𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu mal. Khamis shin wanda yake cikin janaba zai iya karanta Alkur'ani ko zai bari ne sai ya yi wankan tsarki?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Mafi yawan malaman Fiƙhu daga Mazhabobin
nan huɗu sun tafi a kan cewa
haramun ne ga wanda yake cikin janaba ya karanta Alkur'ani ko ya taɓa shi har sai ya yi
wanka tsarki bisa ga wani hadisi da suka kafa hujja da shi cewa babu abin da
yake hana Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) karatun Alkur'ani sai dai
janaba. Kuma sun kafa hujja da faɗin Allah a Suratul Waƙi'ah (aya ta 79):
لَّا
يَمَسُّهٗۤ اِلَّا الۡمُطَهَّرُوۡنَؕ
"Babu mai taɓa shi sai masu
tsarki".
Imamut Tirmizhiy ya
bayyana cewe: "Wannan fahimtar ita ce maganar mafi yawan ma'abota ilimi
daga cikin Sahabbai da Tabi'ai, da waɗanda suka biyo bayansu, kamar su Sufyanut
Thauriy, da Ibnul Mubárak, da Assháfi'iy, da Ahmad da Ishaƙ". Sunanut
Tirmizhiy (1/195).
Haka nan Alkásániy ya
ce: "Ba ya halasta ga mai janaba ya yi karatun Alƙur'ani a wurin
gamayyar malamai". Badá'i'us Saná'i'i (1/37).
Shaikhul Islam Ibn
Taimiyya ya ce: "Haka nan mai janaba ba zai karanta Alƙur'ani ba a fahimtar mafi
yawan malaman mazhabobin Fiƙhu guda huɗu, da ma wasunsu,
kamar yadda Sunnah ta yi nuni a kan haka".
Duba Majmú'u Fataawá
na Ibn Taimiyya (17/12).
Haramun ne ga mai
janaba ya karanta Alkur'ani, ko da kuwa kaɗan ne, har sai ya yi wankan tsarki. Ba a
yarda mutum ya taɓa littafin Alkur'ani
(Mus'haf) ko rubutunsa ba alhali yana da babban hadasi kamar janaba. Amma yana
iya yin zikiri (ambaton Allah), tasbihi, da kuma addu'a a dukkan halin da mutum
yake ciki, amma banda karatun kai tsaye daga Alkur'ani.
Ana son mutum ya yi
gaggawar yin wankan janaba domin ya koma cikin ibadarsa ta yau da kullum kamar
Sallah da karatun Alkur'ani. Amma idan zai jinkirta wankan (misali kafin ya
kwanta barci ko ya ci abinci), yana da kyau ya fara yin alwala domin rage
kaifin janabar.
Saboda haka ba ya
halasta ga mai janaba ya karanta Alƙur'ani har sai ya yi
wankan tsarki, wanda kuma ya yi karatu a cikin janaba ya yi kuskure a bisa
fahimtar mafi yawan malamai. Kuma wannan ita ce Fatawar da Lajna suka bayar a
mujallad na biyar shafi na 429.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.