𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam ina jin daɗin nasiharku Allah ya ƙara wa malam basira da lafiya. Malam wallahi ina cikin damuwa da rudani, ni da mijina ba ma zaman lafiya sai ya zama yana zargina, ni kuma da na ga haka sai na gaya wa ƙanwar mahaifiyata ta kaini gurin wani malami akatsina. Saboda wallahi malan a lokacin zuciyata sai na ji ba na son zama da shi na cewa malamin ya raba mu. Ya ba ni wasu takardu ya ce insa wani a masai wani kuma in kona duk nayi, Kuma muka rabu yaranmu biyu da shi kuma Walahi malam bayan mun rabu abun ya dameni naso yadawo amma Allah be ƙaddara ba, ina cikin jimami sai wani bawan Allah ya kirani dana ganema manufarsa akaina na ce masa ina cikin idda kar yaƙara kirana amma sai yake turo min da kati, ya zo yana ba almajirin gidanmu sako yana kawowa aba ma 'yata duk ina cikin idda. ka san rauninmu ni kuma sai na fara daga masa waya muna magana kafin in gama idda har mun yi maganar aure. Da na gama idda aka sa mar sadaki aka ɗaura mana aure. malam bari intaƙaice maka labari shi ma Tun da muka yi aure babu kwaciyar hankali Malam. Meye matsayin aurenmu?. Gaskiya malam labarin metsawo ne yanzu haka muna kotu da wannan sabon mijina kuma wallahi ba don Kuɗinsa ya sa na aureshi ba. asali ma tsohon mijina ya fishi sukuni. Wannan kwatakwata bai da kishi, be san hakkin iyalinsa ba. Matarsa tana yin abin da ta ga dama bai iya yi mata magana ga rashin kula da iyali. Ina zargin kaina saboda abin da na aikata malam dan Allah meye abunyi? inata istigfari malam ka taimake ni wallahi ina cikin damuwa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Tabbas kin aikata
kurakurai masu yawa a cikin wannan abin da ya faru. Tun daga zamanki a gidan
mijinki na farko, zuwa wannan na biyun:
1. Kin aikata abin da
zai kawo zargi azuciyar mijinki.
2. Rashin neman
hanyar da za ku daidaita da shi.
3. Zuwa wajen malamin
duba.
4. Jefa ayoyin Alƙur'ani a cikin Masai.
5. Shirya maganar
aure tun baki kammala iddah ba.
6. Rashin zaman
lafiya da Mijinki na biyu.
7. Kaiwa Ƙararsa kotu.
Waɗannan laifukan gaba Ɗayansu manya ne. Amma
Kaba'irori daga ciki sune zuwanki wajen boka, yarda da abin da ya fada, da kuma
jefar da Takardar nan a cikin Masai (shadda). Sai kuma shirya maganar aure a
cikin iddah.
Watakila wasu laifuka
kike aikatawa irin na zargi, shi ya sa har Mijinki na farko yake zarginki ɗin. Sannan zuwa wajen
boka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: "DUK WANDA ya je WAJEN
BOKA KO ƊAN DUBA, KUMA YA YARDA DA ABIN DA YA FAƊA, TO HAKIKA YA
KAFIRCE MA ABIN DA ANNABI MUHAMMADU (Sallallahu Alaihi Wasallam) YA ZO DA SHI".
(Muslim ne ya ruwaito).
To kinga anan kalmar
kafircewa ta hau kanki. Sannan kuma jefa takarda a cikin Masai, wacce watakila
tana kunshe da Basmalah ko kuma wasu ayoyi na Alƙur'ani, Shi kam
kafirci ne tsantsa.
Malamai sun ce duk
wanda ya wulakantar da Alƙur'ani ko kuma wani sashe daga gareshi da gangan, to
wannan ya kafirta, ya yi ridda.
Hakanan shirya
maganar aure a cikin lokacin iddah, ana kirga wannan a cikin manyan laifuka.
Watakila alhakin waɗannan manyan laifukan
ne ya janyo miki rashin samun dacewa a cikin sabon auren da kikayi.
Shawarar da zan baki
anan ita ce:
1. Ki tuba zuwa ga
Allah (SWT) cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake so.
2. Ki gyara halayenki
yadda za ki iya zama lafiya da kowanne Miji.
3. Idan da hali kije
ki nemi yafewar Mijinki na farko ɗin nan domin hakika kin cutar da shi.
4. Ki dena yawan yin
shawara da 'yan uwanki mata. Musamman wannan Ƙanwar mahaifiyarki ɗin nan. Domin lallai
za ta rika jefaki a cikin hallaka ne.
Daga karshe muna yi
miki fatan Allah ya gafarta miki damu baki ɗaya. Allah ya daidaita miki lamuranki. Ameen.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ƘARIN BAYANI
HUKUNCIN SIHIRI, WULAƘANTA ALKUR'ANI,
DA YIN MAGANAR AURE A CIKIN IDDAH
Tambaya
Assalamu Alaikum Malam. Ina cikin damuwa da rudani. Ni da
mijina na farko ba ma zaman lafiya saboda zargi, sai na biye wa shawarar ƙanwar
mahaifiyata muka je gun wani malami a Katsina. Ya ba ni takardu na jefa a masai
(shadda), wasu kuma na ƙona don a raba aurenmu, kuma hakan ya faru. Bayan mun
rabu, ina cikin iddah wani ya fara turo min kati da kyaututtuka, har muka fara
maganar aure kafin iddah ta ƙare. Bayan na gama, muka yi aure, amma shi ma
yanzu babu zaman lafiya kuma ba shi da kishi ko kula da iyali. Shin mene ne
matsayin aurenmu, kuma mene ne abin yi don neman gafara?
Amsa
Wa'alaikumus
Salám wa Rahmatullāhi wa Barakatuh. Tabbas kin tafi babban kuskure wanda yake
buƙatar tuba ta gaskiya (Taubatan Nasuha). Kin aikata ayyuka na ridda da kuma
saɓawa ka'idojin aure na Musulunci. Ga bayanin dalla-dalla:
1. Zuwa
Wajen Boka Da Yin Sihiri
Zuwa wajen
boka don raba aure babban zunubi ne (Kaba'ir). Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana
cewa yin hakan yana fitar da mutum daga Musulunci idan ya yarda da bokan.
Hujja daga
Hadisi:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ
عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ أَتَى
كَاهِنًا، أَوْ عَرَّافًا، فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ، فَقَدْ كَفَرَ بِمَا
أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ»
Fassarar
Hausa: Daga Abu Hurairah (R.A), daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya
je wa boka ko ɗan duba, ya gaskata abin da yake faɗa, to haƙiƙa ya kafirce wa
abin da aka saukar wa Muhammadu (S.A.W)." (Sunan Abi Dawud: 3904).
2. Wulaƙanta
Alkur'ani (Kafirci Tsantsa)
Jefa takardu
masu ɗauke da ayoyin Alkur'ani ko sunayen Allah a cikin masai (shadda) aiki ne
na kafirci wanda yake fitar da mutum daga Musulunci baki ɗaya. Malamai sun
ittifaƙi cewa wulaƙanta Alkur'ani ridda ce. Dole ne ki yi kalmar shahada ki
dawo Musulunci baki ɗaya.
3. Neman
Aure Da Magana A Cikin Iddah
Allah ya
haramta yin tayin aure ko maganar aure a sarari ga macen da take cikin iddah.
Allah yana cewa:
Hujja daga
Qur'ani (Suratul Baqara):
﴿وَلَا
تَعْزِمُوا عُقْدَةَ النِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبْلُغَ الْكِتَابُ أَجَلَهُ﴾
Fassarar
Hausa: "Kuma kada ku ƙulla ƙudurin ƙulla auren (a cikin zukatanku) har sai
takardar (iddah) ta kai ga ajalinta (ta ƙare)." (Suratul Baqara: 235).
Yin maganar
aure har da tsara yadda za a yi kafin iddah ta ƙare babban kuskure ne, koda
yake auren yana inganta idan an ɗaura shi bayan iddah ta ƙare (a ra'ayin mafi
yawan malamai), amma albarkar auren tana raguwa saboda saɓon da aka fara da
shi.
Matakai Da
Za Ki Bi Don Gyara
1. Tuba Ta
Gaskiya: Ki yi wanka, ki yi sallah raka'a biyu, ki yi kalmar shahada don
sabunta Musuluncinki. Ki yi kuka ga Allah da neman gafara kan wulaƙanta
ayoyinsa da kika yi.
2. Neman
Gafara Gun Miji Na Fari: Hakika kin cutar da shi ta hanyar yin asiri don raba
aurenku. Idan akwai dama, ki nemi gafararsa (ba lallai sai kin faɗa masa asiri
kika yi ba, amma ki nemi ya yafe miki abubuwan da kika yi masa).
3. Kiyaye
Mashawarci: Ki nisanci shawarar mutanen da ba su tsoron Allah, koda kuwa
danginki ne. Wannan ƙanwar mahaifiyarki ta tura ki zuwa wuta ne, ba gidan dadi
ba.
4. Haƙuri Da
Halin Yanzu: Wannan rashin zaman lafiyar da kike ciki a yanzu, watakila
sakamakon kura-kuran da kika aikata ne (Alhaki). Ki dage da istigfari, watakila
Allah ya sassauta miki.
Allah Ya karɓi tubarki, Ya kuma baki zaman lafiya a rayuwarki.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.