Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mafarki Mai Ban Tsoro Bayan Barin Shafa'i Da Wutiri Yana Da Wata Ma'ana?

TAMBAYA

Assalamu alaikum malam, barka da wuni. Malam, Allah ya taimaka, ya ƙara ilimi mai amfani. Malam, ɗan Allah tambayata ita ce: Duk lokacin da na kwanta barci ban samu yin shafa'i da wutiri ba, sai na yi mafarkin wani ƙurji ya fito min a farce yana fitar da ruwa farare, kuma wasu ƙwari suna fitowa a cikinsa, sai na ji tsoron abin. Na biyu kuma, na kwanta ban yi shafa'i da wutiri ba kuma, sai na yi mafarkin kaza tana sarata a ƙafa. To malam, kuma idan zan kwanta ina yin azkar. Malam, mene ne shawara? Na gode.

AMSA:‼️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

'Yar'uwa, mafarki ba koyaushe yake zama saƙo ko alamar wani abu ba. Annabi (SAW) ya baya yiana cewa mafarkai sun kasu gida uku: akwai mafarki mai kyau daga Allah, akwai mafarkin da Shaiɗan ke jefa wa mutum domin ya tsoratar dashi, sannan akwai mafarkin da yake fitowa daga abubuwan da mutum yake ta tunani a rayuwarsa.

Dangane da mafarkan da kika ambata na ƙurji, ruwa, ƙwari ko kaza tana zakwata ƙafa, ba za a iya fassara su da tabbaci ba, kuma bai dace a gina hukunci a kansu ba. Idan mafarkin ya kasance mai ban tsoro ko damuwa, to mafi kusanci shi ne ya kasance daga Shaiɗan domin ya razana ki.

Abinda Annabi (SAW) ya koyar damu shi ne: idan mutum ya yi mafarki mara daɗi, ya nemi tsarin Allah daga Shaiɗan da sharrin abin daya gani, ya tofa busasshen yawu kaɗan sau uku zuwa hagunsa, kada ya ba da labarin mafarkin ga wanda zai iya fassara shi ba tare da ilimi ba, sannan ya juya gefen da yake kwance ko ya tashi ya yi sallah idan hakan ya yi masa sauƙi. Da izinin Allah, wannan mafarkin ba zai cutar dashi ba.

Game da barin Shafa'i da Wutiri, yana da kyau ki dage wajen yin su kafin kwanciya idan kina jin tsoron ba za ki tashi ba, domin Wutiri sunnah ce mai girman falala. Haka kuma ki ci gaba da karanta azkar na kwanciya, kamar Ayatul Kursiya yiu, Suratul Ikhlas, Falaƙ da Nas sau uku, sannan ki yi addu'o'in kwanciya da suka tabbata daga Annabi (SAW).

Saboda haka, kar ki firgita da irin waɗannan mafarkai, ki ci gaba da kiyaye salloli, Shafa'i da Wutiri, da azkar na kwanciya, ki kuma yawaita roƙon Allah Ya baki kariya daga Shaiɗan da duk wani sharri. Allah yasa mudace 🙏

Wallahu ta'ala aalam

✍️MT ABDULLAHI

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments