Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saduwa Da Mace Mai Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum, malam Khamis, meye hukuncin wanda ya sadu da matarsa a lokacin tana cikin jinin haila? Kuma shin akwai kaffara a kansa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Haramun ne mutum ya sadu da Matarsa tana cikin jinin haila ko nifasi, domin Allah madaukakin sarki ya ce

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ

Suna tambayar ka dangane da jinin haila ka ce musu kazanta ne, ku kauracewa matayen ku lokacin da suke cikin jinin haila, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki, idan suka yi tsarki ku je musu ta inda Allah ya umarce ku, Allah yana san masu yawan tuba kuma yana san masu tsarki. (Suratul Bakara Aya ta 222)

Bai halatta ga Miji ya jewa matar sa a lokacin da take cikin jinin haila ko Biƙi ba har sai ta yi wanka ta yi tsarki tukuna, sannan zai iya zuwa mata.

Idan mutum ya sadu da matar sa tana cikin jinin haila ko nifasi hakika ya aikata mummunan laifi, kuma zunubi ne babba daga cikin manyan zunubai, wajibi ne ya tuba, kuma kaffara ta wajaba gare shi a mafi ingancin maganganun malamai, shi ne zai bayar da Sadakar rabin dinare ɗaya ko kuma dinare ɗaya idan Mai Hali ne, ya bincika nawa Farashin Dinare ɗaya da Kuɗin naira Nigeria sai ya cire Kuɗin ya yi sadaka da shi ga mabukata wannan shi ne kaffarar sa kuma ya ji tsoron Allah kada ya sake aikatawa sa'annan ya ji tsoron Allah ya bayar da sadaƙa idan bai bayar anan duniya ba toh a Lahira zai bayar.

Imamun Nawawi acikin sharhin sahihu muslim (3/204) ya ce, Idan ya kasance da mantuwa ya yi ko ba shi da masaniyar hailar ta, ko kuma bai san hukuncin hakan ba, ko kuma tursasashi aka yi toh babu komai a kansa babu kaffara a kansa, idan kuma ya sadu da ita da gan-gan, ya san tana cikin haila sabida jaraba da fakewa da wai shi Hariji ne ko ai yana da Karfin Sha'awa idan bai yi ba zai samu matsala, kuma ya san haramcin saduwa da Mace mai haila da Biƙi, da so da zabin sa ya yi Jima'i da ke, hakika ya aikata babban zunubi daga cikin manyan zunubai, wajibi ne ya tuba.

Shaik bin Usaimin rahimahullah a cikin sharhin mumti'i (1/571) ya ce, Kaffara ba ta wajaba a kan wanda ya sadu da matar sa tana cikin haila ko nifasi sai da sharudda kamar haka

1. Yakasance ya san da hailar!

2. Ya kasance ya san haramcin saduwar!

3. Ya kasance cewa Yana son yin Jima'i da ita daman ba ruwan sa da yin jinin hailar ta kuma da zabin sa ya yi saduwar da ita bawai tilasta masa aka yii ba. toh dole ne ya yi Kaffara.

Idan ya jahilci haramcin, Ko hailar, ko mantuwa, toh akwai Kaffara, idan tursasa matar aka yi, ko kuma hailar ta zo suna cikin jima'in toh babu laifi a kansa kuma babu kaffara a kansa.

Maza ku tsoron Allah ku Sani cewa duk abun da Allah ya ce ma Haramun ne yin sa toh fa ya hana ka aikata abun ne domin kare lafiyar ka, wallahi idan ka fake da kai Hariji ne ko kuma ai Kai me Karfin Sha'awa ne idan ba kayi Jima'i da ita ba za ka samu matsala ka matsa Mata kana yin Jima'i da Matar ka alhalin tana Jinin haila, toh bayan Zunubin da ka ɗauka kana iya kamuwa da Ciwon da za ka yi ta amfani da magani amma ba za ka samu Sauki ba, don haka a ji tsoron Allah jinin haila ba zai wuce sati 1 ba ya ɗauke don haka wajibi ne a yi hakuri a bi dokokin Allah matukar ana son ganin me kyau idan an ƙi lallai bayan Zunubi za ka kamu da Ciwo. Kwayoyin cuta (bacteria) na iya shiga cikin mafitsaran namiji, wanda ke kawo zafi lokacin fitsari ko fitar farin ruwa.

Saduwa a wannan lokacin yana da haɗari ga lafiyar namiji da ita macen kanta, domin yana iya tura kwayoyin cuta sama zuwa mahaifa, wanda ke janyo ciwon marra mai tsanani kuma yana iya janyo matsalar rashin haihuwa nan gaba.

WALLAHU A'ALAM

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments