𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Allah gafarta malam matar abokina ce aka same ta da wani mutum, 'yan sanda ne suka kama su amma ba su samesu suna aikata wani abu ba. Amma sun kaisu office nasu sun sanya sun yi rubutu akan lallai sai sun amsa cewa sun aikata lefin zina. Ita kuma sun ce ta ba su Naira dubu hamsin (₦50,000) Sannan za su rufa mata asiri. Suka sallame ta amma ba ta bayar ba. Daga baya maganar ta fito, sai mijinta ya saketa saki ɗaya amma ta yi rantsuwar ba ta aikata komai da shi wancan mutumin ba kuma ta nemi yafiyar mijinta ya yafe mata. Amma 'yan uwan mahaifiyarsa sun ƙi amincewa ya dawo da matarsa. To Malam mene ne hukuncin wannan a addinin Musulunci? kuma wacce shawara za a ba su, domin gudun shiga wata hanyar.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Kama matarsa da akayi
ta keɓance da wani namiji
wanda ba Muharrami gareta ba, tabbas wannan laifi ne babba. Kuma watakil Allah
ne ya nufeta da alkhairi shi yasa asirinsu ya tonu tun kafin su aikata komai.
Kuma tunda ta roki afuwar mijinta kuma ya ce ya yafe, kuma yana so zai dawo da
ita amatsayin matarsa, to ai babu mai hanawa. Domin a addinin musulunci, miji
ne kaɗai yake da ikon sakin
matarsa ko kuma dawo da ita bayan sakin.
Kuma idan har miji ya
furta cewar ya dawo da ita, babu wanda keda ikon cewa ba za ta dawo ba. Mutukar
dai ba ta riga ta kammala iddarta ba. Idan ma ta kammala iddar, ai mijin nata
shi yafi kowa chanchanta da ita musamman ma idan akwai haihuwa atsakaninsu.
Dangin mahaifiyar
mutum, 'yan uwa ne na zumunci amma ba su da damar juya mutum bisa tilas.
Musamman akan abinda shari'a ba ta ba su dama ba. Kuma musamman ma akan abinda
maslahar shi mutumin ba ta cikin abinda suke ra'ayi din.
Dangin mahaifin mutum
sune waliyyansa kuma sune dangi mafiya karfi. Sune awasu lokutan shari'a takan
ba su damar shigowa cikin sha'anin mutum har su tirsasashi akan duk abinda suka
hangi maslaha a cikinsa.
Misali kamar mutumin
da ya zamanto safeehi (wato ga'bo ko marar wayo) to akan sanya igiyar aurensa
ahannun waliyyinsa mafi kusanci da shi. Kamar mahaifinsa ko yayansa ko
Baffansa, suna da ikon su wakilceshi su sakar masa matarsa, ko wani abinda ya
yi kama da haka.
Yanzu dai tunda yana
son dawowa da matarsa, to yana da cikakken ikon yin hakan ko da su wadancan din
ba su amince ba. Musamman idan akwai maslaharsa ko maslahar 'ya'yansa a cikin
dawowarta ɗin. Allah Ya ce
...وَبُعُوۡلَتُهُنَّ اَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ
فِىۡ ذٰ لِكَ اِنۡ اَرَادُوۡٓا اِصۡلَاحًا ؕ وَلَهُنَّ مِثۡلُ الَّذِىۡ
عَلَيۡهِنَّ بِالۡمَعۡرُوۡفِ وَلِلرِّجَالِ عَلَيۡهِنَّ دَرَجَةٌ ؕ وَاللّٰهُ
عَزِيۡزٌ حَكِيۡمٌ
Kuma mazan aurensu su
ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi
nufin gyarawa. Kuma sũ matan
suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata
daraja a kansu (su matan). Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima. (Suratul Baƙarah ayah ta 228).
Al Imam Ibnu katheer
akarkashin wannan ayar ya ce "Ai mijin da ya saketa shi ne yafi chanchanta
ya mayar da ita, mutukar dai tana cikin iddah (ba ta kammala ba). Kuma mutukar
ya nufi sulhu da kuma alkhairi a cikin komawar".
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.