Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Wajibi Ne Yin Azkar Din Safe Da Yamma?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Mallam. Shin yin Azkar na safiya da maraice wajibi ne a kan Musulmi. Sai kuma mene ne falalar yinsa?

SHIN WAJIBI NE YIN AZKAR ƊIN SAFE DA YAMMA?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Yin Azkar na safiya da maraice ba wajibi ba ne, Amma na daga cikin zikiri da addu'o'in da Annabi ﷺ ya koyar da al'ummarsa, kuma suna daga cikin sunnonin da aka ƙarfafa Musulmi ya kiyaye, Sannan akwai kariya ta musamman da bawa ya nema daga ubangijinsa a dalilin wannan azkar ɗin.

Saboda haka, wanda ya kiyaye su yana da lada mai girma, kuma yana samun falalar Allah. Wanda kuma ya bari, ba ya zama mai laifi saboda barin su kawai.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

وَاذْكُر رَّبَّكَ كَثِيرًا وَسَبِّحْ بِالْعَشِيِّ وَالْإِبْكَارِ

Ka yawaita ambaton Ubangijinka, kuma ka yi tasbihi da yamma da safe.

Annabi ﷺ ya ce:

مَثَلُ الَّذِي يَذْكُرُ رَبَّهُ وَالَّذِي لَا يَذْكُرُ رَبَّهُ مَثَلُ الْحَيِّ وَالْمَيِّتِ

Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayye ne da matacce. (Sahihul Bukhari).

 Annabi ﷺ ya ce:

مَنْ قَالَ حِينَ يُصْبِحُ وَحِينَ يُمْسِي: سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ مِائَةَ مَرَّةٍ، لَمْ يَأْتِ أَحَدٌ يَوْمَ الْقِيَامَةِ بِأَفْضَلَ مِمَّا جَاءَ بِهِ، إِلَّا أَحَدٌ قَالَ مِثْلَ مَا قَالَ أَوْ زَادَ عَلَيْهِ

Wanda ya ce da safe da yamma: SUBHANALLAHI WA BIHAMDIHI sau ɗari (100), babu wanda zai zo ranar Alƙiyama da abin da ya fi nasa, sai wanda ya faɗi irin abin da ya faɗa ko ya ƙara a kai. (Sahih Muslim).

Wannan  suna nuna girman falalar zikiri da kuma falalar azkar na safe da yamma. Don haka, bai kamata Musulmi ya yi sakaci da su ba. Amma azkar ɗin ba wajibi ba ne, sai dai sunnoni ne masu girman falala.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

      ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments