Ticker

6/recent/ticker-posts

Sigogin Adon Harshe a Wasu Wakokin Siyasa Na Kamilu Hussaini Nguru

Citation: Musa Muhammad CHIROMARI (2020). Sigogin Adon Harshe a Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kamilu Hussaini NguruYobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Ɓol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State Uniɓersity, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

SIGOGIN ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN SIYASA NA KAMILU HUSSAINI NGURU

Musa Muhammad CHIROMARI

Tsakure

Wannan takarda ta yi nazari ne a kan amfani da adon harshe a waƙoƙin siyasa na Kamilu Hussaini Nguru. Saboda haka, maƙasudin gudanar da bincike shi ne nazari a kan waɗannan waƙoƙi don gano hikimar da ke tattare da amfani da adon harshen da kuma amfanin yin hakan a cikin waƙoƙinsa. Domin gano hakan ne muka yi amfani da ra’in Gusau (2003). A hanyoyin tattara bayanai kuwa an yi amfani da hira da sauraron waƙoƙin tare da juyarsu, an kuma yi zaiyarce-ziyarce. Sannan a yayin binciken an gano cewa wannan mawaƙi lallai ya yi amfani da adon harshe sosai, waɗanda suka haɗa da kamantawa, siffantawa, jinsintarwa, alamtarwa, ƙarangiya da kuma kinaya. Har wayau na daga cikin dalilan amfani da wannan salo ga mawaƙin, kamar yadda muka gano, shi ne bayyana hoto, ƙiyasi, ba da haushi, kambamawa da ƙara wa waƙa armashi da karsashi wajen masu sauraro.

1.0 Gabatarwa

Masana irin su; Gusau (2008) da Yahaya da wasu (2007) da Ɗangambo (2007) da Abba da Zulyadaini (2000) da ma wasu masana sun bayyana cewa waƙoƙin baka na Hausa sun daɗe da faruwa, tun kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa. Kuma har ya zuwa yanzu ana aiwatar da wannan fasaha ta baka. Duk da canje-canje da zamani kan haifar, waƙa a wajen al’ummar Hausawa bunƙasa da inganta da sha’awa ta samu a ƙasar Hausa. Shi kuma adon harshe masana irinsu; Gusau (2003) da Yahaya (1995) da Dija (1997) sun bayyana cewa wata dabara ce da ake yi wa harshen waƙa ko furuci kwalliya domin ƙara mata armashi da daɗi. Wani lokaci kuma yakan zama ma’auni da gwada hikimar zance da balagar da Ɗan-adam yake da ita domin burge mai sauraro. Ita wannan takarda an gabatar da ita ne a kan Sigogin Adon Harshe a wasu Waƙoƙin Siyasa na Kamilu Hussaini Nguru.

An haifi Kamilu a wani ƙauye da ake kira Beta, da ke ƙaramar hukumar Sumaila ta jihar Kano a shekarar 1980. An kai shi karatun Allo wajen malaminsa mai suna Sani Dogon Kwari a garin Nguru na Jihar Yobe tun yana ɗan shekara huɗu da haifuwa, kana daga bisani iyayensa suka ƙauro garin na Nguru. Yanzu yana zaune a unguwar Hausari Zangon Kanwa a garin Nguru. Ya fara waƙa a shekara ta 2008, ya shahara a fannin waƙoƙin da suka shafi siyasa a Jihar Yobe da ma wasu jihohi na Arewacin Nijeriya. Mawaƙin ya yi waƙoƙi da dama kuma waƙoƙinsa na siyasa ne Chiromari (2013).

2.0 Ra’in Bincike

A wannan takarda an yi amfani da ra’in Gusau (2003); wannan ra’i ya yi bayani a kan irin hanyoyin da za a bi don gudanar da nazarin waƙar baka ta Hausa. Masanin ya yi bayani ne a kan yadda adon harshe yake tare da kawo sassansa da kuma yadda za a nazarce su. Wannan kuma shi ne abin da za a binciko a wannan takarda.

3.0 Adon Harshe a Waƙoƙin Kamilu Hussaini Nguru

Harshen Hausa ma, kamar sauran harsuna yana cike da adonta harshe. Saboda haka, waƙoƙin mawaƙa da makaɗan baka na Hausa, cike suke da irin wannan dabara domin isar da saƙontsu cikin salo mai armashi da burgewa tare da ƙawatarwa. Sannan adon harshe yana da sassa da dama waɗanda suka haɗa da: kamantawa da siffantawa da jinsintarwa da kinaya da ƙarangiya da kuma alamtarwa, ga misalansu daga cikin waƙoƙin. Dangane da haka Kamilu Hussaini Nguru ma ba a bar shi a baya ba wajen amfani da adon harshe don ƙawata waƙoƙinsa ga masu sauraro da waɗanda yake yi domin su. kamar yadda za mu gani a bayanan da ke biye:

3.1 Kamantawa

Gusau (2003, sh.55), ya bayyana kamantawa da cewa “Dabara ce wadda ake kwatanta abubuwa biyu dangane da wasu darajoji da za su iya zama na daidaito ko na fifiko ko kuma na kashi”. Ana amfani da wasu kalmomi da ke nuna kamance a fili da ake kira kalmomin kamantawa ko kalmomin tsakani. Misali, kamar da ca kake da tamkar da awa da kama da sai ka ce da daidai da bai kai da wadda ya wuce da I kaza da gaza da wane da fi da makamantan waɗannan kalmomi da yawa. Kamantawa tana iya zama kamantawar daidaito ko fifiko ko kuma ta kashi.

3.1.1 Kamantawa Ta Daidaito

A kamantawar daidaito, kamar yadda sunan ya nuna, mizanin kan bayyana daidaituwar abu da ta wani abu daban. Wato kamanta abubuwa masu daraja iri guda. Misali waƙarsa ta Ali Idris Diginsa yana cewa:

Jagora :Shi rowan shayin ga akwai zafi mu mun ƙyale shi ya ɗau sanyi,

:Ahmad burgun dutse gwamna mu mun gode maka sai mun yi,

:Wancan Difitin ba ya ƙyauta mu ya ƙyale mu kamar bayi,

(Nguru, K. H; Waƙar. Ali Idris Diginsa).

A wannan gunduwa da ta gabata ya yi kamantawa ta daidaito a inda ya kamanta kansu da bayi sanadiyar rashin kulawa da yake cewa Difiti ya musu. Kamar yadda mawaƙin ya nuna da su da bayi daidai suke a wajen Difiti.

3.1.2 Kamantawa Ta Kashi

Mawaƙa suna amfani da wannan dabara ce ta hanyar kwatanta abubuwa biyu sai a ƙasƙantar da guda, ta yadda kowa ya saurara ya san cewa kaza ya gaza kaza. Misali:

Jagora Jirgin ruwa komai linƙaya nina san bai yi ya kifi ba

 :Gaskiya a siyasa ba ƙarya Dan Idi ba su yi kamar kai ba

 :- - - - - - - - - - - - -

(Nguru, K. H; Waƙar, Ali Idris Diginsa)

A wannan gunduwa mawaƙin ya ƙasƙantar da jirgin ruwa ne yana nuna cewa komai iya linƙayarsa a ruwa bai kai kifi ba, a gaba kuma yake ƙasƙantar da abokanan hamaiyar gwarzonsa da cewa a wajen yin gaskiya ba su yi kamar shi ba.

Jagora :- - -

 :Ahmad mun yadda batun tsere ɗan zomo bai yi barewa ba.

(Nguru, K. H; Waƙar Ali Idris Diginsa)

A nan ma ya ƙasƙantar da ɗan zomo ne yana mai nuna cewa idan batun gudu ake yi to bai kai barewa ba.

Amshi : Jaki bai fi rago ba

: Ai idan daraja ake nema

: Ali Ɗan Idirisa ke godiya a wajen Allah maso bayi

 (Nguru, K. H; Waƙar Ali Idris Diginsa)

A wannan waje da ya gabatar ya ƙasƙantar da jaki ne inda yake nuna idan magana ta daraja ake yi to rago ya fi jaki. Za mu gane haka ne yayin da muka duba matsayin rago na daraja da yake da ita misali ta fuskar halaccin namansa da kuma matsayinsa a layya ba kamar jaki ba.

3.1.3 Kamantawa Ta Fifiko

A wannan hanya a kan kwatanta abubuwa biyu ne ta hanyar ɗora ɗaya bisa ɗaya. Wato a nuna abu kaza ya fi abu kaza. Misali;

Jagora : Riɗi da gyaɗa akwai garɗi

: Soyayya ma akwai daɗi

: Shi mutunci wadda ya fi kuɗi

-                      - - -

(Nguru, K H; Waƙar Ali Idris Diginsa).

A wannan gunduwa da ta gabata mawaƙin yana nuna fifiko tsakanin mutunci da kuɗi.

Jagora :- - - - -

 :Magana ta zumunci mai ƙarfi mata fannin haka sun fi maza

 :Ƙere-ƙere marar adadi wannan sai an koma gun Turawa

(Nguru, K. H; Waƙar Ali Idri Diginsa)

A wannan waje mawaƙin yana nuna irin fifikon da mata suka yi wa maza a ɓangaren sada zumunci, wato riƙo da zumunta a tsakanin mutane.

3.2 Siffantawa

Ɗangambo (2007, sh. 43), ya bayyana siffantawa da cewa, “Siffantawa kamar kwatantawa ce, sai dai ita kwatance ne na kai tsaye. A kan ɗauki darajar wani abu ko halayyarsa, a ɗora wa wani kai tsaye, wato a ce ‘kaza’ ko kaza, kaza ne, shi ne kaza”. Siffantawa ta kasu kashi biyu, wato gajeriya da doguwar siffantawa.

3.2.1 Gajeriyar Siffantawa

Gajeriyar siffantawa kwatance ce ta falan ɗaya, wato sau ɗaya ake kwatanci. Ɗangambo (2007, sh. 44). Misali;

Jagora :- - - -

 :Waƙar zan haɗa mahauta bangaru sai aminan asali

 :Indai mutum mahauci ne shi kara gare shi ba shakku ba.

(Nguru, K. H; Waƙar Baba Machina)

A wannan waje mawaƙin ya siffanta mahauta da halinsu na rashin jin tsoro ko shakkar mutum, idan abu ya haɗa ku sai dai idan suna jin kunyarka su maka kara, ba wai don tsoro ba.

Jagora :Kun san tashi sama sai tsuntsu,

: A ci zali ai dawa sai kura

: A faɗa a cika ɗan Diginsa ya Ali mun gode maka talakawa

(Nguru, K. H. waƙar Ali Idriss Diginsa).

A nan mawaƙin yana siffanta tsuntsu ne da cewa tashi sama yake yi ba kamar dabba ba, ya kuma siffanta kura da halinta na cin zali da kuma tsoro.

3.2.2 Doguwar Siffantawa

Ɗangambo (2007, sh. 44), ya bayyana doguwar siffantawa da cewa kwatantawa ce mai rassa mai yaɗo. Za a iya kiran ta da hoto cikin bayani, wato idan aka siffanta abu tamkar ana nuna shi a hoto ne, wani lokaci wadda ya ƙunshi kwatantawa. Misali:

Jagora  :Masu Babura na acaɓa ku taso ku matsa babur ku ma,

 :Samu awa kashe wa minti sai ɗan acaɓa ƙarshen nema,

 :Shi ɗan acaɓa babu ruwansa wajen tsegumi da zancen gulma,

 :Laifinsa guda ɗai ya kai yara makaranta su tashi bai ɗauko ba.

(Nguru, K. H; Waƙar Baba Machina)

Mawaƙin yana siffanta ‘yan acaɓa da halayyarsu na matsa Babura da ƙoƙarin neman kuɗi, idan an samu kuma a kashe su a lokaci guda. sannan ga halayensu na rashin tsegumi sakamakon koyaushe suna kan nema ga kuma rashin zuwa ɗaukan yaran makaranta a kan lokaci.

Jagora  : Wani mai waƙarsu mai roƙo,

: Ka gano shi ciki kamar baƙo,

: Jangwam-jangwam ya miƙo,

: Wai nan mota yake roƙo,

: Ko riga bai yi canji ba.

(Nguru, K. H; Waƙar Malam Sani)

A wannan gunduwa mawaƙin yana bayyana siffofin makaɗin jam’iyar da take hamayya da jam’iyar da yake yi wa waƙa, yana nuna cewa ga shi jangwam-jangwam wato a rame da yunwa a jikinsa, ta yaya wanda ba a ba shi abinci ya ƙoshi ba har za a ba shi mota.

3.3 Jinsintarwa

Kamar yadda Gusau (2003, sh. 59), ya bayyana jinsintarwa da cewa, “Dabara ce ta ɗaukar daraja ko sifa ko hali ko yanayi ko aiki na wani jinsi a ba wa wani jinsi na daban”. Misali a ɗauki wata halayya da jinsin da mutum kawai aka san shi da ita a ɗora wa jinsin dabba ko tsuntsu, kuma jinsintarwa ta kasu zuwa; mutuntarwa da dabbantarwa da abutarwa.

3.3.1 Mutuntarwa

Abba da Zulyadaini (2000, sh.122), sun bayyana mutuntarwa da cewa “Mawaƙa kan yi amfani da wannan dabara ce ta hanyar ɗaukar wasu halaye ko siffofi ko wasu abu masu kama da haka na Bil-Adam, sa’annan sai a lanƙaya su ga wani wanda ba mutum ba”. Misali:

Jagora  :Yau ga wawan kare za shi kwartanci har shimfiɗar kura,

 :Amma da zuwansa sai na ga ya riƙe bindi yana ƙara,

 :Kare cewa yake ni fa kwarto ne magana yake ƙarara,

 :A tsugunne yana ta kuka yana ihunsa yana kiran tuba.

(Nguru, K. H; Waƙar Adam Dala Dogo)

A wannan gunduwa mawaƙin yana ɗaukar siffar ɗan Adam ta magana da kuma kwartanci yana danganta su da kare.

Jagora  : In za ka ji gobe aboki na ka tuno dai gobe akwai saura,

: Wai kare aka ba alƙalanci ai ƙaryar mage ta kai ƙara,

: Kuliya ta lalubi lauyoyi a ciki na hangi akwai kura,

: Wannan shari’a za ai rigima don na gane haka ɗan baiwa.

(Nguru, K. H. waƙar. Ali Idiss Diginsa)

Idan aka duba wannan gunduwa za a ga yadda mawaƙin ya ɗauki wasu ɗabi’u na ɗan Adam kamar alƙalanci da ɗaukar lauyoyi da ma shari’ar kanta yana ɗaukan ɗabi’un yana nuna cewa dabbobi sun yi.

3.3.2 Dabbantarwa

Abba da Zulyadaini (2000, sh. 124), sun bayyana ma’anar dabbantarwa da cewa “Hanya ce da mawaƙa kan mayar da mutum ko wani abu dabba. A irin wannan dabara akan kwatanta Bil-Adama da wasu halaye ko siffofi irin na dabba”. Misali;

Jagora  : - - - -

:Ga haziƙin gwamna ba mu yadda da tinkiya ko jaki ba,

:Jaki uban gardama ka fito ka ga haziƙin gwamna kai ma.

(Nguru, K. H; Waƙar Ɗan Tumba)

Mawaƙin ya dabbantar da abokin takarar gwamnan jam’iyarsa, inda ya kira shi da jaki da tunkiya.

Jagora :Amadu Mirwa wanda ake yayin sa a ko’ina sha nema

:Damo ne shi uban haƙuri Allah ya nufe shi ba ya gulma

:Ya Amadu Jalla shi ya naɗa ka muna bayanka koyaushe ma

:Duk jama’a ku zo ga mai ƙaunarmu ba za mu ɗau jaki ba.

(Nguru, K. H. waƙar Malam Sani)

Idan muka duba za mu ga yadda mawaƙin ya dabbantar da gwaninsa ya lira shi da damo, domin yta nuna cewa mutum ne mai haƙuri. Sannan ya dabbatar da wanda yake yi wa habaici inda ya kira shi da jaki.

3.3.3 Abuntarwa

Abba da Zulyadaini (2000, sh. 125), sun bayyana abutarwa da cewa “wata hikima ce da ake mayar da mutum ko dabba ko tsuntsu ya zuwa wani abu marar rai”. Misali:

Jagora:  : - - - -

 :Jama’a duk sun faɗa ga Amadu Mirwa a daina taɗin kowa,

 :Ga naman saniya su ba za su ci naman kulɓa ko jaki ba.

(Nguru, K.H; Waƙar Amadu Mirwa)

A wannan waje ya abutar da wanda yake zuga ya ce shi naman saniya ne domin ya nuna darajarsa a ɓangare guda kuma ya abutar da abokan hamayyar gwaninsa da naman kulɓa da na jaki domin ya nuna ba abin so ba ne ga jama’a.

Jagora : Allah ka ƙara salatin Annabi Mustafa kogin adalci,

: Allah haɗa da Umar Usmanu Aliyu ƙusa gatan benci,

: - - - -

(Nguru, K. H; waƙar Kun Ji Kunya ‘Yan PDP)

Mawaƙin ya abutar da Aliyu ne don ya nuna irin matsayinsa a wurin Manzon Allah (SWT) da kuma Musulunci, domin ƙusa a benci aba ce mai matuƙar daraja da muhimmanci.

3.4 Alamtarwa

Gusau (2003, sh. 60), ya bayyana alamtarwa da cewa “Wata hanya ce da ake bayyana wani abu ta ba shi wata alama da ta yi kama da shi dangane da shi ko yanayi ko ɗabi’a ko hali ko jarunta ko ƙasaita da sauransu”. Wata alama ce da take wakiltar wata manufa, musammam takan zamo madadin sunan abu. Misali;

Jagora  :- - - - -

 :Kafin na ce komai kowanku ya dakata ga farkon shafi,

 :Kun tabbata lokacin sanatan Ɗan Tumba dai ba mu sha daɗi ba.

(Nguru, K. H; Waƙar Kun Ji Kunya ‘Yan PDP)

Mawaƙin ya alamta kalmar dan Tumba a matsayin alama da ke wakiltar sunan ɗan takarar jam’iyyar da take adawa da tasu, wanda kuma tsohon sanata ne.

Jagora : Ina so na lallaɓo na gaya muku ɓera gare ku masu awaki,

: Ina da tambaya ina fadawa ga wani can da shi da matar sarki,

: Buri yake yah au ref don ya ci mu ya ba mu garin kwaki,

: ƙaryarka ta riga ta ƙare tun wuri ka zo da ragon tuba,

(Nguru, K. H. waƙar Baba na Machina)

Mawaƙin ya alanta kalmar ƙwai a matsayin arziƙi, wato zama cikin wadata da jin daɗi, sai kalmar garin kwaki wacce take alama ta nuna talauci da yunwa.

3.5 Ƙarangiya

Gusau (2003, sh. 61), ya bayyana ƙarangiya kamar haka “Dabara ce ta luguden harrufa ko kalmomi ko wasa da harshe cikin baƙaƙe da kalmomi. Haka kuma akan iya maimaita wata gaɓa ko ƙwayar sauti, sautinsu ya dinga tafiya bai ɗaya a cikin kalmomi”. Misali:

Jagora  :Turmi ka ture kura ke kura ki tashi ture turmi,

 :Ƙarƙaballu kai da mulki fam-fam-fam sai ka tada babban ƙaimi,

 :- - - - -

(Nguru, K. H; Waƙar Baba Machina)

Jagora : Faɗar falala filin Fulani farilla ban haka dan faɗa ba,

: Cire ciwo a cikin cikin mai ciki cikas yake ka ji babba,

: Tunanin zancen tuntuɓar tafiya ta ban taɓa tuntuɓe ba,

: Sayan sa don sarasi sukuni sahihi sa a ce babba.

(Nguru; K. H. waƙar PDP rigar Ƙaya)

A waɗannan gunduwowi an ga yadda mawaƙin ya nuna iya ƙwarewa a harshe, wato yadda yake luguden kalmomi da haruffa masu sauti iri guda, inda a gunduwa ta farko ya kawo kalmomin ‘turmi ture kura, kura ture turmi’, a gunduwa ta biyu kuma ya kawo kalmomi masu sauti iri ɗaya waɗanda suka haɗa dal faɗar falala filin fulani farilla faɗa da kuma kalmomin cire ciwo a cikin ciki mai ciki cikas da sayan sa sarari sukuni sahihi sa’a, Wannan ya nuna fasaha da ƙwarewarsa a harshe.

3.6 Kinaya

Gusau (2003, sh. 60), ya bayyana kinaya da cewa “Wata dabara ce ta sakaya zance wadda take juyar da abu daga asalinsa wato ma’anarsa ta farko zuwa ga wata ma’ana ta biyu wato sakayawa”.

Jagora :Ku ‘yan uwana zan shiga waƙa kowa ya ji ba wai ba,

 :Kuma gaskiya ce za ni faɗi ba wai gyara miya ta ba,

 :- - - - -

(Nguru, K. H; Waƙar Musa Gamcho)

A wannan gunduwa za a ga yadda mawaƙin ya sakaya ma’anar kalmar gyara-miya wacce take nashe da ma’anar fadanci ko faɗin son rai domin a so mutum.

Jagora :Kai su o-o da o-o ‘yan cuta,

: Bara fa jirgi za ya ɗauka ta,

: Na zamo cikin mahajjata,

: Ga suna na da lamba ta,

:‘Yan uba ba su bar ni tashi ba.

(Nguru, K.H Waƙar Malam Sani)

A wannan gunduwa da ta gabata mawaƙin ya yi kinayar kalmar ‘yan uba wacce tana ɗauke da ma’anar maƙiya ko mahassada.

4.0 Kammalawa

Binciken ya nuna cewa adon harshe yana da muhimmanci wajen kwatantawa da bayyana hoto cikin bayani da ƙiyasi da bayar da haushi da kuma kambamawa da sauransu. Adon harshe yana iya zama tamkar gishiri a miya a cikin waƙoƙin baka na Hausa domin yana ƙara wa waƙa zaƙi. Sannan adon harshe yana tasiri wajen nazarin waƙar baka ta Hausa domin yana iya sa a fahimci salo da kuma saƙon da mawaƙi yake son isarwa cikin sauƙi. An kawo taƙaitaccen bayani akan waƙar baka da adon harshe tare da kawo tarihin Kamilu Hussaini Nguru da kuma ra’in da aka yi amfani da shi a wannan takarda. Sannan an gabatar da misalai na adon harshe tare da yin ƙarin bayani a kan su, a cikin waƙoƙin siyasa na Kamilu Hussaini Nguru sannan an gabatar da bayanai a kan kowane ɓangare na adon harshe da aka kawo a matsayin misali, waɗanda su ne aka gudanar da wannan takarda a kansu.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B (2000), Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Cooporation.

Chiromari, M. M (2013), Adon Harshe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Nazari a Wasu Waƙoƙin Siyasa na Kamilu Hussaini Nguru. [Kundin Digiri na ɗaya]. Sashen Koyar da Hausa, Jami’ar Jihar Yobe, Damaturu.

Dija, Ɗ. (1997), Nazarin Adon Harshe a Cikin Wasu Ƙagaggun Labarai na Hausa. [Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Ɗangambo, A (2007), Ɗaurayar gadon feɗe waƙa (Sabon Tsari). Triumph

Gusau, S. M. (2003). Jagoran nazarin waƙar baka. Benchmark Publishers.

Gusau, S. M. (2008). Dabarun nazarin adabin Hausa. Benchmark Publishers.

Yahaya, A. B. (1995). Siffantawa bazar mawaƙa: Wani saƙo cikin waƙa. A cikin A. U. Kafin Husa, A. Y. Bichi & L. D. Yalwa (edc.). Studies in Hausa Language, Literature and Culture. The Fifth Hausa International Conference. Benchmark Publishers

Yahaya, da wasu (2007). Darrussan Hausa 1 don manyan makarantun sakadare. Uniɓersity Press.

Yobe Journal Vol. 8

Post a Comment

0 Comments