𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu,
Malam.
Tambayata ita ce: Kayan lefe da ango yake kai wa gidan amarya, shin al'ada ce kawai ko kuma akwai wani tushe a addinin Musulunci da ya wajabta wa ango yin hakan? Shin kayan lefen wani haƙƙi ne da amarya take da shi a kan ango, ko kuwa kyauta ce kawai da ake bayarwa bisa al'ada?
Don Allah, Malam, ina son ƙarin bayani game da
matsayin wannan al'amari a Musulunci.
Allah ya saka maka da alheri.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
A taƙaice, kayan lefe al'ada ce mai ƙarfi a ƙasar Hausa, ba addini ba ne, kuma ba hakki ba ne na dole
a kan miji kafin aure. Addini ya ɗauki kayan lefe a matsayin kyauta ta ban girma ko girmamawa da ango yake yi
wa amaryarsa domin nuna farin ciki da ƙarfafa soyayya.
Addini ya ɗora wa miji hakkin tufatar da
matarsa (samar mata da kayan sawa), ciyarwa, da wajen kwana bayan an tare.
Saboda haka, idan miji ya yi lefe, ya rage wa kansa nauyin sayen kaya na wani
lokaci bayan sun yi aure. Idan bai yi ba kuma, hakkin sayen kayan sawa yana nan
a kansa bayan sun tare.
A al'adar Hausawa, lefe yana da matukar muhimmanci (kusan kashi 99.9% na
auren ƙasar Hausa ana yin sa). Nuna girmamawa ne ga amarya da danginta, kuma yana ƙara wa auren armashi. A
al'adance, idan ango ya kawo kayan lefe (akwatuna), su kuma iyayen amarya suna
fuskantar kalubalen yi mata "kayan ɗaki". Masana addini da dama (kamar yadda wasu malamai ke bayani) suna
jaddada cewa samar da kayan dakin ma asali hakkin miji ne, ba na mahaifin
yarinya ba, amma al'ada ta juye abin.
A shari'ance, ba hakki ba ne na dole kafin aure. Idan ango ba shi da iko ko
hali, mace ko danginta ba su da ikon tilasta masa ko janye aure saboda rashin
lefe ta fuskar addini. Sayen akwatuna da cika su da leshi ko shadda ya dogara
ne a kan aljihun ango da abin da zai iya daidai karfinsa. Sai dai saboda nauyin
al'ada, rashin yin sa yana kawo matsala ko jinkirin aure ga matasa da dama a
yanzu.
Lefe bashi da wani matsayi a addinin Musulunci. Kuma bashi acikin sharudda
ko Qa'idodin Qulla aure. Abu ne na bidi'ah wanda mutane suka dora ma kansu.
Kuma yana daga cikin abubuwa ko dalilai dake kawo rashin yin aure, ko jinkirin
yin aure ga Matasa. Sai dai wasu jama'ar dake ganin kyawun abun suna ɗaukarsa amatsayin wata kyautatawa ce ta musamman wacce
namiji zai yiwa matar dazai aura. Amma dai duk da hakan ba a yi saɓani ba game da cewar shi bidi'ah ne, da kuma wajibcin
tsawatar da matasa kada su rika zurfafawa acikinsa. Domin zurfafawar tana janyo
matsaloli da kuma rashin Qarkon aurarraki da dama.
Daga cikin abubuwan da zan iya tunawa ana yinsu anan Qasar hausa game da
bidi'o'in aure akwai:
1. Kayan "Na-gani-inaso".
2. Kuɗin Tambayar arziki.
3. Kayan Sa-rana.
4. Kuɗin Mijin-baya (wanda ake bama
'ya'yan kawunnan amaryar).
5. Kuɗin rigar waliyyi.
6. Kuɗin Uwar Amarya.
7. Kuɗin Sa-lallen Amarya.
8. Party, Picnic, etc.
9. Fulani day.
10. Kauyawa day.
11. Arabian Night.
12. Kuɗin sayen bakin amarya.
Waɗannan kaɗan ne na zakulo. Koda ba a yin wasu daga cikinsu ayankin
da kake rayuwa, to awasu yankunan duk ana yi, ko fiye da haka ma.
Waɗannan abubuwan duk sun saɓa ma sunnar Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam), wanda
Shi Allah ya aiko mana kuma ya ce mu kwaikwayi aikinsa. Tabbas hakika Manzon
Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi aurarraki da dama, kuma shi ma ya
aurar da dukkan 'ya'yansa mata. Amma ba a ruwaito cewa an taɓa aikata koda guda ɗaya cikin Waɗannan abubuwan alokacin bikinsu ba.
Lokacin da ya auri Nana A'isha wasu mata ne 'yan tsiraru suka rakota, kuma ba
a yi wani biki ko kade-kade ba, ballantana cakudar maza da mata. Haka kuma
lokacin da ya aurar da 'yarsa Fatimah wacce ita ce Shugabar dukkan matayen
duniya da lahira amma ba a yi biki ko rawa ko shagali ba.
Imamu Ahmad bn Hanbal ya karbo ta hanyar Nana A'isha (Allah ya yarda da
ita) tace Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce "Hakika auren da
yafi albarka shine wanda dawainiyarsa tafi sauki"
Awani hadisin kuma ya ce "Albarkar mace shine: Saukin sadakinta, da
saukin dawainiyar aurenta, da kyawun halayenta.
Shu'umancin mace kuma yana cikin tsadar sadakinta, Wuyar dawainiyar
aurenta, da kuma munin halinta.
Shaikh Muhammad Bakru Isma'eel ya ce "Da yawa daga cikin mutane sun
jahilci wannan sanarwar ta Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) shi yasa
suke kauce mata suke bin hanyoyi irin na zamanin jahiliyyah cikin zurfafa sadaki
(ko dawainiyar aure) suna la'akari da Qarairayin abubuwa bayyanannu. Sai kaga
mutum yana Qin aurar da 'yarsa ga wani mutum komai matsayin ilimin mutumin ko
mutuncinsa ko rikon addininsa. Sai dai (in sunga alamar cewa) mutumin zai iya
biyan sadaki mai yawa, basu damu da halin mutumin ba.... Sai kace ita yarinyar
da za a aurar ɗin ta zama wata kadara ce za a saye
ko sayarwa".
Don Allah mu guji zurfafawa ko tsanantawa game da kayan lefe tunda babu shi
acikin tsarin aure na musulunci. Al'adah ce ta kawoshi. Don haka arika
sassautawa ana yin nasiha ga ɓangaren gidan maza cewar kada su matsa wa kansu, su kawo abin da ya sawwaka
kawai. Kuma adena la'akari da cewar ai an kawowa wance kaza-da-kaza, don me mu
ba za a kawo wa tamu 'diyar ba!!! Muyi koyi da Manzon Allah (Sallallahu alaihi
Wasallam) tunda auren nan dai sunnarsa ne. Mu guji aikata abin da zai kwashe
albarkar auren.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.