Ticker

6/recent/ticker-posts

Rantsuwa Da Alkur'ani A Kan Karya Saboda Guje Wa Zargin Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamualaikum malam. Shin idan saurayi bai taɓa zina ba Kuma ya auri mace amatsayin ita ma budurwa ce ba ta san namiji ba, to sai ya zamana ita ta san namiji kafin ta aure shi amma ta hanyar zina. Shin mijin nata yana da haƙƙi a kanta saboda ɓoye masa aibu da ta yi? Sannan bayan ya aure ta ba ta san me yaji agari game da ita ba sai ya tambayeta ya ce ta fada Masa tsakani da Allah kafin ta aure shi ta taɓa yin zina? Sai ta yi masa karya tace ita ba ta taɓa yin zina ba, har ma ta ɗauki Alkur'ani ta rantse tare da cewa in karya take fushin Allah da azabar Allah su sauka a kanta. Kuma in karya take yi Allah ya tozarta ta ya yi dugu-dugu da ita. Tambaya a nan malam sune kamar haka:-

1. Shin Yana da wani haƙƙi akan ta saboda yaudara da karya da ɓoye masa aibu da ta yi?.

2. Shin Kuma azabar da tozartar da tsinuwar da wula kantar za su sameta? na gode.

RANTSUWA DA ALƘUR'ANI A KAN ƘARYA SABODA GUJE WA ZARGIN ZINA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Gaskiya dukkanku kunyi kuskure dake da mijin naki. Kuskuren da mijin ya yi, shi ne zargi da kuma binciken kwakwaf akan matarsa. Allah (SUBHANAHU) ya haramta dukkan wannan. Domin shi kansa mai yin binciken, da za ayi masa irin wannan kwakwaf ɗin, shi ma ba zai rasa wani babban aibu ba. Shi yasa Allah Ya ce

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ...

"YAKU WAƊANDA SUKA ba da GASKIYA! KU NISANCI MAFI YAWANCIN ZATO, DOMIN HAKIKA SASHEN ZATO ZUNUBI NE. KUMA KADA KU RIKA BINCIKEN LAIFIN JUNANKU." (Suratul Hujurat Aya ta 12).

 وَٱلَّذِینَ یَرۡمُونَ أَزۡوَ ٰ⁠جَهُمۡ وَلَمۡ یَكُن لَّهُمۡ شُهَدَاۤءُ إِلَّاۤ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَـٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَـٰدَ ٰ⁠تِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِینَ ۝ وَٱلۡخَـٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَیۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَـٰذِبِینَ ۝ وَیَدۡرَؤُا۟ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَـٰدَ ٰ⁠تِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَـٰذِبِینَ ۝ وَٱلۡخَـٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَیۡهَاۤ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِینَ

Kuma Waɗanda suke jifar matan aurensu kuma bai kasance suna da waɗansu shaidu ba sai dai su kansu kawai, to shaidar ɗayansu ita ce: Rantsuwoyi har sau huɗu da Allaah a kan cewa: Lallai ne shi yana daga cikin masu gaskiya. Kuma ta biyar ita ce cewa: Tsinuwar Allaah ta sauka a kan shi, idan har ya kasance daga cikin maƙaryata. Kuma zai kawar mata da horon (jefewa) idan ta yi rantsuwa sau huɗu da Allaah a kan cewa: Shi yana daga cikin maƙaryata. Kuma ta biyar ita ce: Fushin Allaah ya tabba ta a gare ta idan ya kasance daga cikin masu gaskiya. (Sura An-Nuur: 6-9).

Fitar jini alokacin saduwar farko, ba shi ne tabbacin cewar wannan matar ba ta taɓa yin zina ba. Domin akwai dalilai da yawa waɗanda ke janyo fashewa ko yagewar wannan tantanin budurcin. Misali kamar ɗaukar kaya mai nauyi, hawa keke, tsalle-tsalle da guje-guje, Haka nan jinkirin yin aure ma yakan kawo fashewarsa. Wata matar kuma dama chan Alalh bai halicceta da shi ba.

Tun tana gidan iyayenta ya kamata ya yi duk binciken da zaiyi tun kafin ya fara nemanta da aure. Amma yanzu kam tunda har ya riga ya aure ta, ya zama wajibi ya kiyaye mata mutuncinta daga dukkan jama'a. Koda kuwa danginsa ne suka zo da wasu maganganu marasa daɗi bai kamata ya ɗauka har ya rika tuhumar matarsa da laifi ba.

Amma ita kuma kuskurenta shi ne rantsuwar Ƙarya da ta yi, da gangan. Yin rantsuwar Ƙarya da gangan babban laifi ne. Domin kuwa Imamul Bukhariy ya ruwaito cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: "Manyan laifuka sune, yin shirka da Allah, da saɓa wa iyaye, da kisan kai, da kuma rantsuwar Ƙarya"

Yin rantsuwa da Alkur'ani akan karya babbar zunubi ce kuma laifi mai girma wanda malamai suka sanya shi a cikin rantsuwa mai halakarwa (Al-Yaminul-Ghamus). Wannan rantsuwar ta yi muni sosai har ma ba ta da kaffara (kamar ciyarwa ko azumi) domin ta fi karfin ayi kaffara da ita; ta na karkashin babban laifi ne da ake bukatan tuba na gaske da neman gafarar Allah.

Saukin abun shi ne tunda ta yi ne domin kare mutuncinta da kuma aurenta. Domin watakil da ta fito ta gaya masa gaskiya da tuni ya saketa, kuma ya koreta daga gidansa. Kuma koda zaici gaba da zama da ita, watakil sai ya rika wula kanta darajarta saboda wannan dalilin. Abinda za ta yi yanzu shi ne

1. Tuba ga Allah bisa laifin zinar da ta aikata abaya, da kuma rantsuwar Ƙarya da ta yi. Sannan ta ɗauki niyyar cewa har abada ba za ta sake aikata irin waɗannan laifukan ba.

2. Ta cigaba da neman gafarar Allah tare da neman yardarsa ta hanyar yawaita biyayya ga mijinta. Bayan kuma kulawa da farillai da sunnoni.

3. Ta yawaita sadaƙah da sadar da zumunci. In sha Allahu albarkacin nadamar da ta yi, da kuma kyautata ayyukan da take yi, Allah yana iya kankare laifukanta ko kuma ya juyar da tarin zunubanta su zama lada. Allah Ya ce

 إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰ⁠لِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ

"SAI DAI WAƊANNAN DA SUKA TUBA KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN KWA RAI, WAƊANNAN SUNE WAƊANDA ALLAH YAKE CHANZA MUNANAN AYYUAKANSU ZUWA GA AYYUKAN LADA, LALLAI ALLAH YA TABBA TA SHI MAI GAFARA NE MAI JIN ƘAI".

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments