Ticker

6/recent/ticker-posts

Kirgen Lissafin Idda Bayan Kotu Ta Raba Aure

ƘIRGEN LISSAFIN IDDA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam, muna da tambaya ne haka: Mace ce suka samu saɓani da mijinta ta bar gidan na tsawon wata 6 har ta Kai su ga kotu Kuma aka raba auren bayan zaman kotun to za ta yi idda ne daga wannan lokacin ko ta riga ta gama tun da ta Kai wata 6 ba sa tare? Allah ya saka da alheri.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Matar da mijinta ya sake ta, za ta fara kirgen lissafin iddarta ne daga ranar da sakin ya tabbata. ko da kuwa sun kai shekara guda ko fiye da haka basu zauna waje guda ba.

Idan har ya taɓa saduwa da ita a cikin zaman da sukayi kafin samun saɓanin, to wajibi ne sai ta yi iddah. Idan kuma daga daura auren bai taɓa taɓata ba, sai aka samu saɓanin har ya sake ta, to babu iddah akanta kamar yadda Allah ya faɗa a cikin Suratul Ahzab.

Yadda za ta yi iddar kuwa shi ne: idan ƙaramar yarinya ce wacce ba ta fara yin jinin haila ba, ko tsohuwa wacce ta riga ta fidda tsammanin zuwan jinin al'ada gareta, to za ta yi Ƙirgen lissaafin iddarta ne da watanni. Wato watanni uku za ta yi.

Idan kuma tana yin jinin al'ada ko da tana dauke da goyo, to lallai za ta yi lissafin iddarta ne da kirgen zuwan jinin al'adarta, ko Ƙirgen tsarkin da ta samu bayan zuwan jinin.

Idan kuma tana dauke da juna-biyu, to haihuwarta ita ce Ƙarshen iddarta.

NOTE: A bangaren iddar rasuwa (TAKABA) idan mace mijinta ya rasu amma ba ta samu labarin rasuwarsa ba, sai bayan wata ɗaya ko biyu, to za ta yi lissafin takabarta ne daga ainahin lokacin rasuwar tasa ba daga ranar da labarin ya sameta ba.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 ƘARIN BAYANI

Tambaya:

Mace ta samu saɓani da mijinta ta bar gidan tsawon watanni 6, har ta kai kotu inda aka raba aurensu. Yaya za ta yi lissafin iddarta: daga lokacin da suka rabu ko daga lokacin da ta bar gidan?
Assalamu alaikum Malam, da fatan kana lafiya. Muna so a yi mana bayani kan lissafin idda ga mace wacce mijinta ya raba ta bayan sun samu saɓani da aka kai kotu, ko ta fara idda daga lokacin da ta bar gidan ne ko daga lokacin sakin auren kotu?

Amsa:

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A Musulunci, lissafin idda ga mace wacce aka raba ta da mijinta yana farawa ne daga ranar da sakin ya tabbata, ko da kuwa sun rabu ko basu zauna tare ba a cikin lokaci mai tsawo kafin kotu ta yanke hukunci. Wannan ya dace da koyarwar Allah a cikin Alƙur’ani, inda Suratul Ahzab ta ce:

وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ ثَلَاثَةَ قُرُوءٍ

“Matan da aka sallama su zauna cikin kansu na tsawon uku cikakkun tsawon al’ada.”
(Suratul Ahzab 33:49)

Idan mijin ya taɓa saduwa da ita kafin rabuwa, to idda tana da wajibi. Amma idan basu sadu ba kafin rabuwa, to babu idda kafin sakin ya tabbata.

Hanyoyin lissafin idda:

1. Ga ƙarama ko tsohuwa wacce ba ta fara haila ba ko ta riga ta gama tsammanin jinin al’ada: za ta yi idda na watanni uku.

2. Ga mace mai haila ko jinin al’ada: za ta yi idda ne bisa kirgen zuwan al’ada da tsarkin da ta samu bayan zuwan al’adarta ta ƙarshe.

3. Ga mace da ke dauke da ciki: haihuwarta ce ke ƙayyade ƙarshen idda.

Idda idan mijin ya rasu (iddar takaba): idan mace ba ta san rasuwar mijinta ba, to lissafin idda yana farawa ne daga ainahin ranar rasuwar mijinta, ba daga ranar da ta samu labari ba.

A takaice, ranar da kotu ta yanke hukuncin sakin ko ranar da mijin ya rasu ce za a fara kirga idda, ba daga lokacin da aka fara saɓani ko ta bar gidan ba. Wannan yana tabbatar da cewa shari’a tana kare hakkin mace da kuma tabbatar da tsarkin aure kafin ta sake aure.

Allah ne mafi sani.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments