Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Kudun Gusau, Alh. Sulaiman Ibrahim

Jagora:

Ya shiryi zama daku mutanen kudu,

Duk ku kiyaye hali nai

Y/Amshi:

Baya cema bara nai

tahi samo man rance,

Baya cewa yau wane ina kai ma malka,

Babu mai tcira wargi

yaji tsoron ɗamri nai.

Haka dai ☝️☝️Makaɗa Alh. (Dr.) Ibrahim Narambaɗa Tubali ya faɗa a faifansa na Marigayi mai girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Gusau wato Sarkin Kudun Gusau, Alh. Sulaiman Ibrahim mai amshi:

"Mai Gusau raba kaya,

 Ba a kaimaka wargi,

 Mai rabo da yawa

 gamda'aren S/Gobir".

Shi ne Sarkin Gusau/Uban Ƙasar /Hakimin Gundumar Gusau na 13 tun daga Malam Muhammadu Sambo Dan Ashafa da ya ƙirƙiri Gusau ya kuma yi mulki daga 1806 zuwa wafatinsa a shekarar 1827 (shi Malam Muhammadu Sambo Dan Ashafa).

Shi dai ne Sarkin Gusau na 6 daga cikin tsarin Sarakunan Gusau da ba daga gidan Mal. Muhammadu Sambo Dan Ashafa suka fito ba, wato tun daga shekarar 1917 da aka fara naɗa wasu mutane daga Sakkwato ana kai su a matsayin Sarakuna /Uwayen Ƙasar /Hakiman Gundumar Gusau kuma shi ne na ƙarshe a wannan tsari domin bayan rasuwarsa a ranar 1/7/1984 sarautar ta dawo gidan Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Ashafa ya zuwa yau.

A waɗannan ɗiyan waƙa ☝️☝️Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya taskace wasu daga cikin kyawawan halayen Sarkin Kudun Gusau Sulaiman Ibrahim.

Yana bayyana cewa koda aka kawo shi a matsayin Sarki a Gusau ya shiryawa zaman sarauta (Narambaɗa ya kira mutanen Gusau da mutanen kudu) domin Gusau tana kudu maso gabas da Sakkwato ne.

Gusau tana da attajirai sosai da suka shahara a lokacin da aka naɗa shi sarautar garin a ranar 1-8-1951. Amma kamun kai da riƙe girma irin nasa ya hana masa neman buƙata koda ta rance ne ballantana ya yi kwaɗayin abun hannun talakansa.

Ibrahim Narambaɗa ya ci gaba da nuna halin dattako da tawali'u da zuhudu na wannan Basarake ta hanyar nuna duk yadda tsanani ya kai bai taɓa nuna zuwa gidan wani mai abun hannunsa daga cikin talakawan dake ƙarƙashin ikonsa ba domin ya taimaka masa da abinci koda kuwa an shiga yanayin malka/marka, wato a lokacin damina da ake tsulla ruwan sama kamar dai watan Agusta da Bahaushe ke kira watan ruwa( a wasu yankuna na Jihar Zamfara ana kiran wannan yanayi da malkac ci kashin ka) saboda sama ruwa ƙasa ruwa ne, ko kana da hatsi a rihewa /rumbu /sito idan ba a buhu yake ba ruwan da ake yi bazai bari ka samu damar a sussuka maka shi ba ballantana ka samu na kalaci.

A daidai irin wannan yanayi ne masu ɗan ƙaramin ƙarfi da maras sa dangana da kwaɗayi ke ƙoƙarin zuwa gidajen masu abun hannunsu /attajirai da waɗanda ke da abinci a ajiye domin su samu fita daga cikin wannan mawuyacin hali. Wannan shi ne dalilin da yasa ake faɗar "Zan kai wa wane malka/marka".

Saboda zamansa kamilallen mutum wanda ya san daga gidan da ya fito sai Makaɗa Narambaɗa ya bayyana cewa "Baya cewa yau wane ina kai ma malka". Tun da ya kame kansa daga abun hannun talakawansa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ladabtar da duk wanda ya saɓa dokoki ko ƙa'idar zamantakewar yau da kullum ba.

An haifi Marigayi Alhaji Sulaiman Ibrahim a shekarar 1909 a garin Isa ta Jihar Sakkwato. Mahaifinsa shi ne Sarkin Gobir /Uban Ƙasar /Hakimin Gundumar Isa Malam Ibrahim ɗan Sarkin Gobir na Isa Umaru ɗan Sarkin Musulmi Aliyu ƙarami ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi.

Yayi sarautar Gusau daga ranar 1-8-1951 zuwa wafatinsa a ranar 1-7-1984.Ya bar matan aure da ya'ya da jikoki da tattaɓa kunne masu dama.

Daga cikin ya'yansa akwai mai girma Ɗangaladiman Sakkwato, Alh. Shehu Sulaiman da Bunun Sakkwato, Alhaji Aliyu Sulaiman da kuma Ɗan Amar na Sakkwato, Alh. Yusuf Sulaiman.

Marigayi mai girma Sarkin Kudun Gusau Alhaji Sulaiman Ibrahim ne a wannan hoto.

Allah SWT ya jaddada masa rahama shi da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Fiyayyen Halitta Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

Daga taskar

Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.

13/07/2026.

Post a Comment

0 Comments