Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mayar Wa Kirista Ko Kafiri Sallama

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu, Malam.

Tambayata ita ce: Shin ya halatta Musulmi ya yi wa wanda ba Musulmi ba sallama?

Ni dai ina zaune ne a gida ɗaya da wata mata Kirista. Idan na ƙi yi mata sallama, wani lokaci ita ce take fara ce min, “Assalamu alaikum.” Ni kuma sai in ɗaga mata hannu kawai ba tare da na amsa sallamar ba.

Don Allah, Malam, mene ne ya kamata in riƙa yi a irin wannan yanayin? Shin ya halatta in fara yi mata sallama, ko kuma idan ita ta fara yi min, ya kamata in amsa mata ta wace hanya?

Allah ya ƙara maka basira da ilimi. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, Bai halasta Musulmi ya fara yi wa kafiri sallama  ba, saboda akwai hadisai ingantattu da suka hana yin hakan, amma kuma idan wanda ba Musulmi ba ya yi maka sallama, a nan dole ne ka mayar masa da sallama saboda gamewar ma'anar ayar Alqur'ani da Allah ke cewa:

وَاِذَا حُيِّيۡتُمۡ بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوۡا بِاَحۡسَنَ مِنۡهَاۤ اَوۡ رُدُّوۡهَا ؕ

"Idan aka yi maku gaisuwa da wata nau'in gaisuwa, to ku mayar da wadda ta fi ta, ko ku mayar da irinta (ai irin wadda aka yi maku". Suratun Nisá'i 86.

Malamai sun bayyana cewa babu abin da ya bambanta Musulmi da wanda ba Musulmi ba a wannan ayar ta fuskar hukuncin mayar da sallama, saboda haka idan wanda ba Musulmi ba ya yi maki sallama, ke ma za ki mayar masa da sallamar ne.

Abin da aka hana shi ne Musulmi ya fara yin sallama ga kafiri, amma idan shi ne ya fara yi maka sallama babu laifi idan ka mayar masa saboda gamewar ma'nar waccan ayar da ta gabata.

Haka nan an hana Musulmi ya fara gaishe da kafiri, har sai idan akwai wata buqata da ta sa hakan, saboda fara gaishe shi zai iya sa ya ga hakan kamar girmama shi ne da rashin ɗaukar kafircinsa a matsayin abin kyama, amma idan akwai buqatar da ta sa hakan, ko saboda kaucewa cutarwarsa idan ba ka fara gaishe shi ba, to a nan malamai sun ce babu laifi don mutum ya fara gaishe shi ɗin.

Saboda haka ‘yar uwa duk lokacin da wannan abokiyar zaman taki ta yi maki sallama ba ɗaga mata hannu za ki yi ba, mayar mata za ki yi da sallamar kamar yadda malamai suka bayyana a bisa dogaro da waccan ayar. Abin da aka hana ki shi ne fara yi mata sallama.

Domin samun cikakkun waɗannan bayanai sai a duba MAJMÚ'U FATAAWÁ  (3/34) na IBN UTHAIMEEN. Ko a duba  MAJMÚ'U FATAAWÁ (5/406) na IBN BAAZ.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

      ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments