𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu'alaikum, Malam don Allah wata ce mijinta ya ce hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata babu kyau a Musulunci. Shin Malam ya abun yake? Haramun ne, ko kuwa tana iya hudawa tasa dankunne ta yi kwalliya da shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam
Warahmatallahi Wabarkatahu
Toh wannan yana
komawane zuwaga al'adar mutane, idan har a al'adar garinku wannan huda hancin
kawai ana ɗaukar shi ne
amatsayin kwalliya ba wai wata alama bace irinta mutanen banza kamar ace ya
shahara kawai a garinku fitsararrune suke huda hanci toh wannan abun agarinku
yinshi haramun ne. Amma idan kawai amatsayin kwalliyane kowacce mace tana iya
yinsa baya sawa ayi mata wani kallo toh a nan garinku shi ma yazama halal ne
kawai babu lefi.
An tambayi Sheikh
Ibnu Uthaimin akan wannan matsalar ta huda Hancı sai yake cewa: Huda Hancı zai
iya zama canza halittar Allah, amma idan Garin da matar da ta huda hancin take
ana yın ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi a yi hakan.
Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137.
Haka nan an tambayi
Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad akan haka a darasinsa da yake gaba tarwa a Haram,
sai ya ce babu laifi akan haka.
Malamai sunce hujin
hanci da hujin kunne duk ya halatta ga Matayen musulmai. Domin kuwa matan
Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam sun kasance suna yi kuma
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam bai hanasu ba.
A cikin FATHUL-BAREE
juzu'i na 10 shafi na 407-408, Al-Imam Ibnu Hajrin ya kawo wani hadisi wanda
Tabarany ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) Ya lissafta abubuwa
bakwai sunnah ne ga duk wata 'ya-mace. Daga ciki akwai hudar hanci da hudar
kunne.
Bisa Abin da ya gaba
ta ya halatta matar bahaushe ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun
da al'adarsu ce, saboda ya tabba ta sahaban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam
mata suna huda kunnansu suna sanya 'yan kunnaye Kamar yadda hadisin Bukhari mai
lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.
Amma malamai sunce
wajibi ne kowacce mace ta tabba tar da cewa ruwa yana ratsawa cikin wannan
hujin ya yin da ta zo yin wankan haila ko janabah.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.