Ticker

6/recent/ticker-posts

Sahabin Da Aka Ambaci Sunansa A Cikin Alkur'ani Kuma Ake Wa Lakabi Da Masoyin Manzan Allah (SAW)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Mallam Khamis Barka da safiya, da fatan ka tashi lafiya. Tambayata ita ce wanne sahabi ne aka ambaci sunansa acikin Alkur'ani kuma ake wa Laqabi Da Masoyin Manzan Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)

SAHABIN DA AKA AMBACI SUNANSA A CIKIN ALƘUR'ANI KUMA AKE WA LAQABI DA MASOYIN MANZAN ALLAH (SAW):

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Sahabin da akewa laqabi da Masoyin Manzan Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Shine ZAID BIN HARISAH Wanda shine Allah Ya Ambaci Sunansa acikin Alqurani, duk Cikin Alqur'ani bazaka samu sunan Wani sahabi ba inba zaidu kaɗai ba. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:

 ؕ فَلَمَّا قَضٰى زَيۡدٌ مِّنۡهَا وَطَرًا زَوَّجۡنٰكَهَا لِكَىۡ لَا يَكُوۡنَ عَلَى الۡمُؤۡمِنِيۡنَ حَرَجٌ فِىۡۤ اَزۡوَاجِ اَدۡعِيَآٮِٕهِمۡ اِذَا قَضَوۡا مِنۡهُنَّ وَطَرًا ؕ وَكَانَ اَمۡرُ اللّٰهِ مَفۡعُوۡلًا‏

Lokacin da zaidu yaga Baida Buqatar cigaba da zama da zainab bintu jahashin, sai Muka Aura maka ita dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan muminai a cikin (auren matan) ɗiyan hankakarsu, idan sun ƙare bukata daga gare su. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatawa. (Surah: Al-Ahzaab, Ayat: 37).

ZAIDU BIN HARISAH Shi kaɗai ne sahabi da aka ambaci sunansa sarari a cikin Alƙur'ani mai girma (A cikin Suratul Ahzab aya ta 37), wanda hakan ke nuna matsayinsa na musamman.

Nasabarsa da Rayuwarsa Shine sahabi Mai girma Bawan Manzan Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) zaidu bin Harisah bin Sharaheel bin Ka'ab bin Abdul Uzzah bin Imri'i Qais bin Aamir bin Nu'uman bin Aamir bin Abuud bin Auuf bin Kinanata bin Bakar bin Auuf bin Uzrata bin zaidil lat bin Rufaidah bin Saur bin kalb bin Wabrata bin Sa'alab bin Hulwan Bin Imaran bin haaf bin Qazatal kalbi.

Masu tarihi sukace: Mahaifiyar zaidu ta tafi wajan Ahalinta donta ziyarcesu, tana cikin tafiya sai Abokan gaba suka kai farmaki suka sacewa mutanensu Abunda suka iya sata, suka kame na kamewa acikin mutanen akwai Ummu zaidu, sai suka kai zaidu kasuwa donsu sayar da shi, sai hakeem bin Hazzaam ya siyeshi, Saiya baiwa Gwaggwansa khadija, ita kuma khadija saita baiwa Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) Kyautar zaidu tun kafin ayi hijira, ya zauna awajansa lokaci mai tsawo, sai Anmunsa da Babansa sukazo suna neman fansarsa awajan Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Al'amari yana hannun zaidu yazabi wanda ya fiso, idan yaga zaibi babansa ya koma dashi su tafi, idan yaga zaici gaba da zama awajan Annabi yai zamansa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce Su nemi zabinsa, idan yazabi ya bisu su tafi dashi batare da sunyi fansarsa ba, idan ya zabi ya zauna ya zauna, sai zaidu ya zabi yaci gaba da zama awajan Manzan Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kafin ayi hijra.

Babansa yai Mamaki yai masa inkarin wannan abun da ya yi, ya ce da hankalinsa zai zaɓi ci gaba da zama bawa awajan wani, akan ya koma da iyayensa zuwa gidansu, sai zaidu ya ce: Wallahi banga wani Abu daka Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya tsoratar dani koya firgitani ba tunda nake, sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya daukeshi zuwa ɗakin Ka'aba ya sanar dayi masa tabanni, don sauqaqawa babansa Abunda yaji na takaici aransa, ya ce: Yaku taron Quraishawa kushaida zaidu ɗanane zai gajeni zan gajeshi, sai aka wayi gari ana kiransa da zaidu bin Muhammad, har saida Musulunci yazo da haramcin Tabanni  (ɗaukar ɗan wani a maida shi naka na jini), sai sunan zaidu ya koma yanda yake. Allah ya ce:

اُدۡعُوۡهُمۡ لِاٰبَآٮِٕهِمۡ هُوَ اَقۡسَطُ عِنۡدَ اللّٰهِ ۚ فَاِنۡ لَّمۡ تَعۡلَمُوۡۤا اٰبَآءَهُمۡ فَاِخۡوَانُكُمۡ فِى الدِّيۡنِ وَمَوَالِيۡكُمۡؕ وَ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ فِيۡمَاۤ اَخۡطَاۡ تُمۡ بِهٖۙ وَلٰكِنۡ مَّا تَعَمَّدَتۡ قُلُوۡبُكُمۡ ؕ وَكَانَ اللّٰهُ غَفُوۡرًا رَّحِيۡمًا‏

Kudunga kiransu da Sunan iyayensu, shine adalci awajan Allah, idan Bakusan iyayensu ba, ku kirasu da 'yan'uwanku a'addini da Bayinku, babu laifi akanku cikin Abunda kuka kus-kure, saidai Wanda zuqatanku sukai Gan-ganci akansa, Allah ya kasance Mai yawan Gafara Mai Jinqai. (Surah: Al-Ahzaab, Ayat: 5).

Kafin Musulunci ya soke hani a kan ɗaurawa wani sunan uba ba nasa ba, ana kiran Zaidu da "Zaid bin Muhammad" saboda yadda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ɗauke shi a matsayin ɗansa.

Zaidu bin Harisah (R.A) ana kiransa da laƙabin "Hibbu Rasulillah" (Maƙasudin Manzon Allah) ko kuma "Al-Hibb ibn al-Hibb" (Masoyi ɗan masoyi). Wannan laƙabi ya samo asali ne saboda tsananin ƙauna, soyayya, da kusanci na musamman da ke tsakaninsa da Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa ya taɓa cewa game da Zaidu: "Wallahi ya kasance mafi soyuwar mutane a gare ni". Haka kuma, ɗansa USAMA BIN ZAID shi ma ya gaji wannan laƙabi, inda aka riƙa kiransa "Al-Hibb ibn al-Hibb" (Masoyi ɗan masoyi).

Zaidu ya zama yanada soyuwa mai yawa azuciyar Manzan Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) Saidai Bayan Allah ya raba Nasabar zaidu da Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) da sakin Matarsa da ya yi zainab Bintu jahash, Allah yai nufin ya mayarwa da zaidu Alkhairi da Sauqaqa masa, saiya Karramashi da Ambaton Sunansa shi kaɗai acikin Alqur'ani duk cikin sahabbai, ya ce:

فَلَمَّا قَضٰى زَيۡدٌ مِّنۡهَا وَطَرًا زَوَّجۡنٰكَهَا

Zaidu Ya yi Shahada A yaqin Mu'utah ashekara ta takwas bayan hijira, rundunar yaqi ta fita izuwa shaam don Haduwa da rumawa, da Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) ya fuskanci Muhimmancin yaqin saiya zaɓi ruduna uku Masu qarfi, Masu Gwabza yaqi da rana da Bautar Ubangiji cikin dare, lokacin da zaiyi Bankwana da Rundunar ya ce: Ina horanku da Zaidu Bin harisah, idan zaidu Ya yi shahada, ina horanku da ja'afar Bin Abi dhalib, idan Ja'afar ya yi shahada, ina horanku da Abdullahi Bin Rawaha" Allah yaqara Masa yarda ya yi shahada awannan yaqi, dukkan jagororin nan uku sunyi shahada wanda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce ariqesu awannan yaqin, sai Khalid Bin waleed ya riqe ragamar rundunar yaqin, yai amfani da dabara mai yawa wacce da ita ya tarwatsa rundunar Abokan gaba, da Kaiwa Abokan gaba mashi cikin kwanciyar hankali.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya yi baqin cikin rasuwar zaidu, baqin ciki Mai tsanani, har saida yai kukan rasuwarsa, akace menene haka ya manzan Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)? Sai ya ce: Shauqin masoyi ga masoyinsa.

Wannan shine dan taqaitaccen tarihin Masoyin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ZAIDU BIN HARISAH.

Allah ya jiqan zaidu Allah yaqara yarda dashi ya hadamu dashi acikin Aljannar firdausi madaukakiya, ya hadamu da Annabawa da Manzanni da Sahabbai baki daya acikin Aljannar firdausi madaukakiya, da tafkin manzan Allah (sallallahu Alaihi wasallam)

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

      ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments