𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam ya halaschin shafa a kafa yake lokacin da mutum ya sanya safa bayan ɗaura alwala. Bayan ya fita kuma sai fitsari ya kama mutum lokacin sallah, ya halatta ya yi shafa a kafarsa ya yin sake wata alwalar? An yi fitsari amma ba a cire safar ba, kuma sai a sake alwala kuma aka yi shafa sannan kuma aka yi sallah.
HUKUNCIN YIN SHAFA A KAN SAFAR
ƘAFA (SOCKS)
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Bisa Mazhabin Imamu Malik
(Rahmatullahi alaihi) shi ya ce bai halatta a yi shafa a kan safar Ƙafa. Da kuma duk abin da aka yishi da
tsumma. Shi awajensa ba a yin shafa sai dai a kan Huffi na fata, ko kuma
bandeji (ga masu rauni ko miki).
Haka shima abu Haneefah ya
ce bai halatta a yi shafa a kan safa ba. Sai dai daga baya ya dawo daga kan
wannan fatawar kafin rasuwarsa da kwanaki uku ko bakwai.
Amma Imamu Ahmad da Imamush
Shafi'iy da sauran Maluman Fiƙhu
irin su Sufyanuth Thauree, Auza'iy, da sauransu, duk suna ganin halascin yin
shafa a kan safa.
Imam Abu Dawud ya lissafo
sunayen Manyan Sahabbai waɗanda aka ruwaito cewa sun yi
shafa a kan safar Ƙafa.
Acikinsu akwai Imamu Aliy bn Abi Talib (karramal Lahu wajhahu) da Ibnu Mas'ud,
Al-Bara'u bn Aazib, Anas bn Malik, Abu Umamah, Sahlu bn Sa'ad, Amru bn Huraith,
Sayyiduna Umar bn Al-Khattab, Abdullahi bn Abbas, Ammar bn Yasir, Bilal bn
Rabah, Abdullahi bn Abi Awfa (Yardar Allah ta tabbata akansu baki ɗaya).
Amma kafin yin shafar ya
halatta gareka Malamai sun gindaya sharudda kamar haka
1. Ya zamanto Safar tana da
kauri yadda ba a ganin fatar Ƙafarka
ta cikinta.
2. Ya zamanto ta rufe maka
sawayenka har zuwa idon sawu.
3. Ya zamanto ka sanyasu ne
bayan kayi tsarki kayi alwala cikakkiya.
4. Ya zamanto ka sameta ne
ta hanyar halal. Imamu Ahmad ya ce bai halatta kayi da safar da aka sato, ko
aka kwace daga wajen mai ita ba.
Siffar yadda akeyi kuma, za
ka sanya tafin hannunka na dama daga sama, na hagu kuma daga Ƙasa sai ka shafo daga yatsunka zuwa
duga-duganka.
Idan za ka sake alwala bayan
fitsari ko ba-haya ko hutu ba sai ka cire safar ba. Za ka iya yin shafa akanta.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.