Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukunce-Hukuncen Sallar Idi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam ina so sanin hukunce-hukuncen sallar idi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

An Karɓo daga Anas bn Malik (ra) Lallai Yace: Mutanen Jahiliyya Sun Kasance Sunada Kwanaki Biyu a Kowace Shekara da Suke Bukukuwansu da Wasani a Cikinsu. A Yayin da Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Ya Iso Madina Sai Yace: “Kun Kasance Kunada Kwanaki Biyu da Kuke Wasanni a Cikinsu, Hakika Ubangiji Ya Musanya Muku da Mafiya Alkhairinsu: Sune Idin Azumi da Idin Layya”.

Idi yana da hukunce-hukunce da yawa ga wasu saga ciki:

1. Azumtar ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin Abu-sa'id Al-kudry, -Allah ya yarda da shi - cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana azumtar ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito.

2. An ruwaito daga Umm Ad'iyyah(RA) ta ce: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umarce mu a sallah karama da sallah babba da mu fitar da yantattun yan mata da masu aure, da tsofaffi, amma ya umarci masu haila da su nisanta daga gurin sallar musulmai.

3. Wanka Kafin fita wajan Sallah idi, kamar yanda hadisi yazo ingantacce a cikin Muwadda, Abdullahi Bin Umar ya kasance yana Wanka ranar idi, Kafin ya tafi zuwa wajan Sallar idi, Muwaddah (428). Nawawi Ya Ambaci ittifaqin Malamai Akan Mustahabbancin wanka A sallar idi.

4. Ado da Kwalliya: Jabir yace: Annabi Sallallahu Alaihu wasallam ya kasance ya nada riga ta Musaman da yake sawa a idi da juma'a. Baihaqi ya ruwaito ibnu Umar yana Sanya Mafi kyawun tufafinsa yayin fita zuwa idi, abunda yafi dacewa da na miji ya Sanya mafi kyawun kayansa. Amma mata: Su guji yin ado, idan zasu fita, domin An hanesu bayyana ado ga maza waɗanda ba muharramansu ba, haka haramunne su sanya turare, ko wata shiga da zata kai da fitinar maza, domin zata fita don ibadane da biyayyar Allah.

5. Daka Waleed bin Muslim yace; Na tambayi Auza'iy da Maik bin Anas akan bayyanar da kabar-bari ranar idi, yace: Abdullahi bin Umar ya kasance yana bayyanar dashi a idin qaramar sallah har liman ya fito. Daka Abiy Abdurrahman Sulami yace: ( Sunfi tsananta kabar-bari a idin Qaramar Sallah sama da Babbar Sallah. Duba Irwa'ul Galeel (3/122). Darul Qudny ya ruwaito ibnu Umar idan zai tafi sallar idin babbar Sallah da Qarama yana qoqari Sosai wajan kabbara harzuwa wajan Sallah. Ibnu Abu shaiba Ya ruwaito da Sanadi ingantacce daka zuhry yace: Mutane Sun kasance suna Kabar-bari a idi tun daka gidajensu harzuwa wajan Sallah, idan liman yazo sai suyi shiru idan yai kabbara suyi. Duba Irwa'ul galeel (2/121). Yin kabar-bari tun daka gida har zuwa wajan sallah al'amarine shahararre sosai awajan Magabata Nakwarai.

6. Yana daka cikin ladubban idi taya juna murna da kalmomi kyawawa masu daɗi, duk yanda lafazin yake matuqar yana nuna Sam barka da farin cikin Samun damar yin idi, Kamar "Allah ya karɓa mana, ko Allah yasa munyi idi Mai Albarka" Da Sauran lafuzza kyawawa. Kamar Yanda sahabban Annabi Sallallahu Alaihi wasallam suka kasance sunayi, kamar yanda jubair bin nafeer ya ruwaito, ibnu Hajar yace: Isnadinsa kyakkyawane duba fatah (2/446).

7. Daka jabir bin Abdullahi Allah ya qara musu yarda yace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya kasance ranar idi yana Saba hanyar zuwa data komawa, Bukhari (986).

Hikimar haka, wasu sukace: don hanyoyi biyun suyi masa shaida ranar Alqiyama, wasu sukace: Dan bayyanar da wata alama ta musulunci. Wasu sukace: Don qunsawa Munafukai da kafirai baqin ciki, da tsoratar dasu da yawan Musulmi, wasu sukace: don ya biya buqatun Mutane da koyar dasu da fansar wasu, wasu suce: don ya bayar da sadaka ga Mabuqata, wasu suce: Don ziyarar 'yan'uwansa.

Lokacin Sallar Idi Yana Farawa Ne Yayin da Rana ta Ɗan Ɗago Kaɗan. Wannan Shine Mazhabin Malikiyya da Hanabila da Shafi'iyya kuma da Hanafiyya.

Hakika Ya Tabbata A Sunnah Lokacin Sallar Idi Yana Farawa ne Lokacin Hantsi Har Zuwa Lokacin da Rana Tayi Zawali. Abinda Yafi dacewa Shine A Gaggauta Yin Sallar a Idin Layya, Sannan a Jinkirtata a Idin Azumi. Wannan Shine Abinda Jamhur Suka Tafi Akanshi Kuma Shine Zantukan Malaman Malikiyya.

Ana yin sallar idi ne raka'o'i biyu, za'a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud.

Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori, to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da kubce masa ba na kabbarori, saboda sunnoni ne ba wajibai ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments