𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Mene ne hukuncin jinin Istihada ga mace? Shin za ta yi Sallah ko azumin na fila sannan mijinta zai sadu da ita lokacin da take jinin Istihada? Kuma yaya tsarkinta yake?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam
warahmatullahi wabarakatuh.
Jinin Istihada baya ɗaukar hukuncin jinin
Haila. Saboda haka, mace mai Istihada za ta ci gaba da yin Sallah da Azumi,
Sannan mijinta in yaso zai iya saduwa da ita. Domin tana cikin hukuncin mace
mai tsarki.
Manzon Allah ﷺ ya ce
إِنَّمَا
ذَلِكِ عِرْقٌ وَلَيْسَ بِالْحَيْضَةِ، فَإِذَا أَقْبَلَتِ الْحَيْضَةُ فَدَعِي
الصَّلَاةَ، وَإِذَا أَدْبَرَتْ فَاغْسِلِي عَنْكِ الدَّمَ وَصَلِّي
Wannan jinin na wata
jijiya ne, ba jinin Haila ba. Idan lokacin Haila ya zo, ki bar Sallah; idan ya
wuce, ki wanke jinin daga jikinki sannan ki yi Sallah.
Saboda haka, mace mai
Istihada za ta yi Sallah kuma za ta yi Azumi. Za ta wanke wurin da jinin ya
fito, ta sanya abin da zai taimaka wajen hana jinin yaɗuwa, za ta dinga
alwala a lokacin da Sallah ya shiga.
Allah ne mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.