Ticker

6/recent/ticker-posts

Jan Hankali Ga Masu Yin Gulma

TAMBAYA❓

Assalamu Alaykum

Allah ya jikan malam

A ja hankalin Yan'uwa musulmi gama da cin nama Yan'uwan da yanzu ya Zama fashion.

A ja hankalin Mutane cewa har yanzu Yana nan a matsayinsa na haram bai canzawa

Allah ya kare mu daga gulma

Aameen

AMSA:‼️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah,

Dan'uwa gaskiya ne abin da ka fadi kuma lallai ya kamata a rika jan hankalin al'umma a kai domin gulma wato gheebah KA ambaci dan'uwanka musulmi da abin da baya so a ce game da shi, ko a bayansa ko a gabansa, zunubi ne mai girma da Allah Madaukaki Ya amba ta a cikin Alkur'ani mai girma a Suratul Hujurat aya ta 12, inda Ya kwatanta shi da cin naman dan'uwanka wanda ya rasu, Allah Yana cewa "Kada wani daga cikinku ya yi gulmar wani, shin daya daga cikinku yana son ya ci naman dan'uwansa daya mutu? Za kuki wannan!" wannan kwatanci mai karfi yana nuna irin kaskancin da gulma yake da shi a wurin Allah, domin kamar yadda hankali da zabi'a suke kin cin naman gawar mutum, haka ya kamata hankalin musulmi ya ki wannan zunubi na harshe

Annabi ﷺ ma ya tabba tar da wannan lokacin da aka tambaye shi mene ne gulma, sai ya ce "Ka ambaci dan'uwanka da abin da yake ki," aka ce masa to in har gaskiya ne abin da nake fada game da shi fa, sai ya ce In har gaskiya ne abin da kake fada shi ke nan gulma, amma in ba gaskiya bane to ka riga kayi masa kazafi wanda hakan yake nufin ko gaskiya ne ko karya, magana a bayan mutum da ba zai so ba haramun ne, kuma abin takaici a zamanin yau mutane da yawa sun mayar da wannan babban zunubi wani irin nishadi ko fasahar zance da ake yi a tarukan biki, wurin aiki, cikin gidajen abinci, har ma wasu lokutan a cikin majalisun da ake ganin na addini ne, ba tare da sun tuna cewa Allah da ManzonSa sun haramta wannan aiki ba, kuma wannan shi ne babbar alamar da malamai suke yi wa gargadi, cewa zunubi na iya zama abin da ake ganin na yau da kullum ne har mutum ya manta girmansa a wurin Allah,

saboda haka ina jan hankalin dukkan Yan'uwa musulmi damu tsare harsunanmu, mu bar wannan mummunar dabi'a, mu tuna kalmar Manzon Allah ﷺ cewa Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya yi magana mai kyau ko ya yi shiru, Allah Ya taimake mu Ya kuma tsarkake harsunanmu daga gulma da sauran zunuban harshe,

Wallahu ta'ala aalam

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments