𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barka da wannan lokaci, malam. Ni ce na kira ka a waya ɗazun. Allah ya ƙara wa malam lafiya da nisan kwana. Malam, dama tambaya ce zan yi: Na kasance ina yawan mafarkin na rabu da mijina na bar shi. Kamar sharrin shaɗan ne, ban damu ba, sai na ga na ci gaba da yi. Tun ban damuwa har abun ya fara damuna, domin jiyama har takarda ta ya ba ni, kuma duk a mafarkin ne. Shi ne nake tambaya a ɗan duba min, malam. Gaskiya na damu, Allah ya ƙara basira.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Yawan mafarkin rabuwa
da miji na iya zuwa ne sanadiya yiar tsoron da ke zuciyarki, yawan tunani, ko
kuma wani sakamako na damuwa da shaidan ke kokarin jefa miki a zuciya don ya
bace miki da kwanciyar hankali.
A fassarar malamai da
yawa na Musulunci kamar IBN SIRIN ba lallai yana nufin rabuwar aure ta zahiri
ba, a mafi yawan lokuta yana nuna babban canji a rayuwa, gushewar damuwa, ko
sauyin yana yi. Mafarkin yana nuni da cewa rayuwarki za ta fuskanci gagarumin
sauyi. Wannan zai iya zama barin wani tsofaffin halaye ko canza wurin zama ko
gida. Fassarar tana canzawa dangane da yana yin da mace take ciki a zahiri.
Idan mace tana cikin
wata damuwa ko matsalar rayuwa, mafarkin rabuwa ko saki na iya zama alamar
karshen wannan damuwar da samun sassauci. Idan mace ba ta da lafiya sannan ta
yi mafarkin an sake ta saki guda (ɗaya), malaman fassara sun ce hakan na nuni da
samun waraka daga rashin lafiyar.
Wani lokacin mafarkin
baya ɗauke da wata fassara
ta daban, illa ruda zuciya da tsoron abin da zai iya faruwa. Idan kina yawan
fargaba ko fuskantar matsalolin kishi a gida, ko tsoron rasa aurenki ko akwai
wata ‘yar rashin jituwa tsakaninki da mijinki, hankalinki na iya juyawa zuwa
wannan mafarkin.
Idan mafarkin ya zo
da firgici ko ɓacin rai mai tsanani,
yana iya zama daga cikin hargitsawa da tsoratarwa irin ta Shaidan domin ya dasa
gaba tsakanin miji da mata. Kamar yadda kika fada, Shaiɗan yana son raba
tsakanin miji da mata don haka yana iya amfani da mafarki domin ya jefa muku
fargaba, zargi, da ɓacin rai a
tsakaninku.
Ki duba ko akwai wata
'yar matsala ko rashin fahimta tsakaninki da mijinki a fili, sannan ku zauna ku
gyara ta cikin kwanciyar hankali. Sannan Ki tabbata kina Alwala kafin ki
kwanta. Ki karanta Ayatal Kursiya yiu, Suratul Ikhlas, Al-Falaƙ, da An-Nas, sannan
ki tofa a tafukan hannunki ki shafa a jikinki. Idan kika yi mummunan mafarki
kika farka, ki tofa hagu sau uku (ba tare da miyau ba) ki yi addu'ar neman
tsari daga sharrin Shaiɗan da sharrin abun da
kika gani (A'UZU BILLAHI MINASH-SHAIƊANIR-RAJIM WA MIN
SHARRI HAZIHI-RU'YA).
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fada cewa idan mutum ya yi mummunan mafarki, kada
ya fada wa kowa, domin yin hakan mafarkin ba zai cutar da shi ba. Idan kika
tashi daga irin wannan mafarkin, ki juya ki koma wani ɓangaren daban na
kwanciya.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.