𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As Salamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakatuh. Da fatan malam yana lafiya. Please, malam ya halatta a sa hoton mamaci a social media kamar a profile ko status?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
A Musulunci, malaman
addini sun bayyana cewa bai halatta a riƙa saka hotunan
mutane, ciki har da na mamata, a shafukan sada zumunta kamar DP (Profile) ko
Status ba.
Abin da Malamai suka
tabbatar a nan shi ne: Idan dai ba da larura (kamar na passport don shiga
makarantu ko neman aiki ko fita ƙasashen waje da
makamantansu) ba, musulmi ba ya yin harka ko mu’amala da hotuna na
abubuwa masu rai (kamar mutum, dabba, tsuntsu, ƙwaro da sauransu), ko
masu inuwa ne (kamar sassaƙaƙƙu ko ginannu), ko
marasa inuwa (kamar waɗanda aka zana da
hannu ko aka ɗauka da kyamara
(camera). Saboda irin kausasa magana da tsawa mai tsanani da shari’a ta yi a
kan haka:
Abu ne sananne cewa:
Hotuna su ne dalilin farko na kaucewar mutane daga kan hanyar Allaah tun a
zamanin Annabi Nuhu (Alaihis Salaatu Was Salaam). Mutanen zamaninsa su ne suka
sassaƙa hotunan manyan malamansu domin tunawa da su a farko,
amma daga baya sai suka zama abubuwan bauta ba Allaah ba!
Daga ƙarshe kuma da aka
turo Manzon Allaah Mai wa’azi na farko a duniya: Annabi Nuhu (Alaihis
Salaam) domin ya hana su, sai kawai suka kangare kuma suka taurare, har ma suka
riƙa
faɗa wa mutanensu, kamar
yadda Allaah Ta’aala ya ambato daga gare su:
وَقَالُوا
لَا تَذَرُنَّ آلِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ
وَيَعُوقَ وَنَسْرًا
Kuma suka ce: Kar ku
yarda ku rabu da Waddu da Suwaa’u da Yaguthu da Ya’uqu da Nasru.
A ƙarshe ƙissar dai hallaka ce
ta same su, kamar yadda Allaah ya ce:
مِمَّا
خَطِيئَاتِهِمْ أُغْرِقُوا فَأُدْخِلُوا نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا لَهُمْ مِنْ دُونِ
اللَّهِ أَنْصَارًا
Saboda irin
laifuffukansu sai aka nutsar da su a cikin ruwa kuma aka shigar da su cikin
Wuta, kuma ba su samu wani mataimaki ba a bayan Allaah.
Sannan a cikin
Hadisai sahihai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi
tsawa a kan al’amuran hotuna, kuma bai bambance ba a tsakanin nau’ukansu, kamar
inda ya ce:
أَشَدُّ
النَّاسِ عَذَاباً الَّذِينَ يُضَاحُونَ بِخَلْقِ اللهِ
Mafiya samun tsananin
azaba daga cikin mutane su ne: Waɗanda suke kwaikwayon halittar Allaah Haka
kuma inda ya ce:
أَشَدَّ
النَّاسِ عَذَابً يَوْمَ الْقِيَامَةِ الْمُصَوِّرُونَ، يُقَالُ لَهُمْ أَحْيًون
مَا خَلَقْتُمْ
Mafiya samun tsananin
azaba daga cikin mutane a Ranar Ƙiyamah su ne: Masu
yin hotuna, za a ce da su: Ku raya irin abubuwan da kuka halitta.
Al Imamul Bukhaari
(3226) da imam Muslim (2106) sun ruwaito hadisi daga Abu Talhah (Allah ya ƙara masa yarda) cewa
Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce; “Mala'iku basa shiga
gidan da da akwai hoto acikinsa.”
Al Imamul Nawawi
(Allah yaji kansa da rahama) ya ce: Malamai sun ce: Dalilin da ya sa basa shiga
gidan da akwai hoto acikinsa saboda akwai zunubi mai raɗaɗi, kuma gasa ne da
halittar Allah.
Don haka, ba daidai
ba ne musulmi ya riƙa amfani da hotunan mutane (rayayyu ko matattu, manya ko
yara, kuma maza ko mata, haka ma sauran dabbobi ko tsuntsaye da sauransu) a
cikin ‘social media’ kamar yadda aka
bayyana a cikin tambayar, ko kuma a wani wurin da ba wannan ba, in dai ba da
wata larura mai ƙarfi ba.
Maimakon sanya
hotunansu wanda zai iya zama laifi a shari'a, ana ƙarfafa musulmi da su
maye gurbinsa da; Yin musu addu'ar neman rahamar Allah da gafarar zunubai.
Yimusu sadaka domin samun ladan da zai kai gare su.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.