TAMBAYA
Assalamu alaikum malam fatan an yini lafiya ya gida ya aiki, dan Allah malam ina da tambaya, ina da saurayi to sai yake min wasu abubuwa tun ba na so har ya kai nima ya saba min, idan ya zo gurina sai ya dinga kama min mama na ko ya dinga sanya gaban sa cikin gabana na yi masa faɗa yaƙi dainawa har ta kai ya yi min ba adadi, shin malam wannan mijin aure ne ko ba mijin aure ba? Na gode Allah saka da alheri kuma a ja hankalin ƴan uwa na Mata saboda dayawa suna aikata haka.
AMSA
Wa alaikum salam
warahamatullahi wabarkatuhu lafiya lau alhamdulilah, to da farko dai ƴar uwa kin zubar da ƙimar ki kuma ki sani
cewa ba ko wani na miji ba ne zai iya auren ki idan kika bashi kanki ya sanki a
ya Mace ba ta hanyar aure ba koda ya aure ki ba zai ɗauke ki da daraja ba
kullum yana cikin zargin ki da kuma tuhumar ki.
Duk namijin da ya
miki haka to ba ke yake so ba da yana son ki ba zai so ya miki haka ba kuma ki
sani kinyi babba kuskure da kika yardar masa.
Duk na miji da zai
dinga miki maganar da ki yarda koda malami ne ko ustaz ya dinga jayo miki wasu
ayoyin sa wanda zai rude ki ko ya ce zai miki fushi idan baki yarda ba to
wallahi kar ki yarda kaf Alkur'ani babu inda aka hallata hakan kuma hukuncin ku
kamar kun aika zina kuyi saurin tuba zuwa ga Allah.
Kuma ki sani duk na
mijin da ya aure ki zai gane sn kwanta da ke.
Allah a cikin
littafinsa mai tsarki yana cewa:" Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita
ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya."
Suratul Isra'i aya ta
34 zuwa 35 safaha ta 285
Kuma mu sani alƙawari ne Allah ya yi
duk wanda ya yi zina to zai auri Mace daidai dashi wadda ita ma haka take yi.
Kamar yadda Allah
yake faɗa a cikin Alkur'ani
mai girma:" " Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika,
kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta
wannan a kan mũminai."
Suratul Noor aya ta 3
zuwa ta 4.
Wannan ayar ta zamo
mana izina a gare mu domin duk wanda ya aika zina da ƴar wani ya sani fah
ba Allah ya yi ma wayo ba shi ma Allah zai haɗa shi da daidai dashi.
Kuma mu sani duk
wanda yake aikata munana kamar zina to shi ma Allah ya yanke masa hukumcinsa ga
wanda zai rayu dashi tun nan duniya domin ba a yi ma Allah wayo a cikin Suratul
Noor aya ta 26 zuwa ta 27
" Miyãgun mãtã
dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma
tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan
mãtã suke...."
Duk wani wanda ya
aika zina to ya tuba idan har ba a yi masa hukunci anan gidan duniya ba idan
yaje Allah zai yi masa nasa.
Hukuncin abin da kuke
yi kamar zina kuka yi
Abin da kuka yi tun
da har yana sanya gaban sa cikin gaban ki to wannan kamar zina ce kuka aika ta
kuma hukuncin wanda bai da aure shi ne bulala 100 kamar yadda ya zo cikin
Alkur'ani mai girma:" Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su,
bũlãla ɗari 100. Kuma kada
tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin
ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su
halarci azãbarsu."
Suratul Noor aya ta 2
zuwa ta 3
Wannan hukunci ne da
Allah ya yanke shi idan har ana yin sa to za a yi musu wannan hukuncin su duka
kuma a kora su daga garin saboda kar su lalata wasu.
Amma wanda suke da
aure to jefe su za a yi har sai sun mutu idan aka musu rangwame kuma to Allah
zai yanke musu nasu hukuncin.
Jan hankali na ga yan
uwa🦻👂
Kada sha'awar ka tasa
ka aikata zina da ƴar wani haka kema kada son ranki da rudin shaidan ya sa ki
aikata wannan ɓarnar.
Kuma ki sani ke uwar
wasu ce kuma za ki haifa haka kaima uba ne ga wasu dan haka kada ka yi nadama
daga baya idan ka haifi ƴaƴa suka zamo suna da irin halin ka.
Allah ya kare mana
imanin mu ya kuma tsare mu baki ɗaya.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.