𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahatullahi wa bara ka tuhu Allah ya karawa malam lafiya tambayata ita ce malam wanne lokaci ya kamata mutum ya yi raka'atanil-fijir kuma yaushe lokacin ta yake karewa? sannan dan Allah mutum ne ya kwanta da niyyar ze tashi sallar dare se bai yi wutiri ba yana nufin idan ya yi sallar cikin dare se ya yi to sai kuma ya makara bai yi sallar daren ba be kuma yi wutirin ba ga lokacin asuba ya yi to malam yazeyi da wutirin daya bari Allah ya kara lafiya
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Lokacin yin sallar
raka'atanal fajari yana farawa ne daga zarar alfijir ya keto kuma yana ƙarewa kafin a tada
sallar farilla ta Asuba. Idan aka yi ta kafin alfijir ya fito, ba ta inganta a
matsayin raka'atanal fajari ba. Mafi alheri da dacewa shi ne ka yi ta da
wuri-wuri bayan shigar lokaci kafin a tsayar da sallar jam'i ta Asuba a masallaci.
Idan ka shiga masallaci har an tada sallar Asuba (farilla), za ka shiga jam'i
ne kai tsaye. Bayan an idar da sallar Asuba, za ka iya kawo ramuwarta nan take
(a ra'ayin wasu malaman kamar na shafi'iyya da hanabila), ko kuma ka bari sai
rana ta fito ta ɗaga sama (bayan shuruƙ).
Bukhari da Muslim da
Sunan Abu Dawuda sun ruwaito cewa: Haƙiƙa ya tabba ta cewa
barci ya rinjayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da Sahabbansa a wata
tafiya, ba su farka ba har rana tafito sai suka sallaci rak'ata yil fajr sannan
suka sallaci asuba.
A wata ruwaya akace
Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya umarci da a kira sallah sannan ya
sallaci raatiibat (rak'ata yil fajr), sannan ya umarci ayi iƙaamah bayan haka sai
ya sallaci farillah (sallar asuba).
Saboda haka ya
halatta a fara yin rak'ata yil fajr kafin sallar asuba idan an rasa jam'in
asuba ko da rana ta fito ne. Idan ba ka samu damar yin ta ba kafin sallar
asuba, za ka iya ramawa bayan an idar da sallar asuba, ko kuma mafi kyau bayan
rana ta fito ta ɗaga sama kamar
lokacin sallar walaha.
Wannan nafila tana da
muhimmanci sosai, domin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana
cewa: "Raka'a biyu na alfijir sun fi duniya da abin da ke cikinta
alkhairi." (Sahih Muslim).
Lokacin sallar wutiri
yana farawa ne da zarar an idar da sallar isha'i yana kuma karewa da ketowar
alfijir saboda fadin Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) sallar dare raka
biyu-biyuce, idan ɗayanku yana tsoran
kada yakasa farkawa ya yi raka'a ɗaya saita zamto masa wutirin Abunda yasallahta.
Bukhari (472)
Muslim yaruwaito
hadisi daga Abu Sa'idul khudry (Allah yakara masa yarda) daga Annabi
(Sallallahu Alaihi wasallam) ya ce: kuyi wutiri kafin sallar Asuba. Muslim
(754)
Imamu Ahmad yafitar
dahadisi daga Abu dauda da turmuzi hakim ya ingantashi daga karijata bin huzafa
(Allah yakara masa yarda) Ya ce: Lallai Allah yabaku wata sallah wacce tafi
muku Alkhairi samada jajayen rakuma, sai sahabbai sukace ya manzan Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) wacce sallah ce? sai ya ce: wutiri tsakanin sallar
isha'i zuwa hudowar alfijir.
Idan Akayi kiran
Sallar Assalatu Mutum baisamu damar ya yi wutiri ba zai jinkirtashi zuwa
lokacin sallar walaha saiya sallaci abunda yasawwaka agareshi, raka'a biyu ko
huɗu ko sama da haka,
yanda Al'adarsa take, idan kasaba raka'a uku kake daddare bakasamu kayi ba
darana za kayi raka'a huɗune sallama biyu,
idan raka'a biyar kake to inza ka ramata da rana raka'a shida za kayi sallama
uku, haka mutum zai auna yadunga lura dayanda yasaba dakuma ƙa'idar yanda zaiyi idan
darana zai rama, domin Annabi (Sallallahu Alaihi wasalla) yakasance yana yin
wutiri da raka'a goma sha ɗaya, idan wani Abu yashagaltar da shi daddare baiyi ba
baccine ko rashin lafiya ko wani Abun, idan zai ramata darana yana yin raka'a
goma sha-biyune, haka A'isha (Allah yakara mata yarda) tace kamar yanda Bukhari
da Muslim Suka ruwaito wannan kuma shi ne shari'a koyi da Annabi (Sallallahu
Alaihi wasallam). Maj-mu'u fatawa Bin baaz (11/300). Kamar yanda awani wajan
Shaik Bin baaz yasake fada a cikin majmu'u fatawa dinsa (11/305- 308). Hakama
shaik Usaimeen yabayyana a cikin maj-mu'u fatawa dinsa (14/114).
Hakika yatabba wasu
jama'a daka cikin sahabbai sunce babu laifi mutum ya yi sallar wutiri bayan
ketowar Alfijir harzuwa tayarda sallar asuba, daga cikinsu akwai ibnu mas'ud
Nisa'i yaruwaitoshi (1667) Albani ya ingantashi a cikin sahihun nisa'iy. da
Ibnu Abbas malik yaruwaito a cikin Muwadda (255) da Ubada bin Samit malik
yaruwaito a cikin muwadda (257) Allah yakara yarda dasu baki ɗaya.
Shaikul Islam Ibnu
taimiyyah Allah yajikansa darahama ya ce: Wanda bacci yadaukeshi baiyi wutiri
ba zaiyishi daga hudowar alfijir zuwa sallar asuba, kamar yanda Abdullahi Ɗan Umar ya aikata
haka da A'isha dasauransu, Abu dauda yaruwaito hadisi daga Abiy sa'idul khudry ya
ce: Manzan Allah (sallallahu Alaihi wasallam) ya ce: (wanda ya yi bacci baiyi
wutiri ba koya manta baiyi ba yasallaceshi idan yawayi gari koya tuna) ruwaya
ta saɓa daka Ahmad shin zai
rama shafa'i tareda wutiri?
Ingantacciyar magana shi
ne zai ramashi tareda shafa'i, hakika ya inganta daga Annabi (sallallahu Alaihi
wasallam) ya ce: Wanda bacci yadaukeshi baiyi wutiriba koya manta baiyi ba
yasallaceshi idan yatuna, wannan lokacinda daya tuna koya tashi daka bacci shi
ne lokacinsa) wannan yashafi sallar wajibi da kiyamullaili da wutiri da
Nafiloli ratibai. Duba fatawa Kubra (2/240).
Duk wanda mutum ya yi
dai-daine, idan ya rama wutiri kafin atayarda sallar asuba ya yi, idan kuma
yabari sai bayan rana tafito ta washe lokacin sallar walaha shi ma babu laifi.
Abisa wannan
yahalatta rama sallar wutiri bayan Sallar Asuba sai dai idan darana za ka rama
to sai dai kayi shafa'i banda wutiri ba za kayi raka'a ɗaya tilo kayi sallama
ba.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.