𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam. Dan Allah muna bukatan karin bayani. Na taɓa ganin kun ce istimna'i (masturbation) haramun ne kuma na ga wasu suna cewa akwai wuraren da ya halatta? Muna bukatar karin haske. Allah ya ba da ikon amsawa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.
Allah Sarki! Ya Allah Ka horewa duk wani mai bukatar yin aure damar yin
aurennan. Haka suma yan matanmu da bazawarin nan maras aure Allah Ka kawo musu
da mazajen aure nagari. Tabbas Sha'awa ta kasance babbar barazana a rayuwarmu
(matasa) a wannan zamani kuma wannan yana faruwa ne saboda yawaitar
hirace-hirace da samari da yan mata, karance-karance da kuma kallace-kallace
musamman a internet. Yana da kyau idan mutum yana aikata saɓon Allah (zunubi) to yasan cewa fa saɓon Allah yake aikatawa ta yadda watara zai tuba ya daina,
ba wai yaci gaba da bibiyar jama'a ba domin ya samu wata hujja wadda zata
halatta masa saɓon Allahn da yake yi ta yadda zai
dawwama yana mai aikata wannan saɓon Allahn.
To lallai Wasa da al'aura ga mace ko namiji har yakai ga fitarda maniyyi
domin biyan bukata haramun ne kamar yadda bayaninmu ya gabata daga abinda
malamai suka tabbatar daga Alkur'ani da sunnah.
Ibnu Kaseer (rahimahullah) ya ce : Imamu Shafi'i da wadanda suka goyi
bayansa ya kafa hujja da haramcin wasa da gaba da faɗin Allah madaukakin sarki:
وَالَّذِيۡنَ هُمۡ لِفُرُوۡجِهِمۡ حٰفِظُوۡنَۙ
اِلَّا عَلٰٓى اَزۡوَاجِهِمۡ اَوۡ مَا مَلَـكَتۡ اَيۡمَانُهُمۡ فَاِنَّهُمۡ
غَيۡرُ مَلُوۡمِيۡنَۚ فَمَنِ ابۡتَغٰى وَرَآءَ ذٰ لِكَ
فَاُولٰٓٮِٕكَ هُمُ الۡعٰدُوۡنَ ۚ
"Kuma waɗanda suke ga farjojinsu masu tsarewa
ne face akan matan aurensu ko kuwa abinda hannayen damansu suka mallaka
(kuyangi), to lalle su ba waɗanda ake zargi bane. Saboda haka wanda ya nemi abinda ke bayan wannan, to
wadancan sune masu ketarewar haddi" [Al-Mu'minun, 23:5-7]
Imamu Shafi'i (a cikin littafin Aure) ya ce: "Sai ya kasance Allah ya
bayyana kiyaye farjinsu saifa akan matayensu ko abinda damarsu ta mallaka, sai
ya zama haramun idan ba matar ka bace ko kuyangarka sai Allah ya karfafa
maganar dacewa "Wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka
dokokin Allah" Saboda haka bai halatta amfani da azzakari ba sai akan
matarka ko baiwarka, bai halatta jin dadi dashi da hannu ba. (Kitabul ummu na
Imamu Shafi'i.)
Wasu malaman sun kafa hujja ta haramcin istimna'i da faɗin Allah madaukakin sarki:
وَلۡيَسۡتَعۡفِفِ الَّذِيۡنَ لَا يَجِدُوۡنَ نِكَاحًا
حَتّٰى يُغۡنِيَهُمُ اللّٰهُ مِنۡ فَضۡلِهٖؕ
"Wadanda basu samu damar aure ba sukame harsai Allah ya wadata su daka
falalarsa." [Al-Nur, 24:33]
Sukace Umarni da kamewa yana nuna hakuri da rashin samun yin auren ko
kuyangar.
A sunnah kuwa sun kafa hujja da hadisin Abdullahi dan Mas'ud (Yardar Allah
ta kara tabbata agare shi) ya ce: "Mun kasance tare da Annabi (sallallahu
Alaihi wasallam) muna samari bamu samu komai ba sai Annabi (sallallahu Alaihi
wasallam) ya ce damu "ya ku taran samari duk wanda yasamu halin daukar
dawainiyar iyali ya yi aure, domin ya nasa kamewa daka gani, yana kuma tsare
farji, wanda kuma bai samu dama ba to na hore shi da yin azumi domin azumi yana
kariya daga fadawa haram." [Bukhari:5066.]
Akwai wasu dalilan da dama wadanda ke karfafarda haramcin istamna'i amma waɗannan kacal sun isa zama hujja.
Saboda haka sai shari'a ta shiryar lokacin da mutum ya gajiya wajen yin
aure sai ya dunga azumi tare da wahalarsa, shari'a bata shiryar zuwa wasa da
farji ba, tare da saukinsa akan azumi tare da haka ba'a halatta shi ba.
To amma duk da hakan wasu fuqaha (malaman fiqhu) sun halatta shi a wasu
yanuyyan na lalura (conditions of necessity) a bisa wata ka'ida ta shari'a
wadda suka ce idan laifuka biyu suka haɗu kuma ya zama dole ba yadda za'a yi sai anyi dayan to sai mutum ya zaɓi wanda yafi zama qaramin laifi sai ya aikatata shi domin
kore wancan babban domin dama manufar shari'ah shine hana ɓarna ko rageta idan hanin gaba ɗaya ya gagara. Sai suka ce idan matsananciyar sha'awa
tama mutum yawa har yana tsoron aikata zina kuma ba shine ya janyo wannan
sha'awar ba to ba laifi ya yi istamna'i domin kare kansa daga aikata zina. Kuma
zai aikata hakan da niyyar kore ɓarnar ba wai da niyyar jin daɗi ba kuma ba wai ya yi tayi ba a'a daidai bukatar ta lalura.
Haka kuma sun kafa hujja da kariyar lafiya da kawarda cuta ko illa ga mutum
saboda haka suka ce wanda ya tara ruwa (maniyyi) ya cika masa mara sosai kuma
rashin fitar ruwan zai iya janyo masa wata rashin lafiya ko illa a lafiyarsa
tare da tabbatar da hakan daga masana to shima suka ce ya halatta ya yi
istamna'i ya fitarda ruwan domin kariyar lafiyarsa. Ga wasu misalan waɗannan yanuyyan (lalurorin) kamar haka:
1. Ma'aurata ne (mace ko namiji) wadanda sun san daɗin jima'i to sai suka rabu kuma sai matsananciyar
sha'awar mutum ta dinga motsawa haka kawai ba gaira ba dalili (bafa sune suke
janyota ba ta hanyar tunani, hira da jinsi mabambanci, karatun batsa, kallon
batsa da sauransu) sai har ta fara riyawa mutum yaje ya yi zina sa'annan mutum
yana da damar yin zinar idan yaso to sai ya yi wannan domin hana kansa zinar.
2. Matafiyi ne yaje kasar da zina ta yawaita ga mata nan a banza kuma bai
tare da matarsa ko macece kuma bata tare da mijinta kuma lallai matsananciyar
sha'awar mutum ta motsa yana tunanin aikata zina kuma da zaran ya nema zai samu
to bayan ya gama bin duk matakan da ya kamata yabi (kamar azumi, kauracewa
wurarenda ke motsar masa da sha'awa, shagaltuwa da abinda yaje yi, etc) na
kauda wannan sha'awar taqi ta tafi to shima suka ce ya halatta domin kare kansa
daga zina.
3. Ko kuma haka kawai mutum ne matsananciyar sha'awa ta dama wadda ba shi
ya janyota ba ta hanyoyin dake janyota kuma yabi dukkan matakai domin kauce
mata har ya fara tunanin yin zina shima suka ce sai ya yi domin kare kansa daga
zina.
4. Sharadi na huɗu shine mutum ya samu kansa a daya daga cikin yanuyyan dake a sama ko kuma
kila ya yi azumin ramadana ya tara ruwa (maniyyi) sosai ta yadda rashin fitarsa
zai iya janyo masa wata rashin lafiya ko illa ga jiki kuma masana suka
tabbatarda hakan to shima suka ce ya hallata ya yi.
Amma fa mai karatu ya sani cewa duk da waɗannan sharuddan wasu malamai sunce haramun ne amma dai
zance mafi inganci da rinjaye idan dai waɗannan sharuddan dake a sama sun tabbata kuma mutum ba shine silar janyo
sha'awar ba to ya halatta ya yi ɗin domin kare kansa daga aikata zina ko kariyar kafiyarsa
kamar yadda malaman suka tabbatar.
Saidai mutum ya lura da cewa muddin yasan cewa waɗannan sharuddan basu cika ba harammune ya aikata hakan
haka kuma koda sun cika ka sani da niyyar wadancan dalilan zaka yi ba da niyyar
jin daɗi ba. (Kuma yawancin masu irin
wannan tambayar duk bada wannan niyyar suke yi ba suna yine da niyyar jin daɗi saboda irin kalar hira da karance-karance da
kallace-kallace da ake yi saboda haka mutum ya sani haramunne yake yi kuma ace
za'a kama mutum a lokacin to lallai za'a hukunta.
Baya ga zamansa haramun babba bincike ya juna wannan dabi'ar tana da illoli
sosai ga lafiyar jiki babba daga cikinsu tana kashe maka mazakuta ko matsalar
rashin haihuwa kuma gashi ance idan mutum ya saba da yin abin baya iya dainawa
saboda haka dai kamewa daga aikatawa shi yafi tare da bin waddan matakan domin
maganin sha'awar dake damun mutum.
YADDA MUTUM ZAI MAGANCE WANNAN DABI'A SUNE KAMAR HAKA:
1. Wajibi ne mutum ya kubutar da kansa daga wannan al'ada dan nisantar
abunda Allah ya haramta da kwatanta bin umarninsa da gujewa fushin sa. Yan mata
ku daina irin chating dinnan da samari musamman irin wanda ke motsarda sha'awa
tsakaninku.
2. Kawar da wannan da lafiyar jiki shine aure saboda wasiyyar manzan Allah
(sallallahu Alaihi wasallam) ga samari.
3. Kawar da hadurra da waswasi da zuciya zata dunga sakawa, da shagalta da
tunani cikin abunda zai amfaneka duniya da lahira, domin yawan waswasi da
tunani yana kai mutum zuwa ga aikata abu, sannan mutum ya saba ta yanda zai
masa wahalar gasken gaske wajen kubuta daga aikata shi .
4. Kamewa daga gane-gane domin kallace-kallacen wasu abubuwa da hotuna na
zane da masu motsi rayayyu ko matattu yana kai mutum zuwa haram.
5. Shagaltuwa da ibadoji kala-kala dakin barin sarari ga aikin saɓo.
6. Izna da cutukan dake haifarwa jiki na raunin gani da gaɓɓai da ciwan baya da sauransu.
7. Riko da maganin manzan Allah (sallallahu Alaihi wasallam) shine azumi.
8. Lazimtar ladubban shari'a ya yin bacci na karanta zikirori .
9. Kaskantar da kai ga Allah da neman taimakonsa.
10. Gaggauta tuba da istigfari da aikata ayyuka na gari, tare da rashin ɗebe tsammani daga Allah.
11. Mutum ya nisanci kwana shi kaɗai a ɗaki domin Annabi (sallallahu Alaihi
wasallam) ya hana mutum ya kwana a ɗaki shi kaɗai. Kuma tabbas kwana a ɗaki yana haifarda mutum ya yi duk abinda yake bukata na
saɓon Allah.
Lallai cika waɗannan sharuddan ga wanda ke son a halatta masa istamna'i abu ne mai matukar
wuya, matukar kuwa mutum bai bi duk waɗannan matakan na hana kansa janyo sha'awarsa ba to lallai ya sani koda ya
yi shi to haramun yake yi ta hakan ma wataran zai ji tsoron Allah ya daina.
Bari na qara tuna baya ga zunubin da mutum zai samu gashi tabbas bincike ya
tabbatarda idan mutum ya fara wannan dabi'ar baya iya dainawa kuma ga yawaita
yinsa yana kawo illaloli sosai ga lafiyar mutum. Mafi yawan masu wannan dabi'ar
matasa ne samari da yan mata marasa aure saboda haka sai kaga sun bata
rayuwarsu a wannan harkar sai mutum yazo ya yi auren idan namiji ne gashi ga
macen amma baya iya komai saboda istamna'i ya riga ya kashe masa gaba. Idan
kuma macece sai kaga gata yanzu ta samun namijin mai kashe mata kishiryar
sha'awarta amma kuma koda sunyi ɗin ba zata wadatu ba dole sai tayi wasa da kanta ɗin saboda abin ya zame mata dabi'a. Saboda haka mafita ita
ce kamewa tare da kiyaye duk wani abu na saɓo wanda ke janyowa mutum matsananciyar sha'awar.
Allah ya qara kare mu. Ya Allah waɗanda basa da aure daga cikinmu Allah ya bamu damar yinsa.
Domin neman qarin bayani sai a duba:
ﻣﻄﺎﻟﺐ ﺃﻭﻟﻲ ﺍﻟﻨﻬﻰ ﺷﺮﺡ ﻏﺎﻳﺔ ﺍﻟﻤﻨﺘﻬﻰ ( 6/226)
ﺍﻹﻧﺼﺎﻑ ( 10/252)
ﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ (
302 /)
ﺍﻟﺸﺮﺡ ﺍﻟﻤﻤﺘﻊ ( 14/318)
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.