𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslamu alaikum malam Allah ubangiji ya kara lafiya da nisan kwana masu albarka da imani. Dan Allah malam ina tambaya akwai aure a tsakanin ɗan kanwar uwa da yar yayar uwa na gode.
HUKUNCIN AURE TSAKANIN ƊAN ƘANWAR
UWA DA ‘YAR
YAYAR UWA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam
warahmatullahi wabarakatuh.
Aure yana halatta tsakanin ɗan
kanwar uwa da ’yar yayar uwa, domin basa cikin waɗanda
Allah Ya haramta aurensu. Ɗan
kanwar uwa da ’yar
yayar uwa ba ’yan
uwa ne na jini waɗanda shari’a ta haramta
aurensu ba, don haka kowannensu na iya auren ɗayan,
matuƙar babu wata dangantaka ta shayarwa ko
wani dalili na shari’a da
zai hana auren.
Allah Maɗaukakin
Sarki Ya bayyana waɗanda aka haramta aure a
cikin Suratun Nisa’i, inda Ya ce
حُرِّمَتْ
عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ
وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي
أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُم مِّنَ الرَّضَاعَةِ...
An haramta muku uwayenku, da
’ya’yanku mata, da ’yan’uwanku mata, da innoninku (’yan’uwan mahaifi), da
’yan’uwan mahaifiyarku mata, da ’ya’yan ’yan’uwanku maza, da ’ya’yan
’yan’uwanku mata, da uwayenku mata waɗanda
suka shayar daku, da ’yan’uwanku mata ta hanyar shayarwa...” (Suratun Nisa’i
ayata 23)
A cikin wannan ayar Allah Ya
ambaci waɗanda aka haramta wa mutum aure, kamar
uwa, ’ya, ’yar’uwa, ’yar’uwan uba, ’yar’uwan uwa, ’yar ɗan’uwa
da ’yar ’yar’uwa, da kuma waɗanda aka haramta saboda
shayarwa. Amma ’yar yayar uwa ko ’yar kanwar uwa ba ta cikin waɗannan
waɗanda
aka haramta, saboda haka a asali aure tsakaninsu halal ne.
Saboda haka, idan aka ce ɗan
kanwar uwa zai auri ’yar yayar uwa, babu wani haramci a cikin hakan. Haka kuma,
ba muhanramai ba ne ga juna kafin aure, don haka dokokin mu’amala tsakanin
namiji da mace waɗanda ba mahramai ba suna nan
a tsakaninsu. Sai dai idan akwai dangantakar shayarwa da ta sanya su ’yan uwa
ta shayarwa, to a wannan lokacin ba za su iyayin aure ba, domin Annabi (SAW) ya ce: “Abin da ya haramta
saboda shayarwa shi ne abin da ya haramta saboda nasaba.” (Sahih al-Bukhari da
Sahih Muslim).
WALLAHU A‘LAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.