Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Neman Arziki Mai Albarka

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Mallam Khamis da fatan ka wuni lafiya, Malam khamis talauci ya yi min yawa, ga yawan cin bashi, don Allah ina bukatar addu'a kawo arziki mai albarka. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Babu wata addu'a ta musamman da ta kebanta da kawo arziki wacce aka tsara ta kaɗai.

An tambayi Shaykh Ibnu Uthaimeen(RA): Menene Addu'an Kawo Arziki Da Kawo Albarka Cikinsa? Sai ya amsa da cewa: "Ban san wata addu'a na musamman ba domin kawo arziki, sai dai Taƙawar Allah (Kiyaye dokokin Allah) yana daga cikin manya manyan sabubban kawo arziki, Allah Maɗaukaki ya ce

وَمَن يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَل لَّهُ مَخْرَجًا ۝ وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ

"Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita. Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato.

Don haka Taƙawa da addu'a suna daga cikin sabubban jawo arziki.

Akwai sahihan addu'o'i da aka karɓa daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da suke neman wadatar arziki da albarka. Idan talauci ko bashi suka yi wa mutum yawa, Musulunci ya koyar da addu'o'i masu yawa na inganci waɗanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya umarci muminai su karanta domin neman budi, yalwar arziki, da yaye damuwa. Ga manyan addu'o'in da mutum zai iya mayar da hankali a kai

• اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلَالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ

"Ya Allah! Ka wadatar da ni da halalinka daga haraminka, kuma Ka wadatar da ni da falalarka daga bukatar kowa bayanka."

• اللَّهُمَّ بَارِكْ لِي فِي رِزْقِي، وَوَسِّعْ لِي فِيهِ، وَاجْعَلْهُ رِزْقًا حَلَالًا طَيِّبًا مُبَارَكًا

"Ya Allah! Ka sanya mini albarka a cikin arzikina, Ka yalwata mini shi, Ka sa ya zama halal, mai kyau kuma mai albarka."

• اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْمًا نَافِعًا، وَرِزْقًا طَيِّبًا، وَعَمَلًا مُتَقَبَّلًا

"Ya Allah! Ina roƙonka ilimi mai amfani, arziki mai kyau, da aiki da za ka karɓa."

• اللَّهُمَّ أَنْتَ الْأَوَّلُ فَلَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ... اقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ، وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ

"Ya Allah, Kai ne na farko babu komai kafin Ka... Ka biya mana bashinmu, kuma Ka wadatar da mu daga talauci."

• اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ، وَالْعَجْزِ وَالكَسَلِ، وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ، وَضَلَعِ الدَّيْنِ، وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ

"Ya Allah, ina neman tsari gare Ka daga damuwa da bakin ciki, da gazawa da kasala, da rowa da tsoro, da nauyin bashi, da kuma rinjayen mutane a kaina."

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya koyar da wani sahabi mai suna ABU UMAMAH wannan addu'ar lokacin da talauci da bashi suka yi masa yawa.

Bayan waɗannan addu'o'i, malamai sun bayyana cewa akwai wasu ayyuka da suke buɗe kofofin arziki cikin gaggawa

1. TAƘAWAR ALLAH: Kiyaye dokokin Allah da barin saɓawa Ubangiji.

2. TAWAKKALI: Dogara ga Allah da gaskiya wajen neman abinci na halal. Allah maɗaukakin sarki Yace: "Duk wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita. Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato".

3. YAWAN ISTIGFARI: Yawaita neman gafarar Allah (Astaghfirullah) yana buɗe ƙofofin arziki. Allah ya faɗa ta harshen Annabi Nuuhu (alaihis salam) yana gaya wa mutanensa "Ku Nemi Gafarar Ubangikinku, Domin Shi ne Mai Gafara. Zai Saukar Muku Da Ruwa Mai Yawa Daga Sama. Kuma Zai Ƙaro Muku Yawan Dukiya Da 'Ya'ya Kuma Zai Sanya Muku (Albarka) A Gonakinku, Kuma Zai Sanya Muku Albarka A Koramu (Wato Rafuka Da Koguna).

4. YAWAITA SALATIN ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam): Salati yana yaye damuwa kuma yana sa addu'a ta karbu cikin sauri.

5. YIN SADAKA: Taimakon mabukata koda da kaɗan ne.

6. TASHI NEMAN HALAL (AIKI): Wajibi ne mutum ya fita ya nemi na kansa ta hanyar kasuwanci ko kwadago, domin Allah ba ya sanya albarka.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments