Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Nahawun Wakar Yabon Harshen Hausa Ta Isa Lawan

Citation: Hafiz Yusuf IMAM & Abdulhadi Uba GABARI (2021). Nazarin Nahawun Waƙar Yabon Harshen Hausa Ta Isa Lawan. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

NAZARIN NAHAWUN WAƘAR YABON HARSHEN HAUSA TA ISA LAWAN

By

Hafiz Yusuf IMAM

Abdulhadi Uba GABARI

Tsakure

Nahawu matattakala ce da ake takawa domin yi wa mutum jagora wajen samar da jimloli ko kalmomi don samar da zantuka masu ma’ana. Manufar wannan takarda ita ce nazarin yadda aka sarrafa rukunonin nahawu a waƙar ‘Yabon Harshen Hausa’ wadda Isa Lawan ya rubuta. Hanyar da aka bi wajen gudanar da wannan bincike ita ce karanta waƙar a lokuta daban-daban tare da la’akari da yadda aka gina ɗangwaye cikin baitocin waƙar domin su dace da manufar mawallafin kan isar da saƙon waƙar. Takardar ta yi amfani da hanyar Nazarin Nahawun Waƙa wadda Mukhtar (2005) ya kawo a littafinsa mai suna Bayanin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Nazarin ya gano wasu rukunonin nahawu da aka yi amfani da su a cikin waƙar a matsayin Dabarun Jawo Hankali wajen isar da saƙon waƙar. A ƙarshe an fahimci cewa babu wata waƙa da za a rubuta ta isar da saƙonta ba tare da an yi amfani da ɗaya daga cikin rukunonin nahawu ba.

1.0 Gabatarwa

Manyan masana irin su Abdulƙadir (1973) da Ɗangambo (1981, 2007) da Yahya (2007) da sauransu sun share fagen nazarin rubutacciyar waƙa sosai da sosai. Sai dai, yawancin nazarce-nazarcen da ake gudanarwa a kan rubutacciyar waƙa wasu sun fi karkata ga nazarin Jigo da Salo da Sarrafa Harshe da Sauran Dabarun Jawo Hankali na cikin waƙa. Wannan takarda wani yunƙuri ne na nazarin rukunonin nahawu a cikin rubutacciyar waƙa. An yi haka ne domin a takalo hankalin manazarta a kan wannan fagen nazari mai muhimmanci da ya kamata a ba shi kulawa ta musamman. Duk da cewa, Mawallafin waƙa ba ruwansa da bin ƙa’idojin Harshe (Nahawu) wajen shirya waƙarsa, amma a kaikaice yana amfani da rukunonin nahawu ne a wani ɓangare wajen isar da saƙo cikin harshe mai cike da balaga da zurfin ma’ana na kalmomin da suka gina ɗangwaye na waƙar ba tare da ya sani ba. Aikin mai nazari ne bibiyar yadda mawallafin waƙa ya sarrafa tunaninsa ta bin ƙa’idojin harshe ko akasin haka wajen cim ma buri a cikin wallafarsa.

Saboda haka, madosar wannan takarda ita ce, yin nazarin rukunonin nahawu na Hausa da suka ɓulla a cikin waƙar Isa Lawan mai suna Waƙar Harshen Hausa domin a ga yadda rukunonin nahawu suka taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙon cikin waƙar.

1.1 Dabarun Gudanar da Bincike da Ra’in Bincike

Wannan bincike, an gudanar da shi ne ta hanyar duba matanin Waƙar Yabon Harshen Hausa Ta Isa Lawan. Haka kuma, binciken ya yi hasashen cewa rukunonin nahawu da suka ɓulla a cikin waƙar sun taimaka sosai wajen isar da saƙon waƙar. Kazalika, an waiwayi kundayen bincike da muƙalu da mujallu da sauran takardun ilimi masu alaƙa da wannan bincike domin samun ƙarin haske. Har ila yau, a wannan bincike an yi amfani da Mukhtar (2005) da Ɗangambo (2007) da suka yi bayanin hanyoyin nazarin rubutaccciya waƙa ta fuskar nahawu.

1.2 Bitar Ayyukan Magabata

Mukhtar (2005) da Ɗangambo (2007) duk sun yi bayanin hanyoyin nazarin rubutaccciya waƙa ta fuskar nahawu. Daga ciki akwai Amfani da Kalmomi da Samarwa da Korewa da Zaɓen Kalmomi da Ginin Ƙirar jimla da Amfani da Sunaye da Ma’auni da Giɓin Jimla da Ƙarfafawa da Siffatau da Umartau da Fayyatau da sauransu.

Masana da Manazarta sukan tsarma wasu batutuwa da suka shafi nazarin nahawu a cikin ayyukansu a matakai daban-daban. Misali; Sani (2012) ya yi nazarin ‘Yabon Ma’aiki da Gargaɗi a Diwanin Waƙoƙin Hajiya Halima, inda ya nuna cewar waƙar tana ɗauke da rukunin nahawu guda, wato sunan aikatau mai ɗafa ƙeya da –wa, a ƙarshen kowane baiti, kamar amsawa, shiryawa, ganewa, da sauransu. Sannan kuma kalmar aikatau da waƙar take ɗauke da ita gaɓa uku ce, in ban da aikatau da yake baiti na biyu na cikin waƙar da yake ƙarewa da gaɓa biyu. Kazalika, Ahmad (2012) ta yi sharhin waƙar ‘Azancin Magana’ ta Audu Sha’iri Gwandu. Ita ma ta kawo wuraren da mawallafin ya yi amfani da rukunin nahawu a cikin waƙarsa kamar, Samarwa da Korewa, da kuma amfani da Kalmomin fannu, tsofaffi da sababbin kalmomi da Sauransu. Waɗannan ayyuka da aka ambaci sunayensu, sun ƙara wa wannan takarda ƙaimi wajen ƙara zurfafa bincike domin zaƙulo wasu rukunonin nahawu da waɗancan masanan ba su kawo su a cikin ayyukansu ba.

2.0 Nazarin Kalmomin Nahawu a Waƙar Hausa Ta Isa Lawan

A wannan sashe za a yi ƙoƙarin kawo ma’anar kalmar Nahawu sannan a yi bayanin rukunonin nahawu kamar yadda suka wanzu a waƙar Yabon Harshen Hausa wadda Isa Lawan ya rubuta.

2.1 Ma’anar Kalmar Nahawu.

A ma’ana ta Harshe an bayyana nahawu da cewa ƙa’idojin sarrafa harshe, Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006, Sh.355).

A ma’anar nahawu ta fannin Ilimi kuwa, Mukhtar (2005) ya yi bayanin cewa; Ita kalmar Nahawu asalinta kalmar Larabci ce kuma da Hausawa suka ara suka yafa suna amfani da ita daidai da yadda Larabawa ɗin suke amfani da ita wajen li’irabin jimloli (laƙabi). Ke nan, Nahawu fannin ilimi ne na kimiyyar harshe wanda ya dangaci ginin jimlolin harshe (Sani, 1999, Sh. 57). Shi kuwa Wakili (2018) cewa ya yi Nahawun harshe wani tsari ne da ake nuna yadda kalmomi ke sarrafuwa a cikin jimla lokacin magana. Wato ana nuna yadda kalmomi ke kasancewa ne da kuma yadda ake haɗa su bisa ingantaccen zubi don a tayar da jimla mai ma’ana wacce masu magana da harshen suka amince da ita. A taƙaice nahawu shi ne a tsara zance cikin jerin kalmomi masu ma’ana da za su isar da saƙon mai magana kuma a fahimta.

Abubuwan da wannan takarda take ƙoƙarin fito da su da suka shafi amfani da kalmomin nahawu a cikin waƙar Yabon Harshen Hausa ta Isa Lawan su ne kamar haka:

2.2 Ginin Jimla

Ginin jimla ya danganci yadda mawallafi yake ƙera jimlolinsa walau dogaye ne ko kuma gajeru. Ginin jimla shi ne irin matakan da mawaƙi ya bi wajen gina jimloli masu ma’ana ta yadda za su dace da zantukan da suka shafi saƙonsa. A waƙa ana duba yadda mawaƙi yake faɗar jimloli a cikin zantuka gajeru ko dogwaye da kuma yawan kalmomi da ya zuba a ciki har suka bayar da cikakkiya ma’ana a harshen waƙa (Yakasai, 2014, Sh. 188).

Malam isa Lawan, mawallafin waƙar Yabon Harshen Hausa ya gina waƙarsa da jimloli gajeru kuma masu sauƙin fahimta ga duk wanda ya karanta waƙar ko kuma ya saurara. Babu kalmomi masu tsauri waɗanda sai an sha wahala kafin a gano ma’anarsu. Jimloli ne da suke isar da saƙon waƙar. Misali:

1. (a) Waƙe nake so zan wa harshen Hausa, Harshe abin fakhri da ban mamaki. (baiti na 3)

(b) Hausa ina ƙaunar ki kuma na tabbata, A cikin harasa babu wadda ta kai ki. (baiti na 12)

(c)Kin kwalliya kin sha ado da turare, Kuma kin fito kowa yana sha’awar ki. (baiti na 15)

A waɗannan ɗangwayen da aka kawo a sama, jimloli ne masu sauƙin fahimta kuma sun bayyana manufar mawallafin na kishin harshensa da kuma yabon harshen saboda tarin hikimomi da suke cikinsa.

2.3 Amfani da Sunaye

Mawallafin ya yi amfani da adadin kalmomi 1003 wajen gina waƙarsa. A cikin kalmomin akwai sunayen da suka ɓulla ta fuskar nahawu kamar haka:

2.3.1 Sunan Yanka

Sunan Yanka shi ne suna fitacce, keɓantacce ga mai shi. Sunan na mutum ne ko na wuri. Sunan Yanka a cikin waƙar ya ƙunshi;

2. (a) Baban Ruƙayyatu Ɗaha mai shabbaki, (baiti na 2).

(b) Duba Faransa da Ingila da Amerika, (baiti na 13).

(c) An kai ni har birnin Makka da Madinatu, (baiti na 21).

(d) Mai Martaba Sarkinmu Ado Bayero, (baiti na22).

(e) Har ma Sa’idu Gusau ina gaishe da kai, (baiti na 27).

Sunan Ruƙayyatu da Ingila da Amerika da Makka da Madinatu da Ado da Bayero da Sa’idu da Gusau da sauransu duk Sunayen Yanka ne da mawallafin waƙar ya kawo su don ya nuna matsayinsu da muhimmancinsu a zamantakewar rayuwar Hausawa. 

2.3.2 Suna na Laƙabi

Suna na Laƙabi shi ne sunan da ya dace da halin da aka haifi yaro ko yarinya (Zaria, 1981: Sh. 4). Ana samar da irin wannan suna dangane da rana ko yanayin shekara ko jerin jinsin abin da ake Haifa (maza ko mata). Misali;

3. (a) Ɗalladi Ɗalliti Tala gaishe ki, (baiti na 39).

(b) Sannan Talata Talle shi ne sunan, (baiti na 40).

(c) Sannan Balarabe Laraba aka haifar (baitina 41).

(d) Sannan da Ɗallami na ranar Alhamis (baitina 42).

(e) Sannan da Ɗanjimmai na ranar jumu’a (baiti na 43).

A cikin sunayen laƙabi da ake samu a cikin al’ummar Hausawa akwai Danliti da Tala da Talatu da Talle da Balarabe da Laraba da Ɗanlami da Ɗanjimmai da Jummai da sauransu.

2.3.3 Suna Gama-gari

Suna gama-gari suna ne a sake yake babu ƙaidi. Suna ne na tarayya. Misali;

4 (a) Koyar da yadda ake abinci a ɗaki, (baiti na 29).

(b) Harshe abin fakhri da ban mamaki (baiti na 3).

(c) Da akwai abinci iri-iri ‘yan Hausa, (baiti na 30).

Ɗaki da Harshe da Abinci sunaye ne gama-gari a nahawun Hausa. Idan aka ɗauki kowane suna aka haɗa shi da wata kalmar za su iya samar da sabuwar ma’anar na wasu abubuwa masu tarin yawa a Hausa. Misali; Harshe zai iya zama harshen Hausa ko harshen wuta ko harshen damo da sauransu. Sannan kuma, abinci zai iya zama abincin da mutane suke ci ko abincin dabbobi ko abincin kaji ko abincin ɓera da sauransu.

2.3.4 Suna Gagara-ƙirga

Suna gagara ƙirga shi ne sunan abu wanda ba ya ƙirguwa. Wato abin da ba za a iya ƙirga shi ba. Misai;

5. (a) Za ka tsallake kogi ka zam ɗan zaki, (baitina 9).

(b) Da tuwo da shinkafa akwai alkaki, (baiti na 30).

Shinkafa da Ruwan Kogi abubuwa ne da ba za a iya ƙirga su ba ko a san adadinsu.

2.3.5 Suna ɗan aikatau

Suna Ɗan aikatau ya fito ne daga kalmar Aikatau. Ma’ana aikatau ne ke samar da shi. Misali;

6. (a) Tattaka takalmin ka tattara taki, (baiti na 6).

(b) Duk wanda ya faɗya zamo ɗan kirki, baiti 7.

(c) Sannan akwai kaya na YaƙHausa, baiti na 63.

Kalmar tattaka ta samo asali daga kalmar aikatau ‘taka’misali ya taka ko yana tattaka takalmi. Haka nan, kalmar tattara ta samo asali daga ‘tara’ misali ya tara ko yana tattara taki 

2.4 Wakilin Suna

Wakilin Suna nau’in kalma ne da ke wakiltar suna a magana. Ana amfani da wakilin suna a madadin suna. Ire-iren wakilin suna da aka yi amfani da su a cikin waƙar su ne kamar haka;

2.4.1 Wakilin Suna Rakaɓau

Wakilin suna Rakaɓau shi ne wanda yake iya zama shi kaɗai ba tare da ya haɗu da wani abu daban ba (Wakili, 2018, Sh. 14). Irin wannan wakilin suna a rakaɓe yake tare da cin gashin kai. Misali;

7. (a) Da akwai dalilin zan faɗa a cikin ki, baiti na 4

(b) Harshenmu ni na san da wasa ƙwaƙwalwa, baiti na 8

(c) Ita ce a cakuɗa harsuna a cikin ki, baiti na 1.

(d) Shi ne ya sa ya fi su daɗin Harshe, baiti na 26.

Wannan misalai da aka kawo a (7a-d) za ga cewar kalmomin ki, ni, da kuma ita, da aka yi amfani da su a waɗannan ɗangwayen waƙar suna matsayin wakilin suna Rakaɓau ne. Kasancewarsu suna cin gashin kai, ba a liƙa su da kowace irin kalma ta nahawu ba. Abin nufi sun fito a gurbin suna kai tsaye.

2.4.2 Wakilin Suna Tambayau;

Wakilin suna tambayau shi ne wanda ake amfani da shi a cikin jimla don tambaya ga wanda ya yi aiki ko Magana, ko wanda aiki ya faɗa a kansa (Junaidu da ‘Yar’aduwa, 2007, Sh.18). Wakilin suna tambayau da aka yi amfani da su a cikin waƙar Isa Lawan su ne;

8 (a) Wa zai faɗan haka sau bakwai fa da sauri? (baiti na 7).

(b) Me za na ce harshe na Hausa a duniya? (baiti na 20).

2.4.3 Wakilin Suna Zagin Aikatau;

Wakilin suna zagin aikatau koyaushe zuwa yake yi kafin aikatau, ko kuma a ce gaban aikatau. Wato da ka gan shi za ka ga kalmar aikatau biye da shi. Misali,

9. (a) Duk wanda ya faɗya zamo ɗan kirki, (baiti na 7).

(b) Za ka tsallake kogi ka zam ɗan zaki, (baiti na 9).

Wakilin Suna Zagin Aikatau da aka yi amfani da su a ɗangwaye na sama su ne ya da ka kuma kalmomin da suka biyo bayansu duk aikatau ne wato ‘faɗa’ da ‘tsallake’

2.4.4 Wakilin Suna Nunau;

Wakilin suna nunau shi ne wanda yake nuni da abu na kusa ko na nesa. Shi kuma iri biyu ne; akwai dogo da kuma gajere.

10. (a) Kuma ba a so wancan ya ƙwaru da wancan, (baiti na 10).

(b) Im ma waɗancan su suna ƙyamar ki, (baiti na 25).

Kalmar wancan tana nuni da abu na kusa tilo ko guda ɗaya. Sannan kalmar waɗancan tana nuni da wani abu fiye da guda ɗaya wanda yake nesa.

2.5 Aikatau

Aikatau muhimmiyar kalma ce a tsarin nahawun Hausa. Yawancin kalmomin Aikatau suna bayyana yanayi da irin aikin da aka aiwatar wanda yake tafiya da halin rayuwa na al’ummar Hausawa. CNHN (2006, Sh. 6) an bayyana aikatau da ‘wani ɗan aiki da za a yi don samun abin masarufi ko kalma mai bayyana aiki a nahawu.’

Masana irin su Bagari (1986) da Sani (1999) da Wakili (2018) da sauransu sun bayar da ma’anar Aikatu a ma’anoni daban- daban. Aikatau kalma ce mai ɗauke da ‘aiki’ a jimla.

Ana iya karkasa ajin ajin aikatau dangane da tsarin karin sauti Ko yanayin ƙarshensu. Waɗannan aikatau na Hausa an karkasa su zuwa gida bakwai don haka ma aka kira su da Darajoji Aikatau ɗin Hausa (Bagari, 1986; Shf.106).

A wannan takarda an lura Isa Lawan ya yi amfani da waɗannan Darajojin Aikatau ta fuskar yanayin ƙarshen gaɓa a cikin waƙarsa kamar haka;

2.5.1 Aikatau Mai Daraja Ta Ɗaya;

Aikatau mai daraja ta ɗaya a kullum wasalin –ko -aa ƙarshen gaɓar kalma. Kuma dukkan aikatau da ke kan wannan daraja ta ɗaya, masu ɗaukar karɓau ne. Misali;

11. (a) Na farà waƙata da sunan Rabbana, (baiti na 1).

(b) Da akwai dalilai zan faɗà a cikin ki, (baiti na 4).

(c) Tattàkàa takalminka tattaràa taki, (baiti na 6).

Harafin –da –aa da aka samu suke ƙarewa a kalmomin ‘faràa’ da ‘faɗà’ da ‘tattakàa’ da kuma ‘tattaràa’ su ne suka samar da Aikatau Mai Daraja ta Ɗaya.

Dangane da karin sauti (Hawa da sauka na murya). Idan aka dubi waɗannan misalai na (11 a-c) za a ga cewar kalmar farà tana da karin sautin sama a gaɓar farko da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta biyu (SƘ). Ita ma kalmar faɗà sautin shi ne SƘ. A yayin da kalmar tattàakà take da karin sautin sama a a gaɓar farko da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta biyu da karin sauti ƙasa a gaɓa ta uku (SƘS).

2.5.2 Aikatau Mai Daraja Ta Biyu;

Shi ne wanda yake ƙarewa da wasalin -i, ko -ee, ko -aa, ƙarshen gaɓar kalmar. Misali;

12. (a) Da akwai karda salon batu a cikin ki, (baiti na 5).

(b) Tabbata tana taka takadda tai tuɓus, (baiti na 6).

(c) Ita ce a cakuɗaa harsuna a cikin ki, (baiti na 11).

A misali na (12a-c) kalmar kàri tana da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta farko da karin sautin sama a kan gaɓa ta biyu(ƘS), sannan tàka (ƘS), haka kuma, càkuƙà tana da karin sauti ƙasa a kan gaɓa ta farko da karin sautin sama a kan gaɓa ta biyu da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta ƙarshe(ƘSƘ).

2.5.3 Aikatau Mai Daraja Ta Uku;

Shi ne mai ƙarewa da gajeren wasalin –a ƙarshen gaɓar kalma. Kuma ba ya ɗaukar karɓau. Misali;

13. (a) Da akwai dubun hikimda ban mamaki, (baiti na 26).

(b) Makaɗnake so ‘yan kaɗan zan bayyana (baiti na 73).

A waɗannan misalan ɗangwaye na sama da aka bayar, Karin sautin hìkimà da màkaɗà dukkanninsu sun kasance gaɓoɓin farko karin sautin ƙasa ne da karin sauti a gaɓa ta biyu da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta uku (ƘSƘ).

2.5.4 Aikatau Mai Daraja Ta Huɗu;

Shi ne mi ƙarewa da wasalin-ee/-e ƙarshen gaɓar kalma. Ana samun aikatau masu daraja ta huɗu kalmomi masu ɗaukar karɓau da kuma marasa ɗaukar karɓau. Misai;

14. (a) Waƙèe nake so zan wa harshen Hausa, (baiti na 3).

(b) Tabbat tana take takadda tai tuɓus, (baiti na 6).

(c) Za ka tsallakee kogi ka zam ɗan zaki, (baiti na 9).

A waɗannan misalai na sama (14a-c), Kalmar waƙee tana da karin sautin sama a kan gaɓar farko da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta biyu (SƘ), sannan Kalmar tsallàkee tana da karin sautin sama a kan gaɓa ta farko da karin sautin ƙasa kan gaɓa ta biyu da karin sautin sama a kab gaɓa ta uku (SƘS).

2.5.5 Aikatau Mai Daraja Ta Biyar;

Shi ne mai ƙarewa da –ar + (da) ƙarshen gaɓar kalma. Aikatau mai daraja ta biyar yana ƙarewa ne da –ar, kuma akan yi amfani da harafin da a tsakanin aikatau ɗin da karɓau ɗinsa, sawa’un karɓau suna ne ko lamiri. Duk gaɓoɓin aikatau suna ɗaukar karin sautin sama-sama ne SS (Bagari,1986, sh.109). Misali;

15 (a) Koyar da yadda ake abinci a ɗaki, (baiti na 29).

Kalmar koyar da, da ta zo a wannan ɗango na cikin waƙar tana da karin sautin (SS).

2.5.6 Aikatau Mai Daraja Ta Shida;

Shi ne mai ƙarewa da wasalin –oo ƙarshen gaɓar kalma. Ana iya ƙirƙiro aikatau mai daraja ta shida mai ɗaukar karɓau ko marasa ɗauka. Misali;

16 (a) Duk wanda ya faɗa ya zamoo ɗan kirki, (baiti na 7).

(b) Dukkansu na watsoo shiri a cikin ki, (baiti na 13).

(c) Kuma ga samarin Jami’a duka sun fitoo (baiti na 16).

Kalmomin zamoo da watsoo suna da karin sautin sama a kan gaɓa ta farko da karin sautin sama a kan gaɓa ta ƙarshe (SS).

2.5.7 Aikatau Mai Daraja Ta Bakwai;

Shi ne mai ƙarewa da wasalin –ƙarshen gaɓar kalma. Haka kuma aikatau mai daraja ta bakwai a kullum gajeren wasalin –ne, kuma aikatau ɗin ba ya ɗaukar karɓau. Babbar ma’anar da ke ƙunshe cikin aikatau mai daraja ta bakwai shi ne nuna tsananin aiki ko kuma aikata aiki sosai lokacin da aka yi amfani da shuɗaɗɗen lokaci, amma idan an yi amfani da lokaci mai zuwa ne, ma’anarsa takan ƙunshi yiwuwa ne. (Bagari,1986, sh.110). Misali;

17 Kuma ba a so wancan ya ƙwaru da wancan, (baiti na 10).

Kalmar ƙwarù ɗango na sama tana sama a kan gaɓa ta farko da karin sautin ƙasa a kan gaɓa ta ƙarshe (SƘ).

2.6 Ƙarfafawa

Ƙarfafawa ta ƙunshi kalmomi ko harrufa da aka yi amfani da su domin a nuna muhimmanci abin da ake zance a kai (Mukhtar, 2005, Sh. 40). Ana amfani da kalmar fa domin a nuna ƙarfafawar. Wuraren da aka yi amfani da ƙarfafawa a cikin waƙar ta Isa Lawan su ne kamar haka:

18(a) Wa zai faɗan haka sau bakwai fa da sauri, (baiti na 7).

(b)Sannan fa kun san alkubus akwai daɗi, (baiti na 37).

(c) Joha fa kowa ya sani riga ce, (baiti na 60).

2.7 Giɓin Jimla

Giɓin jimla shi ne cire ko shafe wani abu daga cikin jimla da ya kamata a ce akwai shi. Mawallafin ya yi amfani da rage ko shafe wani abu daga cikin jimloli waƙar domin ta tafi da amsa-amo bai ɗaya na cikin waƙarsa (Mukhtar, 2005, Sh.38).

Shi kuwa Sarɓi (2007, sh.150) ya bayyana, wannan da wata hikima ce da mawaƙa sukan yi amfani da ita domin yin ƙari ko ragi a cikin kalma ko jumla domin daidaita waƙoƙinsu.

An sami yanaye-yanaye mabambanta a ɗangwayen waƙar Isa Lawan ta fuskar giɓin jimla musamman ta yadda ya jujjuya wasu kalmomi da kuma ginin jimloli sannan ya sarƙa su a wajen ƙulla matanin waƙar. Misali:

2.7.1 Yanayin Shafewa

Shafewa wani yanayi ne inda ake cire wani ɓangare da yake cikin kalma ko shafe wata kalma a yayin da ake gina ɗango na waƙa. Ga bayaninsu kamar haka:

2.7.1.1. Shafe Wasali

Sani (2005, sh. 40) ya ba da ma’anar shafe wasali da cewa;’abin da ake nufi takamaimai shi ne cire wasali daga kalma domin taƙaita lafazinta’. An sami ɓullar shafe wasali a wannan ɗango na waƙar:

19 (a) Za ka tsallake kogi ka zam ɗan zaki, (baiti na 9).

Wannan misali ya nuna yadda aka sami shafewar wasali a cikin kalmar zama. A nan, mawaƙin ya shafe wasalin /a/ daga kalmar zama inda ya mayar da kalmar ta koma zam kawai. Saboda haka ana iya cewa an sami giɓin jimla ta fuska shafe wasali da yake cikin wata kalma domin daidaita awon waƙar.

2.7.1.2 Shafe Gaɓa

Umar (2014, sh.51-52) ya bayyana ma’anar gaɓa da cewa; yanki ne na furucin kalma mai tsarin baƙi da wasali (BW) a jere. Kuma tsarin gaɓoɓin Hausa yana tafiya ne tare da kashe- kashen gaɓa waɗanda suka haɗa da buɗaɗɗiyar gaɓa wadda ta ƙunshi goshi[1] da cibiya[2]. Ita kuwa rufaffiyar gaɓa tana da tsarin goshi da cibiya da kuma ƙeya[3]. Dubi wannan misali mai zuwa kamar haka;

20 (a) A cikin harasan duniya duka ba yake, (baiti na 4).

A wannan ɗango na sama, Isa Lawan ya shafe cikakkiyar gaɓa (wadda ta ƙunshi baƙi da wasali (BW) = bu. Kamata ya yi ɗangon waƙar yakasance kamar haka;

A cikin harasan duniya duka babu yake.

Amma saboda lalura ta waƙa domin awon ta ya tafi daidai sai ya shafe gaɓa ta biyu ta cikin kalmar.

2.8 Yankin Umartau

Umartau su ne kalmomi ko harrufa da ake amfani da su wajen wani domin ya yi aiki. To, amma saboda addini za a iya cewa roƙo ne ko kuma fata ne (Mukhtar, 2005, Sh. 40). An yi amfani umartau a wannan jimla kamar haka:

21 Koyar da yadda ake abinci a ɗaki, (baiti na 29)

Idan aka dubi wannan misali na (21) za ga cewa kalmar koyar da, da ta zo a cikin ɗangon waƙar ta zo da sigar bayar da umarni da a koyar da yadda ake abinci. Bagari (1986) ya yi bayanin cewa ‘Duk kalmar aikatau da take ƙarewa da –ar kuma aka yi amfani da harafin da a tsakanin aikatau da karɓau ɗinsa, sawa’un karɓau suna ne ko lamiri, wannan yana a matsayin ‘sakawa’ wato a saka mutum ya aikata wani abu’ 

2.9 Tsigalau

Kalmar tsigalau tana zuwa ne a jimla don nuna ƙanƙantar abu ko kuma jingina shi da wani yanayi ko sana’a da sauransu. Kuma tana zuwa ne kafin suna ko abin da suke nuna ƙanƙantarsa (Wakili, 2018, Sh.52). Kalmomin tsigalau da suka bayyana a cikin waƙar su ne kamar haka:

22. (a) Duk ɗan halak shi ne yake fahari da ke, (baiti na 14).

(b)Tijjani ɗan Hashim Galadiman Kano, (baiti na23).

(c)Waina gurasa mun sani ‘yan Hausa ne, (baiti na 31).

Ana amfani da ɗan dangane da jinsin namji tilo. Idan kuma jam’i ne akan yi amfani da ‘yan. A misali na 22 (a), mawallafin waƙar, ya fito da halin da duk wanda yake alfahri da harshen Hausa ya zama ɗan halak. Yana cikin wani yanayi da jama’a za su so, shi kuma su yi alfahri da shi saboda kisihin da yake yi wa harshensa

A misali na 22 (b), ana so a nuna cewa Tijjani, Galadiman Kano mahaifinsa shi ne Hashim.

A misali na 22(c) an ambaci wasu nau’o’in abinci da ake samun su a ƙasar Hausa. 

2.10 Dirka

Dirka kalma ce a nahawu da take zuwa a matsayin ‘ya raɓa- dan-ni. Wato ‘yar rakiya ce na wasu kalmomi a cikin jimla. kuma tana biyo bayan kalmomin da take rakiyar. Kalmomin dirka su ne; ne (jinsin namiji tilo) da ce (jinsin mace tilo) da ne (dangane da jam’i). Misali;

23 (a) Nai alƙawar ni ne mijinki a Jami’a, (baiti na 17).

(b)Tamatansa ce Larai ina gaishe ki, baiti na 41.

Kalmomin ne da ce da aka kawo a ɗangwaye na (22a-b) domin su daidaita ko su dace manufar gina ɗangon waƙar.

2.11 Ma’auni

Ma’auni kalma ce da ke fitowa a jimla da nufin nuna ƙimar abu ko don a ƙirgo abubuwa. Ma’auni da aka yi amfani da su a cikin waƙar su ne;

24 (a) Wa zai faɗan haka sau bakwai fa da sauri, (baiti na 7).

(b) Miliyan ɗari na dala sadaki na ki, baiti na (17 da 18).

A baiti na 24 (a) Isa Lawan ya yi amfani ma’auni na adadi wato a ƙidaya salon magana na Hausa cikin sauri sau bakwai. A misali na 24 (b) kuma, Dala miliyan ɗari da mawallafin waƙar ya yi alƙawari zai bayar yana kimanta tare nuna darajar abin da zai bayar a matsayin sadaki.

2.12 Yankin Siffatau

Yankin Siffatau kalmomi ko harrufa da suke daɗa siffanta wani abu a cikin jimla (Mukhtar, 2005, Sh. 46). Misali:

25. (a) Sarkin Sarauta mai sani Mai mulki, (baiti na 1).

(b) Da akwai hikima da ban mamaki, (baiti na 2).

Mawallafin waƙar ya yi amfani da kalmar Siffatau mai, a misali na (25a) domin ta daɗa jaddada irin iko na Allah maɗaukakin Sarki wato sarkin sarauta masanin dukkkan al’amuran bayi kuma mai iya gudanar da mulki cikin ayyyukansa.

A misali na (25b) kuwa, kalmar siffatau da ta zo a cikin ɗango ita ce ban, abin nufi harshen Hausa cike da hikimomi sannan kuma ga ban mamaki ga masu koyo ko masu nazari a cikinsa ko ma masu magana da shi a matsayin harshen uwa.

2.13 Kalmomin Fannu

Kalmomin Fannu su ne kalmomin da mawallafin waƙa ya yi amfani da su domin ya tayar da jigon waƙarsa. Mukhtar (2005) ya bayyana kalmomin fannu su ne keɓaɓɓun kalmomi da aka yi amfani da su a waƙar domin cim ma burin abin da ake so a bayyana. Kowane fannin ilimi kamar kimiyya ko fasaha ko aikin gona ko siyasa ko likitanci da sauransu akwai kalmomin da suka keɓanta da fannin da za a yi amfani da su domin cim ma manufa.

A wannan waƙar, Isa Lawan ya yi amfani da kalmomin fannu da suka danganci Harshen Hausa da al’adun Hausawa kaɗan daga ciki su ne; wasa ƙwaƙwalwa da zaurance da ingausa da shirye-shiryen Hausa a kafofin watsa labarai na ƙasashen waje da sunayen Hausawa na gargajiya irin su Ɗanliti da Talle da Larai da sauransu da sunayen abincin gargajiya kamar alkubus da ɗanwake da tubani da dambu da sauransu. Tufafin Hausawa da aka ambata a cikin waƙar domin isar da saƙon waƙar sun ƙunshi; aska takwas da aska tara da shabka ‘yar shara da shakwara da jamfa da sauransu. Misali, Wasa ƙwaƙwalwa a cikin waƙar inda yake cewa;

2.13.1 Wasa-Ƙwaƙwalwa;

Harshenmu ni na san da wasa ƙwaƙwalwa,

Ga ɗan misali zan faɗa a cikin ki.

(baiti na 8).

2.13.2. Salon Magana;

27 Kura, kare, akuya, da gari naka ne,

Za ka tsallake kogi ka zam ɗan zaki.

Kuma ba a so wancan ya ƙwaru da wancan,

kuma ɗaiɗai ake so ka kai su da aiki.

(baiti na 9, 10, da 11).

2.13.3 Sunayen Hausawa Na Gargajiya;

28 Sunannakin rana akwai su a Hausa,

Ɗalladi Ɗanliti Tala gaishe ki.

Sannan Talata Talle shi ne sunan,

Sannan Talatu macensa na gaishe ki.

Sannan Balarabe Laraba aka haifar,

Tamatansa ce Larai ina gaishe ki’

(baiti na 39-41

2. 13. 4 Tufafin Hausawa Na Gargajiya

29 Kayayyaki sawa akwai su a Hausa,

Riga wando har da hular saƙi’

Riga ta saƙi ma akwai ta a Hausa,

Sannan billen kaji sarkin aiki.

Aska bakwai Aska ta Takwas Aska tara,

Sannan da Adda don gabanta da aiki.

(baiti na 50-52).

Dangane da shirye-shiryen Gidajen Rediyo da kafofin watsa labarai na ƙasashen waje suke gabatarwa cikin harshen Hausa, Isa Lawan ya kawo wasu daga cikinsu kamar;

30 Duba Faransa da Ingila da Amerika, Dukkansu na watso shiri a cikin ki.

(baiti na 13).

Waɗannan ƙasashe da aka ambaci sunayensu a baitin waƙar a siyasa da tattalin arziki da cigaban zamani ta fuskar ƙere-ƙere suna kan gaba. Kuma ƙasashe ne masu faɗa a duniya. Amma duk da wannan da suke da shi sun ware lokuta a Gidajen Rediyoyinsu suna watsa shirye-shirye da harshen domin duniya ta saurara. Misali, Sashen Hausa na BBC London da Rediyon Muryar Amurka (ƁOA) da Rediyon Faransa (RFI) da sauransu.

2.13 Kalmomin Aro

Kalmomin aro su ne kalmomin da marubucin waƙoƙin Hausa ya ɗebo su daga cikin wani harshe ya yi amfani da su a cikin Hausa.Wani lokaci akan yi wa irin waɗannan kalmomi kwaskwarima domin su dace da wurin da aka yi amfani da su. Wani lokaci kuwa akan bar su ma yadda suke a harshen a asali (Sarɓi, 2007, sh.140-141).

A cikin wannan waƙa ta ‘Harshen Hausa’ mawallafinta ya yi aron kalmomin musamman daga harshen Larabci kamar haka:

Kalma fassara da Hausa baiti

31 (a) Rabbana Ubangijinmu (Allah) (baiti na 1).

(b) Mulki gudanar da harkokin hukuma kan jam’a (baiti na 1).

(c) Shabbaki Ɗakin Allah (Ka’aba) (baiti na 2).

(d) Fakhri Abin alfahari (baiti na 3).

(c) Halak Abin da ya hallata a yi (baiti na 14).

2.14 Karin Harshe

Harshen Hausa yana da kare-kare iri daban daban, duk da cewa akwai daidaitaccen kari wanda masana suka fi amfani da shi kuma ake amfani da shi a hukumance da makarantu da kuma kafafen yaɗa labaru. Zulyadaini (2003) ya bayyana Karin Harshe da cewa shi ne yadda fasihan mawaƙa kan sarrafa karin harshe a cikin waƙoƙinsu saboda dacewa da buƙatunsu na ƙawata ayyukansu na fasaha ko fita daga wata lalura irin ta waƙa. Shi kuwa Sarɓi (2005) ya bayyana ma’anar Karin Harshe da cewa bambance- bambance ne da ake samu tsakanin masu magana da harshe ɗaya, dangane da shiyya/yanki da zamantakewa da kuma nau’in sana’a.

Fagge (2001) da Sani (2009) da Salihi (2012) da Mukhtar (2017) da sauransu sun yi bayanin ire-iren Karin Harshe a cikin ayyukansu. Mawallafin wannan waƙa Bahaushe ne, amma ya sako kalmomin Sakkwatanci. Wataƙila ya yi hakan ne saboda lalurar waƙa. Wasu daga cikin kalmomin na Sakkwatanci su ne kamar haka;

32 (a)Tabbat maimakon tabbata (baiti na 6).

(b)Takadda maimakon takarda (baiti na 6).

(c) Tai maimakon ta yi (baiti na 6).

(d) Nai maimakon na yi (baiti na17).

(e) Gai maimakon gaisar (baiti na 23).

(f)A kai maimakona ka yi (baiti na 38).

2.15 Lokaci

A wannan ƙaramin sashe za a dubi yadda Isa Lawan ya yi amfani da lokutan Hausa wajen isar da saƙon waƙarsa. Lokaci yana taka muhimmiyar rawa a cikin jimla domin shi ne yake bayyana lokacin da aka gudanar da aiki. Lokaci a nahawu yana nufin sa’ar wanzar da aiki ne a cikin jimla. Aikin zai iya kasancewa an wanzar da shi ya wuce, ko an wanzar da shi a halin yanzu ko kuma za a wanzar da shi a nan gaba (Sani, 1999, Sh. 71). Ana iya gane lokaci idan aka liƙa wani harafi a jikin wakilin suna. Ire-iren lokutan Hausa da suka ɓulla a Waƙar Hausa su ne kamar haka:

2.15.1 Shuɗaɗɗen Lokaci na 1

Shuɗaɗɗen Lokaci shi ne yake nuni da wani aiki da aka gudanar a wani lokaci da ya wuce. Wato an riga an wanzar da aikin. Misali:

33 (a) Naa fara waƙata da sunan Rabbana, (baiti na 1.)

(b) Kin kwalliya kisha ado da turare, (baiti na 15).

(c) An kai ni har birnin Makka da Madinatu (baiti na 21).

Alamar shuɗaɗɗen lokaci na 1 shi ne –a, da –n, da karin sautin (SS) da ake liƙawa jikin wakilin suna kamar yadda suka ɓulla a misali na 33(a-c).

2.15.2 Lokaci na Yanzu

Lokaci na Yanzu shi ne wanda yake nuni da aikin da ke gudana a halin da ake ciki a yanzu. Misali:

34. (a)Tabbat tana take takadda tai tuɓus, (baiti na6).

(b)Kowa yana nema ya zam auren ki, (baiti na 16).

(c)Dr. Magaji ina ta miƙo gaisuwa, (baiti na 29).

Alamar lokaci na yanzu shi ne –na da karin sautin (ƘS) da ake liƙawa a jikin wakilin suna kamar yadda aka yi amfani su a misali na 34(a-c).

2.15.3 Lokaci Mai Zuwa Na Ɗaya

Lokaci mai Zuwa na Ɗaya shi ne yake nuni a kan aikin da za gudanar ko wanzar da shi a wani lokaci nan gaba. Misali;

35. (a) Wa zai faɗan haka sau bakwai fa da sauri, (baiti na 7).

(b) Za ka tsallake kogi ka zam ɗan zaki, (baiti na 9).

(c) Me za na ce harshe na Hausa a duniya, (baiti na 20).

Alamar lokaci mai zuwa na 1 –za, da karin sautin (SS) da yake zuwa a farkon jimla ko tsakiyar jimla kamar yadda suka zo a misali na 35(a-c).

3.0 Kammalawa

Wannan takarda ta yi bayani ne dangane da yadda aka yi amfani da wasu rukunonin nahawu a wata rubutacciyar waƙa mai suna Waƙar Hausa wadda Isa Lawan ya rubuta. A wannan takarda an fahimci cewa da wuya mutum ya wallafa waƙa ba tare da ya yi amfani da ɗaya daga cikin rukunoni nahawu ba. Sai dai yadda ya yi amfani da su a cikin waƙar shi ne abin dubawa. Kazalika, binciken ya gano a cikin waƙar an yi amfani da waɗannan rukunonin nahawu; Ginin jimloli gajeru kuma masu sauƙin fahimta da amfani da sunaye iri-iri har ma da na gargajiya da aikatau da ƙarfafawa da giɓin jimla da tsigalau da dirka da ma’auni da Karin Harshe da sauransu.

Sannan kuma, an fahimci cewa waɗannan rukunan nahawu da suka ɓulla a cikin waƙar an yi amfani da su ne a matsayin Salo da Sarrafa Harshe domin mai sauraro ko mai karatu ya fahimci saƙon da waƙar take ɗauke da shi cikin sauƙi.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Northern Nigeria Publishing Company.

Abdulƙadir, Ɗ. (1974). Waƙoƙi na da da na yanzu. Northern Nigeria Publishing Company.

Ahmad, A. A. (2012). Sharhin azancin waƙar Hausa. Champion of Hausa Cikin Hausa a Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad, 200-211.

Auta, A. L. (2008). Rubutattun waƙoƙin faɗakarwa a kan jigon ilimi a ƙarni na ashirin. [Kundin Digiri na Uku]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero Kano.

Bagari, D.M. (1986). Bayanin Hausa jagora ga mai koyon ilimin bayanin harshe. Imprimerie ElMaarif Al Jadida.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa na jami’ar Bayero. Ahmadu Bello University Press.

Ɗangambo, A. (1981). Rikiɗar azanci: Siddaarun salo da harshe cikin tabarƙoƙo. Tahmisin Aliyu Ɗansidi Sarkin Zazzau. A Cikin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar gadon feɗe waƙa. Amana Publishers.

Ɗangambo, A. (2009). Adabin Hausa da mazhabobin tarke na duniya; wa ta duba? Cikin Baldi, S. da Yakasai, H. M. (Editoci). Proceedings of the 2nd International Conference on Hausa Studies; African and European Perspectiɓes, 82-97.

Ɗangambo, H. A. (2014). Gudummawar Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo ga adabin Hausa cikin littafin ɗaurayar gadon faɗe waƙa. Cikin Gusau, S.M. da Sani, M.A.Z. da Birniwa, H.A. da Mukhtar I. da Aliyu, I. da Adamu, J.S. (Editoci) Garkuwan Adabin Hausa. A Festrschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Ahmadu Bello University Press.

Ɗangambo, S. A. (2014). Waƙoƙin yabon Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo. K. D. G. Publishers.

Fagge, U. U. (2001). Ire- iren karin harshen Hausa na rukuni. Bench-mark Publishers.

Funtuwa, A. I. (2011). Manufar waƙa a siyasa; Ire-iren jigogi waƙoƙin siyasa na Hausa. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, 2(1).

Gabari, A. U. (2014). Tarken waƙar harshen Hausa ta Isa Lawan.The Kumbotso Teacher Edicator (KUTEJ): A Journal of Multidisciplinary Studies, Vol.5.

Junaidu, I. da ‘Yar’adu’a, T. M. (2007). Harshe da adabin Hausa a kammale.

Spectrum Books.

Mukhtar, A.B. (2017). Hausa da karorinta. Goɓernment Printing Press.

Mukhtar, I. (2005). Bayanin rubutattaun waƙoƙin Hausa. Countryside Publishers.

Sai’d, B. (2002). Rubutattun waƙoƙin Hausa na ƙarni na ashirin a jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara: Nazari akan bunƙasarsu da hikimomin da ke cikinsu [Kundin Digiri na Uku], Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Salihi, T.M. (2012). Sakace a kan karin harshen Hausa. Ɗorayi Babba Commercial Press,

Sani, M.A.Z. (1999). Tsarin sauti da nahawun Hausa. Uniɓersty Press.

Sani, M. A. Z. (2009). Siffofin daidaitacciyar Hausa. Bench-mark Publishers.

Sani, M.A.Z. (2012). Yabon Ma’aiki da gargaɗi a diwanin waƙoƙin Hajiya Halima. Cikin Amfani, A.H. da AL-Hassan, B. S. Y. da Malumfashi, A. I. da Tsoho, M. Y. Amin, M. L. da Abdullahi, B. (Editoci), Champion of Hausa Cikin Hausa A Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad, 200-211.

Sarɓi, S. A. (2007). Nazarin waƙen Hausa. Samarib Publishers.

Sarɓi, S.A. (2005). Tasirin Harshen Hausa A Kan Wasu Keɓaɓɓen Harsunan Jihar Nassarawa. Kundin Digiri Na Biyu, Sokoto; Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodio University.

Satatima, I. G. (2014). Harshen waƙa: Ma’anarsa da rabe-rabensa. Cikin Gusau, S.M. da Sani, M.A.Z. da Birniwa, H.A. da Mukhtar I. da Aliyu, I. da Adamu, J.S. (Editoci) Garkuwan Adabin Hausa. A Festrschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo.

Shu’aibu, M. (2013). Tasirin mazhabobin adabi na duniya a kan tarken adabin Hausa. [Kundin Digiri na Uku], Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Umar, M. M. (2014). Gamayyar tasarifi da tsarin sautin kalmomin Hausa masu yawan gaɓoɓi shida. A Cikin Himma Journal of Contemporary Hausa Studies Vol.5(1).

Yakasai, M.G. (2014). Nazarin kwatanta salo da waƙoƙin Shehu Abubakar Atiku Sanka da Na Liman Muhammadu Ɗan’amu [Kundin Digiri Na Uku], Sashen Koyar da Harsunan Nijeria, Jami’ar Bayero, Kano.

Wakili, S. S. (2018). Bitar nahawun Hausa. Al-ameen Printing Publishing Company.

Yahaya, I. Y. da Zariya, M.A.Z. da Gusau, S.M. da ‘Yar’aduwa (1992). Darrusan Hausa don manyan makarantun sakandare. Uniɓesity Press.

Yahya, A. B. (2007). Jigon nazarin waƙa. Fisbas Media Serɓices.

Zaria, A. B. (1981). Nahawun Hausa. Thomas Nelson Nigeria.

Zulyadaini, B. (2003). Dialect miɗture in Hausa poetry, [PhD thesis]. Department of Languages and Linguistics, University of Maiduguri.


[1] Baƙin farko wanda ke zuwa a cikin gaɓa.

[2] Wasalin da ke zuwa bayan gaɓa, wato yana biyo bayan goshi ke nan.

[3] Baƙi ne wanda yake zuwa a ƙarshen gaɓa, musamman rufaffiya. 

 Yobe Journal

Post a Comment

0 Comments