𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Daga ina ya fi dacewa a fara sahun sallah na-biyu, daga tsakiya ko daga dama?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa
Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Abu na-farko dai da ya dace
kowannenmu ya sani shi ne, ba a fara sahu na-biyu sai in sahu na-farko ya cika,
kuma ba a fara na-uku har sai na-biyu ya cika, haka nan dai har zuwa ƙarshe. Al-ImaamAbu-Daawud (671)ya
riwaito daga Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) daga Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« أَتِمُّوا الصَّفَّ الْمُقَدَّمَ ، ثُمَّ الَّذِى يَلِيهِ ، فَمَا كَانَ مِنْ نَقْصٍ فَلْيَكُنْ فِى الصَّفِّ الْمُؤَخَّرِ »
Ku cika sahu na-gaba, sai
kuma wanda yake bin sa, kuma duk abin da zai rage sai ya kasance a sahu na-ƙarshe.
Haka kumaAl-Imaam Muslim (996)ya
riwaito daga Sahabi Jaabir Bn Samurah (Radiyal Laahu Anhu), daga Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« أَلاَ تَصُفُّونَ كَمَا تَصُفُّ الْمَلاَئِكَةُ عِنْدَ رَبِّهَا »
Ba za ku yi sahu kamar yadda
Mala’iku suke yin sahu a wurin Ubangijinsu ba?
Da suka tambaye shi, yadda
Mala’iku suke yin sahu a wurin Ubangijinsu, sai ya ce:
« يُتِمُّونَ الصُّفُوفَ الأُوَلَ وَيَتَرَاصُّونَ فِى الصَّفِّ »
Suna cika sahuhuwan farko,
kuma suna haɗuwa da juna a cikin sahu.
Abu na-biyu: Malamai sun
nuna akwai falala a gefen dama na sahu, saboda hadisin daAl-Imaam Abu-Daawud (676)ya
riwaito da isnadinsa kyakkyawa har zuwa ga Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal
Laahu Anhaa), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« إِنَّ اللَّهَ وَمَلاَئِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى مَيَامِنِ الصُّفُوفِ »
Haƙiƙa!
Allaah da Mala’ikunsa
suna yin salati ga geffan dama na sahuhuwa.
Sai dai kuma kodayake
hadisin yana da matsala ta mataninsa, don haka ne ma Al-Imaam Al-Mujaddid
Al-Albaaniy ya saka shi a cikinDa’eef Abi-Daawud: 104, amma kuma akwai wasu
hadisan da ba su da wata matsala, waɗanda
kuma suka zo a kan haka, kamar hadisin Al-Baraa’ Bn Azib (Radiyal Laahu Anhu) wanda
Al-Imaam Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin Sahih Abi-Daawud: 628 mai lafazin:
كُنَّا إِذَا صَلَّيْنَا خَلْفَ رَسُولِ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - أَحْبَبْنَا أَنْ نَكُونَ عَنْ يَمِينِهِ ، فَيُقْبِلُ عَلَيْنَا بِوَجْهِهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
Mun kasance idan muka yi
sallah a bayan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) mukan so
mu zama ta gefen damansa, sai ya fuskance mu da fuskarsa (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) (bayan sallama).
Saboda irin waɗannan
hadisan ne wasu malamai (Allaah ya saka musu da alkhairi) suke ganin a fara
sahu na-biyu daga gefen daman masallaci. Wannan fahimta ta iya zama daidai ce.
Amma kuma Al-Imaam Muslim ya
ƙulla babi a cikin Sahin Littafinsa wanda
ya ba shi suna:
باب تَسْوِيَةِ الصُّفُوفِ وَإِقَامَتِهَا ، وَفَضْلِ الأَوَّلِ فَالأَوَّلِ مِنْهَا ، وَالاِزْدِحَامِ عَلَى الصَّفِّ الأَوَّلِ ، وَالْمُسَابَقَةِ إِلَيْهَا ، وَتَقْدِيمِ أُولِى الْفَضْلِ ، وَتَقْرِيبِهِمْ مِنَ الإِمَامِ
Baab: Daidaita sahuhuwa da
tsayar da su, da falalar sahun farko sai mai bin sa a cikin haka, da cunkoso a
kan sahun farko, da yin tsere da juna zuwa gare shi, da gabatar da ma’abuta
falala a wurin haka, da kuma kusancinsu ga liman.
A ƙarƙashin
wannan babin sai kuma ya kawo hadisai masu yawa, a ciki har da wannan da ya
riwaito daga Sahabi Abu-Sa’eed
Al-Khudriy (1010) daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a
lokacin da ya ga Sahabbansa suna yin baya-baya a ƙarshen
masallaci, sai ya ce:
« تَقَدَّمُوا فَائْتَمُّوا بِى وَلْيَأْتَمَّ بِكُمْ مَنْ بَعْدَكُمْ »
Ku gabato ku yi koyi da ni,
sai kuma waɗanda suke a bayanku su yi koyi da ku.
Daga wannan hadisin, idan
mutane biyu suka zo kafa sahu sai ɗayansu
ya tsaya a saitin liman, ɗayan kuma ya koma ƙarshen gefen dama na masallacin a kan
sahun…
1. Wanne ne daga cikinsu za
a ce ya bi umurnin wannan hadisin a fili?
2. Wanne ne za a ce ya
gabata ko ya yi kusa da liman?
3. Sannan kuma wanne ne yake
a matsayin ji da ganin liman yadda ya kamata?
4. Kuma wa za a ce yana iya
koyi da Limamin yadda ya dace?
5. Wanne ne za a ce ya zama
abin koyi ga na-baya a haƙiƙa?
A fahimtarmu, wanda ya tsaya
a saitin liman shi ya fi a cikin duk waɗannan
tambayoyin fiye da wanda ya je gefe.
Don haka dai idan aka zo
dasa sabon sahu na-biyu, gara a fara a saitin liman amma ta gefen dama kaɗan,
domin a samu haɗa falalar damaitawar da kuma
kusanci da limamin, in shaa’al Laah.
Allaah ya datar da mu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam
sahun Sallah ta dama za a fara ne ko ta hagu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum assalam. To ɗan'uwa
sahun da yake bin liman zai fara ne daga bayan liman, ma'ana a sanya liman a
tsakiya, saboda faɗin Annabi (Sallallahu alaihi
Wasallam): "Masu hankali daga cikinku, su bi bayana", kamar yadda
Muslim ya rawaito a Hadisi mai lamba ta 116. Da faɗin
Anas (R.A.) lokacin da yake ba da labarin ziyarar da Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya kai gidansu: "Sai muka tsaya ni da marayan a bayansa",
kamar yadda Bukhari ya rawaito a Hadisi mai lamba ta 694. Daga nan kuma sai a
ci gaba da cika shi ta ɓangaren dama.
Haka nan ake so sahu na biyu
shi ma ya kasance, ya fara daga tsakiya ya tafi zuwa dama, saboda faɗin
Bara'u ɗan
Azib (R.A.): "Mun kasance idan muka yi sahu a bayan Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) mu kan so mu kasance a damansa, ya fuskanto mu da
fuskarsa", Muslim a Hadisi mai lamba ta 709.
Allah ne mafi sani.
𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.