Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Kishi Da Hassada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam da fatan kana lafiya. Don Allah Malam shin da hassada da kishi da mata ke yi wai duk abu ɗaya ne? Idan suna da bambanci shin mene ne bambancinsu a addinance?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Kishi da Hassada abubuwa daban daban ne. Sai dai kowanne yakan janyo faruwar ɗayan idan har mutum bai ji wa'azi ya gyara zuciyarsa ba.

KISHI: halal ne Mutukar zai taimaka wa mace wajen neman yardar Allah ta hanyar zage damtse wajen yawaita ladabi da biyayya da kyautata wa mijinta, kuma kishi yakan zo da ma'anar "gasa" ko tsere da juna" atsakanin matayen dake karkashin namiji guda. Kowacce takan yi kokari wajen ganon ta kula da hakkokin mijinta fiye da sauran abokan zamanta, domin samun cikakkiyar soyayya daga gareshi, kasancewar ita zuciyar ɗan Adam an horar da ita ne bisa son mai kyautata mata, da kuma Qin mai munana mata.

A addinance, kishi abu ne mai kyau da ya halatta idan dai bai wuce iyaka ba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sahabbai (RA) sun yi kishi. Kishi shaida ce ta tsantsar soyayya da kima a zuciya. An bayyana namijin da baya kishin matarsa (wanda ake kira da Dayyuth) a matsayin wanda ya sabawa koyarwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma ya cancanci tsananin fushin Allah da barazanar shiga Aljanna. Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce kishi yana daga cikin imani, kuma Allah Yana kishin haramcin sa, kamar yadda mumini ma yake yi.

HASSADA: Muguwar dabi'a ce ta son wata ni'ima ta gushe daga hannun wani mutum ko a samu rashin jin dadi kan ganin wani ya samu rabo. Wannan haramun ce. Babu wani alkhairi cikinta. Tunda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: "Ina tsoratar daku daga yin hassada. Domin hakika ita tana cinye kyawawan ladan mutum kamar yadda wuta ke cinye Qirare".

Malamai sun bayyana cewa mumini na gaskiya yana yin "giba" (fatan samun irin alherin da wani ke da shi ba tare da fatan alherin ya gushe ba), yayin da munafiki kuma shi ne mai yin hassada (fatan alherin ya gushe baki daya).

Da yawa daga cikin mata suna kasa rarrabewa atsakanin waɗannan halayen guda biyu. Maimakon suyi tsere da abokiyar zamansu wajen kyautata wa maigidansu, sai su rika yi mata hassada da ita da 'ya'yanta. Suna Qin Kada wani abun alkhairi ya sami abokiyar zamansu. Daga nan sai abun ya juye ya koma hassada da gaba da Qiyayya, wani lokacin ma har da Tsafe-tsafe don neman cimma mummunan burinsu akan abokiyar zamansu.

Ya zama wajibi ga duk matar dake son rabauta a lahira ta kiyayi zurfafa kishi (wato baqin kishi) wanda ke makantar da zukata ya raba mutum da imaninsa. Da zarar kinji alamar hassada azuciyarki game da abokiyar zamanki, ki nemi tsari daga sharrin Shaiɗan, sannan kiyi mata addu'ar alkhairi. Nan take zakiji hassadar tabar zuciyarki.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments