Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Salon Rubutun Mujallar Fim

Citation: Hauwa Shitu LAWAL (2018). Nazarin Salon Rubutun Mujallar FimYobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 6. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

NAZARIN SALON RUBUTUN MUJALLAR FIM

Hauwa Shitu LAWAL

Abstract

The Mujallar Fim (Fim Magazine) is a monthly magazine produce in Hausa, which cover most of the activities of the Hausa film industry (Kannywood). Buying and reading the magazine every month gave the opportunity of coming into contact with the many orthographical errors being made repeatedly by the writers and publishers of the magazine. As Hausa language is really in need of a harmonized writing system. I saw a chance of bringing out these orthographical errors to the publishers notice and public in general for rectifications. The paper therefore brought out these errors which usually distort the meaning of what is intended to conveyed or communicated. The research employed reading the magazine and extracting the places where the standard Hausa orthography was not properly adhered to a method of data collection, and provided the correct versions based on the standard Hausa orthography. As the Mujallar Fim (Film Magazine) is a popular magazine, it should give its own contribution in the harmonization of Hausa writing system.

Tsakure

Wannan maƙala ta yi nazarin Mujallar Fim wadda ke bayar da labarai, musamman waɗanda suka shafi harkokin fina-finan Hausa, tare da duba ire-iren kura-kuren da ke tattare da labaran. Ta hanyar tu'ammali da wannan mujalla ta fim da kan fito wata - wata ne, na fahinci yawan kura-kuren da ake maimaitawa a kowane bugu, na kuma ga cewa ya dace in fargar da mawallafan Mujallar domin a yi gyara, a kuma kyautata ma'ana ga abin da ake rubutawa. Haka kuma wannan maƙalar ta yi ƙoƙarin fito da waɗannan kura-kuren da aka tafka a wajen rubutu na yau da kullum. Akasari, mutanen da ba su san da waɗannan ƙa'idoji ba, sukan ɓata ma'ana ko zance ko manufar da ake son isarwa. Hanyoyin da aka bi aka yi binciken su ne, ta hanyar karanta Mujallar da tsakuro wuraren da ba a bi ƙa'idojin rubutun ba. Sannan kuma da duba kalmomin harshen Hausa da masana suka taru suka tace, suka amince a yi amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa. Irin karɓuwar da Mujallar Fim ta yi, ya dace a ce tana bin waɗannan ƙa'idojin rubutu na Hausa don ta bayar da ta ta gudunmowar wajen samar wa Hausa rubutu bai ɗaya.

1.0 Gabatarwa

Harshen Hausa, harshe ne da kimanin ƙasashe ashirin ke amfani da shi wajen zirgazirgarsu da sadarwa ta hanyar kasuwanci da waɗansu mu’amuloli na yau da kullum. Harshen Hausa shi ne mafi girma kuma mafi sanannen harshe a nahiyar Afrika. Harshen Hausa ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama’a da ba Hausawa ba ne a nahiyar Afrika. Kasancewar harshe ne wanda ya samu karɓuwa a duniya, ya sanya masana da dama suka ga ya dace a riƙa tsarkake ƙa’idojin rubutun da ke tattare da harshen.

Alal haƙiƙa an gudanar da tarurruka da dama a wurare daban-daban waɗanda suka ƙunshi masana ilimin harshen Hausa domin tabbatar da yadda za a riƙa rubutun wannan harshen ta hanyar amfani da daidaitacciyar Hausa. Kamar yadda Wurrna, (2005) ya ce, “Daidaitaciyar Hausa, ita ce wadda aka tace ta, kuma masana ilimin harshen a tarurruka daban-daban suka amince a yi amfani da ita”. Ya ci gaba da cewa, “An yi duka waɗannan tarurruka domin amincewa da kalmomin harshen Hausa waɗanda za a riƙa amfani da su a rubutu. Saboda haka daidaitacciyar Hausa ita ce wadda ake amfani da ita wajen rubuta ƙasidu da littattafai sannan kuma a wajen sadarwa ta yau da kullum ta zama ita ce ake amfani da ita".

Kamar yadda Sa'id (2004) ya ce, "Tun shekarar 1932 ne aka fara yunƙurin samun ingantacciyar hanyar rubuta Hausa, saboda muhimmancinta wajen wallafe-wallafe cikin harshen Hausa". Saboda haka ya wajaba ga kamfanonin Mujallu da na yaɗa labarai na Hausa su kiyaye tare da bin ƙa'idojin wannan dokar.

Sanin kowa ne kafofin yaɗa labari suna taka rawa muhimmiya, musamman ma a ƙasar Hausa wadda aka sami ɗaya daga cikin koma baya wajen karatu da rubutun boko.

1.1 Mujallu

Mujalla ba kamar jarida ba ce da take fitowa kullum, ita Mujalla takan fito ne bayan kowane wata shida ko uko ko biyu ko ɗaya ko ma bayan duk sati biyu ko ɗaya. Wannan dai ya danganta da masu buga ta. A kan haka ne ma, Wurma, (2005, p. 11) ya ce, "Mujallu kamar Jaridu suke, sai dai akan yi masu bango mai laushi irin na ƙaramin littafi, sannan kuma sukan fito bayan mako ɗaya ko biyu ko wata, dangane da yadda aka tsara da buƙatar jama'a".

1.1.1 Mujallar Fim

Wannan Mujalla ce da ke watsa labaranta na yau da kullum da harshen Hausa, kuma tana yaɗa manufarta da tallace-tallacenta. Tana fitowa ne sau ɗaya a kowane wata. Sai dai kamar yadda aka yi bayani a baya, cewa za a yi nazari ne a kan labaran da take watsawa a idon duniya tare da gano da kuma fito da kura-kuran da ke tattare, ƙarara domin hannunka mai sanda ga marubuta labaran.

 

Ga yadda labaran sukc a rubuce kamar haka;-

Labari na Farko

"Mahaifiyar Jamila Umar Tanko ta Rasu"

“Allahu Akbar! A ranar Lahadi, 17 ga Afrilu, 2016 Allah ya karɓi ran Hajiya Yalwa Ahmad Turaki a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Marigayiyar, mai shekaru 58 a duniya, ta rasu ne da misalin ƙarfe 10 na safe bayan ta sha fama da rashin lafiya inda ta shafe tsawon lokaci ta na jinya a asibitin. Bayan rasuwar ta an ɗauke ta aka kai ta mahaifar ta, wato garin Gumel a Jihar Jigawa, aka yi mata jana’iza, daga nan aka dawo Kano aka yi zaman makoki.

Hajiyar ta rasu ta bar 'ya'ya bakwai, maza uku, mata huɗu, ciki har da fitacciyar marubuciyar nan Hajiya Jamila Umar Tanko.

Marubuta da dama sun je gidan su Jamila din da ke Giginyu su ka yi mata ta'aziyya.

Muna fatan Allah Ya jiƙan ta, kuma Ya albarkaci, abin da ta bari. amin."

Yadda aka ruwaito a Mujallar Fim (“Yakubu” 2016, p. 49).

Har ila yau a wannan labarin, marubucin ya haɗe kalmar aikatau da ta 'yar mallaka wuri ɗaya. Sa'id, (2005, p. 11) ya ce, “Babbar manufar kula da raba kalmomi ko haɗe su a muhallin da ya dace ita ce, don a tabbatar da ma'anar da ake nufin rubutawa ba ta canza ba". Don haka ga yadda ya kamata a rubuta, Allah ya ji ƙanta ba "Allah ya Jiƙan ta ba" Haka kuma an rubuta “mahaifar ta” maimakon mahaifarta. Marubucin ya saɓa wa dokar nahawun Hausa. Masana da dama sun bayyana cewa kalmomin gajeruwar 'yar mallaka a haɗe suke da abin da aka mallaka ba a raba su.

Sa'id, (2005, p. 6) ya ce "n" da "r"… ana amfani da su ne wajen mallaka ko jingina wani abu da wani. "n" a gurbin namiji ko jam’i. "r" kuma a gurbin mace.”

Labari Na Biyu

"Zee-Zee ta caza ƙwaƙwalwar masoyan ta

FITACCIYAR jaruma kuma mawaƙiya Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta shirya gasa ga abokan ta na shafin ta na BBM. A gasar, wadda ta sanar tun kusan wata biyu da suka wuce, ta ce za ta bada tambayoyi goma game da ita, duk wanda ya amsa daidai kuma ya fara tura mata, za ta ba shi kyautar N100,000.

Kuma haka aka yi, domin kuwa ran Asabar, 9 ga Mayu, 2015, da misalin ƙarfe 1:00 na rana ta tura wa dukkan abokan ta da ke bin ta a shafin nata na BBM sako da ce wa: “Salam friends, yau ne ranar gasar da na ce zan yi. Zan aiko da tambayoyi goma a game da ni, wanda ya fara amsa su daidai zan ba shi kyautar N100,000 ran Litinin. Kuma sai ran Litinin zan fadi wanda ya yi winning. Sannan Pls kowa sau ɗaya kawai zai bada amsa. Na gode, a saurari tambayoyin, zan aiko bada jimawa ba in "God I trust"

“Bayan kamar awa ɗaya haka, sai ga shi ta aiko da tambayoyin kamar haka:

1. Menene cikakken suna na?

2. Ni wace yare ce?

3. Shekaru na nawa?

4. Wane gari aka haife ni?

5. Wane abinci na fi so?

6. Wane kala na fi so?

7. Wace ƙasa na fi zuwa hutu?

8. Menene sunan mawaƙina na Indiya?

9. Menene sunan Sahabin Annabi da na fi so?

10. A wane gari na ke da zama?

Nan take aka fara aiki, kowa ya yi ta caja ƙwaƙwalwar sa don ganin cewa ya bada amsa daidai kuma ya fara turawa don ya samu nasarar lashe wannan kyauta.”

Yadda aka ruwaito a Mujallar Fim (“Muhammad” 2015, p. 15).

A labari na sama akwai kura-kurai da aka yi wajen rubuta kalmomin 'yar mallaka. Sa'id (2005, p. 69) ya ce, “Mallaka kalma ce wadda ke nuna mallakar wani abu, ta rabu zuwa gida biyu …. akwai doguwa da kuma gajeruwa.

Wani abin la'akari da shi a nan, shi ne a duk inda aka ga doguwar mallaka, to za a ga cewa ba liƙe take da abin da aka mallaka ba. Haka kuma a duk inda aka ga gajeruwar 'yar mallaka, to za a ga cewa liƙe take da abin da aka mallaka.

Doguwar Mallaka

Gajeruwar Mallaka

Gida nawa

Gidana

Mota tawa

Motata

Gona tasa

Gonarsa

Ga sauran kura-kuren da wannan labari yake tattare da su tare da gyare-gyaren da aka yi kamar haka:

Kuskure

Daidai

Masoyan ta

Masoyanta

Menene

Mene ne?

Abokan ta

Abokanta

Shafin ta

Shafinta

Suna na

Sunana

Shekaru na

Shekaruna

Mawaƙi na

Mawaƙina

A wane gari na ke da zama?

A wane gari nake da zama?

Ƙwaƙwalwar sa

Ƙwaƙwalwarsa

Su ka

Suka

Bada

Ba da

Wane kala na fi so?

Wace kala na fi so?

Haka kuma marubucin wannan labari ya yi kuskure wajen rubuta kalmar wakilin suna tambayau, ya rubuta “menene" a maimakon mene ne? Abin lura a nan shi ne, tambaya aka yi, amma sai ba a nuna alamar tambayar ba. Sa’id, (2005) na da ra'ayin cewa ayar tambaya takan zo bayan an gama tambaya. To amma wannan Mujallar wajen bayar da wannan labarin ba ta yi amfani da alamar tambaya ba.

A tasu gudumuwar, Abdulkadir da wani, (2017, p. 37) sun ce “Alamar tamabaya ana amfani da ita ne a lokacin da aka yi tambaya”.

Labari na Uku

“Ali Show ya samu Haidar, kuma ya yi rashin mahaifi.

ALLAH Sarkin daɗi, inji ɓarawon takanɗa. Allah Ya albarkaci fitaccen mawaƙin nan Aliyu Mukhtar, wato Ali Show, da matar sa Maryam da samun ɗa namiji. Maryam ta haihu da misalin ƙarfe 12:00 na dare a ranar Asabar, 29 ga Janairu, 2017 a asibitin tarayya mai suna Federal Medical Centre da ke Katsina.

An raɗa wa yaro suna Aliyu, wato ya ci sunan mahaifin sa kenan. Amma kuma da Haidar za a riƙa kiran shi.”

Yadda aka ruwaito a Mujallar Fim (“Doro” 2017, p. 36).

Labari na Huɗu

"Alƙalam Ta Karrama Gwarzayen Adabi

An jaddada tasiri da matsayin Alhaji Abubakar Imam

MANYAN masu jawabi a wajen wani taro da ya zo daidai da Ranar Marubuta ta Duniya da aka yi a Kaduna a watan jiya sun ƙara jaddada matsayin marigayi Alhaji Dr. Abubakar Imam a fagen adabin Hausa, suka ce har yanzu babu kamar sa. Taron wanda aka yi a ranar Asabar, 4 ga Maris, 2017, ƙungiyar marubuta mai suna Alƙalam ce ta shirya shi domin tunawa da Imam tare da karrama wasu mutane da su ka agaza wa ci gaban adabi.

A bikin, an karrama Imam da bayyana ayyukan sa da lambobin yabo da ya samu da kuma bayar da kyauttutukan yabo ga wasu marubuta littattafan Hausa da su ka yi ftce a fannonin adabin Hausa guda huɗu, da kuma jinjina ga wasu da suka bayar da gudunmawa wajen haɓaka adabin Hausa. An fara bikin da misalin ƙarfe 11:05 na safe a babban ɗakin taro na Arewa House, da ke Unguwar Sarki Kaduna.

Da farko mai gabatarwa Malam Hassan Umar Kainuwa, yu umarci Malam Shehu Ayatullahi ya buɗc taro da addu’a.”

Yadda aka ruwaito a Mujallar Fim (“Muhammad” 2017, p. 45).

Marubucin wannan labarin ya fara rubuta shi ne da manyan haruffan Hausa. A dokar nahawun Hausa babban harafin farko ne kaɗai ake fara rubutu da shi. Marubucin ya rubuta "MANYAN masu jawabi” a maimakon Manyan masu jawabi.

Abdulkadir da Wani, (2017, p. 22) sun ce “Akwai wurare da dama inda ya zama wajibi a fara rubutu da manyan haruffa. Waɗannan wurare: rashin fara rubuta su da manyan baƙaƙe kuskure ne”. Sun ci gaba da cewa waɗannan wurare sun haɗa da farkon rubutu ko farkon magana....”

Haka kuma a wannan labarin na sama, marubucin ya yi kuskure a wajen rubuta kalmomin manunin lokaci shuɗaɗɗe. Misali ya rubuta su ka a maimakon suka. Haka kuma an rubuta kalmomin lokacin gaba kamar haka "Mu na a maimakon, muna. Wurma (2005, p. 64) ya ce, “Manunin lokaci shuɗaɗɗe su ne kalmomin da suke nuna cewa an aikata wani abu, kuma ga yadda ake rubuta su tare da kalmomin aikatau masu gaba ɗaya…."

Kuskure

Daidai

Ayyuna sa

Ayyukansa

Su ka

Suka

Mu na

Muna

3.0 Naɗewa

Harshen Hausa, harshe ne da ya riga ya haɓaka ƙwarai, amma babbar matsala ita ce har yanzu rubutunsa bai zama bai ɗaya ba. Ba Mujallar fim kawai ba, har Malaman Hausa da Ɗaliban da Hukuma da Gidajen Rediyo da na Talabijin, da sauran kafafen sadarwa da yawa, suna da babbar rawar da ya kamata su taka don ganin wannan mashahurin harshe ya samu hanyar rubutu bai ɗaya a duka duniya. Ana da tsananin buƙatar yaɗuwar wannan fanni, saboda masu sha’awar rubutu a cikin Hausa a kullum daɗa yawa suke yi. Don haka ya dace a yawaita wallafe- wallafe cikinsa ana yaɗawa. Ita kuma Mujallar Fim, saboda irin karɓuwar da ta yi, ya dace a ce tana bin waɗannan ƙa’idojin rubutu sau da ƙafa don ta bayar da ta ta gudunmuwar wajen samar da rubutun Hausa ya zama bai ɗaya. Hukuma (wato gwamnati) da malamai da sauran ɗaliban Hausa da sauran masu faɗa a ji da kuma musamman gidajen rediyo da talabijin da sauran kafafen yaɗa labarai kamar su Jaridu da Mujallu su yi ƙoƙarin taimakawa wajen ganin wannan harshe ya samu hanyar rubutu bai ɗaya. Haka kuma yana da kyau kamfanonin Mujallu na Hausa su zage dantse domin ganin an magance faruwar waɗannan kura-kuren, ta hanyar ɗaukar ma'aikata ƙwararru, musamma masu takardar digiri a fannin Hausa.

Manazarta

Abdullahi, G.W. (2006). Daidaitacciyar Hausa da ƙa'idojin rubutu. Kaduna. Olatunde Rasheed Publishing Works.

Abdullahi, Y. da Ɗangambo, A. (1986). Jagorar nazarin hausa. Zariya. Kamfanin Buga Litattafai na Nijeriya ta Arewa.

Abdulƙadir, K.A. da Mika'il, A.M. (2017). Jagoran mai rubutun Hausa. Kano, Albarka Publishers.

Bargery, G.P. (1934). A Hausa - English dictionary and English - Hausa Ɓocabulary. Zaria. Ahmadu Bello University Press Limited Nigeria.

Bello. S. (2005). Ƙa'idojin rubutun Hausa: Jagora ga marubuta. Kano. Benchmark Publishers Lid. Nigeria.

Doro, I. B. (2017, March). Ali show ya samu haidar, kuma ya yi rashin mahaifi. Mujallar Fim, p. 36.

Muhammad, A. (2015, June). Zee-Zee ta caza ƙwalƙwalwar masoyonta. Mujallar Fim, p. 15.

Muhammad, A. (2017, Afril). Alƙalam ta karrama gwarzayen adabi. Mujallar Fim, p. 45.

Shehu, M. (2010). Hausa ba dabo ba ce: Nazari a kan kura-kuren da wasu kafofin yaɗa labarai ke yi a wajen rubuce-rubucensu na Hausa cikin JOLALI, Volume I. No. 1 School of Languages Federal College of Education, Katsina.

Shehu, M. (2013). Hausar rediyo: Nazarin gurɓatar ma’ana cikin matani "a rediyon Jamhuriyar Muslunci ta Iran", cikin Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies Vol. 1 Number 5. Sokoto, Department of Nigerian Languages, Usman Ɗanfodiyo University.

Yahaya, I. Y. (1988). Hausa a rubuce: Tarihin rubuce - rubuce cikin Hausa Zaria: Kamfanin Buga Litanafai na Nijeriya ta Arewa.

Yakubu, M. (2016, May). Mahaifiyar Jamila Umar Tanko ta rasu. Mujallar Fim, p. 49.

 Yobe Journal Volume 6, 2018

Post a Comment

0 Comments