Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Yana Son Kiss Amma Ba Ya Tsaftace Bakinsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis barka da yamma da fatan ka wuni lafiya. Malam Khamis muna godiya sosai yadda kake amsa tambayoyin mu, Allah Ya saka da alheri. Tambaya ta a nan shi ne; Mijina yake son kiss ni kuma ba na yi masa saboda warin bakinsa, ba ya tsaftace bakinsa shi ne yake jin haushina, ni kuma abin yana damuna ina ganin kamar na shiga hakkinsa shi ne nike so na ji mene ne hukuncina kuma ya zan yi na samu mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Wannan matsalar na bukatar aiki da hikima da kuma hakuri. A addinance, ba zaki shiga zunubi ba idan kin ki yi masa kiss saboda wari ko rashin tsaftar bakinsa, domin kowa zai kyamar hakan. Amma mafita ita ce ki samu wata dabara ta musamman domin gyara shi ba tare da kin ɓata masa rai ba. Kada ki nuna masa kyamar sa a duk lokacin da ya zo kusa da ke. Hakan na iya sa shi fushi ko tunanin ba ki kaunar sa.

Ki samu lokacin da kuke cikin natsuwa da walwala, ba a lokacin da kuke shirin saduwa ba, ki yi masa magana cikin nuna ƙauna da kulawa. Maimakon ki nuna laifin sa, sai ki rika yi masa kyautar abubuwan da za su taimaka wajen tsafta ba tare da ya gane cewa shi kike nufa ba. Misali: Ki rika siyo masa tsumburbura masu kamshi (mint) ko cingam (chewing gum) masu kashe warin baki, kuna ci tare. kina iya sayo masa abubuwan wanke baki (misali: man goge baki mai kamshi da tuntube ko ɗan wanke bakin (mouthwash) da goge baki (toothbrush) a matsayin kyauta mai kyau ki bashi.

Idan har yana da wari mai tsanani, zai iya zama matsalar lafiya ce (kamar coughs, matsalar hakori, ko ciwon ciki). Cikin dabara da nuna kulawa, sai ki bashi shawarar cewa ya je asibiti a duba lafiyar bakinsa ko hakoransa.

Maza da yawa suna matukar bukatar kulawa da shauki daga matansu, kuma wannan na daya daga cikin hanyoyin da ke kara karfin soyayya a cikin aure. Hakan yana nufin yin amfani da wadannan matakai na gyara zai taimaka wajen cike wannan gurbin cikin ruwan sanyi.

Idan kika bi wadannan matakai baiyi aiki ba kawai ki fito fili ki faɗa masa gaskiya, Ki nuna masa cewa kina matukar son yi masa wannan kiss din, amma wani lokacin warin baki ko rashin tsafta yana hana ki. Ki ce masa: "Miji na, ina son na rika yi maka kiss yadda kake so, amma don Allah ka taimaka ka rika wanke baki da goge hakoranka, domin hakan zai fi sani na ji dadin jikin ka." Ki nuna masa cewa ke ba kiss ɗin ne ba ki so ba, ke da shi ɗin ku riƙa tsaftace bakinku kafin ku kai ga sumbantan junanku, ina ganin kamar hakan shi ne mafita, saboda idan aka cigaba da yi masa kawaici ba zai gane dalilin da yasa ba ki bashi haɗin kai ba, kuma kullum zai ta jin haushinki, ke kuma ba za ki fita daga damuwar da kike ciki ba.

Idan ya ƙi gyarawa kina da uzuri har a wurin Allah, saboda tsafta yanki ne na imani kamar yadda hadisin Muslim ya tabbatar. Tsarki da kyautata kamshi suna cikin sunnonin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Babu laifi kuma babu zunubi a gare ki na kin yi masa kiss (sumba) matukar akwai karni ko warin baki da ke kawo miki cikas. Hakki ne a kansa shima ya kiyaye tsaftar bakinsa don jin dadin rayuwar aurenku.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments