Ticker

6/recent/ticker-posts

Biyayya Ga Iyaye Da Hatsarin Saba Musu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam malam. Ina so a yi min bayani a kan wajibcin biyayya ga iyaye da hatsarin saɓa musu. Allah ya ba da ikon amsawa. Allah ya jiƙan iyaye.

BIYAYYA GA IYAYE DA HATSARIN SAƁA MUSU

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Hakika Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi mana umarni kamar yadda Allah da kansa yayi mana umarnin akan yin biyayya da kuma kyautata mahaifa, da kuma hani daga saɓa masu da kuma cutar dasu, saɓawa mahaifa da rashin kyautata masu yana cikin mafi girma zunubai da ake yiwa Allah anan duniya.

lallai yin biyayya da ɗa’a ga iyaye, a lokacin da suke raye da kuma bayan mutuwarsu, yana daga cikin manyan farillai da wajibai da Allah ya rataya a kan kowane Musulmi, in dai har Musulmin kwarai ne. Kai yana ma daga cikin mafiya girman ayyukan Ibadah, bayan bautar Allah Ta’ala. Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:

وَاعۡبُدُوا اللّٰهَ وَلَا تُشۡرِكُوۡا بِهٖ شَيۡــًٔـا ؕ وَّبِالۡوَالِدَيۡنِ اِحۡسَانًا

 “Ku bauta wa Allah, kada ku yi masa shirka da komai. Kuma ga iyaye ku kyautata.” [Surah: An-Nisaa, Ayat: 36].

Kuma Allah Maɗaukakin Sarki Yace:

وَوَصَّيۡنَا الۡاِنۡسٰنَ بِوَالِدَيۡهِۚ حَمَلَتۡهُ اُمُّهٗ وَهۡنًا عَلٰى وَهۡنٍ وَّفِصٰلُهٗ فِىۡ عَامَيۡنِ اَنِ اشۡكُرۡ لِىۡ وَلِـوَالِدَيۡكَؕ اِلَىَّ الۡمَصِيۡرُ‏ 

“Kuma mun yi wasiyyah ga mutum game da iyayensa, mahaifiyarsa ta ɗauke shi wahala kan wahala ta kuma shayar da shi na shekara biyu, (don haka) ka gode mani kuma ka gode wa iyayenka, (sannan) gare ni makoma take.” [Suratu Lukman: 14]

Allah yayi umarnin a kyautata masu, musamman idan sun tsufa, Yace:

وَقَضٰى رَبُّكَ اَلَّا تَعۡبُدُوۡۤا اِلَّاۤ اِيَّاهُ وَبِالۡوَالِدَيۡنِ اِحۡسَانًا ؕ اِمَّا يَـبۡلُغَنَّ عِنۡدَكَ الۡكِبَرَ اَحَدُهُمَاۤ اَوۡ كِلٰهُمَا فَلَا تَقُلْ لَّهُمَاۤ اُفٍّ وَّلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُلْ لَّهُمَا قَوۡلًا كَرِيۡمًا‏  ۝  وَاخۡفِضۡ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحۡمَةِ وَقُلْ رَّبِّ ارۡحَمۡهُمَا كَمَا رَبَّيٰنِىۡ صَغِيۡرًا ؕ‏

Meaning:  Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci.  ۝ Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rnõna, ina ƙarami."  [Israi: 23-24]

Abdullahi (RA) yace: Na tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa wane aikine Allah mai girma da ɗaukaka yafi so sai yace: "Sallah akan lokacinta, sai nace sannan me? Sai yace: Bin Iyaye, sai nace sannan me? Sai yace: Sannan Jihadi don ɗaukaka kalmar Allah. Sannan yace ya faɗa mun wainnan abubuwan kuma da naso ya karamun da ya karamin".

Abdullahi bin Umar (RA) yace: Yardan Allah yana cikin yardan iyaye, kuma fushin Allah yana cikin fushin iyaye. Wato wanda iyayensa suka yarda dashi to Allah zai yarda shi, haka ma idan iyayensa suna fushi dashi to Allah ma yana fushi dashi. A wani hadisin kuma Abdullahi dan Abbas yace: Lallai ni ban san wani aiki wanda yafi kusanci zuwa ga Allah ba fiye da biyayya ga Mahaifiya. [Duka hadisan suna cikin Al-Adabul Mufrad].

Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi Allah waddai da wanda bai yi wa iyayensa biyayya da ɗa’ar da zasu kai shi Aljannah ba, yayi addu’a, yace: “Ya Allah ka turmusa hancinsa, Ya Allah ka turmusa hancinsa, Ya Allah ka turmusa hancinsa!” Sai Sahabbai suka ce wanene Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)?” Sai yace: “Wanda ya riski mahaifansa lokacin tsufansu, ko ɗaya daga cikinsu ko dukkansu biyu, amma bai shiga Aljannah ba.” [Muslim]

Don haka mu sani, kyautata wa iyaye, da ɗa’a da biyayya gare su dole ne, tilas ne, kuma wajibi ne, kuma wannan har bayan ransu, kai ko da ace kafirai ne, wajibi ne ayi masu biyayya a cikin komai da komai, in dai ba saɓon Allah da Manzonsa ba ne.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya baiyana mana illa da girman laifin mai saɓawa Mahaifansa, ga kaɗan daga cikin su:-

1. Mai Cutar da mahaifansa Tsinanne ne inji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Daga Abu Hurairaita R.A yana cewa :- "Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa:- La'antacce ne mai cutar da mahaifansa ko mai saɓawa mahaifansa).

2. Allah bawa kallon mai saɓawa Mahaifansa a ranar alƙiyama. Daga Ibn Umar R.A yana cewa:- "Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: Mutane guda ukku Allah bazai kallesu ba a ranar alƙiyama, ɗaya daga cikin su shine Mai saɓawa mahaifansa.

3. Mai saɓawa mahaifa baya shiga aljanna". Daga Ibn Umar R.A yana cewa:- "Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: Mutane guda ukku bazasu shiga aljanna ba a gobe alƙiyama:- Mai saɓawa mahaifa da Mai kwankwadar giya da Mai yin gorin abinda ya bada.

4. Babu mai shiga aljanna sai ya kasance yana biyayya ga mahaifansa kuma baya saɓa masu". Wani mutum yazo wajan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) sai yace Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) "Na shaida babu abin bautawa bisa hakki da gaskiya Sai Allah kuma kai Manzon Allah ne, kuma nayi salloli biyar na farilla kuma na bada zakka kuma nayi azumin watan Ramada?? Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: Wanda ya mutum akan haka yana tare da Annabawa da Shahidai Siddiƙai a ranar alƙiyama matuƙar bai saɓawa Mahaifansa ba.

5. Allah baya karɓar aiyuka na mai saɓawa mahaifansa inji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Daga Abi Umamah R.A yana cewa: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: Mutanan guda ukku Allah baya karbar aiyukan su na farilla da na nafila:- Mai saɓawa Mahaifansa da Mai gorin abinda ya bayar da Wanda yake karyata Ƙaddara.

6. Saɓawa mahaifa yana cikin mafi giraman zunubai inji Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam). Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa:- Shin bazan faɗa maku ba mafi girman zunubi ba?? sai Sukace: Eh ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) sai yace; Yin shirka da Allah da Kuma saɓama Mahaifa ya kasance yana Kishingide sai ya tashi zaune sannan yace; Ku saurara da maganar zur da Shaidad Zur.

Ya Allah ka nisantar da mu daga aikata abinda zai sanya mu saɓawa Mahaifanmu. Ya Allah ka jikansu kamar yadda suka kulamu lokacin muna yara, Allah ka gafarta ma mahaifan mu baki ɗaya.🤲

   ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments