𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin keɓance ranar Juma’a domin zuwa ziyartar ’yan uwa yana da asali a Shari’a, Sannan akwai wani nassi da ya kwadaitar da yin hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Asalin ziyartar ’yan
uwa da sadar da zumunci abin so ne a Musulunci. Amma keɓance ranar Juma’a
musamman domin wannan ziyara, Babu nassin daya tabba tar da hakan.
Sheikh Ibn Baz R.A ya
bayyana cewa babu wani dalili da ya keɓance wani lokaci na musamman domin sadar da
zumunci; mutum zai iya sadar da zumunci a lokacin da ya samu dama.
Haka nan
Lajnatud-Da’imah ta bayyana cewa sadar da zumunci abu ne da Shari’a ta umarta,
amma ba a keɓance wani lokaci na
musamman domin hakan sai da dalili.
Allah S.W.T yake cewa
a cikin littafinsa mai girma
وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي
تَسَاءَلُونَ بِهِ وَالْأَرْحَامَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَيْكُمْ رَقِيبًا
Ku ji tsoron Allah
wanda kuke roƙon juna da Sunansa, kuma ku kiyaye zumunci. Lalle Allah
Ya kasance Mai kula da ku.
Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce
مَنْ
كَانَ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيَصِلْ رَحِمَهُ
Duk wanda ya yi imani
da Allah da ranar Lahira, to ya sadar da zumuncinsa. (Bukhari da Muslim).
Kaga dukkanin nassin
da muka amba ta ba'a kawo ranar juma'a kaɗai ko fifikon yin zumunci a cikinta ba.
Idan mutum ya ziyarci
’yan uwansa ranar Juma’a saboda ya samu dama, babu laifi. Amma idan ya yi imani
cewa ziyartar ’yan uwa ranar Juma’a sunnah ce ta musamman, to wannan yana buƙatar dalili, kuma
babu dalili sahihi da ya keɓance Juma’a da wannan ibada.
Allah ne mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.