Ticker

6/recent/ticker-posts

Bin Umurnin Uwa A Saki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mahaifiyarsa ta umurce shi ya sake ni, amma dayake bai iya rubutu ba sai matarsa (kishiyata) ta rubuta. Da ya miƙa mini takardar sai na ga saki uku ne, shi kuma ya ce saki ɗaya ne kawai ya ce. To, mene ne matsayin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Bin umurnin iyaye a wurin sakin aure ba wajibi ba ne, kuma saɓa musu a kan haka ba laifi ba ne, sai fa ko in akwai wani dalili na shari’a da suka dogara a kansa. Amma hadisin nan sahihi da Abu-Daawud (5138) da At-Tirmiziy (1189) da Ibn Maajah (2088) suka riwaito daga Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ cewa:

كَانَتْ تَحْتِى امْرَأَةٌ وَكُنْتُ أُحِبُّهَا ، وَكَانَ عُمَرُ يَكْرَهُهَا ، فَقَالَ لِى : طَلِّقْهَا ، فَأَبَيْتُ ، فَأَتَى عُمَرُ النَّبِىَّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - فَذَكَرَ ذَلِكَ لَهُ ، فَقَالَ النَّبِىُّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - : « طَلِّقْهَا »

Ya kasance ina da wata matar aure wadda nake son ta, shi kuma Umar yana ƙin ta. Don haka sai ya ce mini: Ka sake ta, ni kuma na ƙi. Sai Umar ya tafi wurin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya faɗa masa haka, sai Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce mini: Ka sake ta.

Malamai sun ɗauki wannan wata mas’ala ce da ta shafi wannan matar ita kaɗai, ba abu ne da ya shafi kowa da kowa ba. Shiyasa a lokacin da wani ya kawo kuka wurin Al-Imaam Ahmad _(Rahimahul Laah)_ a kan cewa mahaifinsa ya umurce shi da ya saki matarsa, sai ya ce masa: Shin babanka kamar Umar ya ke?!

A taƙaice dai duk lokacin da wani daga cikin iyaye ko dukkansu suka nemi ɗa ya saki matarsa, ba a gaggawan bin maganarsu, har sai lokacin da aka binciki matsalar kuma aka tabbatar da gaskiyar matsayinsu. Kamar idan aka fahimci cewa cigaba da zamansu tare zai raunana ko ya rushe addinin ɗayansu ko dukkansu.

Wanda aka tilasta masa a wurin saki, sakin bai auku ba. Domin wanda ba shi da zaɓin ransa, kamar wanda aka tilasta masa, ko mai maye, ko ruɗaɗɗe, ko wanda yake cikin matsanancin fushi, malamai sun rinjayar da rashin aukuwar sakinsa ne saboda faɗin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):

لَا طَلَاقَ وَلَا عِتَاقَ فِي إِغْلَاقٍ

Babu saki ko ’yantawa a cikin rufewar hankali ko tilasci. _(Sahih Abi-Daawud: 1919)._

Bai kamata kishiya da taimaka wurin sakin kishiyarta ba. Domin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya hana hakan a cikin hadisinsa sahihi a cikin Al-Bukhaariy da Muslim cewa:

« لاَ تَسْأَلِ الْمَرْأَةُ طَلاَقَ أُخْتِهَا ، لِتَسْتَفْرِغَ صَحْفَتَهَا ، وَلْتَنْكِحْ ، فَإِنَّمَا لَهَا مَا قُدِّرَ لَهَا »

Kar wata mace ta nemi a saki ’yar uwarta domin ta ƙarar da akushinta, ta yi aurenta kawai. Domin dai tana da abin da aka ƙaddara mata ne kawai.

Don haka, abin da wannan mijin ya yi nufi a zuciyarsa kuma har ya furta da bakinsa, shi ne abin lura kawai, ba abin da wani ya rubuta ba. Watau dai, saki guda ne kawai a kan wannan matar wanda kuma yana iya dawo da ita ta hanyar kome, a duk lokacin da ya so kafin cikar iddarta.

Shi kuma alƙali bayan ya bincika kuma ya tabbatar da gaskiyar abubuwa, yana iya yi wa mahaifiyar nasmatariha da gargaɗi yadda ya dace. Ita kuwa wannan yana da ikon horar da ita a kan abin da ta yi na saɓa wa hadisin, da ƙoƙarin raba musulma da gidan aurenta da haramta mata aure da mijin da Allaah ya halatta mata bai haramta ba.

Allaah ya datar da mu gaba-ɗaya ga abin da yake so kuma yake yarda da shi.

 _Wal Laahu A’lam._

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments