Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Mazinaci Ne, Zan Iya Neman Saki?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, mallam mijina ya kasance mazinaci kuma ni na tabbatar da hakan kamar yadda sharia ta tanadar, kuma har magani mun karɓa a asibiti sakamakon cututtukan dake samuwa sakamakon haka, na yi hakuri ganin bai rageni da komai ba. na yi tayi masa addu'a shekaru da dama amma ba wani canji, kuma yanzu baya ma kusanta ta. Mallam zai iya neman saki? Meye abinyi a shari'ance?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu:

Abin da ya kamata shi ne ki sanar da magabatan ku. Domin kuwa wannan bayanin da kika yi, ba Ƙaramin abu bane. Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya hana yin aure a tsakanin Mazinacin miji da kuma Mace mumina wacce ita ba ta Zina. Acikin suratun Nuur ayah ta 3 yana cewa;

لَا يَنْكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنْكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ ۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ

Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai auren ta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai. (suratun Nuur ayah ta 3)

Malaman tafseeri suna kafa hujjah da wannan ayar cewar aure a tsakanin mazinata da muminai bai halatta ba. Kuma akwai hatsari mai yawa a gare ki cikin zama da wannan bawan Allah. Domin kuwa wata rana zai iya zuwa ya kwaso miki H.I.V AIDS ko kuma wata cutar mai wahalar magani.

Kwanakin baya can da akwai wadda ta taɓa min irin wannan tambayar Mijinta Zina yake aikatawa a yanzu haka ya ɗauki H.I.V daman matansa biyu ne toh ita H.I.V ɗin bai kama ta ba tukuna amma ɗayan Matarsa ta kamu, shi ne ta ke neman shawara ya zatayi da zaman Auren ta wai ya halatta ta nema Saki?

Akwai wata kuma ciwon ya Riga ya kama ta Amma bai gama yin Karfi a jikin ta ba wai ya zatayi?

Yakamata mata ku gane cewa indai irin wannan ya faru da mijin ki toh kawai ki nema saki ku rabu matukar ke ciwon bai kama ki ba idan ya kama ki ne toh yanzu duk ɗaya kuke sai ki ci gaba da zama da shi a hakan har zuwa ta zo muku, Amma indai ke ba ki kamu ba toh kiyi gaggawar rabuwa da shi kawai ko Yara nawa kuka Haifa da shi ku rabu, domin a cikin ku babu wadda ya San waye zai Riga mutuwa, yanzu idan kema kika kamu da Ciwon sai shi Mijin ya Riga ki mutuwa ko kuma sai ya sake ki, don Allah ya zakiyi da rayuwar ki kuma ga shi ke karamar Yarinya ce ba ki wuce wani ya Aure ki ba amma kina ɗauke da Ciwo wai zai zo ya Aure ki?

Sabida haka matukar Mijin ki yana harkan Zina a waje Kun yi magana ya ƙi ji Kun yi Nasiha ya ƙi ji, kin gayawa Waliyyin sa da Waliyyin ki ya ƙi, kin gayawa duk wadda za su gaya masa magana ya ji ya ƙi sauraron su toh ko shi ne Ɗan autan Maza kiyi gaggawar rabuwa da shi, shine yafi dacewa, tunda baya Jin maganar kowa sa'annan ya zaɓi ya ci gaba Saɓawa Allah akan ya ji maganar kowa toh kin ga ke a matsayin ki na wadda ba mazinaciya ba Wajibi ne gare ki nema saki ya sake ki, ki rabu da shi ko Yaran ku sun kai 100 ne ki rabu da shi kawai, Allah zai kawo miki wani wadda yafi sa wadda za kula da ke da Yaran ki idan Kuma kin ce a'a ai kina son sa wallahi ba ki son rabuwa da shi ai Uban Yaran ki, toh lallai kina cikin matsala da tashin hankali sa'annan ke kina goyon bayan ma ya ci gaba da Saɓawa Allah ɗin kenan.

Sa'annan kuma kowacce mace burin ta shine Uban 'ya'yan ta ya zamto mai kyawun halaye Da tarbiyya yadda zai zama abin alfahari a wajen 'Ya'yan sa. Amma ya kamata lallai ki zauna tare da waliyyan auren ku ki bayyana musu halin da kike ciki sannan su kuma su tunkare shi da maganar ki sanarwa manyansa na, sannan ayi masa nasiha, Wa'azi, tunatarwa, Idan ya yarda ya tuba ya chanja halayen sa, toh shikenan sai ku ci gaba zaman Auren ku.

Amma idan ya ƙi yarda, ko yayi tawaye, toh mafi alkhairi a gare ki shine a raba auren kawai kada ki damu da maganar wasu Cewa ai tunda ba ke kike aikatawa ba ina ruwan ki ai laifin shi ya shafa ke Ina ruwanki ki bar shi yayi abun da yake so tunda ya ƙi, toh kawai ki ce tunda ya ƙi ke kuma ba za ki zauna da wadda baya Jin maganar iyayensa ko Manyan sa ko Waliyyin sa tare da saɓawa Allah ba kawai ya Sake ki. Idan ba haka ba, zai iya sanya ke ma ki kauce hanya idan ba Allah ne ya kiyaye ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...


 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments