𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Allah ya kara wa rayuwa malam albarka tare da dukkan iyalinka. Don Allah Malam idan za a canza ma mutum suna wacce hanya za abi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salamu wa
rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu
ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Kawai za ka ambaci sunan da
ka canza ga mai sunan ne. Domin Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya canza wa
sahabbai sunaye mazan su da mata, ba tare da yanka ko wani dogon zance ba.
Kawai idan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ji sunan ka bai dace ba, sai
yace kawai sunan ka wane, shike nan misali, wata tace sunan ta LANTANA, sai
yace, a'a, sunan ki JAMILA.
«4954» حدثنا
أحمد بن حنبل ومسدد قالا: حدثنا يحيى عن عبيد الله عن نافع عن ابن عمر أن رسول
الله صلى الله عليه وسلم غير اسم عاصية وقال: ((أنت جميلة)).
Ya kuma ji sunan shi ASRAM,
sai yace a'a, sunan ka ZUR'AH.
عَنْ
عَمِّهِ أُسَامَةَ بْنِ أَخْدَرِيٍّ أَنَّ رَجُلاً يُقَالُ لَهُ أَصْرَمُ كَانَ
فِي النَّفَرِ الَّذِينَ أَتَوْا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((مَا
اسْمُكَ)). قَالَ أَنَا أَصْرَمُ. قَالَ: ((بَلْ أَنْتَ زُرْعَةُ)).
Wani ma yace sunan sa
ABUL-HAKAM sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace, Allah shine AL-HAKAM. Ya
tambaye shi ko kana da yaya, sai yace eh. Sai yace wanene babban su, sai yace
SHURAIH, sai yace, toh a kira ka ABU-SHURAIH.
عَنْ
أَبِيهِ هَانِئٍ أَنَّهُ لَمَّا وَفَدَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَعَ قَوْمِهِ سَمِعَهُمْ يَكْنُونَهُ بِأَبِي الْحَكَمِ
فَدَعَاهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: ((إِنَّ
اللَّهَ هُوَ الْحَكَمُ وَإِلَيْهِ الْحُكْمُ فَلِمَ تُكْنَى أَبَا الْحَكَمِ)).
Haka ya ji an kira wani da
sunan HAZNUN, sai yace a'a, sunan ka SAHLU.
عَنْ
أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ
لَهُ: ((مَا اسْمُكَ)). قَالَ حَزْنٌ. قَالَ: ((أَنْتَ سَهْلٌ)).
قَالَ
لاَ السَّهْلُ يُوطَأُ وَيُمْتَهَنُ. قَالَ سَعِيدٌ فَظَنَنْتُ أَنَّهُ
سَيُصِيبُنَا بَعْدَهُ حُزُونَةٌ.
Wallahu ta'ala a'lam
Amsawa: Malam Aliyu Abubakar Masanawa
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.