Ticker

6/recent/ticker-posts

Tuba Daga Barin Sallah Da Rama Sallar Da Aka Rasa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum barka da dare, malam. Ina da tambaya. Wata ce ba ta sallah tana wasa da sallah amma ta ji wa'azi da yaratsata yanzu kuma tana so ta tuba malam yanzu maye mafita shi ne idan ta tuba Allah zai karɓi tubanta kokuwa sannan kuma shin sai ta rama sallar da ba ta yi ba abaya kokuwa malam maye mafita dan Allah muna so ayimana karin haske muna gida malam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuhu.

Da farko, a sanar da wannan ’yar uwa cewa ƙofar tuba a buɗe take, kuma kada ta yanke ƙauna ko ta yi tunanin cewa saboda ta yi sakaci da sallah a baya Allah ba zai karɓi tubanta ba. Allah Maɗaukaki Ya ce

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

"Ka ce: 'Ya bayina waɗanda suka yi wa kansu Ɓarna ta yawan zunubi, kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya. Lalle Shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai, (Suratul-Zumar ayata 53)

Wannan aya tana ba da babban fata ga wanda ya dawo ga Allah da tuba ta gaskiya. Annabi ﷺ kuma ya ce: “Allah yana farin ciki da tuban bawansa fiye da farin cikin wani mutum wanda ya rasa abin hawansa a jeji, sannan ya same shi.” (Bukhari da Muslim).

Don haka idan wannan ’yar uwa ta ji wa’azi ya taɓa zuciyarta, ta gane kuskurenta, sannan ta yanke shawarar komawa ga Allah, wannan abu ne mai girma. Ta tuba yanzu, kada ta jira. Tubarta ta gaskiya ta ƙunshi abubuwa kamar haka: ta daina barin sallah, ta yi nadamar abin daya wuce, ta ƙuduri aniyar ba za ta sake komawa ga wannan sakacin ba, sannan ta riƙa kiyaye salloli daga yanzu. Idan kuma akwai haƙƙin wani da ta cutar saboda wannan al’amari, sai ta gyara abin da ya shafi haƙƙin.

Game da sallolin data bari a baya, malamai sun yi saɓani kan yadda wanda ya bar salloli da gangan zai yi. Mafi yawan malamai sun ce wajibi ne ta rama sallolin da ta sani cewa ta bari, tare da tuba ga Allah. Saboda haka, idan za ta iya ƙididdige adadin sallolin da ta rasa, ta fara ramawa a hankali tare da sallolin yanzu. Misali, tana yin sallar da take kanta a lokacin, sannan ta ƙara wata ko fiye daga cikin sallolin ramuwar da ta bari gwargwadon ƙarfinta, ba tare data sake barin sallolin yanzu ba.

Amma idan ba ta san adadin sallolin da ta bari ba, kada ta shiga damuwa har ta daina komawa ga Allah. Ta yi ƙoƙarin ƙididdige abin da tafi tsammani cewa ta bari, sannan ta fara ramawa gwargwadon wannan ƙididdigar. A lokaci guda kuma ta yawaita istigfari da salatin annabi Muhammad ﷺ da ayyukan alheri.

Abu mafi muhimmanci shi ne kada tace: “Na yi salloli da yawa a baya, ba zan iya gyarawa ba.” Wannan tunani bai dace ba. Ta fara daga yau. Idan ta mutu kafin ta gama abin da take ramawa bayan ta yi ƙoƙari da gaskiya, Allah Shi ne Mai sanin halin bawansa kuma Mai adalci da rahama. Kada kuma ta bar sallar yanzu saboda tana rama ta baya; sallar da take cikin lokacinta ita ce tafi gaba tarwa, sannan ta tsara ramuwar a hankali.

Saboda haka, mafita ita ce: ta yi tuban gaskiya yanzu, ta fara kiyaye salloli biyar daga wannan lokaci, ta rama sallolin da ta bari gwargwadon abin da ta sani ko ta ƙiyasta, kuma ta yawaita neman gafarar Allah. Kada ta yanke ƙauna, domin Allah Ya ce: “Lalle Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya.” (Zumar 39:53).

Allah Ya karɓi tubanta, Ya gafarta mata abin da ya gaba ta, Ya taimake ta wajen kiyaye sallah, Ya sanya wannan wa’azin da ta ji ya zama sanadin sabon farawa a rayuwarta.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments