Ticker

6/recent/ticker-posts

Wajibcin Yi Wa Mahaifa Nasiha A Kan Addini Da Maganin Hawan Jini

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum warahmatullah. Gaisuwa da fatan alkhairi ya fama da jama'a Allah ya saka da mafificin alkhairi ameen. Malam don Allah tambaya ce da ni: Malam mahaifiyata ce Allah ya jarabce ta da ciwon hawan jini kuma ta dade da shi har ya fara taɓa mata kwakwalwa tana fama da yawan mantuwa da wasu abubuwan, har takai ga idan lokacin sallah ya yi sai dai arika kirga mata yawan raka'o'in da za ta yi tana yi ana kirga. Idan ba hakaba kuwa ba za ta iya yin cikakkar sallah ba ita kaɗai. Sannan Wani lokacin sai tace ta yi sallah alhalin ba ta yi ba. Kuma idan aka cigaba da yi mata maganar ba ta yi sallarba sai ta yi ta kuka, to ni kuma malam ina tsoron in ci gaba da yi mata haka kada Allah ya kamani da laifin saka mahaifiyata kuka. Na gode Allah ya ba da ikon amsawa. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wajibi ne kiyi hakuri kici gaba da yi mata nasiha tare da yi mata umurni akan abinda ya shafi ayyukan addini, musamman ma sallah wacce ita ce ginshikin addini. Amma cikin tausassar murya da kalamai masu daɗi, ba tare da tsangwama ko hantara ba.

Allah ya faɗa a cikin Alƙur'ani cewa

يٰۤاَيُّهَا الَّذِيۡنَ اٰمَنُوۡا قُوۡۤا اَنۡفُسَكُمۡ وَاَهۡلِيۡكُمۡ نَارًا وَّقُوۡدُهَا النَّاسُ وَالۡحِجَارَةُ عَلَيۡهَا مَلٰٓٮِٕكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَّا يَعۡصُوۡنَ اللّٰهَ مَاۤ اَمَرَهُمۡ وَيَفۡعَلُوۡنَ مَا يُؤۡمَرُوۡنَ‏

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su. (Surah: At-Tahrim, Ayat: 6)

Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) Yace ma'anar ayar ita ce: "Kuyi aiki da biyayyar Allah kuma ku kiya yi ayyukan saɓon Allah, kuma ku umurci iyalanku da ambaton Allah, Allah zai tseratar daku daga shiga wuta".

Mujahid yace Ma'anar ayar ita ce: "Kuji tsoron Allah kuma ku yi wa iyalanku wasiyyar cewa suji tsoron Allah".

Ƙatadatu bn Da'amah (rah) yace abinda ayar take nufi shi ne : "Ku umurci iyalanku da bin Allah, kuma ku hanesu daga saɓa masa, kuma cewa ku tsaya akansu bisa umurnin Allah, ku umurcesu da yinsa, kuma ku taimakesu akan bin Allah ɗin. "Idan kuma kaga alamar wani aikin saɓon Allah daga garesu, to ka tsoratar dasu, kaja hankalinsu akan su gujeshi."

Dhahhak da Muƙatilu bn Hayyan suka ce "Hakki ne bisa kowanne musulmi ya sanar da iyalansa da makusantansa da bayinsa maza da kuyanginsa su san hakkokin da Allah ya farlanta akansu, da kuma abinda Allah ɗin ya hana agaresu".

To kinga idan kika lura da maganganun nan da waɗannan manyan Maluman magaba ta ɗin suka faɗa, za ki ga ashe wajibi ne gareki kici gaba da hakuri kina umurtarta da yin Sallah mutukar dai ba haukacewa ta yi ba.

Amma idan an tabba tar cewa ciwon hauka ne tare da ita, to farillancin yin sallar ma ya sauka daga kanta kenan. Saboda hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda a cikinsa yace An dauke alkalamin rubuta alhaki daga kan mutum uku. Aciki yace "Da Mahaukaci Har Sai Ya Wartsake".

Wannan kukan da takeyi, ba zai janyo miki komai ba daga gun Allah sai Ƙarin lada da kuma samun yardarsa. Kedai kada ki rika yi mata tsawa ko firgitarwa.

Dangane da larurar hawan jinin dake tare da ita kuwa, ki nemo ganyen ayaba ki yankashi kanana. Ki shanya a inuwa. Idan ya bushe ki hada shi da habbatus sauda ki dakasu ki rika zuba mata ashayi (tea) tana shansa safe da yamma (tea spoon 1 safe da yamma). Allah ya sawwake.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments