode.

    ReplyDelete

Post your comment or ask a question.