𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, Mallam Khamis. Wasu daga cikin mata sukan rubuta wasu surori ko ayoyi a cikin Alkur'ani, sai a buɗe duk wata mimun a sa sunan mijin su ko saurayi da nufin su mallake su. Don Allah, mene ne hukuncin hakan? Mene ne hukuncin wacce ta yi wa mijinta da wacce ta rubuta mata, da kuma wacce ta yi wa wasu hanya aka rubuta musu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
To wannan irin
shaidanun matan sun fada tarkone daga cikin tarkunan bokaye. bokaye ne suke
saka rigar malunta sai su dinga ƙarya da Alƙur'ani suna yaudarar
mutane, musamman mata, sai suce ki rubuta wasu ayoyi wai wajem mimun sai ki
budeshi kamar dai yadda kika fada, to duk wanda za kiji yana baki irin wayannan
ababen to ba malami bane, boka ne, kuma sharri ne yakeso ya koya muku. Dan haka
sai kuyi watsi da su, so sukeyi su rabaku da Allah su hadaku da shaidan.
Haɗa rubutun Alƙur'ani da sunan miji
ko saurayi domin janyo hankalinsa ko soyayyarsa ya yi daidai da abin da ake
kira TIWALAH (sihirin soyayya). Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya
fada a hadisi ingantacce cewa: "Lallai duba, da laya, da Tiwalah (sihirin
soyayya) shirka ne." (Abu Dawud).
Duk abin da mutum zai
yi don juyar da zuciyar wani, in dai ba addu'a bace to haramun ne. Idan ana son
soyayyar miji, ana yin addu'a ta gaskiya ga Allah, da kyautata masa, da kwalliya,
ba tare da an juya hankalinsa ta hanyar asiri ko rubutu na musamman ba.
Babu wani mallakar da
za ku samu ta wannan hanyar, ko za ku samu to sai dai kusamu na dan lokaci
kafin shaidanun naku su juya baya sai kuma komi ya zo ya lalace kuma.
Ladabi da biyayya da
kyautata mu'amala gamida kiyaye dokokin ubangiji sune manyan hanyoyinsa sukesa
miji ya ƙaunaceki, kamar yadda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
ya ƙaunaci
khadijat har bayan mutuwarta, idan yana zaune ya hangi wata daga cikin ƙawayenta za su wuce
to shi da kanshi ze tashi yaje ya tarbosu saboda tunawa da abin da ƙawarsu ta yi mishi na
kyautatawa, kai sai da takai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yakan shirya
abinci na ƙasaita ya yanka rago kawai ya rarrabama ƙawayen khadija,
abayan mutuwarta akayi wannan.
Aisha duk ƙaunarda yake mata,
sadda tafadi wata magana mara dadi ga khadija, wata guda Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya kwashe yana kausasa mata baƙar magana, shin ke
kin isa ki samu irin wannan mallakar da khadija ta yi wa Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) dan gatan Allah????
Toh danme za kije
kina ba ta lokacinki agun bokaye suna amshe miki yan kudadenki suna rabaki da
tauhidi, kuma na san ba za ki samu rabi-rabin matsayinda khadija ta samu awajen
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ta dalilin biyayya da take masa, amma ke
kuwa kin kama hanyar rabuwa da Allah wanda shi ne yake cusa ƙauna da soyayya
tsakanin mutane kin tafi kina nemanta ta hanyarda ba za ki samuba, dan haka
lallai mata ku canza tunani.
Kyawawan ɗabi'u da kyautata
mu'amala su ne tushe na gaskiya da mutum zai mallake zuciyar abokin rayuwarsa,
matuƙar babu kyakkyawar mu'amala a tsakanin mata da miji, to
tabbas komin siddabarun da boka zai ba mutum ba zai taɓa samun nasarar
mallake abokin rayuwarsa ba, in ma ya samu to na ɗan lokaci ne aka yi masa talala kafin
Allah ya kama shi.
sannan kuma ga
fuskantar mummunar makoma a wurin Allah ga wanda yake harka da bokaye da ƴan tsibbu, ko da mai
harka da bokaye ko ƴan tsibbu ya ga kamar ya ci nasara, to ya sani ba nasara
ya samu ba, talala Allah yake masa domin ya turmutsa shi a Jahannama, saboda
duk wanda ya mutu yana mu'amala da waɗannan miyagu to lallai zai haɗu da fushin Allah.
Manzon Allah (sallal
Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) Ya ce "ba ya cikinmu duk wanda yaje
chamfi ko kuma akayi masa chamfi, ko ya yi bokanci ko akayi masa bokanci. ko ya
yi tsafi ko akayi masa tsafi dominsa. Duk wanda yaje wajen boka kuma ya yarda
da abin da ya gaya masa, to ya kafirce wa abin da aka Saukar Wa Annabi Muhammad
(Sallallahu Alaihi Wasallam)". (Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi da isnadu
mai kyawu).
Don haka duk wacce
taje wajen boka aka ba ta wani abu ta yi amfani da shi ko kuma ta sayar wa waɗansu matan sukayi
amfani da shi, to tabbas gaba dayansu laifin ya shafesu (wato kafirci kamar
yadda hadisin ya bayyana).
Mata kuji tsoron
Allah ku fahimci cewa samun mallakar zuciyar miji ta hanyar amfani da layoyi ko
kulle-kullen tsafi ba samun yardar Allah bane. Hasali ma hanya ce ta kafirci da
gushewar imani. Amma za ku iya samun mallakar mazajenku ta hanyar ladabi da
biyayya da girmama miji tare da gyaran jiki da kyautata halaye.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.